Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 13-14

Sponsored Links

Page 🖤13••14🖤

 

 

 

_*RAYUWAR BOMBEE A BARIKIN SOJOJI*_

 

Saida Bombee tashafe kusan sati guda kafin ta warware daga shock ɗin zaman motar da tayi,dama kuma kafin sannan ta jigata da rashin cin abinci datayi a Lokacin.
Iduwanta da farin POP ɗin dakin tafara tozali,zaro ido tayi cikeda tunanin shin yau kuma wacce duniyar ta kawo kanta,kodai kai buguwar datayi a cikin motar nan ta mutu,amma kuma a kawo ta farin waje irin wannann kaman wacce take aikata daidai,yanzu haka fah da laifuka masu yawa tabaro garinsu,taya kuma zata dace da wannan rayuwar.
Duk a kanta take wannan magananun,abu daya yadawo da ita zahiri shine muryar Hajiya Zulaiha dataji,wacce takeyiwa wata yarinya mai suna Nu’aimah.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda cewa. Inaga to a cikin mafarki take idan ta farka komai zai zo daidai.
Mikewa tayi daga kwancen da take tana dafe da kanta,wanda har yanzu bai daina yimata ciwo ba.
A hankali ta zaro kafafunta daga kan gadon ta saƙƙo.
Cikin sanyin jiki take tafiya har fito falon,a nan kallo yake wajen Bombee,dan sakin baki tayi dagaske tana kallon sama,inda decoration lamp take lanƙaye a sama.
Muryar Hajiya Zulaiha taji tana ƙiran sunanta cikeda dariyar ganin abinda Bombee take,ta saki baki galala.
“Bombee kin tashine,naga kin rike kai har yanzu yana miki ciwo ne?”
Sakin kan tayi tareda ɗaga kai a hankali,jawo hannunta Hajiya Zulaiha tayi ta zauna tareda kawo mata abinci,babu bata lokaci kuwa ballanta fulako ta hau kansa kaman gareshi aka aikota.
Saida Bombee tasake sati a gidan su haidar babu wanda ya tambayeta dalilin biyosu da tayi,sosai hajiya Zulaiha ke kulada itah. Babu laifi tasake dasu sosai,musamman Haidar shida ma tasanshi,sai Nu’aimah itakuma kanwarsa,da kuma Farouq sai Nabeelah. Rayuwa suke gudanarwa mai abin sha’awa da tsari,sannan kuma ga kayan alatu komai yaji,kasancewar Gen Muhammad Bello babbane sosai a barrake na sojoji dake abuja,Aikin dayaje gembu ma na shirye shiryen ƙara masa girma ne.
Yau tunda safe Hajiya Zulaiha ke jirga jirga a kitchen itada Nu’aimah. Saboda dawowar Gen Muhammad daga Rasha,wanda yatafi kaiwa wani result ɗin case daga headquarter su wancan satin.
Haidar kuma shida Bombee suna game a falo na combat,gabaɗaya sun cika wajen da hayaniya.
Kallonsu Hajiya Zulaiha tayi daga kitchen ta jijjiga kai,dan takula Bombee akwaita dason gagara da kuma shirgi na maza,shiyasa ma tasu tazo ɗaya da Haidar,musamman da baya da abokai dama sosai,saboda rashin zaman sa a ƙasar.
Babu yadda Gen Muhammad baiyyi dashi ba akan su tafi tareda tunda a can Rasha yake karatu amma yaƙi tafiyah,ganin sannan Bombee bata tashi ba,sai kawai ya fake da cewar ai hutunnasa bai ƙare ba da saura.
Da murna Farouq suka taroshi daga waje bayan drivernsa ya ɗauko shi daga airport. Duk murnar taryarsa da suke Bombee tana kallonsu daga inda take zaune,ɗan murmushi kawai tayi tareda sha’awar ganin kansu a haɗe,abinda ta tashi tarasa tsakaninta da ƴar uwarta kenan wato shaƙuwa,tun ranar data gane cewar munafurci takeyi mata bason gaskiya ba.
Saida yaran suka gama murnar oyoyon kafin Bombee tayi masa sannu da dawowa,da fara’a ya amsa kaman ko yaushe,sai kace ba soja ba.
