Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 60

Sponsored Links

CHAPTER 60

Zaro idonta tayi kaman zasu faɗo ƙasa tasoma wutsul wutsul da kafanta ba bakin magana saboda rufe mata bakinta da yayi da tafin hannun sa ɗaya sai”um um um kawai ta iya cewa.

Falo yanufa da ita a hakan daga ita sai ƴar riga mara nauyi da tasa na shan iska”me zan gani haka ni ikilima yau sauke mun ƴa Anty hajia ke magana daidai shigowan sa falon ɗauke da ita kaman wata ƴar tsana.

Kusan duka waƴanda suke zaune a falon miƙewa tsaye sukai idan kacire yah faisal da kallo ɗaya yamasa yacigaba da aikin da yake a systerm din da ke saman cikinyan sa fuska ƙunshe da murmushi.

“A’a Anty hajia dan Allah karki tsaidani taurin kai takeson yimun idan bata bini a hankali ba wallahi fitan da zanyi da ita ta tafi kenan wai kaman ni zan bata umurni amma yarinyar nan saboda taurin kai ko motsawa batayi daga inda take zaune ba,almost 30mnt nabata dan ta ƙimtsa amma tayi kunnen uwar shegu da maganana”to naji yanzu de sauketa yi hakuri ta fada tana nufosa dole yasa yadireta badan yaso ba,sake tamke fuska yayi yana kallon wani direction ɗin yace”hijabi kawai zata ɗauka tazo mutafi kokuma….”a’a bazayi haka ba ta dakatar dashi dafaɗin haka yanzu de dan barmun ita tayi koda breakfast ne.

“Ai taƙoshi kuma anty hajia idan ba abunki ba ina kika taɓa ganin ango bayar amaryar sa da yunwa ai tattaleta zanyi ai gwara ni na zauna da yunwa da in barta dashi ki yarda dani yakare maganan cike da zolaya.

Sannan ya ɗan kalli faisal da khalid dake tsaye ƙiƙam kaman dogari yace bros anjima around 8 zaku rakani wajen taron wancan yarinyar,baki sake suka bisa da kallo”wace yarinya?

Khalid yayi karfin halin tambayan sa duk da yafahinci wa yake nufi amma yaga tunda suka fara shagalin su ba wanda ya hallarta”daddy yakira yanzu yake tamun faɗa dan nace bazani ba yasake faɗin haka da damuwa kwance saman fuskan sa.

Ke malika ki haɗo mun da kayan da zata canza kuma na gayyace ku dasu umma salma gaba ɗayanku kuje,murmushi faisal yayi ya ajiye aikin da yake gefe sannan yace”kai akeson gani ba wasu tarin yara akeson gani ba har kana wani gayyato su auta kaide kawai zamu maka rakiya dan fidda kai kunya gani ga khalid sai nawwar zan kira dr sapwan a waya anjima inaga mun wadatar ko?kai kawai ya gyada masa.

Amma zancen wayannan yaran barsu a gefe sannan ita Aisha kabarta su tafi da malika tunda….saurin katsesa yayi da fadin nine zan kaita ai taƙi tafiya dasu malikan tun tuni yana gama mafadin haka yaja hannunta tana turjewa tana me yafita da ita,saida yasata mota ta zauna ya kullo ƙafar sannan shima yaxaga yashiga ta ɓangaren driver yaja suka fita daga gidan dan duk yanda Anty hajia taso sutafi da malika tare ƙi yayi daga karshema sai ce mata yayi wai anti hajia tsoron me kike?nagade matatace ina da hakkin keɓewa da ita da sauri anty hajia tashiga tattaɓa kunnenta da hannu tana cewa”kaide baka da kunya sai ku tafi amma ka maidomun da ƴa da wuri dan bazan lamunci….”haba anty hajia ki barsu su tafi kina ɓata musu lokaci cewa malika dake zaune tana daddana waya wani irin harara Aisha ta zabga mata ganin kaman tana sake zugashi.

