Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 40

Sponsored Links

CHAPTER 40

Saida ya sassauta da dariyar dayake sannan ya dubesu ɗaya bayan ɗaya yace”kafin sannan na san kai Alh hamza kasani cewa koda giwa ta faɗi tafi karfin…..be barshi yakai karshen maganan ba yace”haba haba ya alhaj karkaji komai ba wata matsala kawai de mundan shiga ruɗune kasan sha’anin kuɗi ba abun wasa bane ba.

Alhaji ɗahiru ya amshe da cewa”kuma kaima kanka Alhaji sunusi kasan harka ta kuɗi kaman yanda bakason wasa dasu haka muma dan idan mutum yace ze shiga tsakanin mu da samun mu to wallahi yanzu ne zamuyi uwar watsi da shi.

“Aisha yakira sunan ta.

Ɗaga masa hannu tayi murya na rawa tace”kaini gida kawai ba lalle ne karamin kwakwalwata ta iya ɗaukan abunda kake cewa ba.

A karancin shekarun nan nawa ba lalle na fahinci mai kake cewa ba,da kace mahaifina yana yaraye gwara kace dani anga mahaifiyata wannan shine abunda zan iya yarda da shi.

“Amma Aisha kinsan bazan miki karya ba ko?
Yafaɗa yana tsareta da ido.

Saida ta share hawayen da ke kwaranƴa a idanunta sannan tace”aiko yanzu yaya faisal bance karya kayi nun ba,amma menene dalilin ka nacewa mahaifina na raye?

Tsawon wannan lokaci shekara goma fa ba kwana goma bace ba?

Abu ɗaya nasani shekara tara baya an tsinci motar sa ta ƙone hakan yana nufin be tsira da rayuwar sa,idan ko yana raye yaci ace tsawon wannan lokacin wani ya gansa koda hatsari yayi ya kamu da cutan mantau wata ƙila wani yagansa ko ayi cigiyar ƴan uwansa amma ina anyi haka?

Idan kuma bayani kake so na baka gami da abunda yashafi aikin ka ba wai sai kabi dani ta nan ba zan faɗa maka iya abunda nasani,zanyi hakan ne dan cikan burina dakuma ta iyayena amma zancen wata NATASHA kabarta nan daga haka taja bakin ta ta tsuƙe duk yanda Faisal yaso ta bashi haɗin kai suyi magana taƙi dole bawai dan yaso ba ya ƙyaleta dan bata daman tayi tunani.

Ahmad zaune yake a main falon gidan su yana tura wasu samfuran kaya wa customer ɗin sa,Ammin sa dake zaune gefe tana kallon tashar sunnan tv ta ɗan maida kallon ta kansa tace”kasan yaune kai lefen ka ko?

“Nasani ya amsa mata cikin halin ko in kula.

Kallon sa tayi da mamaki ganin bema nuna damuwar sa ko wani zumuɗin sa kan wanna. auren ba,cigaba tayi da maganan nata tasake cewa”wani tanadi kaiwa bikin naku dan naga Alhaji yaɗauki abun da mahimmanci sosai.

Sannan kuma dama ina tason muyi magana da kai gami da yarinyar da nace zan zaɓa maka to Alhamdulillahi an rigada an ɗaura auren ka da ita tuntuni da wani irin sauri ya ɗago da kansa yana kallon Ammin nasa dake magana saide duk kwafkwafinka baka isa kace ga yanayin da yashiga ba.

Tuni yaji ƴawun bakin sa ya ɗauke magana yake son yi amma yakasa furta koda kalla gudane.

Sai cigaba da magana da Ammi tayi bata damu da sai yace komai ba,Ahmad na tabbata zakayi alfahari da wannan auren,nan gaba dan yarinyace mai hankali da sanin yakamata na yaba da tarbiyarta da kuma hankalinta shi yakaini ga sha’awan aura maka ita.

Idan kasamu lokaci zaka iya zuwa gidan Antinku hajia tana can da zama tun bayan daura aurenka da ita zamanta ya koma can.

Kafin ta sake wani magana Alhaji badamasi ya banko ƙofar falon ko sallamar kirki babu yashigo cikin falon yana aunawa Ahmad din harara shiko Ahmad ƙasa da kansa yayi dan yasan kwanan zancen”lafiya Alhaji?

