Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 28

Sponsored Links

Chapter 28

Lumshe idanun sa yayi sannan ya budesu tarr saman fuskarta da tasha make up tayi shar da ita”fine ya amsata a gajarce yana mai miƙewa tsaye yasoma tattare kayayyakin sa mikewa tayi ita ma ganin kaman fita zeyi kuma be nuna wani ze kulata ba yasa tace”fita zakayi?
“Eh ya amsa a gajerce faɗawa tayi jikin sa tasaki kuka mai tsanani Allah yana gani tana masifar sonsa bazata rayuwa ba tare dashi ba,wani irin ƙanƙamesa tayi tana kuka irin mai cin ran nan”why ahmad?
Why meyasa kake hakane?
Me lefina dan nace kai nakeso ka kaddara ƙawarka ce ni ko wata ƴar uwarka kace ni yazakaji aranka idan wani yana mata irin yanda kake mun?
Shikenan tace tana ɗagowa daga jikinsa wallahi zan kashe kaina shikenan kaima ka huta da taƙura ta saide kasani kafin na mutun sai nabar wasiya cewa kaine silar mutuwata ta kai karshen maganarta bata bashi daman cewa da ita komai ba,tayi waje a guje tana kuka.

Jikin sa yayi sanyi sosai dan shi mutum ne mai tausayin mata Allah ya ɗaura masa tausayin su saboda raunin su,iska mai dumi ya fesar yana sake dafe kansa da yakejin yaɗauki dumi dan ya marasa wani irin tunani zeyi zumbur ya miƙe yana mai furta cewa a fili”dolene. na dakatar da wannan yarinyar da sauri yamike yafita daga office ko tsayawa rufewa beyi ba motar sa yanufa cikin sauri yashiga ya tadata da wani irin gudu yabar harabar ma’aikatan nasu dan so yake ya isa dawuri dan dakatar da ita aiwatar da wannan mummunan ƙuduri nata nason kashe kanta,yasan tafaɗa masa hakan kuma shi bega alamun wasaga maganarta ba.

Fadila fitowarta gidan su Aisha yayi daidai dashawo kwana da aisha tayi kallo kallo suka shiga yiwa junan su sai aishace ta kauda da komai takira sunan ta.
A yatsine fadilan ta juyo tana kare mata kallo daga ƙasa har sama kaman yaune ta soma ganin nata sai can ta buntsure baki tana”a’a kece dama wajenki nazo amma rashin samunki da banyi ba yasa na barmiki sallaho wajen gyatuma idan kin shiga ciki kyaji amma duk da haka bara in faɗa miki abu ɗaya kiyi hankali dan bakin rami ba wajen wasan makaho bane.
Kaman bazan tanƙa taba sai kuma naga yana da kyau tagane shirun danayi bawai na tsoro bane ba,fadila naji abunda kikace amma kinfi kowa sanin koni wacece bana haɗa uwata da duk wata shashanci dan ita ɗin duniya tace ita zan kuma iyayin komai akanta duk wani tsegarecinki ya tsaya kaina karki kuskura insake ganin ƙafarki a gidan nan harma da mamarki da bata iya riƙe girmanta ba,kaman yanda tashata layi tsakanina dake ai har yanzu ban tsallake layin ba kode bata faɗa miki tashata layin bane?
Hmmm fadila kawata ina tausaya miki irin rayuwa da kika ɗauka sannan karkiji da wai nasan komai kuma kifaɗawa daƙiƙin alhajin nan naki yabar bibiyata dan ni ba kashin dankali bace da duk wani shakatafi ze tayani a karshede ina mai gargadin ki da kitsaya iya limint ɗinki karki wuce ina ganin ƙimarku a idona karki bari yazube dan duk halin da zaki tsinci kanki ciki koda bama tare zanfi kowa shiga damuwa saboda kaunarki a gareni daga haka gida nashiga nabatta nan tsaye tana mai jin haushi da tsanata mai tsanani.

Ahmad wani iko Allah ne kawai yakai shi gidansu basma lafiya yana parkin motar sa ko tsayawa kasheta beyi ba yafito da gudu yafaɗa cikin falon gidan bakinsa dauke da sallama ihun hajiya mariyah dayaji daga saman ɗakunan yasashi sankarewa yakasa motsa koda dan yatsansa ne balle ya iya yin wani yunkuri saboda take wani irin kasala yarufesa kansa sai ɗaukan dumi yake.
Zubewa yayi agun yana ambato innalillahi sabida son daidaita kansa.

Leave a Reply

Back to top button