Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 64

Sponsored Links

CHSPTER 64

A guje drivern babban motan da yaron matan sa dama bakaniki dake gyara motan sukabar wajen dan tsiratar da rayuwar su,karkashin babban motar tasu motar tashiga gaba ɗaya sun rikice sun kuma ɗimauce dan ganin mutuwa sukai muraran a gaban su saide Allah ya taƙaita musu daf ɗin a tsaye take da tafiya take sunan su sorry ta bakin bature.

Duka cikin motan ihun suke idan kacire Aisha da bakinta dake adaure sai ido ba abunda takeyi sai zikirin da take cikin zuciyar ta,tare da rintsa ido dan so take inma mutuwarce ta dauke ta idonta rufe ba tare da taga irin mutuwar da zasuyi din ba,amma tanajin yanda kartin ke ihun sai kuma taji dif bata sake sanin inda kanta ke ba.

Kaman kiftawa da bismillah haka wayan nan katti sukayi dif suka ɗauke wuta na ɗan wani lokaci kafin kuma suka fara babbaƙewa da wani irin dariya ganin sun tsira da ransu shiko maƙwa da kansa ya daki glass ɗin gaban motan tattaɓa jikinsa yashigayi da hannu saida ya tabbatar da lafiyan sa sannan yashiga yin dariya saide nan da nan dariyar tasa ta dauke ganin wayan da suke tsaye gefe da gefen motan nasu.

Ance ko a gidan giya kake akwai babba to hakance takasance dasu maƙwa ko bakin magana shikan be samu ba saijin saukan naushi daya dauke masa jinsa da ganin sa besake sanin inda kansa yake ba,daddy ishaq dake zaune bayan wannan honda dake biye dasu Makwa dasuka dauke da Aisha sanda motar tanufi shiga karkashin daf ɗin nan”innalillahi wa’inna ilalhir raju’na Allahumma ajirni Allahumma ajirni yashiga faɗi saboda yanda zuciyarsa ta tsinke ba abunda zuciyar sa keyi sai wani irin luguden bugawa da karfi da karfi idan kana zaune kusa dashi zaka iya ganin yanda zuciyar tasa ke ɗagawa yama kasa ƙarashe addu’a daya ɗauka rintse idonsa yayi da karfi yanajin wani irin faɗiwar gaba dan ganin ƴarsa kuma yana ganin kaman ze rasata wannan shi ake kira ga ƙoshi ga ƙwanan ƴunwa.

Faisal na fita a hotel ɗin nan haka kawai yaji yakasa yarda da nan wajen parkin space ɗin gani yake kaman Aisha na wajen dan sanda suka isa wajen da malika yaga wani matashin saurayi mai tsukakken wando suna haɗa ido da wannan saurayin yaga ya rikice ya duririce yama rasa me yadauke masa hankali lokacin sai yanzu ma abun yazo kansa dafe kansa yayi yaɗan bigi bencin dake gabansa yamiƙe da sauri yana ma abokin aikin sa magaba suka fita duka a tare.

Ahmad tunma kafin yaje gidan nasu yashiga kiran Ammin sa a waya saide harta ƙatsa ba wanda yaɗauka sannan yamaida akalan kiran nasa ga ƙanwarsa fadwa tana ƙauka beko saurari sallama datake masa ba bare ya amsa jifa mata tambaya yayi”Aisha tazo gida”a’a batazo ba yayah amma lafiya ko?meya sami Aishan?ba tare akace take dakai ba?duka wannan tambaya lokacin ɗaya ta jeromasa”shikenan sai nadawo karkice da kowa komai yana cewa haka ya kashe wayan,maida akala kiran nasa yayi ya kira faisal da shima hankalinsa yake a tashe suna mota tare da abokan aikin sa guda biyu kan hanyarsu ta komawa hotel din sai ga kiran Ahmad Faisal na ɗaga wayan yashiga cewa”kana ina?”gamu kan hanyar mu ta koma hotel din wani abunne ko Aishan takoma gidane?”No bata koma ba saide nima gani na juyo dan komawa can ɗin dan inajin kamsn Aishan na can ina kuma ji ajikina kaman wani abu na shirin faruwa zuciyata takasa tsayuwa gudaya”kwatar da hankalin ka ba abunda ze sameta in sha Allah,a sanyaye Ahmad ya amsa da Allah yasa yanda ya amsa da rauni shi kansa Faisal sai yaji dan uwan nasa yabashi tausayi.

