Cinikin Rai Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 5

Sponsored Links

005
“Kai Shu’iba ka rufawa kanka asiri, ko a tashe ka da nakiya. Ko kuma a turo yan bindiga dad’i su alburushe ka.” har ga Allah maganar tayiwa Lalla Salmah zafi. “Shi yasa baku rabuwa da abin kunya a kowacce magazine ba. Ai gara Malik ya tsare kansa da dukiyarsa ce,ba mutumin banza ba ne.” Tana gama fadar haka ta mike zata bar kwaryar Majalisar. “Ya tabbata dai yan PKO party basu da abin faɗa, tunda karen farautar da suke karewa ta kusan kare mishi. Shugaban majalisa a tsige Malik Menk Jordan kawai.”

Shiru tayi sannan ta cewa shugaban majalisar koli. “Yallabai kafin ka yankep hukunci ka fara nazari, idan kace zaka biyewa yan amshin shata zasu kaika su baro ka, su basu da nasu sai na wasu. Kullum ra’ayin wasu ke yawo a kansu banbancin uban nan gidansu da Ubangidan mu kenan.” daga haka ta fita ta bar kwaryan majalisar koli da hayagaga.

Tana fita ana mika mata wayarta, amsa tayi tana faɗin. “Elbashir ina ka shiga ka bar ni sa tashin hankali? Kasan abin da ya faru kowa?” amsa maganar yayi da cewa. _Ina sane, sai dai Malik ya hana ni dawowa ne, ya ce nayi fucus din matsalar gaba na, amma please ki tuntubi Mr Shatima, a madadina ya je ofishin jam’iyyar PKO yayi magana akwai lauya malik._

“Shi kenan, zan tabbatar haka ya faru.” ta fada tana me kashe wayar. Tasan dole yau ta isa Keivroto city kome dare tunda har Malik ya iya hana Elbashir Jamal Arab dawowa tow wannan shi ne lokacin da ya dace tayi kokarin ganin ta shigar da bukatarta. Sai dai izuwa yanzu take da damar shiga ga Malik ko dan Maidah tunda an soke zancen Nadra Shatima. Dama tun can ta tsani yarinyar sai kuma aka yi rashin dace Malik yayi rejected ɗin bukatar Shatima. Domin bata mantawa a lokacin yan mata dayawa sunso shi. Haka ko Wahiba da Wahida, basu amshi Nadrah ba. Shi kuma Malik yana tafiyar da rayuwarsa ne daidai da fahimtar Yaran. Bayan abin da zai tab’a ran su, shi yasa ya dauke su a garin Keivroto ya mai da su demark su yi karatu. Da wannan damar itama take amfani idan zata taso Gista ta tura mishi Maidah. Sai dai wani lokaci bata jin wani gamsashhen bayanin sun hadu ko basu hadu ba, ba kamar duk lokacin da Nadrah taje ba, tana samun ganinsa. Ko last year kafin Mr Shatima ya mai da Maidah Demark wurin su Wahiba da Wahida, Malik da kansa ya bashi Shawaran ya mai da ita wurinsu, sannan ya dauka rashin aurensu daga Allah ne, don baya son haka ya tab’a relationship ɗinsu. Koda yake taji a bakin Mr Khamis Shatima ne da bai da sirri, bai san itama burinta ta tura yarta ga Malik din ba ne. Murmushi tayi, izuwa yanzu ta koyarwa Yarta duk abin da zata kama zuciyar namiji, imma ta koya mata yadda zata iya daukar kowanni abu daga namiji, imma ya kama da affairs ne da namiji ta yarda, amma bata son yarta tayi mu’amala da wani namijin domin tana bukatar yadda yarinyar zata kama Malik. Tow amma me yasa Malik yaki auren Nadrah Khamis Shatima? Domin tasan kuma yarinyar tafi yarta kyau, nagarta da son jama’a. Banbancin ta da Maidah koda yake ai Barewa bata gudu danta yayi rarrafe, halinta halin Yarta. Koma mene ne ohon musu kanta ta sani, ba wasu ba yarta ta samu shiga ga Malik ko nawa zata barar zata san yadda zata cusa yarta ga Malik. Koda kuwa zata kama da bin malamai da bokaye ne sai sun mallake shi.
**
A cikin abun da bai wuce sati daya ba, aka d’aga curfew inda aka bar kowa, dakin Ammyn Abbas ta nufa, tana me shiru. D’ago kai Ammyn Abbas tayi tana murmushi. “Zainaba” a hankali ta iso gabanta tare da riko hannunta. “Gaya min akwai da wani abu ne?” kansa a sunkuye ta ce mata. “Ammyn aikin da na samu, sun ce min lallai dole sai dai na zama me gayyato musu mutanen da zasu saka hannun jari a kamfaninsu. Kaina ya kunce ban saba ba, ban iya mu’amala da.” murmushi tayi tana me zaunar da ita ta ce mata. “Inji waye ya ce ba zaki iya ba? Zaki iya mana, kika iya daukar na wasu ma balle naki, Allah ya sa’a.” “Ina son tsoro ne kar a samu matsala, na ga sun addabe ni da lallai na fara aikin ne, shi yasa na fara jin kamar akwai wata manufa a kasa.”
“Ki yarda a ranki zaki iya, sannan ki saka nutsuwa a ajiye jagaliyancin nan, ki fuskanci reality dinki, da yau Alhaji Badaru Daniyal yana raye kina nufin zai barki ne a haka? Shi ya so ya inganta Miki rayuwar ne, bai da burin ki rike wuka ko gatari.”

