Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 71

Sponsored Links

CHAPTER 71

Sosai su hajia mariyah suka tsorata da yanayin malamin take hajia bilki da tafi hajia mariyah sanin halin sa tazube gaban sa tana mai shimfiɗa hannuwanta tana roƙon sa ganin haka itama hajia mariya tashiga bashi hakuri dakyar de suka samu ya hakura yace sukoma su zauna,komawa sukai suna nazama yadube su dukkan su ganin yanda sukai laushi yasashi gyaran zaman sa yana kallon su yace”shikenan da nace kece zaki aiwatar amma yanzu nayi duba naduba naga bazaki iyayi da kanki ba,zaki iya sawa aimiki.

Amma da sharadi zaki bawa duk wanda zeyi muku aikin amma ki tabbatar kina tsaye saiyaje ya burne sannan zaki je ki kwanta wannan shine idan zaku iya to idan ko bazaku iya ba kutashi kubar mun waje.

Da sauri suka ce wallahi zamuyi yanda kace malam mude ka taimaka kar asamu matsala”bakuda matsala matukar kukai yanda nace gashi wannan layace yama sunan su?
Nan suka faɗa masa sunan ya rubuta jikin laya daga nan yamiƙa masu tace sutashi sutafi ajiye masa maƙudan kuɗaɗe sukai kafin suyi gaba zuciyoyin su cike da jin daɗi.

******
Jikinta sai mazari yake cikin nuna jarumta da rarrabewar murya tace”dan Allah wai me haka kake yine?

Buɗe gajiyayyun idanunsa wanda suke ruɗata yayi yazube a kanta kaman bazeyi magana ba sai kuma yabude kaman wanda akasa dole yace”inane kika tafi tsawun kwana biyu?

Kallon sa tayi tamaka masa wani zazzafan harara tare da murguɗa masa baki tawatsar dashi tana mai kai kanta gefe batare data amsa tambayarta dayayi ba.

Direct asibitin da aka kwantar da Anty hajia khalid yanufa dasu,zaune suka tadda ta saman gado Ammi na fama da ita kan koɗan shayine tasha Faisal dake tsaye daga fege yace”haba anty hajjia dan Allah ki daure kisha ko kaɗan ne zama da yunwa ma kanta itama wata cutace inde Aisha ne ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu namiki alkawari za’aganta zatazo garemu cikin aminci….sallamar da khalid yayi musu daga bakin ƙofar dakin shiyasaka suyin shiru suna kallon ƙofan khalid ne a gaba sai Ahmad dake biye dashi daga bayansu kuma sai Aisha,wani irin zabura Anty hajjia tayi sai gata tadiro ƙasa daga saman gado a sukunce ita Aishs ta karasa shiga ɗakin daga tsaƙiyan ɗakin suka rungumi juna suka fara kuka ita de Anty hajia sai Alhamdulillah take ta nanatawa hakan yadauke su kusan minti biyu sannan Anty hajia ita tafara janye jikin ta daga na Aisha tana binta da kallon tuhuma.
Ganin yanda take kallon nata yasaka Aisha tsunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da zoben hannun ta”inane kika je kika barmu da zullumin ba inda bamu nemeki ba amma ko labarin wanda yace yaga mai kama dake ma bamuyi ba.

Itade Aisha taƙi ɗagowa ta kalli kowa dake ɗakin sai sharan hawaye da take,ganinta hakan yasa yah faisal gyaran murya yace”Anty hajia ki bari ta nutsu tukunna yanzu zauna kisha koda shayi ne ko,cewar Ammi komawa tayi saman gadon ta zauna hannun ta rike dana Aisha kaman zaƙwace mata ita”yanxu kan zansha yayah haɗamun harda abincima zanci dariya duka sukai mata tanaci ana ɗan taɓa hira da ita Ahmad ko ya tsurawa Aisha ido kaman maison gano wani abu,duk ɗagowa Aisha zatayi sai sun haɗa ido dashi idsn yakashe mata ido ita kuma ta murguɗa masa baki duk abun nan dasuke Anty hajia na hankalce dasu.

Anty hajia na kammala cin abinci tace”kai tadago tana kallon su tace”ai sai akira likitin ya sallamemu mutafi gida ko”ggida suka haɗa baki wajen tambaya.

“BAD kace kai kaga yarinyar ko?

“Eh ranka yadaɗe Alhaji na ganta ido da ido wallahi zuciyata tafarfasa take Alhaji idan natuna dalilin ta yasaka bansan inda ƴan uwana suke ba,yakare maganan yana hucin bacin rai.

“Kwantar da hankalin ka Bad tunda kaganta ai komai ma yazo da sauki kaga gobene ƴan matan zasu gudanar da bikin kamu tom inason ka kasance a wajen ko Allah zesa taje”Alhaji inaga fa duk yanda akai da ita wannan yarinyar ake ɗana tarko wajen kame mana yara duba fa kagani ko su lion wayanda suke wajen sunce yarinyarce taje wajensa tasayi kaya daga zuwa pos shikenan labarin yasha bambam yanzu kuma su maƙwa abun nan fa yana bani tsoro Alhaji,Alhaji bala ne yakema Alhaji sunusi maganan shiko Alhaji sunusi bazaka gane yayinda yake ciki ba saboda bushewar zuciya.

