Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 30

Sponsored Links

30- baki ɗaya barci kaurace mishi yayi ya tashi zaune yana jin wani abu yana motsa mishi ranshi a kan cikin Zainab ɗin. Murmushi me sauki yayi, burin ana gama wannan hayaniyar ya saka Zulfah da Jalilah a gaba da ita ya kai su garin danginsu. Ta haihu a can shima kuma ta koma kano ya ga nashi dangin amma ina ta lalata mishi tsari. Yana zaune a wurin yake nazarin yadda zai bullo mata, domin kuwa baya son wani abu ya a taba ta, ko ya shafe ta.
***
Shatima..
Shi ya dauko Lalla Salmah, yana faɗin. “Na san halinsa sarai, koda yake zuwa yanzu bai san mun shigo ba.”
“Malik din ne bai san mun shigo?” Garin yayi corne kawai ya daki wani me mashin, suka fadi can. Komawa gefen titin suka yi. Suka fito ganin mutumin ya tashi tare da cewa. “Wash! Da sauki zaku iya tafiya, ku dai ku kula da hanya.”
Daga haka ya koma wurin machine din da abokinsa, suka bar wurin. “Yan shaye shaye ne!” Suna barin wurin Shatima ya bisu da idanu. Kafin ya koma cikin motar shi da Lalla Salmah. Suka fara tafiya har sun kusan isa gidan da yake boye.

