Auren Wucin Gadi 47
CHAPTER 47
Suna shiga cikin ɗakin sukaja suka tsaya ganin ba wani alaman wannan mata ta motsa,inna fure ce ta kalli boɗɗo cikin harshen fillanci ta kai dubanta ga boɗɗo tace”anƴa bakarya kika mana ba matan nan ta motsa kuwa?
Cike da yarintar ankirata da makaryaciya ta shiga dirza ƙafa tana mustsuke ido ta ƙwaɓe baki tasaki kuka kai da gani kasan kukan shagwaɓane cewa tayi”am inna aide naji tace ruwa ruwa inma karya nake kutashe ta ita zata faɗi,kanta modibo yashafa yace “yi shiru boɗɗon Abba ai nisan bakya karya inna inaga mubata ruwan taimakawa inna fure yayi suka ɗan ɗagota suka shiga bata wani ruwan jiƙon magani da Abba yanemo cikin daji ya jiƙa,sunyi mamakin yanda tasha ruwan dadama,inna fure kasa hakuri tayi fuska ƙumshe da annuri tace”da alama fa lafiya tafara sumuwa tunda tsawon wannan lokaci data ɗauka cikin wannan hali dakyar ruwa yake wucewa ta maƙoshinta amma duba yau kaga hamdullahi tasha dadama wannan ma wata nasara ce.
*****
Daddagewa tayi da datsa masa cizo a harshen sa ai kuwa besan sanda yature ta daga jikin sa ba idon nan nasa sunkada sunji jajur,share hawayenta tashiga kana tace”kwarto anfaɗa kwarton saika tsireni ta kwasa a guje tayi waje bangaje juna sukai da jamila dake laɓe tana dakon fitowarta ai kuwa batayi wata wata ba ta damƙota ji kake fass fass ta sharara mata ruka har sau biyu,ita ma Aisha cike da jarumta dan ita bataga dalili da za’a mareta haka ba,tunda bada saninta taxo ta bigeta ba.
Ramawa tayi tana nunata da yatsa tace”idan kina cin kasa kikiyayi ta shuri bada sani na bangajeki ba amma kiyi hakuri harta juya ta fara tafiya sai kuma ta dawo da baya tace bafa hakuri akan marin da narama nake baki ba a’a hakuri akan bangazan ki danayi ne.
Baki sake jamila ke binta da ido dan kusan suman tsaye tayi ita kan ta bata taɓa kawowa a ranta wannan ƴar ficikar yarinyar zata iya ɗaga hannu ta rama marin da tamata ba,dan haka tanaji tana gani Aishan tabar wajen harta ɓacewa ganin ta bata iya yin komai akai ba.
Alhaji badamasi zaune suke da abokin sa Alhaji manzo nan Alh manzo ya ƙurɓi lemon mai sanyi saida ya ajiye cup din hannun sa kana yadubi abokin nasa dacewa”kaman naji kishin kishin wai an ɗaurawa Ahmad aure da wata bayan ƴar gidan Alh sunusi da kowa yake tsammani,wani irin zabura Alhaji badamasi yayi yace”mai nakeji kake cewa ne kode nine banjika da kyau ba.
“Karde kace dani bakasan abunda ke tafiya a gidan naka ba,to inde haka lalle da…..sai kuma yayi shiru take zufa yakaryoma Alh badamasi inda yatuna maganan su da Alh sunusi na karshe inda yace dashi nayarda ƴata zata tare gidan ka bisha wasu dadilai amma kasani auren ɗanka da ƴata ba saki babu kishiya babu taƙura duka abunda takeso shi zatayi matukar ɗanka ya tsallaƙe daya daga cikin wannan sharuɗan jinin sa ya halatta dan zamu sadaukar da jinin sa wa dodon mu.
Yana kawowa nan da tunanin sa kawai ya miƙe zumbur yashiga safa da marwa yama rasa tacewa sai shi Alh manxo ne daya ƙara dacewa”yanzu me mafita kasan sharaɗin da Alh sunusi ya ginɗaya maka kuma a gaban dodo akai wannan yarjejeniyar nima kaina da wannan labarin ya zomun na kaɗu sosai nasan tabbas ba’a saninka hakan yafaru ba.