Bayan komai ya lafah yayi wanka ya huta aka fito cin abinci gabaɗaya,su Nu’aimah sai labarin makaranta suke masa da kuma tambayar tsarabarsu..
Magabar da baban su haidar ya jeho mata bayan gama cin abincinne yasakata cikin nazari kafin ta bada amsa.
“Maryam kin shiga motarmu kin boyimu amma har yau baki faɗamana dalilin hakan ba,munyi shuru bamu tambayeki ba saboda kada kiji babu daɗi a zamanki tareda mu,shin mai menene yasakaki barin danginki kika zabi biyomu nan?”
“Bana biyo bane domin naƙi mahaifata inason zama dakuba,nabiyokune saboda banida wani zabi dazayyi sanadiyyar fitata daga garin saiku kaɗai. Sannan kuma inada muradin mallakar ƙarfi da kuma iko,ta hakanne kaɗai zan kare kaina akan gaskiya ta,harma da innice da laifin. Wannan shine maƙasudin shigowa rayuwarku danayi,Dan Allah abban Haidar kasakani inda zan samu training na ƙarfi wanda zan yi amfani dashi wajen kare kaina da kuma rama abinda akayi min. Inason koda zan koma garina sainayi ƙarfin dana fi gaban nuna yatsa balllanta zartar min hukuncin da banida masaniya akai. Ka taimakeni da hakan koda yana nufin akwai abinda zan biya dashi”
Sauƙa Bombee tayi daga kujerar tana roƙon abban haidar a ƙasa har cikin ranta.
Hajiya Zulaiha ce ta tashi daga kan kujerarta ta ɗagata,dan shikammma yarasa mai zaice illah gyaɗa mata kai dayake cikeda alfahari da zancenta,domin haka yake son yaga mutum da zuciya.
“Karki damu yarinya naji batunki,kuma indai maganar dakika faɗa hakane tabbas zan taimakeki,nima kukana zaki sharemin lokacin da nima zan sharemiki naki,shi wannan nayi nayi dashi yaɗau fagen daga a makarantarsu,amma sai ya ɗauki fannin masu aiki da na’urah. Karki damu zanyi iya ƙoƙarina wajen taimakamiki akan cikar mafarki inshaaallah”
Godiya Bombee tafara suburbuɗawa Gen Muhammad kaman yabiya mata kyautar makkah.
Tundaga ranar Bombee taƙara sakin ranta a cikin sosai,saidai kusan ko yaushe bata gida tabi gen Muhammad barrak,dan wani Lokacin tun kafin ya isa motama ta rigashi shiga,haiƙan take shiga cikin masu training,wani Lokacin ayita mata dariyah amma baruwanta. Shima kuma gen Muhammad hakan ba ƙaramin burgeshi yake ba,dan sai ya zauna yayi ta mata zancen abinda yashafi yaƙi da sojoji kaman ya samu abokiyarsa.
Wasa wasa an ja lokaci,haidar yana shirin komawa makarantar sa ta horon sojoji tundaga matakin yarinta.
Kullum maganar sa shikenan zai koma,ita kuwa Bombee hankalin ta gabaɗaya ya karkata a zuwan barrak ɗin datakeyi,dan a ganinta wanann zuwan da take anan zata koyah.
Kaman kullum yauma tabiyo gen Muhammad itada haidar,kalle kallen wajen takeyi cikeda shauƙi,matsawa gefen haidar tayi tareda cewa.
“Naga yawancin sojoji anan gidansu yake,maiyasa ku naku yake cikin gari toh?”
“Hakan ra’ayin abbane,bayason zama cikin barrak ,inta kama ma shikaɗai yake zuwa ya zauna har yagama abinda zayyi,ummah ce take tsoron zaman nan ɗin,tun tana amarya aka taba kawo hari,to datagani shine sai tasamu trauma da zaman barrak”
“Ohh na fahimta,shiyasa idan ana zancen zuwa bata magana”
Ɗaga kai haidar yayi tareda yin murmushi daya tuno irin tsoron ummansu gameda wajen.
“Oh na manta yau anan training na harbi, da kuma faɗa,ko zamuje mugani?”
Da hanzari ya nufi wajen da ake gudanar da gwajin,dan yasan dole Bombee zata biyoshi domin ta gani.
