Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 11

Sponsored Links

Volume:11 fault
Tun da tafita taki yarda, Elbashir ya kaita gida, da kafarta take tafiya. A yau taji Ina da iyayenta SUNA raye, Ina da tana da Wanda zata gayawa damuwarta. Tana tafiya tana share kwalla. Domin kuka ne yake cikin karfinta. Suka fita daga unguwar bakidaya, shan gabanta Elbashir yayi ya fito ya ce mata.
“Ki shiga don Allah!”
Goge hawayenta tayi da bayan hannu, ta shiga motar tana jan hanci, idan ta tuna bata da hanyar da Alumma charity house ya tsira sama da sadaukar da rayuwarta, a hankali ta shiga sobbing, kamar ranta zai fita.

Bata iya shiru ba, kuka take sosai. “Bashir dawo da ita!” “A’a please kai ni wurin Abbashe don Allah?!” “Ka dawo min da ita nace!”
“Ok Malik” wani irin juya motar yayi tare da cillawa a guje, suka nufi whiter town. Har lokacin kuka take sosai. Ko da suka Isa, Elbashir fita yayi ya barta a motar, Malik ya zo ta wurin tukin ya zauna, yana kallon yadda take kuka. “Kukan me kike?” “Kawai idanuna ke ciwo!” “Don try me! Kukan me kike yi?” “Babu kome!” “Tow me yasa kike kukan?” “Me yasa ba zan yi kuka ba? Gaya min nima jikina kake bukata kamar nata?”
Kasa magana yayi ya zuba mata Ido, baki a sake. “Idan jikinki nake so, akan me zan kira aure akan kudina? Mtsew! Kika sake kawo min shirme sai na saba miki.”
Daga haka ya fita a motar, Elbashir ya zo ya tafi da ita gida. Tunda ta shiga gidan bata tsaya amsa maganar su ba, ta haura sama da gudu. Tun da ta shiga dakin ta fashe da kuka , tare da zama a tsakiyar gadonta. Ba kukan abin da ya faru a gidan Malik ba, tsoron kada itama yayi amfani da ita, sannan ya kwace su tashi two zero.
Dakyar tayi sallah, ta kwanta. Cike da mafarkin Malik ya kwace musu gida. Sama sama take jin ihun mutane, d’ago kai tayi aka doke kanta, da wani abu Wanda bata kuma fahimtar kome ba. Sai bayan wani lokaci.
Sama sama take jin maganar mutane, bud’e idanu tayi tana ganin dishi -dishi har ta fara ganinsu sosai. A hankali ta fahimci inda take, “ke kin tashi?” Kallonshi tayi sannan ya ce mishi. “Wani Dan shegiyar ne ya buga min abu a kai?”
Dauketa da Mari Jalilah tayi, sai da ta fadi can. Dake daure hannunta suka yi, inda ta fadi, akwai fasassun kwalabe, ga hannunta a daure, kenan babu yadda zata dauka. “Kai d’ago min ita mugu!” D’agota yayi yana fadin. “Hajiya na jima Ina cike da haushin shegiyar nan, dama kuma abinda nake so kenan na ci ubanta!”
Murmushi Jalilah tayi sannan ta ce. “ku gama da ita!”
“Kai dan daudu idan ka yarda kai namiji ne, ka kunce ni mana!”
“Ke har kina da abinda zaki iya!”
“Hmmm! Ashe ke ba mace ba ce? Ke lusara ce ashe rako mata kika yi, na zata zaki tsaya mu gwabza ne! Me rabo ta sace Malik! Sai gashi kin yi rashin wayo, kin kuma lalata alaƙarku!”
Marinta tai, sai da hancinta ya fashe ta ce mata. “Idan kina raye zaki yo tunanin akan Malik! Wai na tambaye ki, da gurguntaka kike bibiyar shi.” Daria tayi sosai sannan ta ce mata. “Ai kuwa ni kadai nasan abinda nake kwasa a wurin nan, hala bai gaya miki Ina dauke da Doggystyle gift dinsa ba.”
Jalilah bata san lokacin da ta kifeta da Mari ba, ita kuwa tayi ta Dariya, “kuma ki saka idanu Malik yana zuwa yanzu!”
Kiran wayar Jalilah, Lalla Salmah tayi tana fadin. “Ki bar wurin yanzu!” “Zan bar wurin sai na kashe yarinyar nan”