a tare suka ajiye wayan dukkansu ko wannen su da abunda yake aiyanawa a ransa tare sukai parkin din motan su faisal yafito da abokan aikinsa daga nashi motan haka shima Ahmad da sauri ya nufo su faisal ko tsayawa kulle motan sa beyi ba yana cewa da faisa”ɗazu naso ganin kaman mutum a nan a ɓoye kuma naso ganin kaman kalan rigar Aisha na fara zuwa wajen kaga harma nazo nan yana nuni da inda ya tsaya sai malika tamun magana to juyawar da nayi gareta koda nasake juyowa banga komai ba zama kaga sanda kace muje gida muduba zakaga yanda nake ta waiwayan wajen idan ka kula”hakane nima koda muka tafi nayi tunani wani abu dan sanda muka iso nan da malika naga wani matashin saurayi muna hada ido dashi naga duk ya firgice da ganina ban kawo komai a raina ba,dan hankalina yatafi ga rashin ganin Aisha da bamuyi ba wallahi saida na isa office tukun abun yazo mun,yanzu de bara mu fara dubawa,”tom kawai Ahmad yace sannan yanufi wajen shuke shuken nan shima faisal umurni yabawa abokan aikansa biyu daya zo dasu din suka shiga dube dube nan Ahmad yaga warin takalmin Aisha ɗaya a wajen kwalawa Faisal kira yayi aikuwa sai gashi shida abokan nasa ganin Ahmad yayi riƙe da takalmi wari ɗaya yana ganin faisal yashiga cewa”wallahi takaminta ne wannan ɗazu nasa malika takawo wallahi natane nan faisal yace da abokan nasa sufa bincikawa sannan ya juya ga Ahmad dib yace”kwantar da hankalinka in sha Allah zamu ganta yanzu de bara mufara da bincike nan suka rarrabu suka fara takan security suka fara amma duk wanda aka tambaya cewa yake shi bega mai kama da wanda suke tambayan ba,karshe dole suka fara amfani da wayansu suna nuna hoton ta amma shiru ba wanda yace ya ganta harma suncire tsammani sai wani dattijon mai gadi yace”yan samari bande ga yarinya da kuke faman nema ba amma ɗazu wata mota tafita anan da mugun gudu kaman marasa gaskiya kana wani mai mota ƙirar honda baƙa dashiganta nan kenan tamarawa mai wancan mota baya suka fita anan yaro idan kaga yanda suke shara gudu ko waye kai sai kabisu da addu’an Allah yatsare mukanmu da muke zaune anan munyi zargin mai motan farko da yafita kaman bashi da gaskiya,duka zubama dattajon ido sukai suna masu sauraron abunda yake cewan sai wasu mutane dake zauna kusa da shi suma suka amshe suna cewa ai wannan driver jar motan dagani kasan ɗan wiwi ne bakinsa baƙi ƙirin idanun nan nasa jajir dashi dagani saida ya maku yafara tuƙin na gefen sa ya amshe da”kai baka kula bane amma ni saida nayi ƙuri na ƙurewa bayan motan idon kaman mace nagani maza biyu sun sata tsaƙiya bakinta bakinta kaman a daure”kai Kallah kaji tsoron Allah cewa ɗayan”wallahi kuwa modi bakaga ina tama nhu nhu nhu ɗazun nakasa magana sai alama amma daga kai har baba ba wanda yagane me nake nufi.

Susu uku suke zaune a falon ga kugeru na alfarma an ƙawata falon dashi gefe guda wani mutumine kai da gani kasan yana jindaɗi duba da yanda jikinsa yake freesh harma baka iya ganin tsufansa rai a ɓace yake kallon mutanen biyu dake zaune sunyi tsuru dasu suna jiran hukucin daga ogan”wannan ai shashancine mekukeyi dahar yarinyar nan taji abunda kuke tattaunawa shin kunma san fitan wannan abun kaman mun daɓawa kanmu da kanmu wuƙane?”wallahi oga saida nace dashi yabari sai mun haɗu a wani wajen amma yaƙi”dallah malam rufamun baki karka wani ce zaka ɗauramun lefi ca nake da kai kamu tsaya munemi dukma wanda yamana leɓe da kanmu amma sai ɓari kake kaman wanda aka kaɗawa gangi kakasa tsayuwa ka nutsu gu ɗaya sai wani cewa kake dama saida nace…..”kumun shiru yadaka musu tsawa cikin kakkausan muryar ogan ya katsasa hakan ya hanashi ƙarasa abunda yafara yanzu de zama be ganku ba ku tabbata ba samu wata matsala ba muddin aka samu matsala to wallahi kuyi kuka da kanku karkuma wanda yace yasanni a cikin ku….Alhaji surajo kenan kutashi ku bani waje yafaɗa musu yana maui juya musu baya cike da ƙunan rai sannan ku tabbata yau din nan kunkawo yarinyar nan tunda kunce tana hannun yaran da kuka bawa aiki da tom suka amsa dukkan su haka suka miƙe jikin ba ƙwari Alh bala da zuciyarsa ke cike da tsoro sannan ga fargaba kafin su fita falo yakira numban Maƙwa daga cikin yaran da suka saka aiki ringi daya biyu aka dauka”halo Makwa wai haryanzu shiru murya yaji an amsa masa dashi ne yasa wayan hannun sa tsuɓucewa yafaɗi kasa saurin juyowa Alh surajo da Alh sunusi sukai suna duban sa tare da tambayar sa…….

 

Leave a Reply

Back to top button