Tunda motan yafita daga cikin gidan ya hau saman titi kawai sai taji hankalinta ya tashi tashiga rera masa kuka duk yanda yaso basarwa kasayin hakan yayi dan jin kukan nata yake harkasan ransa,samun gefen kwalta yayi ya faka motan ya juya ya kalleta fuskar nan tasa tamƙe kaman hadarin gabas yace”idan baki rufemun bakin kindena wannan ɗan iskan kukan bako to wallahi tafiya da zanyi dake kin tare kenan har sai randa zamanki na wucin gadin ya kare sannan zan maidoki,mukut ta haɗiyi wani abu mai kauri tashiga kunkuni yasanta da tsiwa dakuma rashin tsoro maidawa mutum martani inde abu beyimata ba,tada motan sa yayi yasoma tafiya sai ya tsinkayi muryanta cikin kuka tana cewa”ai wannan zaluncine auren rashin gata dan kawai anga iyayena basa raye har kana wani ikirari da cewa auren wucin gadi zakai dani dan kawai anga bani da gata saboda rashin sanin darajan mace,jin yanda ta taƙarƙare sai zuba take yasashi dakatar da ita ta hanya cemata”ba gwara ni ba ko banza kina kasarki ta gado kuma ai zaman namu naɗan wani lokacine da zaran nasamu abunda nake nema kinga sai nasallameki kikoma ga wanda kikeso kafin sannan kinyi girman da zaki iya rayuwa koma a inane,amma da yanxu na bari mai jan kunnen nan ya aureki kinga nafarko barin ƙasar zeyi dake sannan abu na biyu ba lalle ƴan uwansa su amsheki matsayin surukuwa ba saboda bambancin launin fata,gani nayima taimakonki nayi tunda banbijire wa Ammina ba na amince da aurenki na amsa ai godemun yakamata kiyi.

Wani tuƙuƙin baƙin cikine ya turnuƙe mata zuciya ita akaima aure ana rokonta alfarma tayi hakuri ta zauna dashi amma yanzu saboda yafita baki harze wani ce taimakonta yayi Allah sarki suhail masoyin gaskiya ko ina yake?
Ya zeji idan akace tayi aure tunawa da masoyinta na gaskiya yasata sake barke masa da wani kukan har batasan sanda suka iso ba,saida taji yace”to ai sai ki sauko sannan ta bude idonta da tunɗazu tarufe da tafin hannu ta kai dubanta ƙofa ashe harya zagayo yabude mata ƙofa yace kinga ni ai mutumin kirkine maison kyautatawa na ƙarkashin sa,batade ce masa komai ba sai ƙoƙarin saukowa datake saurin dakatar da ita yayi ta hanya cewa koma ki zauna kawai yanzu a hankanki zaki fita kowa ya kalleki,kallon da tamasane yasashi ankarewa da ɓaram barama da yayi sai kawai ya fuske da cewa karki dauka wai kishinki nake nop kawai kinsan ko banza da igiyar aurena akanki dole na kare abuna dukda auren na wucin gadi ne.

Batasan sanda tasaki wani mugun tsaki maitsawo ba mtsssssss aduk sanda yabude baki yace auren wucin gadi yayi da ita ji take kaman ta shaƙo masa wuya harsai yadena numfashi ta barsa.

Yiyayi kaman beji abunda tayin ba,saima wayansa daya ciro a aljuhun wandon sa yashiga kiran wata numbar itade taji yace gamu nan a waje sai ya kashe wayan ya dan juya ya kalleta yace saura kuma kiyi mata taurin kannan da kika saba idan baki bari anyi miki komai abunda yadace ama amareba wallahi wallahi kinde ji na rantsa miki ko daga nan sai…..sauri katse shi da cewa”ni nacema bazan tsaya amun bane ai ko jiya danaƙi binsu anty malika kaina kemun ciwo mutum bashi da magana sai ta tarewa wama yace maka zamu taren ai bazamu taɓa tarewar nan ba kaman yanda kadauki auren nan a na wucin gadi haka kuwa ze kare a wucin gadi kaida ganin tarewa kuma saide ta wancan mai maka da zabiyan naka,takare magana tana cinno bakinta.

Daidai wata mata da ganinta kaga shuwa da fara’arta ta nufosu gaisawa sukai Ahmad sannan Aishama ta dubeta ta gaidata cikin sakin fuska ta amsa tana cewa wannan itace?
“Eh itace hajia ya amsa.
“Ok to shikenan taho ƴata mushiga ciki ta faɗa tana riƙo hannun Aisha datake tsaye ƙiƙam tana kallon su”hajia duk abunda kikaga yadace ayi mata to ayi sai anjima zanzo ɗaukanta yafaɗa yana dan sosa kansa alaman kunya dariya matar tayi tace”baka da matsala Alhaji in sha Allah zaka yaba da aikinmu sannan ta daura da cewa hala amaryace ko?
Dan kallon inda Aisha ke tsaye yayi sai yaga itama ta kafesa da nata idon donson jin amsa da za bama matan sai ji tayi yana cewa”a’a kanwa tace kuma itace babbar ƙawar amaryar da zan aure kinga dole in fitar da ita saboda harkace ta manya ko zansamu mai tayawa wani irin tuƙuƙin taƙaicine ya turnuƙeta har batasan sanda ta gallah masa uwar harara ba tace da matar”hajia mushiga daga ciki bana juran yawan tsuyuwa daga haka matar tamasa sallama suka shiga cikin shagon nata,babban shagone sunayi gyaran jiki lalle ja da ɓaki halawa dilka wanke gyashi suna kuma sayarda turarukan humra dasu turaren wuta nasawa a daki dana turara kaya da ƴar tsugunne kana shiga wajen kamshi da sanyi wajen kawai ze sauke maka da wani irin ni’ima da nutsuwa haka ya kasance da Aisha dan duk wani tura haushin da Ahmad yamata sai taji tanemasa tarasa sai wani irin nishadi da ta tsinci kanta ciki wajen haɗu iya haɗuwa ga ma aikatan wajen sun iya tarɓan bako ga faran faran da jama’a snack da lemo mai sanyi aka fara bata taci tasha lemon kafin a wanke mata kai sannan daga bisani aka daura mata jar lalle daga gama lalle Aisha ta ɓingire a wajen sai bacci tayi bacci sosai kafin ta tashi sallati dauke a bakinta tayi mamakin yanda tadauki lokaci tanayin baccin saide ba abun mamaki bane duba da yanda bata samu tayi bacci daren jiya ba.

