Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 9-10

Sponsored Links

Page 🖤9••10🖤

 

 

A ranar Sayyada-tateen wuni tayi tana maida labarin abinda Bombee tayi mata,wacce a ƴan shekarunnan babu wanda yataba yi mata,ga kuma babban abin takaicin har sannan Hajiya zeenah batace komai ba,duk yadda takai ga yimata kashedin da koreta,zance ɗaya take faɗamata shine akwai dalilinta na aurota cikin gidan.
A zaune take laure tanayi mata tausa itakuma Maleekah tanayi mata fifita,duk AC dayake kaɗawa a ɗakin bai ishetaba sai an mata fifita da mahuci.
“Kai iyah yakamata ki daina wannan ɗaukar zafin da shekaru irinna ki,tunda tacemiki tanada dalilin kawota inaga akwai dalilin,kibari mana ki gani”
“Bawani dalili,ta rainani ne kawai saboda taga ƴaƴan ta sun kawo kai cikin gidannan suna rikeda komai,shima Aliyun da kaina zanje na sameshi,akan me zai dunga barinta tanayin yanda taga dama a gidannan,idan nayi magana dukku haɗu ku rufemin baki kuga munafukai masu uwa koh,to bazan bar wannan ya wuce ba,dole zata bar gidannan,bari ayi meeting nan da wani satin zan saka a zartar da hukuncin korarta tunda ta kalli tsabar idona tayi min tujara,…….hmmm harda shigomana da shege cikin gida,kaman tasamu gidan gala a agege”
Dariyar da Maleekah take rikewa ce tasamu damar ƙwacewa,aikuwa kaman Sayyada-tateen neman inda zata huce takeyi,duka dakaiwa Maleekah a baya timm,wanda hakan yasaka ta sakin nishi tace.
“Kai iyha naga bani nakar zomonba,wlh tafiyata zanyi na barki,tunda nazo ina miki dannar fushin ma baki ganiba,mun bata dake nayi fushi,zanga mai yimiki kunun turawan idan dare yayi ai”
Tashi Maleekah tayi tabar ɗakin tana cuna baki.
Zaki Sayyada-tateen ta malmala mata,da alama sun bata ɗin,laifin uwarta ya shafeta itama.
“Ke kaure barmin kafar nan haka,tashi kibani waje zan kwanta,wannan mutanen gidan na kula so suke su kashe ni dan kwanana bai ƙare ba,Haba har ina matsala daga wannnan sai wannan? Ohh ni mairamu Sayyada”
Fadawa tayi kan laullausar katifarta mai kamada ta jarirai,ita kaɗai a hankali tana magana.

Madeenah ce zaune a garden tana duba abinda da aka ce takai na defence ɗinsu,dan dama rukuni rukuni akayi,sai yanxu nasu yazo,hankalin ta gabaɗaya ya tafi kan abinda zata faɗa idan lokaci yayi..
Jitayi kaman a sama an fixge takardar datake hannunta.
Dagowa tayi suka haɗa ido da Jawaheer,wacce tasha riga da wando irin falazo ɗinnan pink,sai mayfi karami data naɗe iyah kanta dashi,dan kyau kam tayi kyau,ko mahassadi zai yaba mata,saidai gabaɗaya yanda akayi shigarne indai tanada mai ƙwaba bazata fito da ita ba.
Ƙare mata kallo Madeenah tayi tarda cewa, wai hakan ƴar hausawa ce,Allah dai ya shiryah. A ranta.
Miye kike kallona kinga ajin dayafi naki koh,saura ma shigowata cikin gidanku matsayin matar yayanki,shine wancan lokacin har jimin ciwo koh,saboda kiyimin lahani kina baƙincikin haskawa ta,to ta Allah bataki ba Jawaheer tana nan ƙalau”
Ƴar dariyar rainin hankali Madeenah tayi tareda cewa.
“Hhhh matar yaya manya,kai da alama matan yayan dayawa,indao wannan matar tasa ce dana gani da safe,bazaki kai labari ba a hannunta,bismillah ka wajennan”
“Yeheyeh kullum zancenta kadai ake ji,to waye yafaɗamiki ina jin tsoronta,wanann lokacin da shirina zan tunkare ta,bazan taba bari ta mallake shi ita kadai ba,sonsa a jinina yake gudu,babu jada baya kijira kiga,ina gama school nanda 6 month zakusha mamaki”
“Ohh wai Lubnah kike zance ne yanzu,hala dai mai ɗaure miki gindin batasan cewar Masoyinnaki yayi sabuwar amarya ba koh,ai yau ma tatare da safe,ke kiji wata zazzafar soyayya dan allah”
Wani zare ido Jawaheer tayi tareda zare karamin glass ɗin dake idonta.
“Whatt mai kike cewa aure,no no badai my JJ ba,bazai sake wani aurenba saini,itama tsohuwar matarsa fita zatayi ballanta kuma wata tashigo”
“Zancen kikeso kiyita ji,wai ance da gwauro ya iyali,zaikije kiyi zazzafan bincike kiga shin har kin isama nayi miki ƙarya a munzalinki”
Fizge takardunta tayi a hannun Jawaheer din,wacce gabaɗaya ilahirin jikinta ke zuba rawa.
Juyawa tayi ta nufi hanyar barin garden ɗin,har tana tuntube a hanya da dogon takalminta mai tsini,wani kallo Madeenah tabita dashi tareda cewa.
“Wahallalliya” a hankali.
Ikon Allah ne kaɗai zaikai Jawaheer inda ta nufah lafiya.