Motarsu ta bi ta kan abu, take tayar motar tayi wani irin kara, tare da kwacewa a hannunshi. Dakyar yayi ta tafiya yana kokarin sun isa gidan da yake. Amma motar taki bada hadin kai. Dole suka fita tare da Lalla Salmah, suka shiga gudun ceton ransu. Koda suka isa gidan a gajiye suka isa suna haki. *Ku kula da hanya!* Abin da ya dawo kan Lalla Salmah kenan ta ce mishi. “Na gaya maka Malik yana sane da motsin mu, amma kace a’a.”
“Tow taya zan karya miki zuciyarki da zancen Malik, kawai manta da shi amma dole na dauki mataki akan shi.”
Haka suka kwana rai babu dad’i, Washi gari suka tashi domin su fara tunanin yadda zasu cutar da Malik.
Sai dai maganar gaskiya, ba Malik ba ne ya kai musu barazana, idan zai yi ba zai musu da rayuwarsu ba, tab’a abin da suke so yake. Ya gaya musu yana tare da wane.
Ko ita Lalla Salmah, bata san cewa Malik yana sane da boyayyen sirrinta ba, shi yasa take ganin kamar ai bata da wani abu wanda Malik bai sani ba.
Abin da ya faru Shatima ya saka aka musu haka, domin kuwa ya kara cusawa Lalla Salmah ta yarda cewa Malik yana farautar rayuwarsu.
Yaran da suka buge da da saninshi, yayi haka domin ta kara yardan cewa Malik ne, a ta kowani fuska yana son ya lalata alaƙar Malik da kowa.
Tana fitowa taga fitar daya daga cikin Yaran, kafin ya isa yayi tafiyarshi. Ganin yadda take leke ne ya ce mata. “wani abu kike nima?”
“Ina yaran nan da muka buge su jiya, na ga kamar ya shigo gidan nan ne?”
“Kin ganshi ne?”
“Kwarai da gaske na ganshi, kada Malik ne ya turo shi ya mana wani abu?” Ganin yadda take nuna tsoronta a fili yasa ran Shatima b’aci..
“Malik kike tsoro? Bayan gani a gefenki!” Kallonshi tayi sannan ta ce mishi. “Ko ƙarƙashin ƙasa ka shiga, Malik yana iya binciko ka, balle kuma a sarari ni fa shi yace idan ina da zarar hana shi kome na shigo Keivroto kana tsammanin ba zai iya kome ba ne don kare gefenshi?” Tayi maganar ranshi ya kara b’aci ya ce mata.
“Babu abin da zai iya miki, ina tare da ke. Sannan ki daina kiran shi a gabana, matuƙar ina nan babu wanda ya isa kiran Malik.”
“Hmmm! Kana nufin kawai don ina tsoron Malik sai ka da na kira sunanshi? Bayan nasan cewa kai ma karfin hali ne, da zaka ganshi sai ka sake fitsari a wando ka saka a nimo wannan yaron domin Malik be ya saka shi aiki.”
Duk yadda yaso ta manta da Malik ta tsaya su mishi taron dangi taki, don dole ya kyaleta yana me gaya mata duk inda ta shiga bata tsira ba. Domin Malik yana bibiyarsu. Haka yasa ta fara tunanin hanyar da zata cusawa Malik tashin .
Ba tare da shawara da Shatima ba, ta kira taron manema labarai.
Wuce shi tayi tana me daukar wayarta domin kiran yan jarida, yq fisge wayar yana faɗin. “Akwai kawar matarshi nasan zuwa wani lokaci Matar shi zata so su haɗu, zan saka miki number ta, ki kirata ki ce mata don Allah zaki bata sako ta bawa Zeenobia sai ki tura mata, idan yaso hanyar farko da zamu samu Zeenobia ta fito, so nake na kasheta daga ita har cikin jikinta, yadda zan dasawa Malik bakin cikin da bai isa ya kashe mu ba. Daga haka zai kyale mu, ko ya tattara ya bar kasar ko ya gudu baki daya!”
“Amma me yasa baka gaya min tun farko ba? Da nasan da haka yaushe zan tsaya taron masu nimam labarin da bai zama dole su amshi labarin ba, amma kanka a yana ja!”
“Gashi saka min! Number ta!”
Wayarshi ya ciro ya saka numberta, sannan ya koma ya zauna yana gaya mata. Yadda matukar suka girgiza mata ƙwaƙwalwa da wanna labarin sai taji gara ta kashe Malik.
“Idan kuma bamu samu nasarar kashe ta fa?”
“Idan bamu samu nasarar kashe ta ba, zamu yi kokarin raba shi da ita, ni kuma ta wannan bangaren zan tafi na nimo soyayyarta, bayan na kashe cikin jikinta nasan ko ban yaki Malik gaba da gaba ba, Zeenobia zata yake shi, har dai ta ga ta kai shi kasa. Daga nan zan saka ta, niman a raba dukiyarshi biyu a bata rabi.”
“Eh tow idan tana son cikin jikinta fa?”
“Amma dai ban tab’a ganin mara tunani irinki ba, bayan na gaya miki yadda za ayi idan tana son cikin ba laifi ai, sai na taya ta so, na kaunaci dan na cusa mishi tsanar Malik. Mu ga yadda zai ji idan ya rasa uwar da Yaron.”
“Wai wai! Amma wallahi kacika makiri, tow ni meye makomata a garin nan?”
Shiru yayi domin shi duk tsarin shi bata ciki, bata cikin tunaninshi balle har ta shiga tsarin benefic da wani abu da zai samu a tare da Malik, murmushi yayi ya ce mata.
“Zan tabbatar da Party a sauke Malik a baki matsayinsa.”
“Kana nufin daga yar majalisar kasa zuwa Mayor? Gaskiya matsayin yayi min kaɗan. Ka duba dai a bani koda ministan harkokin mata da yara ko, wani matsayin amma wannan Mayor fa?”
A ranshi kuwa yasan za ayi haka, don haka ya ce mata.”saurin me kike yi ki kwantar da hankalin. Zaki isa wurin ai”