D’ago kai tayi Idanunta sun yi jajjur, har wani kyali suke, alamar ta tuna wani abin da ya shafe ta, kasa tayi da kanta tana faɗin. “Ba laifina ba ne, ayayinda ake tunanin mika ni ga gidan Marayu, shi yayi adopt dina a matsayin second child dinsa, ya tafi ya bar min abu biyu masu daraja. Ammyn don Allah bani da wani abin da ya shafi past dina ne, ina son sani wace ce ni?”
Girgiza kai tayi, sannan ta ce mata. “Bayan takardun da na baki, babu wani abu da na sani game dake, shima Alhaji bai san kome ba, sai abin da aka baki.”
“Shi kenan na gode ma haka, ba mamaki Allah ya turo ni rayuwarku ne, shi yasa na kare nan. Amma ina ji a raina kamar ina da wata rayuwar.”
“Allah ya sa.” Ammyn Abbas ta fada, tana me dauke kanta daga Zeenobia din, har tafi daga dakin.
Bin tayi da idanu, tabbas bata yi hankali da zata gaya mata kome ba, bata samu nutsuwar da zata gaya mata daga wacce duniyar take ba, amma bari tayi digging kad’an daga cikin rayuwarta da abin da suka sani.
***
Zeenobia
_Past_
Alhaji Muhammad Nasr Hadejia, Dan asalin garin Hadeja ne na Jigawar Nigeria, bahaushe ne, da kasuwanci ta shigo da shi garin Fisto kasancewar garin da yake tsubirin lord island, kasancewar gari me dauke da manya manyan duwatsu, halo dai hade yake da ruwa me kyau. Garin Fisto yana daga cikin jahohin Gista da ake yawon shakatawa da bude idanu, sai dai wani abu daya da yake maida garin baya shine kabilanci. Kabilanci yayi tasiri da garin, musamman yadda har turawa suna zuwa yawon buɗe ido.

Kasancewar kasuwanci ya kawo Muhammad Nasr Hadejia, kuma abin burgewa yana da ilimin addini da na boko, wanda yasa shi kallon garin a matsayin garin da za a cigaba sosai. Sai dai wani abu biyu da ya dakushe garin. Kabilanci da zalunci, haka yasa shi fara binciken da bibiyar hukumomin haraji na garin Fisto, Allah ya bashi sa’a zuwan farko ya hadu da Aswad Yamini. Shima dan kasuwa ne, a’a Balarabe daga kasar Yemen. Shima mutum ne mai matukar son kasuwanci da cigaba. Don haka a tare suka yi decided yadda zasu gini bakin tsibirin. Yadda zai bada abin da ake bukata, domin ginin zai kasance a cikin ruwa ne, kamar yadda bora-bora island yake. Wannan shine kudirinsu. A lokacin Alhaji Muhammad Nasr Hadejia yana da matar shi har da Yaransa biyu mata, a garin su Hadeja. Sai dai bai yarda ya kawo su. Aswad Yamini yana da matarsa da dansa daya a garin domin a tare suka zo Fisto.

