Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 48

Sponsored Links

CHAPTER 48

“K kinsan waye ubana da zaki tsaya gabana ina faɗi kina faɗi?
Kallon kasa da sama tamata sannan ta danyi wani juyi da ɗan miƙa kamande da gayya tayi haka illa kuwa sakon ya isa gawanda takeson isarwa dan kusan mutuwar zaune yayi dukda ƙokarin sa nason basarwa dayake dan yamai da hankalin sane kacokan kan systerm din dake ajiye a gaban sa idan baka sani ba sai kaɗauka wani aiki yake mai mahimmanci saide a baɗininsa hankalin sa gaba ɗaya yana kansu dan kallon kasan ido yake binsu dashi”na sani mana ta amsa mata a ƙaikaice mutum ne shi mai hannu biyu kafa biyu ido da baki da hanci sunan sa SUNUSI takare faɗi da tafa hannu sai me?
Dawani irin mugun sauri ya daugo kansa yana kare mata kallo anya yarinyar nan tasan waye mahaifin Basma da harta iya kiran sunan sa tsirara haka,maganan da yakeyi a ransa kenan yayin da Salaha dake laɓa bakin ƙofan shiga office tayi saurin dafa bakinta da hannu tana jan kafarta takoma da baya dan baxata so suyi ido biyu da ƙawatata ba,dan ita tasan waye uban nata a rashin imani.

Ita karan kanta anata ɓangaren mutuwar tsaye tayi dan wannan shine zata iya cewa karon farko datayi kuri da mahaifinta wani mahaluƙi ya kira sunan sa tsirara haka bawani ɗan kara wai wannan yarinyar da haifuwar kaji ma zata iya cewa ta haifi irin take tsaye gabanta ido cikin ido ta kira mata sunan mahaifi haka.

“Waye ubanki anan garin?

Waya ɗaure miki gindi dahar kika samu gwarin gwiwan kiran sunan mahaifina a tsirara haka?

Yanda tayi maganan kawai ze tabbatar maka da ranta na ɓace sosai da hakan.

Itako Aisha ko ajikinta saima cewa da tayi”koba haka sunan sa yake ba?

Nagade sunan da akai masa yanka da ita kenan yo mai nawani nuna damuwa dan ankira mutum da sunan sa,taɓe baki tayi ta cigaba da cewa ni banga abun damuwa anan ba.

Idan dama saboda wannan kika kirani to kinga ninayi nan,takare dafita daga office dinma baki ɗaya,a fusace ta juya kan Ahmad dayayi kaman ma baya wajen cikin muryar kuka take magana”yanzu MY rashin darajata har yakai kana waje ana gayan magana bazaka iya tsawatarwa ba,kanajin fa yanda wannan ƴar mitsitsiyar yarinyar nake takira suna daddy haka gatsar bawani kara ko girmamawa,kawai sai tasaka masa kuka datake ta dannewa tuntuni.

Numfashi ya sauke yana mai ture systerm ɗin gefe yacire eyeglass dayasama idon sa danson kare masu kallon ya ije gefe sannan ya harɗe hannun sa guɗa yana kallon yanda ta dage tana risgar kuka”wai kukan duka na me?
Ya tambaya kaman ma besan meyafaru tsakaninta da Aishan ba,sake sautin kukanta takara batare da tama kula shiba ganin bata da niyar amsa masa yaɗaga kafadan sa yana cewa”anyway tunda bazakiyi shiru ba shike nan inada meetin jirana ake yanzu haka zsn iya tafiya idan kin kuma gida kimiƙa sakon gasuwata ga hajia.
Saurin shangaban sa tayi ganin dagaske fitan zeyi bata tsaya wata wata ba ta rungumesa cikin kuka take cewa”wato baka damu da damuwata shine bazaka kirata ka tsawatar mata yanxu taci bulus kenan duk rashin kunyar da tamun,ni akullum sai sake linƙaya nake a kogin soyayyarka amma kai ko oho saima kakkaucemun dakake wai mazanyi kasoni koda ƙwatancin yanda nake sonka ne.
“Hmmm Bass matsala yafaɗa can kasan maƙoshi yana zameta daga jikinsa kamo hannun ta yayi ya zaunar da ita saman kugera data tashi goran ruwa mai sanyi ya ɗauko yamiƙa mata bamusu ta karɓa tasha dan ita kanta tanada bukatar ruwan,ajiyar zuciya ta sauke tana kafesa da ido,kaman bazece komai ba sai can kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali yace”abunda nakeso kikasani mu ƴan kasuwane bawai ƙarƙashin wani muke ba balle ya mulkemu.
Sannan a harka ta kasuwanci ba nuna ma mutum iko akan abunsa,bakibi hanya daya dace ki mallaki wannan kaya ba,da farko kin nuna kinaso kuma dole a mallakamiki wannan dole ya tsaɓa ka’idan mu ƴan kasuwa,sannan kinnemi mai abun kina bukatar abu awajenta amma kina nuna ita bakomai bace face wata ƙaskantacciya.
Yama za’ayi ta saurareki,da ace sari zakiyi ko pieces dubu kikace kina bukata kunyi ƙudi kinbiya wannan kina da ikon abunda zakiyi dasu koda kingani a jikin wata kafin yaxo gareki hakkinkine kibi diddigi.