Raba mutanen wasa akayi gida biyu,maza sune keyin na faɗa,yayinda mata kuma suke na harbi,kalar harbin akwai na Bindiga,na kwari da baka,da kuma danƙo.
Sukuma maza akwai dambe,langa da kuma Kabali.
Lokacin da su Bombee suka isa wajen anyi wasu wasannin tuntuni,dan haka basufi saura guda biyu a gamaba.
Daga langa wacce ake a lokacin, saikuma Na kwari da baka shine a ƙarshe.
Abin hari suka saitah inda aka bada alama kafin suka harba.
Ansamu ta uku da kuma ta biyu,amma sai na ɗaya mutum biyu sukazo daidai,wanda sune suka samu nasarar sakawa a zagayen da jan launi yake.
Domin sake tantancewa sai akan matsar dashi nesa fiyeda na da,nan ma kuma sai ya zamo sun sake sakawa a gida iri ɗayah.
Sake matsar dashi akayi nesa sosai,wanda hakan yasa suka tsayah kallon kallo,kowa tana tunanin ɗayar ta fara.
Alamar farawa aka basu,inda kowa ta harba,amma babu wacce nata ya isa ga kan abin,hakura akayi kan za’a raba musu kyautukan kawai daidai da daidai.
Bombee dake gefen haidar ta kalleshi tareda cewa.
“Kai ina son nagwada harbawa a inda abincan yake,kana ganin zasu barni nayi?”
Uhm alamar tunani ya tafi kafin daga bisani yace.
“Ehh toh amma jirani barina faɗawa abbbah ko zai tambayesu”
Wajen da manya ke zaune haidar ya nufah tareda yiwa abbannasu magana a kunne,Bombee daga inda take tayi shuru tana jiran taji ko shin zai amince.
Murmushi yayi tareda ɗaga kai kana ya kalli inda Bombee take,suna haɗa ido ta sumkuyar dakai cikin jin kunyah.
Tashi yayi tsaye tareda gayyato hankalin mutanen wajen kansa,dayake shine babban baƙo na wasan nan da nan aka bashi haɗin kai.
“Ku dakata haka,ƴa ta tabuƙaci a bata dama tagawada harbi,shin ina fatan hakan bazai zama matsala ba koh?”
Alƙalin wasanne ya kunna mic tareda cewa.
“Hakan bazai zama matsala ba yallabai,ina take ta shigo filin wasa,bari a matso mata da abin harin kusa”
“Ahah ku barshi inda yake,ganin nisan dakuka sakane yasata jin sha’awar gwadawa”
Shuru wajen yayi bayan sunji bayanin Gen Muhammad,kowa burinsa bai wuce yaga mai harbin ba.
Alama gen Muhammad yayiwa Bombee akan tafito,aikuwa kai a sunkuye tashiga filin kaman mutuniyar arziki,dan dama akwaita da iyah saka fuskoki kala kala.
Mai kulada wasanne wanda kuma shine coarch ɗin dake horar da harbin ya miƙomata kwari da bakar,wacce take ɗauke da kibau guda uku aciki.
Karba tayi tasaita mata riƙo a hannun.
Wani shu’umin murmushi tayi tareda cewa “An dade ba’a haɗuba” a ranta.
Zaro kibau ɗin tayi dukka ukun ta saita su akan tsirkiyar kwarin,muryar Alƙalin wasan taji yana cewa.
“Uhm guda ɗayah zaki saka a jiki ba uku ba”
“Dokace dole sai guda ɗayah,idan ba doka bace karka damu zan iyah harba dukka ukun a lokaci ɗayah,ina harba biyar ma ba iya uku ba”
Shuru yayi mata tareda bata waje badan ya yarda ba.
Karkata kanta tayi tareda lumshe idonta ɗaya domin tasamu damar saita wajen,aikuwa tana dawowa da kanta tasakesu a tare..
A tare suka sauƙa a kan alamar jan dake tsakiyar allon harin dukka su ukun..
Lokaci ɗaya kuwa wajen yaɗauki shewa,kowa na yaba bajinta da kuma ƙwarewa irin ta Bombee.
Gen Muhammad shine yafara tashi yayi tafi,kafin sauran mabiyansa ma suka farayi cikeda jin daɗin su.
Coarch ɗin da kansa ya ɗauki kyautar na ɗayan ya lanƙaya wa Bombee a wuyah,sukansu wanda suka yi wasan ta burgesu matuka.