Ammi tayi tambayarsa dan ganin yanda yake huci,da mugun kallo yabita dashi yana cewa”eh dole ki tambayeni ko lafiya tunda kin iya saka shi gaba ki zugashi.

“Wai meka faruwane?
Alhaji daga tambaya sai cibi yazama ƙari Allah yabaka hakuri.

“Dole kice haka wato ma’arufa kiji tsoron Allah dama ke kike zugashi dan kawai inason ƙulla zumunci tsakanina da abokina amma wannan yaron saboda bashi da mutunci shine ze ce baze halarci duk shagalin biki da za’ayi ba?

“Au dama wannan duk wannan kakewa fushin to shi shagalin bikin farillace da sai Ahmad ɗin ya halarta ni naga jaraba kowa nason ganin farin cikin nasa amma banda kai Alhaji.

“To to to yanzu nagane kice kekika hanashi kuke son maisheni karamin mutum kai da uwarka eh?

Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru.

Ganin ba wanda ya tanƙa shi sai kuma abun ya hasala shi yashiga cewa wato ga mahaukaci nan ina magana kuna jina kunyi shi to wallahi Ahmad bara kaji narantse maka da rawanin kakana na kande muddin baka tsaya anyi komai dakai ba to kanemi gidan wani uban bade nan ba.

Zuba mishi ido Ahmad yayi sannan yace”wai kai Abba mai yasa ko wani uba yana son ganin farin cikin ƴaƴansa amma banda kai,shi wanda kakeyi dan shi be goyi bayana ko ya tambayi dalilina na cewa bazanin ba,bayan ɗiyar sa yagoya amma kai yanzu duba daga zuwa ka hau Ammina da zagi batasan hawa ba batasan sauka ba bama tasan anyi hakan ba.

Kaga Abba ina da tafiya mai mahimmaci a gabana kuma zanyi kwana shida kafin nadawo dan haka ni ban hana kowa yin party ba,suyi shagalin su yanda suke so saide Abba kasani kaman yanda tace dole ƴan gidan mu su halarci wajen wannan ne bata isa ba.

Kuma Abba zancen tarewa ta can gidan babu dan ni ba lusari bane sannan kafadawa abokinka baka haifi lusari da ze tare gidan surukan sa.

Kafin na dawo daga tafiya Ammi kisaka a gyara wannan site ɗin idan sunada buƙata suzo suyi jeren su idan kuma basu da buƙata ok fine ya ɗage kafaɗansa cikin halin ko inkula yayi gaba.

“Kina gani ko nace kina gani ko yaron nan yana neman zagina wato ban haifi lusari ba nine kenan lusarin uba ko?

Danma anason yimaka gata kai kakai Alhaji sunusi ya tsaya neman alfarma a wajenka ne idan ba dan kaci darajan so ba.

Murmusawa Ammi tayi ganin yanda Alhajin nata yake ta bambami tace”a to kyan ƴa mace ɗakin mijinta Allah ya huremana banga abunda su zasu nuna mana na lalle lalle sai yaro ya tare a gidan su ba,saide inda wata a ƙasa,ai wallahi idan ka matsa sai Ahmad ya tare gidan surukan sa wallahi sai malam mai babban riga yajimu da kai wato ƙanin baban shi Alhaji badamasin kenan.

******
Aisha suna komawa gida ko tsayawa daidai parkin bata bari yah faisal yayi ba ta ɓalle marfin motan tafita tashiga ciki da gudu tana tare kukan da yake son kufce mata.

Bata taradda kowa a falon ba da alama anti hajia fita tayi malika bata dawo daga skul ba hakama malik dasu ummu salma.

Ɗaki su tashiga tana shiga ta faɗa saman gado tayi rub da ciki dasaki kuka,saida tayi mai isarta sannan taji dama dama nauyi da takeji a ƙirjinta ya ragu baccine ya dauke ta daga kwancen da take ba ita ta farka ba sai karfe biyu da rabi a gurguje tatashi ta shiga toile wanka tayi tare da dauro alwala tafito daure da towel bata tsaya shafa jikinta da mai ba,ganin yanayi zafin garin sallah tayi taba tashi a wajen ba tanan zaune a wajen tana tilawa bata tashi ba saida tayi sallan la’asar sannan ta miƙe ta naɗe sallayar ta adanata tare da ninke hijabin hula tasaka a kanta tafito falo.

