Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 77

Sponsored Links

CHAPTER 77

Kafin ya karasa gareta tuni ta rotsa da ƙasa ya fashe sake raruman ɗaya dake can kusurwan falon tayi ta ɗauka tasake rosashi da ƙasa,ganin abun nata na neman wuci makaɗi da rawa yasa shi takowa a hankali inda take takai hannu zata dauki plasma tv yariƙe mata hannu sannan ya zuba mata idanun sa masu rikita ta yana kallon ta,ya kai babban yatsan hannun sa ya dauke hawayen ta data kasa tsaida su cikin lower voice yace”ki a danasu za suyi miki amfani nan gaba kaɗan an kaya dakika fasa kuma ki lissafa ki a jiye dan zaki biyani ne ƙwandala ta bazeyi ciwon kai ba…yana kaiwa nan yasaki hannun nata.

Warin mugun takaici ne ya ƙumeta tama rasa me za tayi gashi kukan ma ta yi har taji ba daɗi hawayen ma yaƙi zuwa sai zafi da zuciyan ta ke mata zubewa tayi kasa jagwab a gun.

Kukan ta keson yi amma takasa ta dauki a kalla minti uku a wajen zaune sannan ta miƙe ta nufi tsaƙiyan falon inda ta tadda shi zaune saman kujera ya daura kafa ɗaya kan ɗaya yana waya hankali kwance.

Tana zuwa ta shiga cewa”ni kata shi kamai dani inda ka dauko ni”shiiiii yayi mata alama da tayi shiru yana daura ɗan yatsan sa saman bakin sa.

Ai ba tasan sanda wani hawaye masu dumi ya shiga ziraro mata saman kyakkyawar fuskarta ba,bata damu data goge ba ta shiga babbuga ƙafa irin ta yara tana kukan.

Koda ya gama wayan maida a bunsa yayi ya aje ya ƙima kallon inda take jawo basket din da fauza ta kawo yayi ya dauki a plate da cibi ya shiga zuba a bincin sa hankali kwance ganin da gaske bashi da niyar kulata ya sata wage ɗan karamin bakin ta tace”ni ka kulani,dariya ne yataso masa amma yayi kokarin danne wa dan bayason taga daman sa ta raina shi”ok yace yana maida hankalin sa kanta yaɗan waro idanun sa masu firgitata.

Turo ɗan mitsitsin bakin ta tayi tace”ni ka dena kallo na ka zura mun ido har kasa na mance abunda nake son faɗama.

Da hankali tayi maganan cike da tsiwa harga Allah ta dauka be jita bane shiko sarai ya jita yi yayi kaman beji me take cewa ba.

Sake maida kansa yayi kan a bunda ya keyi,ta dan ɗaga murya tace”ba zaka kulani ba kuma?

Ajiyar zuciya ya sauke ya maida plate din inda ya ɗauko ya maido da kallon sa ka cokan kanta yace”yarinyar nan kina bani ciwon kai ya faɗa yana kafeta da ido”ciwon zuciya ma zan baka ba nakai ba ta faɗa ƙasa ƙasa sai kuma taɗan ɗaga murya ta yanda ze jita da kyau tana cewa ni ka dena kallo na haka ɗaga giran sa ɗaya yayi alamar tambaya.

Murguɗa masa bakin tayi sai kuma tace”to ai ni fitsari nake ji,beyi tsammanin haka zata ce ba,dan haka nuna mata ƙofan ɗakin yayi da yatsa sai kuma yace”idan kin gama sai kiyi alwala kirama salloli da ba kiyi ba.

Zaro manyan dara daran idanun ta masu haske da kallon su ke haddasa masa kasala tayi tace”Allah na tuba ka yafe ni ganan wanda ya bugar dani har lokacin sallah ya wuce banyi ba,kuma wallahi sai Allah ya saka mun zalumta ta dakai kuma bazan kwana a nan ba saide kata shi kamai dani gida wallahi ko kuma in yi ta kururuwa in ce sato ni kayi,yanda take maganan kawai saiya tsurawa ɗan karamin bakin ta ido yana kallon yanda take motsasu.