** ** **

A zaune take a kan kujera guda ɗaya dake jagaye a falon,waya ce a hannunta tana magana,daga yanda takeyi mutum zai gane da masu harkar kasuwanci takeyi.
Dariyah take darewa dashi,tareda jijjiga manya manyan sawunta masu kama da tuke. Da alama wayar tanayi mata daɗi,ta samu riba a kasuwanci.
Ƙarar fashewar abun glass taji a gefenta,tana waiwayawa tayi arba da Jawaheer tana fasa tambulan ɗin da akayi ado dasu a bakin shigowa falon.
Tashi Hajiya rabi tayi da hanzari ta nufeta,ganin ƴar tata tana koƙarin yiwa kanta illah,riketa tayi tareda duba hannayenta wanda tasamu ƴan yankuwa a jiki.
“Ke Jawaheer mai yafaru haka”
Shuru Jawaheer tayi tana wani fisfigewa kamar ƴar yaye.
“Bakyajine kiyimin magana mai yake faruwa da har zaisakaki yiwa kanki illah haka”
“Mom kibarni ki ƙyaleni shin kinsan abinda najiyo kuwa,wai wai………”
Sake fashewa tayi dawani kukan batareda ta ƙarisa ba,saida Hajiya rabi tayi da kyar kafin ta cigaba da bayanin.
“Mom kinaji wai Jabeer aure yayi yau ma amaryar tazo gidan”
“Me aure kuma wanne iri,kai haba haba duk wanda ya shaida miki wannan zancen yayi ne domin yasakaki jin haushi”
“Wlh mom da gaske nakeyi,Madeenah ce fah tafaɗamin yanzu a makaranta,ko ajin ma banshiga ba na dawo,ni wlh mom kisan yadda zakiyi,ni shi nakeso na aura mom in bakiso na mutu da ciwon sonsa to kiyi wani abu akai”.
Kama hannunta tayi daga tsayen ta zaunar da itah,har sannan tunda ta kama kasan bakinta batace komai,jan ajiyar zuciya tayi tareda shafa kan Jawaheer.
“Tabb lallai hajiyah Zeenah tayimin abinda ban tsammata ba daga gareta,aure?? Yo yaushe ma hakan ta faru bansani ba ina zaune. Yi shuru autana haka kinga duk kin yanke hannunki jini yana zuba,ko asibiti kai zamuje……”
Jijjiga kai Jawaheer tayi fuskarnna shabe shabe da hawaye.
“Ni bazan je ba,mom kefah kika ce Nice matarsa,yanzu kuma gashi can ya auri wata matar bayan waccar,ni nagaji da jiran dakuke cewa nayi,ina gama makaranta zaki auran shi”
Tana maganar ne tana sake matso wani hawayen,wanda hakan yake sake ruɗar da hajiyah rabi.
“Kinga jeki ɗaki maza ki gyara fuskarki kizo muje asibiti a gyara miki hannun,ta can sai mu wuce gidan Hajiya zeenatun,dan ƙiran wayama bazai yi ba dole sai naje,amma kafin sanann barina ƙirata naji shin dagaskene. Maza jeki shiryah,wannan abinda kika fasaɗin kuma masu aiki suzo su fita dasu,ki kwantar da hankalin ki autanah”
Tashi tayi dasauri ta nufi dakinta,musamman da taji har gidan zasuje.
Barinta wajenne itakuma ta samu damar ƙiran Hajiya zeenatu.
Ƙiran Hajiya rabi taga ya shigo wayarta bayan shigowarta ɗakin ta dawo daga Aliyu.
Tana ɗagawa tun kafin ma sallama tajiyo muryar Hajiya rabi cike da magana a bakin.
“Hajiya zeenah mai nakeji ne haka yarinyah tazo tana shaidamin wai Jabeer yayi aure,dagaskene ko ahah”
“Eh dagaskene hajiya rabi,amma ba yadda kike zato ba,shima duk yana cikin plan ne,inaga konayi maganar waya bazaki fahimta ba”
“Ahh menene na damuwa ga mota cikeda mai,Jawaheer taji labarin a makaranta wajen Madeenah,tadawomin gida harda yanka hannu,bari idan na kaita asibiti aka duba hannun zamu shigo. Dole kan zanso jin mai zaifaru,sannan ya akayi kika yi komai banma sani ba”
“Hajiya rabi dakin bar dukkan maganar nan saikinzo ɗin,hakan danayi nayine domin ƙarin nasarar aurensa da Jawaheer”
Daga haka suka kashe wayar akan komai sai an haɗu a tattauna.