Harde sannan ba wanda yazo dan haka kitchen tanufa ta daura musu girkin dare sannan itama tasha freesh milk towun semo da miyar ɗanyen kuɓewa da yasha nama ta taura musu take gidan ya kaure da daddaɗan kamshin girkinta sai daf da kiran sallan magariba ta gama ta haɗa musu juice ɗin abarba da kwakwa tasaka a frige sannan ta fito dan gabatar da sallah magariba da aka fara kira.

Shiganta falo da coolar abinci a hannun ta yayi daidai da zuwan su ahalin gidan baki ɗaya harda su khadija.

Sannu da zuwa tama anty hajjia da malika suma yaran suka mata barka da gida”a’a mai aka girka mana ne haka duk gida ya game da kamshi haka cewar Anty hajjiya da fara’a ɗauke a fuskarta.

“Tuwone Anty ta amsa tana ajiye cooler”waw kice yau mubude ciki mu kwashi girki kaman ko kinsa bamuci wani abun kirki ba tun fitan mu.

“Wash wallahi na gaji tafaɗa tana cilli da jakar hannuta”kai anty malika bade lalaci ba ince ko noma kikayi”hmmm Aisha baxaki gane bane aiko wanda yayi noma yau baze nunamun gajiya ba.

Nida nasan irin wannan gida zamu wallahi da a gidan Ammi nayi zamana shegu sai son nunawa mutane su wasune amma tarɓa baƙi common wannan basu iya ba,sunzo sun wani taremu da juice da snack sai kace ce musu mukai muɗin ƙwaɗayayyune mtssss taja tsuka.

Bayan gaba dayan su sunyi sallah sun zo sun halarta a taburin cin abinci Aisha tayi saving kowa cin abinci suke ba mai magana saida suka kammala khadija da Aisha suka kwashe komai suka maida kitchen sun dawo falo sun zauna kenan aka hasko hoton gawar wata yarinya ƴar makaranta wacce ta ɓace sati biyu baya.

mahukunta sunce ana amfani da yaran ne wajen basu hodar iblis ana safara dasu gari gari itama wannan bincike yanuna cewa ansamu akasi ya fashe acikin cikin ta shine yayi sanadin rayuwarta sannan saboda rashin tsoron Allah aka farke cikin bayan ta mutu aka cire sauran hodan.

Da kuka Aisha ta ɓarke tana cewa”wallahi nasanta ajinmu ɗaya a islamiya samira ce Allah yasaka miki Allah yatoni asirin waƴan nan azzaluman.

“Aisha asirin su ze tonune harsai ansami mai tamƙa musu wanda ze zaƙulo ko ya banƙaɗo da sirrikan su,wata zuciya ta amsamata da haka.

Tana cikin kuka da zance zuci ta tsinkayo muryar Anty hajjiya na cewa”ai waƴan nan mutane saide muce Allah ya ruguza su amma cutakan suna cutan bayin Allah duka saboda duniyar su.

Sun lalata rayuwar ƴaƴan mutane da dama sun maida ƴan mata bila adadin karuwai ƴan ƙwaya karfi da yaji duka dan samun duniyar su.

“Anty hajjia mai amfanin hukuma da muke dasu muna da police soja civil difence ndlea harma da ƴan banga amma ace anrasa wanda ze kamasu da hujja dan gurfanasu gaban ƙuliya.

Dafa kafaɗan ta tayi tace”Aisha waƴan nan mutane sun wuce tunanin ki suna aikine da tsafi sannan duk wanda yayi yunƙuri magana kan abunda suke tuni zasu aikashi barzawu ko su ɗauke maka ɗan wannan yasa ba wanda ya isa tanƙamusu suke tsula tsiyarsu son ransu.

Shekarun baya ansamu wanda ya fito yayi magana da kuma rubuce rubuce a kansu amma daga baya shima yaɓace ɓat.

Leave a Reply

Back to top button