Haka taron ya watse kowa na zancen harbin da Bombee tayi,yanda suke mamakin ita batayishi har haka ba,dan ko kaɗan bataga nisan idan suke tunani ba ita.
Suna shigowa gida haidar yafara bawa ummansu labarin abin yafaru.
Dariyah tayi tareda tayata murna amma taƙara da cewa.
“Uhm nida kitchen tashiga ta haɗa wani abincin sabon samufuri da saitafi burgeni sosai”
Matsowa inda take Bombee tayi tareda cewa.
“Karki damu ummah shikansa girkin zan baki mamaki akan sa,ba iyah wannan ba kaɗai”
“Wow mashaallah dakuwa kin burgeni sosai,mace duk inda takai da ƙwarewa kan wasu abubuwan,to a sameta ta bangaren girki ma ƴa ta,koba yanzu watarana hakan zai miki amfani a gaba ina faɗamiki”
Ɗaga kai Bombee tayi alamar taji.
Gen Muhammad dake baƙin ƙofah abin dariyah yabashi,kuma shi kansa Bombee baƙaramin burgeshi tayi ba yau ɗin,lokacin da aka juyo ana tayashi murnar samun jaruma kaamarta,cike da alfahari yake amsawa,danji yake tamkar ƴarsa ce ta cikinsa.
Wata takarda ce a hannunsa,wacce ya biya ya karba suna tahowa.
Miƙawa Bombee yayi tareda cewa.
“Ga kyautata ta musamman bisa bajintar da kika nuna a yau”
Tun kafin ta karba Haidar ya karba tareda buɗewa,takardune a ciki wanda suke ɗauke da sunan Bombee.
“Wow wow Bombee admission ne makarantar mu a Rasha Abba yabaki,kema yasaya miki form yabiya kuɗin makaranta da komai”
Zaro ido Bombee tayi jin maganar da haidar yake faɗa tamkar a mafarki yake yi mata ita,zamewa tayi kamar mutum mutumi,ta kalli wannan kana ta juya ta kalli wanann,tarasa ma shin mai zatace gameda labarin dataji,makarantar sojoji yasakata,hakan ma ba a ƙasar nan ba inda ɗansa yakeyi?
“Ƙwarai Maryam dagaskene abinda yafaɗa miki,munyi magana dama da aminina dake can wanda haidar take wajensa,nayi masa bayani akanki da kuma kuɗurinki na son cikar mafarkinki,a jiyan yagama cike ciken komai da komai na shigarki makarantar.
Dama akwai abinda zai maidani ƙasar,dan haka zamu tafi tareda a gama komai da komai kifara karatu da kuma karbar horo a can,duk da yakamata ace kinshiga tunda wuri,amma munyi musu bayanin ƙwarewarki kuma nasan zaki nuna musu hakan bazaki bamu kunya ba.
Yaraf ta zube akan gwiwoyinta akan abban tareda riƙe ƙafafunsa.
“Mezai sakani baka kunya da irin abinda kayimin abba? Ai ina mai tabbatar maka baxan taba baka kunya ba saima mamaki,Zanyi matuƙar ƙoƙarina nayi amfani da wannan damar daka bani.
Saidai gameda godiya bansan mai zancen ba akai,banida kalmomin dazasu isheni wajen godiyar. haidar Ummah ku taimakeni wajen godiyar wanann gagarumar kyauta dayayimin”
Dukkansu ɗagowa Bombee sukayi daga ƙasa,inbadan idonta ya daɗe da ƙaiƙashewa da kuka ba dayanzu ta zubar da hawaye yayi cikin kofi.
“Baki buƙatar yimin godiya maryam,ni kin wadatar dani dakika nuna ra’ayin yin aikin,saidai abu ɗaya nake so kiyimin alfarma shine……Duk da cewa muradin rankine yasaka ki yin wanann aikin,ina so ki saka muradin kare ƙasarki a farko kafin naki muradin,ta hakanne zaki zamo jarumar a ƙasarki ta gado,kuma ki zamo kariya ga rayukan al’umma.
Idan kikayi hakan kigama yimin godiya akan abinda nayimiki”
“Angama zanyi yadda kace abbah,daga yau zan ajiye muradina har sai na yiwa ƙasata aiki tukunna,na tsaida gaskiyah da kuma adalci tukunna,sannan zan tsayah na kare ƙasata da kuma rayukan al’ummata da rayuwata”
“Shikenan ku shiryah tafiya to Allah yamiki albarka”

