Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 26

Sponsored Links

Chapter 26

Raina wasai na kama gabana ko ba komai ya rabu dani dan a rayuwa banason mutum yace ze taɓamun mahaifiyata wallahi duk girman sa danake gani daga ranan da yataɓa mun Anna ta wallahi mun raba hanya dashi na fahinci ta dalilin sa fadila tazaɓi wulakantani ranan sannan mama rabi tazo har gida tayita zaginmu harda yimana gorin taimako da suke mana a baya,wallahi koda shine autan maxa daya rage a duniya bazan kulasa ba,balle ma tsohu dashi daya gama expire.

Aikina naje naci gaba dayi kusan azahar sai ga manyan ɓaki da alama ba ƴan nan kusa bane duba da yanayin su farari sol kaman larabawa dukkan su su ukun sanye suke da suit ɗaya daga cikin sune ya hau yimana vedio kowa kagani sai gyara zaman sa yake sau ɗaya na ɗago na kalle su shima haɗa ido da mukai da wani kyakkyawan cikinsu bansake gangancin ɗagowa na kalli inda suke ba,saboda yanda yamun kwarjini dakuma yanda zuciyata take dukann tara tara dan bazan iya cewa uku uku ba saboda yafi karfin hakan.
Muryan wannan mutumin naji tsaya kusa dani yana tambayata yanda na koyi ɗinkin irin wannan kaya,Ahmad ne cikin kame fuska ya fassara mun abunda mutumin yace cikin harshen hausa dayake shi wancan da turanci yayi magana,kaina a ƙasa nafara yi masa bayani ahmad na faɗa masa abunda nace ta harshen turanci shikuma sai murmushi yake yana yaba kwarewata dakuma yanda nake magana cikin nutsuwa,sake tambayata yayi cikin harshe larabci ko mantawa yayi oho,nan nashiga yi masa bayani ta larabci dan ina jin larabci sosai turanci ne de sai a hankali gaba ɗaya zubamun ido sukai suna kallona tunda basu taɓa jin ina magana da wata yare bayan hausa ba,shi ɗinma bada kowa nake magana ba,oga Ahmad kuwa rungume hannun sa yayi a kirginsa ya gyara tsayuwar sa yana mun kallon gorillah muryanane yafara rawa saboda rashin sabo da yanda kowa yake kallona.
Jeho mun da wata tambaya yayi da yasani ɗagowa na kalli fuskar sa wanda ya yalwan ta da murmushi”shin zaki iya bina garin mu?shine abunda yace dani
Kai kawai na girgiza masa alama a’a duk yanda yaso nasake yi masa magana ƙin yi nayi dan ni anawa ganin wannan tambayar tasa baya bukatar amsa.
“Ba magana ake miki ba kinyi shiru”tambayar tasa bata bukatar amsa shisa banbasa amsan ba,na faɗa kai tsaye ba tare da wannan tsoron shi danake ji ba,kodan ban dago nakalli fuskan sa bane oho,juyawa yayi naji yana cewa da mutumin suhail mutafi ko,har sun juya sun fara fita sai mutumin nan da naji oga Ahmad yake kira da suna suhail ya ciro wani card mai kyau cikin aljuhun suit ɗin jinkin sa ya ajiyamun saman kekena idan kin yanke abu ɗaya ki nemani shine kawai abunda yace ya juya bazato naga oga Ahmad ya yasa hannun sa ya dauke wannan card din ya jefa a aljuhun sa bayan ya watsamun wani kallo da saida hanjin cikina ya kaɗan saboda tsoro.

Karfe biyar muka tashi mun fito da laila da kuma shamsu inda suke ƙodani da cewa wallahi Aisha bakiga yanda kika burgeni ba da kika fara zuba larabci sai ma kinga yanda oga yake da hararanku keda wannan mutumin hmmm kawai nace dan bani da baki magani sai kuma shamsu ya amshe yana”to wai da oga ya dauke card ɗinda mutumin yabaki mai zeyi dashi?
“Shide yasani kunga bara nayi sauri na tafi dan nabar Annata tana zazzaɓi yau nakare maganar ina yin gaba na barsu a wajen.