** ** **

Ganin sun tafi kuma basuda niyyar ɗaukar kuɗin da suka ajiyene yasaka saka hannu ta daukesu,fitowa tayi daga ɗakin ta nufi inda inna mairo ke har haɗa mata wanke wanken dazatayi kafin ta fito daga wajen gaisawa dasu Jabeer ɗin.
Mika mata kuɗin tayi tareda cewa.
“Inna gashi suka ajiye a ɗakin baffah,nace musu ma su barshi amma saida suka ajiye”
Ɗagowa inna mairo tayi daga sunkuyen tareda amsar damin kuɗin.
Ɗan murmushi tayi tareda cewa.
“Ayyah yaran kirki harda wahala haka,bari a ajewa baffanku,ya fita sun fita ai tare dasho,anya kuwa iyah bugewar hatsarin ce Jaleelah”
Tafaɗa tana kallon Jaleelah cikin sigar zolayah,.
Murmushi tayi tareda jawo gyalenta tashige ɗaki da gudu.
Tana shiga kan katifarta ta faɗa tareda sakin murmushi,wayarta ta ɗakko a gefen katifar ƙaramar nokia,sunan Fareeda ta dannawa ƙira.
Daga can ɗaya barin aka farayin magana..
“Yadai hafeeza Jalee kewata kike hakane bazaki bari muje makaranta ba,yah mai yafaru nasan inaga akwai batu”
“Uhmm wannan wanda ya kaɗeni ne yazo gaisheni yanzu,sunansa Jabeer bakiga ba yanada kirki sosai”
“Lahh farkon sunan ku ma ɗaya,To amma ke mai zakiyi dashi,ko kinfaɗa soyayyarsa kai?”
Fareeda ta faɗa cikeda mamaki
Shurun da Jaleelah tayi batace komai ba yasata tabbatarwa maganarta gaskiya ce kenan.
“Kibari zamuyi maganar kawai a hanya,koma wanne hukunci na yanke zakiji,amma mu baridai sai yasake zuwa kuma yazo da zancen tukunna”
“Uhm uhm Jaleelah karfah ki cuci ɗan mutane,maza nawa kika ƙi amincewa dasu”
“Ehh to saina amince da kowa koh,kekam ki zuba ido ki gani mana”
(Toh idan ana ustaxiyah da smiling ga ustaziyah da loving).
Sauƙe wayar tayi tareda kallon window na tsawon lokaci.
“Kai Madeenah koh,shine wato taje tasau baki tafaɗamata komai,gashi ban shirya sanarda hajiyah rabi abinda na shirya ba sam,yanzu babu yadda zatayi illah ta tunkareta suyi maganar kawai”