“Kin tashi matar ta tambayeta?cike da kunya ta amsa da”eh wallahi tashi tayi daidai matar takira wata mai suna larai zo kicire mata lallen nan tayi sallah cike da cika umurni wacce aka kira da larai tazo tacire mata lalle masha Allah suka faɗa atare duba da yanda lallen yakama yayi maroon shar dashi ga kuma yanda yankan gum din ya zauna raɗau tashu Aisha tayi larai ta nuna mata toilet tashiga tayi alwala taxo tayi sallah sannan matar nan da kanta ta jata wani ɗaki na daban ta bata xtra zani ta daura sannan ta umurceta data zauna saman kujera ƴar tsugo zama Aisha tayi wannan hajiyar tashiga mulketa da nau’in abubuwa kala kala shafa wannan goga wancan lakuta wannan saida tagama dirza mata jiki tass sannan ta kawo ruwan lalle tamata wanka da shi sai kuma ta saka itacen dorot data magarya saina habil tasake cewa Aisha tazo ta zauna saman wata kugerar wacce tsakiyarta da huji zama tayi bayan hajiyar nan tasa waƴan nan ice dana lissafo cikin wani rami ta zuba garwashin wuta ciki take wani hayaki mai dadin kamshi yafara fitowa daga cikin ramin bargo ta dauko ta lulluɓama Aisha sai kanta kawai data bari waje tun Aisha na daukan abun da sauki harta soma gajiya da zaman sai wani irin zufa datake ssaida aka dauki akalla minti talatin sannan hajiyar tazo ta yaye mata bargo ta mika mata zani ta daura suka fita a ɗakin zuwa wani ɗaki na daban,sannan tamika mata wani kufin sulba cike da kunu amsa Aisha tayi dukda batasan kunnun name nene ba amma taji dadin kunnun tana gama sha aka tsantsara mata bakin lalle saman jan ba karya ko ita kanta taji bambanci sosai ajikinta ga wanj irin fitinannen kamshi dake tashi ajikinta sai sheƙi data gashin kanka nayi mata gyara namusamman kana ganinta taga amarya Aisha haka kawai ta tsinci kanta da farinci sai sakin murmushi take ita kaɗai idan ta dago ta kalli kanta ta cikin madubi dake cikin ɗakin.

Hajiya mariya suna zuwa gida ana kiran sallan magariba saboda nisan da dajin da bokan yake da cikin gari a gurguje taje ɓangaren ma aikata tana shiga inda ake girke gurke duka ma aikatan suka zube suna gaidata amsawa tayi da tambaya ina ogansu wani farin dattijone yafito ta wani ƙofa sanye yake da farin kaya da wani dogin hula gaisheta yayi yana cewa”gani hajia wani abu kuke bukata kallon sakon goma tamasa sannan ta amsa”da eh dama inason ganin me da me kuka shirya na tarɓa baki kasan nan da kaman awa daya za fara gudanar da party ko?”eh nasani ranki ya daɗe anma gama komai ya amsa mata cikin rawar jiki”ok mugani wucewa yayi tana biye dashi a baya yafara nuna mata komai ta kuwa yaba yajidaɗin yaba musa datayi godiya yayi harze juya tace”jimana komowa yayi ya tsaya kansa duƙe yana kallon kasa kuɗi taciro cikin jaka tamiƙa masa tace wannan nakane sannan inason zakamun wani aiki zan maka sallama mai tsoka dazaran kamun yanda nakeso”wannan ba komai bane hajiya ya amsa mata cike da jin dadi ta ciro ƙullin magani cikin jakar hannunta tamika masa tace wannan nakeson kazuba ma angon cikin abunci dana sha da anjima za bashi dan Allah kada kabari wannan dama tawuce ni,yanda ta marairaice masa kaman zatayi masa kuka yasashi amsa dan idan yace bazeyi mata ba besan abunda ze biyo baya ba dan yasan irin wayan nan matan daba Allah ne a zuciyarsu ba zata iya masa wani sharrin tunda yasan tasan sirrin sa.

Leave a Reply

Back to top button