Shiryen tafiyar su Bombee aka farayi,dan gabaɗaya gidan suka tafi,inyaso sai su dawo bayan angama komai.
Kaman yanda gen Muhammad ya faɗamata kuwa saida akayi mata gwaji wanda zai tabbatar shin zata iyah ajin da haidar yake,wato division 2C.
Duk da tasha wahala amma kuma tayi nasara,don saida tayi sati guda tana training tukunna.
Satinsu gen Muhammad biyu suka jiyo,bayan sun tabbatar babu wata matsala,kusan haidar yafi kowa murna da zuwan Bombee ɗin,wanda bai taba zato ba.
Bayan shekara Uku da zuwan Bombee Ƙasar rasha zuwanta nigeria baifi Sau uku,kowanne kuma hutun,shima dukka hutun ƙarshen shakane da ake basu. Abubuwa da dama su faru,ciki harda Nasarori data samu da a mission masu yawa da ake yawan turasu kasashe.
Ta girma kwarjini da haiba sun bayyana mata,Iduwanta sun saje da yanayin kasar,inba tayi hausa ba bazakace dama baƙar fata bace.
Tana farin jinin mutane sosai,saidai kuma kowa yasanta bata ɗaukan raini,mussaman ga waɗanda suke a ƙasanta a makarantar.
A cikin shekaru goma sha takwas tayi nasarar shiga matakin finale divition,wanda zasuyi shekara ɗaya a ciki kafin su gama.
Shikuma Haidar yagama nasa karatun wannan shekarar,saboda dama shi nasa bangaren na abinda ya shafi na’ura ne dakuma su haiking ko detecting,shiyasa dole zai koma gida ya barta.
Da farko yaso zama har sai ta gama,kuma dama Air force na yankinsu sun nemeshi yayi aiki dasu,Gen Muhammad ne ya nuna ƙin amincewarsa,kan cewar saidai su dawo gida suyi aiki a inda yake wato Abuja.
Hakanne yasa yataho barta saita gama tukunna.
Kuma dama a lokacin ma bata ƙasar sun tafi practical training a ƙasar Iraq. Wanda aka turasu duk yana cikin Exam ɗinsu.
“Wonder woman nikam zan tafi gida,abbah yacemin nakoma basai na jiraki ba”
“Dama menene najirannawa kaman wata jaririyah,Man a ɗaga hanya ayi gida kawai,saina iso nima inaga zanyi koƙarin gama aikina zuwa nan da wata shida”
“Haka ma zakice bakya kewata koh?”
“Nayi kewarka,Haleesa ce ni(Wata ƴar Lebanon ce a division ɗin su Bombee ta nace shi take so,hakanne ma yasa ta mannewa Bombee tana ce twin sister ce) dazanyi kewarka iyeee?”
“Mtsww dan Allah kibar zancennan mana,wai serious baki damu ba zan tafi na barki”
“Dama dani kazo,ina ka rigani zuwa,nayi ƙoƙari ma daya zamo iya ratan shekara guda zaka bani……kai sai anjima muna cikin sahara ga zafin rana,kayi distarcting ɗina,bakajin ƙarar bullet ne?”
“Inaji mana i know is normal ai,menene na ɗaga hankalin kece fah,Captain ta farko a School ɗin mace mai shekara goma sha takwas”
Yaƙarisa maganar yana dariyah.
“Gerrot bakada aikinyi Ka gaida su ummah,ina bata kewata danna buge mata yara wancan hutun koh”
“Ohh wannan keda ita”
Katse wayar tayi tareda yin ƙaramin murmushi tana tuno Alkhairin familyn gareta,wanda duk tsiyarta bazata manta ba.
Wanda gashi sanadiyyarsu tana shirin cika muradinta na zama jaruma,wacce zata ƙwaci kanta idan za’a zalunceta.