Basma afujajan ta faɗo falon mummynta fa zuwansu kenan daga gidan malamin nasu ita da ƙawarta hajia bilki tana shiga falon tayi cilli da takalminta kallon ta sukai a tare cikin karfin hali hajja mariya da jikin ta ke rawa tabude baki dakyar tace”ke lafiya kika fadowa mutane a bakatatan?

Rushimata tayi da kuka tana cewa”mummy kiyi wani idan nasara shi mutuwa zanyi”ke nutsu kimun dalla dalla yanda zan fahinta,nan ta kwashe komai tafaɗa mata tana karewa tasake fashewa da sabon kuka.

“Kwantar da hankalin ki inda wannane matsalarki to daga yau anwuce wajen dan yanzun nan zuwanmu daga gidan wani malami muke neman taimako ki kaddara cewa kawai matsalanki daga yau yazo karshe kokuma kice yaƙare gaba dayama hajia balki takare magana tana sakin murmushi,cike da farin ciki basma tashga share hawayenta tana dariya miƙewa tayi tsaf daga inda take zaune taje ta rungumi hajia balki tana cewa”nagode mummy maganin kukan mu ni da mummyna dariya ita ma hajia mariya tayi dan ba abunda takeson gani aduniya sama da farin cikin ɗiyar nan tata.

nan sukaci gaba da tattauna yanda zasu gudanar da aikin su,waya hajia bilki ta dauka takira wata lamba ring ɗaya biyu aka ɗauka daga daya bangaren aka shiga cewa”da girman kujeranki hajjia saida sukayi yar wasa da dariya sannan hajja balki tashiga rattabo masa da ƙudurinta shiru tayi saikuma ta juya tana kallon mariya datayi luƙus tana kallon ta dan sonjin abunda suke tattaunawa shike nan zamu baka dubu ashirin ok shikena saida suka gama tattaunawa sannan ta kalli hajia mariya da tayi sakoto tana jiran jin yasukayi da wanda taƙiran taƙagu sugama maganan tamata bayani ganin yanda ta zaƙo hajia balki ta kashe wayan tana kallon ta tace ya yarda anjima zakuje tare ke kitsaya daga bakin ƙofa shikuma ze shiga ciki.

Zaro ido tayi waje kaman ze faɗo tashiga faɗin”amma hajia ke meyasa kika aminci masa kan zamu tare bayan kisani kuma ai ko malam cewa yayi ya amince amun kawai.

Hmmmm mariya kenan inaga baki shirya ƙwatowa ɗiyarki ƴanci ba,ca nake a gabanki malam yace wani ze iya aiwatar miki amma kina tsaya agun idan ko baki shirya ba shikenan idan nice ke wallahi ba abunda ze hanani zuwa hakade tayi ta zugata harta yarda ta bata lambar mutumin sai sannan sukai sallama ta tafi gida.

Itako hajia mariya tun tafiyan hajia balki takasa samun nutsuwar xuciya data ruhi sai safa da marwa take a haka har Alh sunusi yazo gida ta taddata haka shima dayake da tasa damuwar yazo be kula ba balle yagane sauyin dake tattare da ita yana zuwa ɗaki yashiga yace kuma kar wanda yatashesa yana bukatar hutuwane dan haka itama tata ɗakin tashiga kowace daƙiƙan daidai yake da bugun zuciyarta sha ɗaya da rabi daidai ta shirya ta fito samun sa tayi yazo yana jiranta bakin get shi yaja motan suka tafi parka motan yayi dan nesa da makabartan suka fito baysn sun kulle motar suka shiga takawa da ƙafa zuciyar hajia mariya ba abunda yake banda tsalle har suka iso bakin ƙofar maƙabartan ja tayi ta tsaya daga waje tana miƙo masa da layar saida ya karbi layan sannan ya kalle ta yace”gaskiya hajia saide fa mushiga tare idan yaso kitsaya daga ciki gardama ya balle tsakanin su dakyar de ta yarda suka shiga dan ce mata yayi wallahi muddin bazata shiga ba shima baze shigan ba saide sukoma,dole tabiyoshi suka shiga ciki tare tsorace take ciko tafiyan sa yake ba alaman tsoro ko dar saide ko tashiga ciki basuyi sosai ba hajia mariya ta taka wanj rami kasancewa damunane kuma anyi ruwan sama da rana kafarta ɗaya ya rufta ciki,take tasaki wani ƙururuwan ihu harda fitsari saida yakufce mata tana kiran”ma tattu natuba dan Allah karku riƙeni wallahi idan kuka barni yanzun nan zankoma ban shirya zama cikin ku ba layarma na hakura……wayyoooooni daga nan ta sume.

Leave a Reply

Back to top button