Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 70

Sponsored Links

CHAPTER 70

Murtsuƙe idonta tayi wai ko bata gani da kyau bane,amma still koda tasake buɗe idon haryanzun de suɗin take gani hannun su sarƙafe dana juna wani abu mai kauri daya tokare mata makoshi tahaɗiya jikake mukutt take tasoma gani duhu yana neman rufe mata ganin ta,hannun salaha dake tsaye gefenta ta damƙa da karfi harsai da salaha taɗanyi karamin ƙara”aucch ƙawata lafiya?kika damƙeni haka tayi tambayar tana idon ta na kallon inda basman take kallo.

“Kina kallon abunda nake gani kuwa?kode ido na kemun gizo kaman yanda yasoma yimun daga jiya.

Takai dubanta inda basma kenuna mata,sai kuma tasauke ɓoyayyan ajiyar zuciya ganin bataga kowa a wajen ba,tasan halin ƙawartata yanzune zata tada mata da bore tace aikin da bokan yamata beyi ba kuma su samu matsala da ita dan itake kaiwa da bokan customer’s yana ware mata kasonta yawan kudi daya samu awajen mutum itama yawan biyan da zeyi mata.

Abunda basma bata sani ba shine sanda take wa salaha magana Ahmad ya fixge hannun Aisha duk da turge masa da take ta cusata mota da khalid ya kawo wajen,suka fita.

Alhaji sunusi zaune suke da tare da Alhaji surajo suna tattauna yanda meetin din nasu ze kasance shi Alh sunusi yaso ayi zaman meetin din daren yau yayinda Alh surajo yace”gaskiya sunusi bazeyu muyi zaman meetin yau ba dan ita kanta zaman tana da dalilinta dakuma ƙa’idan ta,dan haka dolene sai an zauna a ƙungiya an tattauna batun kafin a zauna idan shugaba ya yarje mana yin hakan.

Cike da ɓacin rai Alh sunusi yamiƙe tsaye yana kallon Alh surajo rai a ɓace yake magana”ammade kasan abunda ke shirin tunƙaro mu ko?”eh nasani same?shima ya amsa masa cikin halin ko in kula.

“oh baka damatsala tunda kasan yaranmu da aka kame babu naka ƙo ɗaya acikin su sannan ba wanda yasan fuskan balle yanuna ka,shisa baka damu da damuwar tamu ba.

“Eh same ?idan nadamu da damuwar taku,a kufule Alh sunusi yace”karka dauka idan rubtawane mu kaɗai ze rubta damu a’a harda kai cikin kuwa.

Daga zaunan dayake ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon Alh sunusi daya cika yana batsewa yace”inason kasan abu guda duk rashin imanina ni surajo maci amana bane dan haka idan ma ruftawance zatazo mun da sauki tunda banci amanan kowa ba amma kai fa?yanuna Alh sunusi dake ƙame kaman andasa shi,dan haka kaje dukma abunda zakayi kayi saide kasani duk tsuntsu dayaja ruwa shi ruwa ze ja.

******
Aisha duk mutsu mutsun son kwace hannun ta da take kasawa tayi yana zurata mota khalid yaja suka tafi,matseta yayi ya kawo fuskansa daf nata harsuna iya jin numfashi junansu saboda yanda kusancin su yake numfashi mai ɗumi yafesa mata saman fuskarta hakan saiya haddasa mata rawan jiki baya tayi niyar ja amma be bata daman yin hakan ba saboda yanda ya matseta jikin kujeran motan rintse idanun ta tayi da karfi jikin ta sai ƙyarma yake take taji jikinta yaɗauki ɗumi kaman mai shirin kamuwa da zazzaɓi.

Shima anashi ɓangaren hakace ta kasance dashi wani irin kasalane yaji yasaukar masa yanda bugun ƙirjinta dayake sama da ƙasa yake gogan nasa ƙirjin take yaji wani abu ya tsargar masa tun daga tsakar kansa har zuwa babban yatsan ƙafar sa.

Kai hannun ta tayi da niyar tureshi saukan tattausan fatan hannunta kaman na jariri saman fuskar dokin wuyan hakan yasaka shi wani irin shock besan sanda ya ƙanƙameta ba.

Yana haɗiye wani abu mai wuyan haɗiya jikake mukut besan sanda yakai kansa tsakanin wuyanta yana shaƙan kamshin turarenta mai sanyi dakuma daɗi hakan sai ya haifarmusu da wata iriyar kasala yayin da bugun zuciyar su ya tsanan ta.

Hajiya mariya da hajia bilki gurfane suke gaban malamin su hajia balki tace”ranka yadaɗe malam aiki zakawa kawata ƴarta zata aurar to ranka yadade yaron ne haryanxu muka rasa gane kansa auren su saura kwanaki kawai sai gashi dawata yarinya kuma ita wannan yarinyar ƴar aikin ita amaryar da ze aurene to shine mukeson amana aiki akanta ita yarinyar ta yanda za dasa tsanarta a zuciyar shi angon adasa masa tsananta yaji duk duniya ba wacce yatsana kuma bayason gani sama da ita.

Sannan munaso shikuma ango a dasa masa soyayyar ita wanda ze aura ta kare maganan tana langwaɓe kai.

Gyara zama malamin yayi yace da hajia mariya tamatso ta ɗauki ɗaya daga cikin carbin daya ajiye,dauka tayi tamiƙa masa karɓa yayi daga hannun nata yana kallo yana jujjuya kansa”lafiya malama?hajia bilki ta tambaya ganin yanda yake jujjuya kannasa kaman wani kadangare mai jan kai yace”hajia aikin ki da sauƙi sannan da wuya.

A ruɗe suka amsa masa”kaman ya malam ka ambaci sauki da wuya lokaci ɗaya”eh sauki shine yanda ƴarki zata mallaki zuciyar mijin ta,wuyan kuma shine yarinya da kuka kawo aiki akanta a tsaye take ma’ana bbata wasa wajen yin ibada dakuma addu’a samunta baxeyi sauki a gare ku ba,har sai idan zaki iya kai laya da zan baki makabarta ki binne shi da kanki cikin dare karfe sha biyu daidai,idan kimyi hakan…..ai basu gama sauraren abunda ze faɗa musun ba hajia mariyah tabude baki murya na rawa tace”kalen inje garin binne laya suriƙeni…..ba hajia bilki da suke tare ba hatta shi kansa malamin nasu saida yaƙura mata ido yana cewa”dama wayace miki neman duniya yana da sauki haka jeki tambayi mijinki maza kutashi kubani waje yafaɗa rai aɓace yana nuna musu hanyan.

Leave a Reply

Back to top button