Dabarun Rubutun Waka

[YADDA AKE RUBUTUN WAKOKIN HAUSA. by MSZ]

Sponsored Links

                DABARUN RUBUTUN WAKA – 

              RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA 

                                     PART 5

  Daga 

Nasir G Ahmad

 Barkan ku da warhaka 

Yau wata tambaya zan amsa:

Ta Yaya Zan Zama Marubucin Waka?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama da ke sha’awar rubuta waka za su iya yi. To ni a ganina amsa ita ce, ba za ka zamo marubucin waka ba, sai ka fara zama makarancin waka, mai sauraron ta, ko mai nazarin ta.

  Ba kuma za ka zama makarancin waka, mai sauraron ta ko mai nazarin ta ba, sai ka zamo kana sha’awar waka. Sha’awar nan ita ce za ta rika ingiza ka ga karanta wakokin mawallafa daban-daban, kan al’amuran rayuwa mabambanta. 

 Ta haka ne za ka nakalci salale iri-iri, har watan wata rana ka yi kokarin rubuta taka wakar, bisa kwaikwayon karin wata waka da ta fi ba ka sha’awa, kake jin dadin karanta ta ko rera ta.

Ga jerin wasu littattafai da ya kamata mai sha’awar waka ya neme su ya rika karantwa:

*Zababbun Wakokin da da na Yanzu. Na Dandatti Abdulkadir

*Tsofaffin Wakoki da Sababbin Wakoki. Na Mudi Sipikin.

*Fasaha Akiliyya. Na Akilu Aliyu

*Wakokin Sa’adu Zungur

*Wakokin Mu’azu Hadeja

*Wakokin Hausa. Na Kamfanin NNPC

*Wakokin Aliyu Dansidi; Sarkin Zazzau

*Wakokin Imfiraji. Na Aliyu Namangi

*Wakokin Hikima. Na Kungiyar Hikima Kulob

*Wakokin Hikimomin Hausa. Na Ibrahim Yaro Muhammad

*Wakokin basirorin Hausa. Na Ibrahim Yaro Muhammad

*Wakar Furen Gero da Tsarabar Madina. Na Aliyu Namangi

*Alkalami a Hannun Mata. Na Hauwa Gwaram da Hajiya ‘Yar Shehu Dambatta

*Cikin Carbi. Kundin Wakokin Malam Kabiru Inuwa Magoga

*Fasahar Garba Gashuwa. Na Mal. Garba Gashuwa.

Da makamantansu.

Allah ya ba mu dacewa.

              Sigogin Rubutattun Wakoki

Abin nufi a nan shi ne, siffofin rubutacciyar waka ko tubalan gina ta, wadanda ta kebanta da su, da su ne kuma ake iya bambance rubutacciyar waka da ta baka.

1. Ma’auni/Kari

Ma’aunin waka shi ne karinta. Wato muryar da ake rera wakar da ita, wadda ga al’ada takan saba da magana ta yau da kullum.

 Rubutattun wakokin Hausa na farko, har zuwa cikin karni na Ashirin, an gine su ne daga ma’aunan wakokin Larabci, inda aka tabbatar da cewa an yi amfani da karuruwa goma sha uku daga cikin sha shida da ake da su a Arulin (ilimin awon waka na) Larabci.

A cikin karni na Ashirin ne aka fara samun sauyi wajen ma’aunan rubutattun wakokin Hausa, inda wasu mawakan suka shiga aro karuruwan wakokin baka iri-iri, suna rubuta wakokinsu da su, ko ma su kirkiri nasu karin na kashin kansu. Misali, Malam Aliyu Namangi Zariya ya ari karin wakar baka ta Caji, ya rubuta wakarsa ta “Imfiraji.” Malam Akilu Aliyu ma ya ari karin wasu wakokin shata da na sauran wakokin baka, ya rubuta wakoki da dama da su. Kamar wakarsa ta “Isra’i” da wakar da ya yi kan samun ‘yancin kan Nijeriya, wadda ya gina bisa bisa karin wakar almajirai da sukan yi ranar Salla.

Mu kwana nan.

anan zamu diga aya sai muhadu a Kashi na gaba.

Daga 

Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.

 Daga naku 

musa s Zage

Leave a Reply

Back to top button