“Ki kyaleta domin Malik zai fusata. ”
“Wallahi ba zan kyale ta ba!” “Kai mugu, ku dauketa, ku sakata a cikin wancan randar, ku jefata cikin ruwa!” “Ka da ki fara abinda zai dame ki, ki kyaleta ta bar nan. Ni kuma tsakaninmu zan duba lamarin. Inji Malik da ya shigo wurin.
“Ba zan kyaleta ba, sai ka amince zaka aure ni.”
“Taya zan aureki? Bayan nayi alkawarin ba zan aure ki ba.”
“Akan meye?” Ta fada tana ihu, “Amma kasan kai ne ka fara lalata min jikina!”
“Na sani amma ai ba da gangan haka ya faru ba, ba a hayacina nayi haka ba. Please ki kyaleta domin bata san kome ba!”
“Ba zan kyaleta ba, ba zan kyaleta wallahi she deserves to death!” “Bata cancanci mutuwa ba! Please kyaleta babu ruwanta.” Hawayena zuba a idanunta, ta ce mishi. “Me yasa baka sona?” “Saboda na fahimci ba ni ne a ranki ba lokaci, akwai Wanda kike so, bayan batar iyayenki da na nimo miki danginki, ki kyaleta.”
“Me yasa ka kore ni? Bayan kasan ba zan iya cutar da Nuratu ba!”
“Zaki iya mana, tunda kika amshi aikin kashe ni Allah bai nufa ba. Shi ne kika kai ta wurin da aka tozartatta!”
” Ba dole ba, ba dole ba. Cewa kayi zaka aure ni Amma hankalinka yana wurin Nuratu. Cewa kayi idan na baka kaina zaka aure ni, bayan an gama kome kawai ka.juya min baya saboda abin da ya faru da Nuratu, kasan Nuratu bata gani sosai idan dare yayi kuma ni da kaina ba zan dauketa na kaita wirin da aka mata fyade ba, Amma ka gaza fahimta. Idan kace sa sakacina a faruwan lamarin na yarda, amma haka.kayi ta dukana har waje kana kirana karuwa, itama wannan yarinyar kasheta zan yi!” Ta doke fuskar Zeeno ta fadi can. A sume.
“Zainab!!!” Ya kira sunanta da karfi, ganin Zeeno kwance sai da jikinta ya sake kuma, bata tab’a kashe ko kuda ba, yau gashi ta duke mutum ya mutu hala mutuwa tayi yar da katakon tayi tana ja da baya, Koda ya Isa wurin sauka yayi daga keken ya zube a gabanta. D’agota yayi ya rungumeta yana girgiza kanta. “Hi baby girl wakeup, wake up gani tare da ke!” Ya girgizata sai da ta motsa, Amma ina ta tafi. Tab’a Bluetooth din kunnen shi yayi. Ya ce. “Bashir maza ku shigo ku kama kowa!” Haka kuwa aka yi, Bashir ya dauki Zeeno yan sanda suka kama ya daban. “Malik!” Jalilah ta kira shi da sauri. “Wallahi ban san zata mutu ba”
“Let me make it clear, har abada ba zan aure ki ba, kamar yadda na fada a baya tow yau ma ba zan tab’a aurenki ba! Kun jima baki kashe ta ba, Ina miki uziri ne