Amma kajeka kabincika a hankali cikin hikima zaka tunkari ita hajiar dan tanada masani komai tunda nima abakin mai ɗakina natsinta.
Da haka suka rabu da Alh manzon inda ko
sallaman kirkiri betsaya yi da abokin nasa ba yanufi motarsa driven sa na ganin sa ya nufosa da sauri yabuɗe masa murfin motan saida yashi ya xauna da kyau shima drivrn ya zajaya yashi yama motar key sannan cikin ladabi da biyayya yace”Alh ina muka nufa?
Muje gida ya amsa masa a gajarce
Koda isarsu gidan be tsaya jiran sai anbude masa motan ba yabude da kansa yanufi cikin fuskar nan tasa hade kaman hadarin gabas zuciya tamasa nauyi har wani huci yake,ko sallama be tsayayi ba,saboda rufewar ido bemaga waƴan da suke zaxzaune a falon ba yana shiga kawai kan Ammi yasauke idon sa.
“Ma’arufa yanzu sabida kinmai sheni mijin hotiho ɗan nawa saide na tsinci labarin kunmasa aure a titi,shin mekike ɗauka kanki dashine ko yanada wani uban bayan ni.
Waima wani ishafeffe da mai ɗinne da harya isa ɗaurawa ɗana aure ba tare da ƴawuna ni ubansa ba.
“Sai ni aka amsa masa daga bayansa a mugun figice ya juya dan jin muryan da beyi tsammanin ji koda wasa ba,ido hudu sukai da tsohu mai rankarfe wato baffan sa wanda suka kira da malam mai babban riga zaune ya hakimce saman daya daga cikin kugerun da sukaima falon ƙawanya sai gefen sa wansa yakubu da kanin sa nafi’u zaune daga ƙasan carpet sai gefe guda kuma ma’aruf wato dan uwan hajia ma’arufa sai kuma yarta yaya bara’atu da kawunta ita hajiar Aminu gefe guda kuma ga setin akwatuna biyu masu kyau da daukan hankali ajiye ganin idon malam mai babban riga be hana Alh badamasi fidda abunda yake ransa ba.
Saida ya daura da cewa ta tabbata ashe gaskiya ake faɗi ba rade raɗe bane to wallahi ma’arufa muddin nine na haifi Ahmad ba wani ya haifamun ba to a yau yau kai yanzu yanzu basai anjima ba ze rubutamun takardar sakinta ya bani a hannuna idan ko ba haka ba…..”Ta tabbata ashe abunda ake faɗi kanka gaskiyane ba karya ba,to wallahi kasani kafita harkar sunusi idan ko ba haka ba akwai ranan nadama ina jiye maka wannan rannan dan abotanka dashi ba abunda ze kareka dashi.
Kuma yaro kaika haifi abunka ba wanda ya haifama saide kaman yanda kake da iko kansa kake kuma da hakki hakama ita uwarsa tana dashi aure de anɗaura ba fashi saide kasani muddin kace zaka raba wannan aure to wallahi kasani ƴar gwal din da kakeson aura masa baxe taɓa auren taba saide ayi biyu babu”dan Allah baffa kayi hakuri yafada sanda yake zama daɓas a gaban baffan nasa wallahi idan ance dole sai anyi wannan abun zamu iya rasa Ahmad ɗin….duk falon ido suka zuba masa suna kallon sa shi kansa besan yayi wannan katoɓarar ba saida yafaɗa sannan yarufe bakin sa da duka hannun sa yana ta muzurai rashin gaskiya.
Hajia mariya ɗaki tashige bayan wucewar Alhajin cikin rawar jiki tashiga laluɓen wayan kawartata wato bilki saida tayi mata kira biyu sannan ta ɗauka wata ƙatuwar ajiyar zuciya hajia mariya ta sauke tana cewa”ƙawata akwai matsala.
“Mecece matsalan?
“Akwai matsala.
“Faɗamun matsalanki koda yakai dutsen auhudune baki da matsala tunda kina dani kwantar da hankalinki kaman kinma sarki karya.