“Yi kururuwan inda wanda ze ji ya kawo miki a gaji sannan ki nutsu karna sake jin bakin ki a nan idan ko ba haka ba,kinga wallahi can waje ɗakin bingo zan maida ki ku kwana dan ba zaki zauna ki hanani bacci ba,a ranta tace bingo kare yake nufi kenan ita a rayuwar ta ba a bunda take tsoro kaman kare dan tsuƙe bakin tayi.

Mukutt ta haɗiye ƴawo mai kauri a hankali cikin karyar da kai tayi kalan tausayi cikin sanyi murya tace”to i nane bayin sake nuna mata ƙofar dakin yayi da yatsan sa manuniya,har zata shiga ciki sai kuma ta ja ta tsaya tace”to da me zanyi sallan yanda tayin sai ta bashi tausayi amma ba yason nuna mata dan yanzu yana nuna tausayin sa kanta sake botsare masa za tayi kai tsaye yace ta shiga tayi alwala yanzu ze sa a kawo mata kaya.

Harta kama handle din ƙofan zata bude sai kuma ta fasa ta juya tace”wallahi nide in a gun wacan zaka karɓo mun banaso nama fasa”ai baki isa ba yanzu nan kika gama haɗani da Allah sannan ki zo kice ba zakiyi sallan ba keee bude kunnen ki da kyau ki jini kafin mubar garin nan kika sake ta damun da hankali ko sai nayi(..)sai kuma yayi shiru.

“Na shiga uku mutum yayi magana ace yayi yayi shiru a cuce shi ni wallahi bazan yarda ba ai koda can cewa anty hajia kai ni ba kalan matar da za ka aura bace ba,sannan ka zo kace auren wucin gadi ai ba’ayi dakai cewa duk inda zaka ka tafi dani ba.

Yanzu ka ɗauko ni ka zo dani wata duniyar mai kake son a cemun bayan ni ma naci bakin ba sonka nake ba,kawai kasa mutane sumun kallon ƴar iska,shiko Ahmad mamakin ta yake yanda magana baya mata wuya idan ta soma babu aya balle waƙafi saide ka jita faaa harsai ta je inda taga yayi mata.

“Mtsss ƙaramin tsaki yayi dan surutun nata ya fara gundurar sa yace to ni ɗan iska ne kinji ko?ya faɗa yana miƙewa tsaye zuwa kofan falon dan amsan sako daya bada ganin kiran da ya gani a wayan sa.

Ranta da gudu tayi dan ita duk a zaton kamata ze yi ya daka saboda ta cika shi da surutun banza duk da hakan bakin nata be mutu ba saida tace.

“Nide bance ba ta faɗa tana share kwalla daya zuba mata,ɗakin ta shiga bata tsaya kallon ya tsarin ɗakin ba da yake shine a gaban ta ba,ƙofa data gani a ciki ta buɗe ta shiga fitsari tayi tayi tsarki sannan tayi alwala tafito tana batun tada sallah ya shigo da wata leda ya aje mata ya fita yana cewa”idan kin gama ki fito ina jiran ki daga haka ya juya ya fita ita kuma jawo ledan tana duba wa hijabaine guda uku sai dogin riguna suma uku sai rigar bacci da mayukan shafawa da turare sai bra da pant,taɓe baki tayi tana ɗaukan daya daga cikin hijaban ta saka sannan ta tada sallah bayan ta shimfida sallaya.

Alh badamasi wallahi banyi tsammanin haka daga gareka ba?”daa()? be karasa a bunda yayi niyar faɗa ba yayi shiru,hakan sai ya kara fusata shi ya cigaba da cewa ai dole kayi shiru dan baka daukeni a bakin komai ba.

Shiru yayi masa kaman ba zeyi magana ba,sai kuma ya magantu da cewa”sunisu bansan a bunda kake magana a kai ba ni yanxu damuwa ta barin gida da ɗana yayi shine kaɗai damuwa ta…a furgice Alh sunusi ya ɗago yana kallon abokin nasa yace”ban gane ba,bade ahmad yabar gida ka keson cewa ba .

To idan yabar gidan ina ya je?waye kuma waze auri basma daya gudu yabar gida a na aure saura kwana uku eh ?

“Kai wannan ce damuwar ka wanda ze auri ƴarka to bara ka ji ahmad yabar gidan ne dan gujewa abun kunya…”wace irin kunya kuma kode wani abun kunya yayi ya gudu to Allah de yasa ba ciki yawa wata ba.