Tsakanin wayar tasu ba’a dadeba taji tsayuwar motarsu a bakin sashenta..labulen ɗakin ta ɗaga tana kallon su,daidai lokacin da Hajiya rabi ta fito tareda matsawa inda Jawaheer take tsaye,sai wani narai narai take da fuska. Kama hannunta Hajiya rabi tayi tana yimata sannu suka shigo.
Maida labulen tayi ta mayar,ita kanta tasan abinda haniya rabi takeyiwa yar ta baya dacewa,sannan batayi kama da matar dazakayi fatan da haifamaka jika ba.
Saidai muradinta shi ya dushe daka waɗannan kurakan tunda da farko. Kasantuwar alƙawarin da hajiya rabi tayi mata tun lokacin da aka haifin Jawaheer,kan cewar idan har Jabeer ya aureta,toh itakuma zata haɗe companynta na Royal fabric da Jaan Company su zama abu guda,wannan nasara da Hajiya zeenah tagano shiya rufe mata ido tasaka ganin duk wani abu da hajiya rabi zata aikata.
Yayinda itama a bangare ɗaya akwai dalilinta nayin hakan,tayi bincike da gano cewar Lubnah bata haihuwa,idan ta aurawa Jabeer ƴarta ta haɗe compnynsu,tasan sai bunƙasa fiyeda yanzu,kuma in ƴar ta haihu a gidan,tunda sune dalilin bunƙasar dole jikokinta ne zasu kulada komai a companyn,shiyasa lokacin da hafsa ta mutu itada yaronta har cikin ranta taji daɗin hakan,nunawa ne kawai batayi ba a fili.
Sallama tayi a falon farko,Hajiya zeenah na jinta tafita taryota,tun a bakin ƙofar bayan gaisuwa suka fara maganar datayi maƙasudin haɗuwar su a wajen.
“Mainnkeji haka ni Hajiya rabi daga wajenki,kaddai tun ba’aje ko inba shikenan kin ruguza abinda muka daɗe muna shiryawa a tsakanin yarannan?”
“Kibari kuje ciki,koma mai ake ciki duk zakiji,ba yanda kike zato bane Hajiya rabi”
Zama sukayi Hajiya zeenah ta bata labarin abinda ya faru tunda ga farko har ƙarshe,harma da matsayin auren da komai da komai.
Ajiyar zuciya Hajiya rabi ta sauƙe tareda faɗin
“Yawwa yanzu naji batu,amma cewarta na shekara ɗaya zata aureshi bai tasoba,wata shidan dakikace shi za’ai,ta gaggauta fitar mana da matarsa itama kuma tafita,tunma kafin ayi aurensu da Jawaheer ɗin,tunda itama nanda wata shida zatayi graduate”
“Ehh to yanda kika ce,amma bakya ganin idan aka faɗamata bazatayi shekara ba kada ta fasayin aikin,dan nikaɗai nasan wahalar dana sha kafin ta amince,yarinyar batada sauƙi ko kaɗan fah,bakiji fah labarin yanda suke da iyayenta bane”
“Kai rashin daɗina dake tsoro wani lokacin,kinason yin abu wani lokacin kina tsoro,ninasan zaman dakene yasa ma har kika iya kawota. Yanzu dai ki bari basai kin kawota ba,saidai kiyi ƙoƙarin faɗamata a dabara cewar tafara miki maganin kishiyarta da wuri,idan muka samu tagama da ita ko baikai wata shidan ba sai muce aikinta yaƙare kenan”
“Ehh to Hajiya rabi kin kawo shawara,kai tun safe kaina yake kulle,sai yanzu yafara suncewa,bari zan ƙirashi da daddare nayi masa bayanin matsayin auren danayi masa,dan baisan da zance ba tukunna,itama kuma zan faɗamata aikin da nakeso tafara min.
Amma bayan ni dake dakuma masu aikina amintattu babu wanda yasan da matsayin auren,kinaga mu sanar dashi domin karma yakai hankalin sa garets?”