Sake baki tayi tana me kallonshi, “Malik ba zaka aure ni ba.” “Har abada kuwa.” Daga haka yayi tafiyarshi ta zube Kan gwiwarta, meye laifinta? Me ta aikata haka da ya saka Malik tsanarta har duniya ta tashi. Lalla Salmah ce tazo ta dauke ta. Tare da zugata kada ta yarda tayi hayar yan iska zasu tayata zanga-zanga. Duk da bata so ba, domin tana ganin Babu abinda zai saka Malik waiwayarta, Amma kuma kulafuncin da take da shi akan Malik ba na wasa ba ne, ta dauki ahawarar Jalilah.
★★★
Menk Jordan world cares,
Aka kai Zeeno, wacce bata san waye akan ta ba. Sai da aka yi ta mata karin ruwa, a lokacin Dr wardah ta kuma tuna musu aikin da ya dace ayiwa Zeeno.
Sai can dare ta farka, ganin ta a gadon asibita ya sakata yunkurin tashi. Amma ya maida ta. “Relax!” Wayar dakin ya dauka ya ce. “she a wake!” Sannan ya ajiye wayar yana kallon yadda ta tsura mishi fararen idanunta. “Sorry kin ji!” Juyar da kai tayi tana fadin. “Ina take?” “Wa kenan?” “Matar nan?” “Mahaukaciya dai ko?” Shigowar Dr wardah ya sa bata bashi amsa ba, cikin girmamawa ta gaida Malik, sannan ta wuce wurin Zeeno ta gama dubata, sannan ta cire mata karin ruwan, “zaki iya wanka ko a na taimaka miki!” “Zan iya!” Haka ta fada sannan ta mike. “Wardah ki turo nurse biyu, da pad!” Sai lokacin Zeeno ta lura da abinda ya faru da ita, komawa gadon tayi ta kwnta yaki yarda ta kalle shi, rufe idanu tayi tam,taki budewa “Mayor ko zaka fita ne?” Murmushi yayi sannan ya ce mata. “Ok!” A hankali ya tura keken shi, ya fita ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta bude idanu. “Dodonki ya fita.” Bata ce kome ba, har Dr wardah ta fita suka shigo da nurse biyu da pad din. Da taimakawarsu tayi wanka ta gyara jikinta, ta fito ta samu Inna da Ammy sai Abbas da Black, Malik na gefe yau ya Kara yarda Zeeno a rayuwarsu wata duniya ce, musamman Abbas da yana ganinta ya fashe da kuka, yana fadin. “Sai na kashe matar sai na kashe matar.”
“Ni fa ban san me ya faru ba?” Zeeno ta fada, tana amsar abincin da Ammy ta mika mata. Kallon Malik tayi tana fadin. “Ammy sake zuba min.!” Ta sauka a gadon ta nufi wurin shi, mika mishi tayi tana fadin kaci. Kallon kwayar idanunta yayi, tayi maza ta juya tare da nufar gadon, ba karamin burge Ammy tayi ba, domin kuwa Zeeno irin mutanen nan masu iya kashe Kansu, su raya wani.

Sai da ta koma ta zauna Ammy ta mika mata, bai da niyyar ci Amma saboda ta kawo mishi, mikewa Ammy tayi ta ce.
“Inna zo mu Dan zaga cikin asibitin!”
Gyada kai tayi, zata fita Abbas ya mike xai bi bayansu. “Zo ka zauna” “a’a zan tafi wurin Hibba ne” murmushi Malik yayi domin kuwa ya yaba da dattakon Ammy.
Suna fita ya turo kekenshi wurinta, ya zuba mata Ido.”me yasa kika zuba!” Dauke kai tayi kamar bata ji ba. “Yarinya!” Kallonshi tayi na dan wani dakikai kafin ta ce.”Ci abincin ka.” Daga haka ya cigaba da cin abincinta. A nutse ya kai faten waken da yaji ganye da hanta, ya kai bakin shi. “Hmmmmm! Garnish yummies!” “Baya cikin ladabin cin abinci, ana magana!’ gyada kai yayi ya cigaba da ci. Da sallama Lalla Salmah ta shigo. “Amin wa’alaikumun Salam” Zeeno ta amsa mata. Shatima ya biyo bayanta, “Zee Baby! Me ya faru da ke?” Ya shigo a rude, ajiye abincinta tayi magana suka had’a idanu da Malik, kwarewa tayi, Malik ya mika mata ruwan da yake cikin gora. Sai da ta sha. “Kiyi a hankali domin kaidin evil eye’s.” Yadda Malik ya hade rai, baki daya kowa ya shiga hankalinshi, musamman ita kanta Zeeno yadda ta kame kanta, ciro hanky’s yayi ya goge mata a bakinta, “na gode!” “No need!” Sai da suka gama cin abincin a tare, ta mike zata ajiye plat din, ya amsa yayi ya ajiye mata, ya tura kekenshi ya dauko mata dankwali, ya mika mata.
Koda ta daura, kallonta yayi yaga yadda take Dan motsi na shanunta suna motswa, a kaikaice ya kalli Shatima. Yaga yadda ya mata kuriiiii da idanu, cire top dinsa yayi ya rufa mata, yana fadin. “Daga yau kada na kuma ganinki babu hijab.” A hankali ya juya tare da kallonsu. “Ba zaku tafi ba ne? Ai gaisuwar ta Isa haka!” Ya fada yana wani hade gira. Idan da bata labari aka bata ba zata yarda ba, Amma yau da ta gani a idanunta, ta yarda Malik bala’i ne. Bai rufe baki ba, suka cikawa bujensu iska. “Mtsew! Sun wani zubawa matan mutane idanu, haba sai kace makafi ko yau suka fara ganin mace ni bana son haka. Kuma ai duk laifina ne shi yasa ”
Ita Kan bata kula shi ba, domin ta lura da yadda yake jin rigima aran shi.
*Ayi hakuri wayata ce ta lalace, don Allah! Ayi hakuri 🥳🤩😁🧐*
500N
07035133148
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button