***
Tun asuba, ta fahimci ita ɗaya ta kwana a dakin don haka, ta mike zaune tare da nufar ban daki tayi wanka da alola, sannan ta dawo dakin tayi sallah. Tana addu’a ta ji kamshin abincin ya sakata bata idar ba, ta nufi waje, tana zuwa ta same shi yana aikin jan kujera tayi ta zauna, tana hadiye yawu. “Kin tashi?” Gyada kai tayi tana kallon abincin, a nutse yayi ta jera mata, yana cewa. “Zan fita kada ki tafi ko ina, ki zauna a gida, ki duba firji akwai duk abin da zaki bukata kafin na dawo. Please kada ki fita ko kofar gida ne?”
“Gaskiya haka zan zauna ban fita ko waje ba? Ni ina son ganin Hafsy ne!” Share ta yayi yana cigaba da aikinshi, har ya gama sannan ya nufi daki yayi wanka ya sauya kaya, sannan ya fito ya same ta. Zama yayi ya fara cin abincin. Bashir ya sauko ya zauna shima. “Uncle Elbashir ka tambaye shi me yasa ya ce kada na fita?”
“Saboda lafiyar cikin jikinki idan ta ni ne , da ya bar ki a can Demark ki karaci shirmenki” shiru tayi tana kallon Elbashir da yafi Malik daukar zafi.
“Zan fita sai dai na mutu, da abincin.”
“Aniyarki ta bi ki!” Ya faɗa yana daukar abincin.
“Zauna ka ci anan!” Komawa yayi ya zauna, yana cigaba da cin abincin. Nad’e hannunshi yayi a kirjinshi. “idan kika gama Hafsah zata zo yayi miki?”
“Zan fita wurin gyaran jiki da kai!”
“Zasu zo su miki har gida.”
“Tow ni haka zan zauna ban fita ba!”
“Duk yadda kika gani daya ne, amma babu wanda ya isa ya barki ki bar gidan nan. Koda kuwa da wasa ne.”
Ran Elbashir ya ɓaci sosai, don haka ta cigaba da cin abincin yana gamawa Malik ya ce masa. “Ka saka a kawo mata Hafsah ta zauna sa ita kafin kome ya dawo daidai.”
“Kana nufin ta dawo nan da zama?”
“Eh!” D’ago kai tayi zata mishi wani magana yana zuba mata idanu, da sauri tayi kasa da idanunta. Mikewa tayi zata bar wurin ya ce mata. “Idan kika tashi zan baki mamaki! Ni ba sa’anki ba ne da zaki mai dani sakarai. Ni ban yi kama da lusarin da zaki na juyawa son ranki ba, ji gaya min me kike bukata, ba haka kawai kika zo nan ba, gaya min me kike buƙata?” Ya daka mata tsawa, ƙasa motsi tayi tana kallon tea din gabanta, wanda hawaye yake d’iga cikin cup ɗin.
“Gaya min me kike so na miki?” Ya faɗa da murya me amo. Rikicewa tayi da kuka. “Malik!”
“Bar ni na goge mata abinda take ji aranta!”
“Idan na rabu da ke,zan iya moving on, kafin ki zo rayuwata ina rayuwa lafiya babu abin da ya faru. Suddenly bayan zuwanki babu abin da ya canza. If you’re think that saboda cikin jikinki zan zama sakarai you think wrong! Ba zan tab’a beg you da ki zauna da ni ba, domin ko baki zo ba, shirina ne na mai dake wurin dangin mahaifinku.” Saka hannun yayi cikin rigar shi. “Wannan shi ne takamarki! Tun kafin na ganki tun bayan gaya min kina da cikina na ajiye a raina zaki bukaci rabuwa da ni! Don haka nan da sati zan mai daki wurin dangnki. Zan iya zama da mace mara kamun kai da hauka, amma ba zan zauna d macen da bata san darajata ba.
Kaf abokan gabana, sun san ba ni da sauki amma ke kin same ni don na baki fuskar da zaki min yadda kike so, na raga miki ne don Amanarku da mahaifinku ya bani da baki isa ki min rashin hankali na kyale ki ba! Tun kina haukar ki nake bibiyar ki balle yanzu da kika zama me lafiya. Cikin jikinki idan kin so ki gaya mishi ina sonshi rashin mutuncinki yasa na hakura d ku, idan kin so ki gaya mishi na mutu wannan matsalarki ce.”
“Malik yarinya ce!”
“Ba yarinya ba ce, tasan me take yi, ta san me take ji, ta kwaso jiki ta biyo ni domin tana bukata ta, bata biyo ni don ta fahimce ni ba. Ni bana cikin mazan da mata zasu juya. Allah na tuba ko asiri ake yi bana cikin mazan da zai kamasu, domin na tsare addinina da ibadana, baki isa ki min kome ba.
A duk inda zan shiga bana fasa niman taimakon Allah akan kome, ke har kin isa ki min renin hankalin? Bari ki ji da kyau bana daukar reni kuma bana rena kowa, duk wanda kika ji muna takun saka tab’a ni yayi idan bai tab’a ni ba, bana tab’a shi don haka baki isa ba wallahi!”

Daga haka ya mike zai bar falon, Elbashir ya ce masa. “Me yasa ka mata haka a gabana, idan jininta ya hau fa,?”
“Jininta ba zai hau ba, domin tana kuka da bata kuka ba zan gaya mata magana ba, tayi kukanta ya ishe ta.”

Ya bar su a falon, yayi tafiyarshi. “Har ga Allah baki kyautawa. Malik yana sonki amma haka kike ta bashi wahala ban san yadda zan gaya miki ba. Amma ki kula sosai Malik ba abin yarwa ba ne an jima za a kawo miki Hafsy!”
Yana fita gidan su Hafsyn suka tafi aka daukota, tare suka dawo ya koma ciki ya dauki kayan Hafsy ta same ta a daki tana barci. “Lafiya yan mata, saura wata guda azumi! Me kike shiryawa mutanen Al’umma charity House…”
Wayarta ce tayi kara, dauka tayi ta ce .
“Waye?”
“Eh nice ga Zeenobia nan.”
Shiru tayi sai.kuma ta mika mata wayar.
“Yan mata amshi ana son waya dake…….
*Waye zai mutu? Waye zai rayu! Marubuci shi ne Ubangijin labarin shi😁🙄*
Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

 

Leave a Reply

Back to top button