Suhail bayan sun fita daga hall ɗin sun koma office ɗin oga Ahmad nan yake kara yabon tsarin wajen da kuma ta yanda ya wadata ma’aikatan sa da kayan aiki irin na zamani tare da zaɓan kwararro waƴanda suka san aikin su,Ahmad yaji daɗin yanda abokin kasuwancin nasa ya yabesa gyara zama suhail yayi ya fuskanci ahmad dakyau bayan ya ɗan kurɓi ruwa mai sanyi yace”gaskiya abokina wannan yarinya tamun wallahi idan zaku bani ita zan iya zuwa 9ja da zama,kallon baka da hankali ahmad ya jefasa dashi shide yasan bawai yanason yarinyar bane amma duk sanda wani yanuna yanason ta sai yaji kaman an hura masa wuta acikin zuciyarsa koda kallonta wani namiji yayi wallahi shi kaɗai yasan yanda yakeji daurewa kawai yake shisa ma jiya yayi magana da khalid kan cewa zasu canza tsarin nasu za mai da matama wajensu daban haka ma maza.
Bakace komai ba suhail yakatsa masa tunani,ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana cikin nutsuwa da nuna irin i dont care ɗin nan yace”indai kasami soyayyar ita yarinyar to ni mai nawa aciki saide kawai nabiku da addu’a murmushi suhail ɗin yayi najin daɗi daga haka yamiƙe yana ɗan duba agogon hannun sa yace”kamata muje ka rakamu airport nan da minti talatin jirginmu ze ɗaga.
Ƴar dariya khalid yayi cike da neman magana yace”kuma kace idan zamu baka mata zaka iya zama garin nan yanzu kuma kana shirin komawa ba tare da….ahmad be bari khalid ya gama maganar ba yace”kana da matsala wallahi shima suhail din kawai yafaɗi hakane dan yaji daɗin bakin sa amma barin kasarsa ya dawo nan da zama ba abune mai sauki ba.

Alhaji sunusi waya ƙange a kunne sa sai gani nayi ya zabure yamiƙe tsaye amatukar yazane yana”ina gaja bashi waya”hello oga gaja ya amsa a ɗaya bangaren”riƙe hello ɗinka ashe gaja baka da hankali kai kafi kowa sanin hatsari dake tattare da kuɓutar ishaq daga hannun mu kace na tara ƙattin banza ina ci daku baku da amfanin komai to wallahi na baku nan da awa 24 duk inda yashiga koda karkashin kasane kufito dashi sannan ku kashe shi dan…”nashiga uku alh wa za kashe muryar hajia mariyah tadaki dodon kunnen sa,katsa wayan yayi ya juya ya kalleta rai aɓace ba tare da yayi mata magana ba yayi ficewarsa waje yana sake kiran wayan duk yaransa yace su taru gayanan zuwa yanzu.
Minti goma tasada shi da tangamemen gidan gonan nasa rai a ɓace yake kallon su dukkan su majiya karfi gasu manya”aikin banza yanzu duk girman ku ace ishaq yatsare baku sani ba amma kun bani kunya mai amfani ci daku da nake”ɗaya daga cikin su yace sorry oga akasi aka samu daren jiya mun shayune da yawa shisa hakan tafaru amma zamu nemosa da yardan ka.
Fuska murtuƙe alh sunusi yayi tattaki gaban wanda yayi maganan yashaƙo wuyasan yace”banza har yanzu mayen be sakeka ba da yardan Allah zakace tuff ya tofa masa ƴawu a fuska ran wannan gayen yayi bala’in baci da abunda alh sunusi yayi masa dan haka yabude baki ciki kakkausan murya yace”ni katufa ma ƴawu alh?cikin ɓacin rai alh sunusi ya juyo gaba garesa yace”an tofa maka mezaka iyayi yafaɗa yana pointin ɗin sa da bindiga,ganin haka yasa sauran suka shiga bashi hakuri dan sun san Alh sunusi ba imanine dashi ba yanzun nan sai yakashe mutum kuma yakashe banza.
sai yanzu gaja ya motsa daga inda yake zaune tun zuwan alh sunusi wajen nasu”kashesi zakayi?
Shine kaɗai tambaya da yama Alh sunusin da mamaki alh sunusi ya ɗago yana kallon gaja fuska a murtuƙe cike da ɓacin rai mai tsanani dan kubcewar ishaq daga wajen su babban bara zanace gareshi dama rayuwar sa baki ɗaya.
Sharce gumi daya gama jiƙashi yayi yabude baki dakyar yace”amma kasan…be barshi ya karasa abunda yayi niyan faɗi ba ya ɗaga masa hannu yace”alh munan dukkan mu haihuwar mu iyaye sukai bawai mun faɗo daga sama bane,kasan muna aiki tuƙuro amma duk sanda kuskure daya tasamu mune da kuskure idan kuma nasarace takace hakan ba zeyu ba,kakawo mana kayan maye munsha to yakakeson muyi in ba bacci ba,kuskurene ya faru tun a waya mun gama magana zamu nemo sa amma kazo kana wa mutune wulakanci to kasa ranka a inuwa zamu nemo sa mukawo maka shi amma da sharadin sai ka haɗo mana da ɗanka usman cikin tawagarmu tashi hankali da basa masa rana ba jagob alh sunusi yazube gaban gaja..

Leave a Reply

Back to top button