Dariya suka kwashe kusan a tare harda shewan su sannan hajia mariya ta kwashe komai dasukayi da Alhajin nata tafaɗa mata.
Ajiyar zuciya Alhaji balki ta sauke sannan tace”kewaya faɗamiki idan anje wajen irin wannan ana faɗawa miji”tabb kice na tabka kuskure fadin hajia mariya”ba ɗanka ɗan ba kuwa dan ai maza basason mace tasan sirrin su idan kuma kina tafiya ire iren wannan wajen yanzu idan bamuje wajen ba zakisan yana wata kungiya ne?
Kai tashiga jijjiga mata kaman suna tare ta daura mata dacewa to bara kiji da kibude kunnenki da kyau ki saurareni yanzu duniya ta canja anfita daga rayuwar duhuwar kai idan kana da kai ka ƙara da wanka idan kina kissa wajen riƙe miji sai kinhaɗa da biyebiyen nan dan samun malakan kansa.
“Kai kawata
“Hmmm kina mamakina to bara na faɗa miki yanzu haka na mallaki gidan kaina kai gidaje ma zance miki bada sanin Abbansu usman ba ina da motoci har uku da akemun aiki dasu keke napen goma duka nayi tanadin abunane dan karta ɓaci,yanzu ke me kika mallaka naki nakanki.
Hammm hajia mariya ta sauke ajiyar zuciya tace”gaskiya nifa ba abunda na mallaka nawa na karan kaina banda ƴan gwal gwale daya saimun da kansa ba abunda nake dashi .
“Tabb kina ruwa ashe ni ina kallonki wayayya ashe da sauranki,waya fada miki yanzu mata suna zama hannu rabbana dole kitashi tsaye ki yakice rabonki kinji abundade boka yace wallahi kika tsaya kallon ruwa sai ƙwaɗo yamiki ƙafa daga nan sallama ta mata ta kashe wayanta,tabar hajia mariya da sake saken xuci dan ita ko keken kanta bata mallaka ba,ashede mata na samun kuɗi ita ta zauna sai abunda aka yaga mata takeda lalle dole nima nashi tsaye abunda take tsakawa aranta kenan sai zarya da take cikin bedroom ɗinta tana bubbuwa wayan a hannunta.
Tunda Aisha ta fita yaxube saman kugera sai maida numfashi yake ruwan gora mai sanyi ya dauka saida ya shanye goran tass ya lumshe ido shiyama rasa mema yake jansa zuwa gareta yarinya da nonuwanta ko lemun tsami basu wuce ba,yama rasa wata jarabace ke damunsa ga manyan mata amma yaɓige da laluɓan ƙwaila ai wannan ma zubda ajine idan wani yagansa sannan sayama kansa rainine wajen ƙaraman yariya da haifuwar kajine ya haifi irinta.
Aisha kuwa tana barin wajen saida ta saita nutsuwarta sannan ta nufi cikin hall dinda suke dinki cikin sakin fuska ta gaggaisa da abokan aikinta nan suka shiga hira da laila nan take ce mata”wai ke me sirrin ne kwana biyu baki zoba sai kinga yanda oga yake zarya zuwa nemanki,tafaɗa tana ƙasa da murya da ƴar dariya kadan kaɗan.
“Duka takai mata a wasance tana cewa”laila yaushe kika fara sharri”wallahi bawani sharri gaskiya nake faɗi,tsakanin sa da khalid bansan wanda yafi zaryan zuwa tambayanki ba,danma shi oga baya magana sai muzurai”Allah ya kyauta tace tana dauka wani yadin material ta yanka tabada zizza kafin ta haɗa wata doguwar riga data dauki hankalin duka abokan aikinta inda nan take suka sakata jikin ƴar tsana suka shiga haska mata hoto kowa kagani burinsa yariga ɗan uwansa yin postin kan kace me,sai ga kira daga costomers irin big girl din nan kowacce burinta ace itace wacce zafara ganin wannan kayan ajikita,basma na zaune da salaha suna cikin abinci a gidan cin abinci salaha dake daddanna waya ita tafara cin karo da wannan post ɗin a IG ganin ruwan comment da yanda dinkin rigar yatsaru saida ta bibiyi waje ta tabbata sannan ta miƙawa basma wayan tace kalli nan ki gani”wai me kinsanfa ni bana saka kaina sabgar media.