“Ahhh haba haba Hajiya zeenah yaushe zaki fara wannna aikin,idan kuma matarsa ta tambayeshi matsayinta fah,munfiso kada kowa yasan yarinyar mai tafiyace wani lokacin,tahaka ne kawai zamu samu Lubnah taɗau zafi da itah sosai.
Amma idan tasan tafiya zatayi dariyama zatayi mana,kibar zancen iya mu sai mutanenki da mutanen,sannan ki shaida mata bakyaso kowa yasan matsayinta a gidannan,ta hakanne zamu samu komai ya tafi yadda muka tsara”
Shawarwarinsu suka cigaba dayi,duk akan yanayin yanda abubuwan zasu tafi musu ne.
A bangaren Jawaheer kuwa da suka barta a falo,maimaikon ta yi sashen su Maleekah,sai ta nufi lambun gidan,wanda yake a gefen new side na Jabeer.
Bata ɗauki mota ba takawa tayi a kafa tana kalle kalle har ta iso wajen sashen.
Har zata shige cikin lambun sai kuma tagano wulagawar mutum ta windown kitchen ɗin side din dake kusada da itah.
Mamaki abin yabata,dan duk zuwan ta gidan tasan ba mutum a bangaren,takawa take a hankali ta nufi sashen domin ganin waye a ciki.
Ƙwararrawar bakin ƙofar ta danna,kaman da minti ɗayah taji an buɗe bakin ƙofar.
Hilyaan ce ta buɗe mata ƙofar tana yi mata kallon mamaki kaman yanda itama takeyi mata,dan bata ganta a cikin yaran gidan ba,sannan a binciken da sukayi babu mai irin fuskarta.
Cikin ɗaure kai Hilyaan ta tambayeta.
“Shin……kozan iya sanin wacece ke,sannan kuma wa kike nema?”
“Sister ke zan tambaya wacece ke,yaushe kika shiga nan wajen,domin da babu kowa a ciki”
“Ikon Allah don da babu kowa a ciki sai akan ce yanzu za’a rasa wasu a ciki,matar wajence a ciki mana,dama ba domin a zauna akayi shi ba,to miyasa zai cigaba da zama haka bayan mai wajen tazo”
Daga yanda Hilyaan ta bawa Jawaheer amsa,lokaci ɗaya tagano wato itace amaryar da aka kawo kenan,wani kallon kanne ido Jawaheer tayi mata mai cikeda raini kana ta ɗora da cewar.
“Ko kece amaryar danaji labari ankawo gidan,to indan kinzo gidannanne kinga an baki nan side din kike wannan ƙafafar,da sannu zaki tattara bijenki ki bar gidannan,domin akan shanyar wata kika ɗora taki,ke in taƙaice miki ba iya shanyar ba,shikansa filin na wani ne.
Ɗan murmushi Hilyaan tayi,dan sai yanzu ta tuno akwai hoton ta a wanda aka turo musu,itace Jawaheer wacce za’a haɗasu aure da Jabeer.
“Kinga ki tattare kayanki ki cigaba da riƙewa,domin basu tsinke a gindin kaba ba,amma idan kina ganin zasu miki wahalar rikewa,to ga can kabar a ciki jeki kwance mata su”
Hilyaan tana karisa faɗin haka ta shige ciki batareda ta rufe ƙofar ba,saboda Jawaheer zatayi ra’ayin shigowa,aikuwa yanda tayi tunani ta shigo ɗin.
Bombee na zaune tana ta plan ɗin yanda aikin dazata gabatar a garin zai kasance.
Rigace a jikinta t-shirt pink,sai blue rabin wando itah gwiwa,santala santalan ƙwanjinta suna waje,wanda suka sha gyara da kuma hutu.
Headphone ne a kunnen,wanda ta ɗorashi akan gashinta da ko parkin batayi masa yana kafaɗarta,kana ganinta bazakace ba mutanen yamma bace,saidai gashinta ne da girarta su baƙaƙene ba ja irinnasu ba.