*Present*
Police headquarters.
“Har yau babu wani shaidan dan da za a iya kama Malik shi, abin da na sani mu jami’an tsaro, zamu yi tafiya kafada da kafada, da hukumar binciken farin kaya. A duk lokacin da sahihan shaidu suka samu a cikin tabbatar an kama Malik tare da gurfanar da shi a gaban kuliya. Na gama magana.”
“Ok sir!” bakidaya an sandan suka amsa, sannan kowa ya mike tare da shugaban yan sanda bakiɗaya. Suna fita yan jarida suka nufe su. “AIG wai da gaske ne kuna yiwa Malik aiki.?” inji wani dan jarida. Shiru yayi kafin ya bada amsa wani gidan jaridar ta kuma wurga mishi tambayar. “shin yau babu tabbacin Malik zai fuskanci kotu kenan? Shin Malik yana da ikon juya kowanni bangare na siyasa kenan?” duk da ba a bashi izinin yayi magana ba, amma dole ya gayawa duniya cewa hukumar yan sanda basu yiwa Malik aiki.
“Yaku yan jarida ina son na sanar muku cewa, hukumar yan sanda basu bin bayan kowanni bangare fecce aiki da gaskiya da Amana, sannan da ace yau hukuma ta kama Malik da laifin kashe Prime minister, da ba a rufe awa ashirin da hudu ba, ba tare an kama shi ba. Duk wani hujjojin da ake bukata mun tanada shi, sannan duk wani binciken da ya dace, anyi bai da masaniya a kan kashe Prime minister.”

“Sai dai har yau muna da labarin cewa, Malik Menk Jordan shi ne yaron da ya kashe Manyan yan siyasa da jami’an tsaro uku, shekaru kusan arba’in da suka gabata, shin wannan ba hujja ba ne da zai iya rufe shi har abada ba?” Kallon dan Jaridar AIG Yasir Aswad Yamini yayi, kafin ya ce mata.
“Har yau muna kan bincike.”
“Yallabai²”
Suka shiga kiranshi, amma ina yan sanda sun kare shi. Har ya isa cikin motarsa. Kallonta yayi ta zuba mishi idanu.
“Omooooo! Me yasa kika zauna a nan zafi ba zai dame ki ba?”
“Taya ba zan zauna ba? Wallahi kaji tsoro Allah, akwai cases sun kai ashirin akan Malik Menk Jordan, me yasa kake tsoron bayanan laifinsa ko kai ma kana tsoron mutuwan ne?”
“Mutane irinku, kullum tunanin su hango laifin wasu baku tab’a zama ku fahimci me yasa wane ya zama haka.” Bata bari ya kawo karshen zancen ba, ta bude motar zata fita, riko hannunta yayi ya ce mata.
“Me yasa kike fushi?” Idanunta cike da takaici ta ce mishi. “Ok ya batun binciken ki?”
“Sake ni!” Bakinsa a dai-dai kunnenta, “let me kiss you.” Ture shi tayi, tana faɗin.
“Ni ba yar iska ba ne…..” Sumbatar ba zata ya kai mata, ta wani ware idanu ta. Hura mata isa yayi. “Asp zaki iya tafiya!” A hankali ta bude kofar ta fita, kallonta yayi yana murmushi. “Ki kula min da kayan alatuna. Zan gayawa Auntynki!” Bata saurare shi ba, tayi gaba. How comes? Taya zata dauki wannan al’amarin.

Haka ya tafi ya barta da Faduwar gaba, tasan Aunty Fannah, da Bala’in kishi. Musamman akan Mijinta bata hada shi da kome ba.
—–
Kamar yadda suka bukata yau ta fara zuwa aikin, sai dai tunda ta isa bata zauna ba. A tarihin rayuwarta wannan lokacin shi yafi kome bata wahala. Sai yawo suke manyan ofisoshin gwamnati, da gidajen masu kudi,babu karya wanka iya wanka yau tayi shi. Shi yasa duk inda suka je cikin ruwan sanyi suke samun ganawa da Mutanen da ta je gani.
Past.
Daga cikin abubuwan da Nasr Hadejia da Aswad Yamini, yasa suka samu ganin Mayor na wannan lokacin, domin a basu damar Fahad Albagwi, a lokacin ya basu full attention dinsa, sannan ya basu damar gini a bakin tsubirin, tare da dauko masu gine-ginen zama daga kasar Canada.
Duk wanda ya saka gaskiya a cikin al’amarinsa, zai ga gaskiya domin a kasa da wata uku suka gama ginin, tare da fara kokarin bude shi, a lokacin manyan attajiran Fisto da Keivroto suka yi ta zuwa……
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI….!

Leave a Reply

Back to top button