“Amma MY dan naga abu nan wajenka inaso bani da matsayi da zaka mallakamun wannan abun matsayina na wacce zaka aura,tafaɗa tana kafesa da ido dan son jin amsa da ze bata.
Be bata amsa ba asalima bashi da niyar sake ce mata komai dan yana ganin yayima kokarin tsayawa yin dogon magana.

“Shikenan ta faɗa tana gyara fuskarta tada ɓaci da ruwan hawaye mikewa tsaye tayi tana kallonsa ok ina bukatar pieces ɗari daga nan zuwa gobe warhaka nakeso kasan idan kuɗine ba matsalata bane,wani shu’umin murmushi yasake mata wanda takasa gane ma’anarsa yana ɗage mata kafaɗa yace”anyway zaki iya zuwa kisami mai kayan sai kuyi magana da ita dan ni kaina saida kikazo nasan da kayan an danko yadinda akai amfani dashi bama dashi anan company….saurin katseshi tayi tana cewa kace kawai bazaka saka baki wannan ƴar matsiyaciyar ta bani kayan ba kenan,to wallahi kasani ko ta halin yayane sai na mallaki wannan kayan fuuuu tafice a fusace tayi hanyan barmasa office ɗin tana mai daddanna wayanta danson dialing Number ɗin daddynta dan ita fa dole saita mallaki wannan rigar dan tunda mummynta ta haifeta bata taɓa nagani abu tanaso rasaba dan haka wannan ma tagani tanaso kuma dole ta mallaka dan ta nan ne kaɗai take ganin zata nunama ƴar matsiyatar nan bambanci dake tsakaninta da ita.

ALH BADAMASI

Zubewa yayi gaban mai babban riga duk yaruɗe yana bada hakuri kan dan Allah a rusa batun auren Ahmad da wata bayan wanda ake saka ran yinsa,yanda yaruɗen kadai ze tabbatar maka ba cikin hayyacinsa yake ba kamande bawa da shugaban sa wajen ƙin tsaba umurni.
“Shikenan zauna ai kabari ko gaisawane mayi ko yayansa yakubu yafaɗi haka kaman bega yanda kanin nasa yaruɗe ba,sai sannan ya maida hankalinsa ga waƴanda suke zazzaune a falon take wani irin kunya ta lulluɓesa dan rabon daya yaje garinsu ziyara koya kirasu ta wayane yaji lafiyan harya manta.
Ƙasa yayi da kansa mai babban riga yasoma gaisarwa sannan yaya yakubu da yaya bara’atu nafi’u da ma’ruf shima suka gaisheshi ruwa mai sanyi da juice mai sanyi Ammi ta gabatar masa beyi musu ba yakuwa sha sosai fiye da rabi sannan ya ajiye kallonsa Malam mai babban riga yayi ya gyara zaman sa dayau yace”badamasi³sau nawa nakira sunan ka?

“Sau uku baffa ya amsa masa,gyaɗa kansa yayi ya cigaba da cewa yaushe rabonka da zuwa dubomu ko waya?
Shiru yayi yakasa amsa masa da tambayan sai hakuri dayaci gaba da badawa”a’a riƙe hakurin ka ai mutum idan Allah ya ɗaukakashi gani yake ƴan uwa da abokan arziki da basuda shi ba ajin sa ba yanxu ya wuce sanin.

Kagode Allah daya baka mace tagari mai son zumunci badan ita ba da mun daɗe da mancewa da munada wani ɗa,amma Allah yabaka mace wacce take tsaye kai da fata dan ganin wannan zumuncin namu be ruguje ba,dan duk wani abu kama daga bikin aure suna ko mutuwa tana zuwa wani bin da yaran baki ɗaya wani bin kuma takanyi mana aike ko suje da ƴan uwata bata taɓa wofintar da duk wani abu namu ba,ko wannan zuwan muzone dominta da ɗanmu Ahmadu bawai saboda kai nayi tattaki daga kazaure zuwa nan kano ba,sai ya dan tsahirta.
“Aure kuma anɗaura bamu da hurumin raba abunda Allah ya hada dan bamusan abunda Allah yaɓoye cikinta na alheri ba,yaya yakubu ne ke wannan magana.