“Kul kul kasake dangan tamun ɗa da mugun nufi,cike da ɓacin rai ya faɗi hakan yana huci kaman kububuwa zaune yake amma besan sanda ya miƙe ya tashi tsaye ba sanda ya ji kalma da alh sunusu yake ji fan ɗan nasa da shi.

“Badamasi yau ni kake wa tsawa haka ya faɗa cike da mamakin abokin nasa yana nuna kansa dan yasan mugun ƙulli da sukai masa ko a gaba ba ze iya musasa ba balle ta kaisu ga ɗaga masa murya lalle a kwai aiki a gaban sa idan har haka ya cigaba da faruwa a tsakanin su.

Yana cikin tunani yatsinkayi muryar alh badamasi inda yake cewa”ahmad be wa ƴar kowa ciki ba,kuma ba ze yi ba ko nan gaba idan kaga ya yiwa wata ciki to ka kaddara halal din sace,ya cigaba da cewa wato sunusi sai yanzu nake da nasanin jan ka jikina da nayi.

Yau a sanidin ka na zama tamkar mujiya cikin tsuntsaye kowa guduna yake duniya tana neman juya mun hatta da yarana basu isa suje makaranta suyi karatu su dawo gida hankali kwance,ba tare da an samu wani ya goranta musu ubansu maci amanan kasa ba da alummar sa ba.

Yau ɗan da nahaifa ma gudun abun kunya da na aikata yake,ni nasan ahmad ya gujewa zaman kotu da za’ayi ne bayason ganin ba,abun kunya dana aikata ze riskane bayaso.”dakata badamasi ai sai kace…shima katse shi yayi yana cewa kaga sunusi ka tafi kawai ka tafi banson ganin ka balle jin mai ze fito daga bakin ka,kuma ko a kotune ni na daukarwa kaina alkawari ba sunan wanda zan kira balle binceke yabi ta kansa zan sauƙaƙa wa kotu dama kaina baki ɗaya kar kaji komai nasan tsoron ka kar sunan ka ya fita ko?to sunan ka ba ze fita ba,ba ma naka ba,har dana sauran yana ƙare faɗan haka ya wuce sama benin inda ɗakunan baccin su yake. a falon ya barshi tsaye yana rasa abun yi.

 

Saide a bunda basu sani ba dukka su biyun wannan musayar ƴawu da sukai kan idon Ammi sukai,ɗagowar da ze yi sai cikin na ta idon data ke tsaye bakin kofan kitchen wani irin kwarjini ta masa fiye ma da yanda take masa a baya.

******

Bayan ta idar da salloyin ta anan saman abun sallan tayi zaune ga yunwa na nuƙurƙusar ta dan rabon ta da cin wani abu ko sha tun breakfast ɗinta na safe shima ɗin ba wani abun kirki taci ba.

Tana nan zaune sai gashi ya shigo dauke da basket ɗin ɗa zun,a jiye mata yayi gaban ta,shi kuma ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ɗaure da towel ta gaban ta yazo wuce wa ya ji tane magana ƙasa ƙasa be ji me tace ba,amma ƙaramin tsaki da tayi hakan ya ankarar dashi take ko dan ta gan shi ba kayane ko me?

Har ya wuce sai kuma ya koma da baya daidai ta miƙe tana batun barin wajen sai kawai taji ta faɗa jikin mutum kyakkyawan riƙo ya mata tana kiciyar kwace wa daga rikon da ya mata ba zato ta ji saukan lips ɗinsa a nata wani irin tsotsa yake musu cike da mugun ta kaman ze cinye mata bakin.

Dama hawayen ta a kur kusa yake sa kawai suka shiga fareti saman fuskarta suna gangarowa nasa,duk da yanda take kukan ga jikinta daya dauki zafi da kuma kyarma da yayi kaman zazzaɓi na neman kamata be saketa ba saida ya tsotse mata baki ya gaji dankan sa ya sake ta,ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya.

sulalewa tayi a gun tasaki kuka mai cin rai tana taɓa bakin ta da yatsunta biyu jin yanda suka soma tasowa.

“Idan kika sake mun tsaki ko tsiwa saina cinye bakin rashin kunyar nan yace yana barin ɗakin.

Leave a Reply

Back to top button