Gabaɗaya duk abinda Hilyaan take da Jawaheer batasani ba sam. Saidai Hilyaan ta ɗauki wayarta ta kashe abinda take ji tukunna. Ɗagowa tayi tambayarta dalilin kashewar,a nanne idonta ya sauƙa kan Jawaheer wanda itama take kallonta da ido a zare,da Alama idonta ne yasakata yin hakan,itama Bombee ta kulada hakan,saidai abube daya zamema jiki ai.
Wani kumbure kumbure ta fara da zare ido tana ƙarewa wajen kallo.Kana ganin fuskarta kaga jinin tsiwa da rashin kwaba.
Tsayawa sukayi suna kallonta batareda sunce komai ba,itama ganin basu tanka mata ba kaman yanda tayi zato yasata zama akan kujerar dake kusada ita.
Kallon Bombee tayi cikeda raini tace.
“Ohhh kece ma’aikaciyar da aka kawo tayimin aikin waccar matar?”
(Tana cikin tafiyah zuwa wajen hajiya rabi tayi mata text ta shaida mata kan cewar ta kwantar da hankalin ta,ba an kawo Bombee bane domin Jabeer yana sonta,sai dan takori Lubnah itakuma ta aureta,amma basu faɗamata auren yarjejenya bane)
Kallon mai kike nufi Bombee tayi mata kafin taja ajiyar zuciya”
“Inna fahimci mai kike kinaso ne kice,kece amaryar masoyina,wacce aka kawo tafitar da tsohuwar matarsa,wacce ta takuramasa nikuma matsoraciya ce bazan iya ba,daga baya kuma bayan ta tafi dan rashin kunya sai naxo ina cewa ina sonsa”
Bombee tayi maganar cikeda maida mata magana,kana ta ƙara da yin murmushi a ƙarshe.
Aikuwa kaman yanda tayi tunani Jawaheer taji haushin maganar sosai,dan lokaci ɗaya ta hassala tafara magana cikin baƙincikin data shaƙeshi a makaranta dasafe bata samu damar amayar dashi ba dukka.
“Hmmm ke kinsan kuwa wacece ni,wlh banda aiki ne yakawoki da kin isa ko hanya ma ki haɗa dani,kuma bar cika baki kina wani cewa ke amaryarsa ce kina wani taƙamada kyan fatarki,wannan jikin babu tasirin dazayyi akan JJ ,keda banza duk ɗayane a wajensa”
Tana maganar ne tana nuna Bombee dayatsa,carfah kuwa takama yatsan tayi shuru.
Hakan datayi ne yasaka bakin Jawaheer mutuwa tana zazzare ido cikeda tsoro,musamman ganin yanda Bombee tahade fuska babu alamar wasa.
“Inda wanda kike magana akansa yana sonki da bazayyi aure har guda uku ba yana barinki,sannan zuwankin nanɗin yatabbatar kina cikeda jin haushin kasancewata matarsa… To ki buɗe kunnuwanki kiji da kyau,ba ayimin ɗaya na bari babu ɗaukar mataki,ko mata ɗari masoyinki ya aura idan ana aure,kedashi dasu baku isheni kallo ba,amma kaff cikinku har matar tasa wacce tayimin kan kara zanyi mata na itace,wannan sunnah tace hakan.
Kema zan barki ne danna farko kikayi,kuma batake nake,ki bari idan so kike ki tanka ki shigo gidan matsayin matarsa tukunna,amma yanzu nafiki iko da gidannan,ke ko karan gidannan ma yafimin daraja dake,bare kuma masu aiki ko mutanen gidan. Ki bacemin dagani yanzu kinada hayaniya zaki tayarmin ɗa daga bacci,aikin banza ku mata bakuda aiki sai faɗa da hayagaga akan maza kaman wasu kaji.
Ƙarisa maganar tayi tareda sakin yatsan Jawaheer kana taja guntun tsaki..
Maida hankalin ta gabadaya kan abinda takeyi,ko kallo na biyu batasake bin Jawaheer dashi ba lokacin datake barin falon.

 

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

___****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button