“Ai wallahi kaman yanda matar uban gidan naka take kurin sunfi karfin kishiya to mu kuma zamu nuna mata cewa sunnan ma’aiki mukebi, faɗin(Allah subuhanahu wata alah)cewa ku aura daga biyu uku hudu idan ko bazaku iyayin adalci ba ku auri ɗaya,to danmu adaline da yardan Allah aurene anyi ba fashi saide idan mutum ze mutu dan baƙin ciki ya mutu.

Wannan magana ta yaya bara’atu kaman ta watsa masa tafashesshen ruwa haka yake jinsa,shi kaɗai yasan irin tashin hankali dayake shirin fuskanta dakuma tarin kalubabe dake tunkarosa.

Shide Alh badamasi banda hakuri ba abunda yake badawa saida nafi’u kaninsa da ma’aruf suka saka baki wajen bawa mai babban riga hakuri da yaya yakubu sannan ya hakura ƙarshe nasiha yashiga yimasa mai ratsa jiki cikin hikima da wayo dakuma dabara irin tasu ta manya,kwarai jikin Alh badamasi yayi laushi dajin yanda mai babban riga yake yi masa nasiha kalma bisa kalma harafi bisa harafi ba wani hargowa ko ɗaga hankali,karshe yasake jaddada masa da kula da zumunci sannan ya daura da cewa masa”karka shiga hurumin da banaka ba,bamusan abunda Allah yaɓoye na alheri cikin wannan auren ba dan haka karmuzama masu ɓata abunda Allah yahaɗa Allah yayi muku albarka ma’arufa kikara hakuri kuma koshi beje kaimana ziyara ba ke karki bar wannan zumunci Allah yanason masu sada zumunci da masu yawan yin alheri.
“Ina shaa Allah malam bazamu taɓa barin kuba aikune madubin dubawan mu baki ɗaya,sannan dan Allah malam ina neman alfarma abar su Inna delu suzo mana wannan karon ranan asabar kaman yanda aka saka shine ranan ɗaurin auren Ahmad da basma sannan kuma tarewar ita ɗayan ma.

Murmushi yayi irin tasu ta manya yace”ai ma’arufa kinfi karfi haka duk ma zasu zo harma da waƴanda baki nema ba,ai koni banzo ba yakuba zasu dawo dasauran yan uwa,ai kosu waƴanda suke masa ganin bashi da ƴan uwa zasu ganema idonsu shiɗin dan dangine gaba da baya dan ya wofinta dasu na.

Mutum idan ba rashin hankali ba kana tsaye da kafafunka mutum yazo rana tsaƙa yaraɓeka amma yace shine wanda ze juyaka katsaya kana rawan jiki baka da kataɓus akan komai sai yanda akai dakai,shide Alh badamasi kansa a kasa fatansa kawai kowa yatafi yabarsu yasamu zazzagema Ammi jakar tsaɓa kanta.

ALHAJI SUNUSi

Lokacin da Basma ke kiran wayan sa shikuma daidai sannan yana wani ɗaki yana ganawa da shugaban su bayan sun gama aikata masha’arsu(wa’iyazu billah Allah yakiyashe mu)dan neman duniyarsa goge jikin sa yayi da wani farin kwalle shima Alhaji sunusi yagoge duburansa a tare suka jefa kwallen tsumman cikin wani tukunyar kasa dake gabansu wuta naci aciki,rufe idon su sukai suna karanta wani dalamirai na tsafi can wutan ta tashi sama kaman an zuba mata fetur ciki a tare suka zabura cike da fargaba shugaban ya dubi Alha sunusi yace”matsala ta samu andaura auren surukinka da wata yarinya muddin wannan yarinyar tana cikin rayuwar sa bazamu taɓa samun yanda yamuke so ba,dan zata lalata mana komai namune akwai inuwan dake bibiyarta haryanzu bankai ga gane inuwar na waye ba.

INUWA INUWA INUWA kawai yashiga maimaitawa kaman wani zararre sabon kamu yana cewa shugaba kode inuwar Ishak da nafi ke bibiyar rayuwata yake son hanani kaiwa ga nasara bayan nasan duk wani sharaɗin dodo nacika harfa mamata ka kwanta da ita tsawon kwana arba’in haka nabaka budurcin ƴata ɗaya tilo nabaku jinin ɗana abun kaunata haryau uwarsa batasan baya duniya ba,ya zauce sai surutai yake”nutsu ka saurara wani murya ne yaratsa inda suke”yi maza kasamo mana jinin budurcin wannan amaryar surukinnaka a daren da aka kaimasa ita,idan karasa darenta na farko kanada dama harzu daren kwana uku dazatayi a ɗakin mijin ta maza tafi kuma cikin dare dodo yanason kakawo masa ƴarka na tsawon kwana uku dan cikan burin ka na har abada.

 

Alkalami🖊️
Yafi takobi⚔️

Leave a Reply

Back to top button