“Kede karɓi kigani tafada tana sake miƙa mata wayan.
Karɓa tayi tana kallo ai batasan sanda ta saki wani ihu ba,har saida hankulan mutane dake cikin wajen ya dawo kansu,sauri miƙewa tsaye basma tayi tana laluɓen numbar wayan Ahmad dan sanar masa da bukatan ta.
Gudu gudu sauri sauri tajeta tabiya kuɗin abincin harsuka shiga mota kiran wayansa take amma be dauka ba,kai tsaye company tanufa ko tsayawa kashe mota batayi ba,sai salaha ce kashe cike da yauƙi tashiga office ɗinsa ko neman izini babu ya lafe jikin kugera idanun sa a lumshe kaman na bacci sai sauka kiss dinta yaji a ƙuncinsa bazato.
Dan tureta yayi yana waro idon sa akanta”sau nawa zan faɗa miki banason wannan ɗabi’a ta yahudancin,cikin ko inkula tace”sorry saura kwana nawane a shafa.
To sai kibari sai anshafan kyayi”yanzu de ba wannan ne yakawo ni nan ba,wayan ta miƙa masa karɓa yayi yana ware idon sa saman hoton basarwa yayi yana maida mata da wayan”nagani sai me?
“Yamunne inason ɗinkin nafison nazama nice wacce zata fara sakashi jibi a wajen party ko wacce classic girl maiji da kanta saide ta gani ajiki na kuma banason asake dinka irin sa cikin kwanakin nan harsai nasaka.
Taɓe bakin sa yayi danshi bega abun zaƙewa anan ba.
“”Ok bara naduba nagani ko wayayi wannan dinkin danni banima da masaniya akansa,yana faɗa yana gyara zamansa da kyau ita dinma zaman tayi ta zuba masa ido tanajin wani irin abu mai karfi gami dashi gira ya ɗaga mata alaman yade”ina son ka shine abunda yafada tana tsare shi da ido jin ko ze tanƙa amma sai taga ya maida da hankalinsa ga wayan da yakeyi tadeji ya ambaci “Aisha kuma ok turamun ita yanzu daga haka yakashe wayan.
Minti biyar tsakani sai gata tashigo bakinta ɗauke da sallama fuskarnan tata tsuke danma kar yace zesake gwada mata rashin M”gani oga tace dashi tana sakeyin ƙasa dakai,nuna mata basma yayi sai sannan ta waigo gareta”barka da warhaka hajia tafaɗa batare data kalli yanayin fuskarta ba,saida tasha ƙamshi tana ƙarewa Aisha kallon dan tayi wani irin freesh taga kamanma ta ƙara mata girma a ido daɗa taɓe bakinta tayi tare da ɗaga kafaɗanta tace”kaya nagani kuma inaso konawane zan biya sannan dole a mallakamun tunda nace inason.
Ba Aisha ba shikansa Ahmad yanda tayi magana cikin isa da nuna iko abun yabashi mamaki saide besaka musu baki ba asalima basarwa yayi kaman baya wajen.
“Bansan wani kaya kike magana akai ba ta amsa mata cikin sanyi murya daya zame mata jiki,tura mata wayan tayi gabanta zata kai hannu taɗauki wayan tayi sauri daukar wayanta tana cewa”ba irin ƙazamai ke taɓamun waya ba,maganan tama Aisha zafi dan haka itama kanta tsaye ido cikin ido take kallonta sannan tace”kuma ƙazaman su suka ɗinka kayan da kika wanko ƙafa kikazi nema,kan kizo dubunki sunzo dan haka wannan kaya ba mallakin kowa bane mallakina ne sai yanda nayi shi koshi kansa mai faɗa aji na wajen bashi da iko akan wannan kaya kina iya ɗauka tsamin kafanki kibar waje dan bazaki taɓa saka kayan nan wajen ba dan dukkanmu masu aikin taron ƙazamanne sai aje can anema awani jen…….