BAYAN WATA SHIDA

A cike filin yaye ɗaliban da ɗumbin mutane,wasu na farincikin gamawar ƴanuwansu,yayinda wasu kuma nasu ƴan uwan sun mutu a practical ɗin dasukayi.
Ƙiran sunaye ake ana basu certificate ɗinsu na shaidar zama cikakkun sojoji.
Anƙira mutane da dama wanda yawanki dukka mazane..
Ana zuwa rukunin mata itace sunanta yazo a na uku,bayan wata ƴar rashan sai kuma ƴar sudan sai ita.
Ita kaɗai tazo ta karbi nata Certificate ɗin cikin sarawa da nuna girmamawa ga manyan nasu.
Kai tsaye tana karba Dorm ɗinsu ta wuce na mata taɗauki ɗan ƙaramin akwatinta.
Daga nan kuwa tajawoshi zuwa waje.
Sa haseela suka haɗo daga gani dama ita take jira.
Gaisawa sukayi kafin tacewa Bombee. (Cikin harshen turanci)
“Maryam yana ganki ke kaɗai,bazakiyi party ko kuma irin hotuna da Familynki ba,zuwa gobe saiki tafi”
“Ahah bana buƙatar wannan abubuwan,family nama basusan da dawowata ba saina isa tukunna su ganni, Dan sunyi zaton ina cikin Masu fita ne nanda shekara guda”
“Eh haka ne,amma ainihi da sai wani wata shidan zamu fita dake,gaskiya keme sa’a ce maryam”
“Kuma jajircewa,dan saida na jajirce tukunna ba iya sa’ar ba,kinga tafiyata nan dama tunjiya nayi booking na jirgi”
“Ehh am maryam Uhm Haidar…….?”
“Ki ƙirashi idan nemansa kike kin matsu,natafi tacan tacan”
Bombee taƙarisa yimata maganar tana cikin tafiya,saida tayi nisa ta ɗagomata hannu batareda ta juyoba tafiyar kena……

Ƙarfe 2:00pm Agogon nigeria Da Niger Jirgin su Bombee ya sauƙo daga rasha,kasancewar tana cikin guda uku na rukunin mata,yasa a cikin kyautar jinjinawarta kawai tiket dama na jirgi.

Bayan ta jo fitowar daga jirgin saida ta tsayah tukunna ta shaqi iska na daƙiƙu.
Murmushi tayi tareda cewa.
“Na dawo da wacce kuma za’a fara Allah masani”
Sanye take a kayan sojoji,ko sanjawa batayiba daga inda ta aka sallameta,After long dress ta ɗora akan kayan baƙa,sai ta saka hulama baƙa akanta,mai makon Jar hularta ta uniforma.
Boot ɗin sojojine a kafar ta,wanda take tafiya kaman tana faret saboda tsabar sabo.
Ga fatar jikinta tana nan da farinta,saidai kana gani kasan bawani jin dadi ta samu sosai ba.

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button