Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 47

Sponsored Links

47- A hankali cikin yake kara girma, lokaci yana ja. A wannan lokacin babu wani tashin hankali, sai ma ajiye aiki da yayi, musamman na mayor yace baya bukata, matarshi da Yaranshi suna buƙatarshi a tare da su.
A bangaren Shatima sun koma ƙasarsu da Yarshi, don suna komawa ko wata uku batayi ba, ta auri wani dan majalisar kasar, ya cigaba da rayuwarta, Lalla Salmah kuwa itama yarta da take fama da lalura ta rungumeta, suka Zauna a oman.

A lokacin da Malik zai ajiye aiki sai da ya tuntubi Elbashir ko yana son zama mayor, cikin tsoro ya ce masa. “Chab Allah ya min tsari da wannan abin. Kawai ka rike kayanka. Kaine zaka iya da mutanen nan.”
“Allah ya shirya ka.”
“Amin Ya Allah! Tab kai kenan, baka sha dadi ba, sai ni ina zaman lafiyata zaka hada ni da masifa da bala’i. Abin da kowa ji yake kamar ya kashe ka a kai, balle kuma ka bani a shiga yawo damu duniya Malik ya sauka ya bawa hannun damansa, dama abun ana mishi kallon gado ne, ko kaima nasan ba dadin shi kake ji ba, tunda babu me saka ka, babu me hana ka.”
“Duk me yayi zafi ne haka Elbashir?”. “Abin da yayo zafi kenan, zaka hada dani masifar duniya, ana zaman lafiya.”
“Allah ya baka hakuri!”
Ya faɗa yana nazarin yadda Keivroto zata koma hannun wanda basu sani ba. “Kasan meye tunani na?” “Ina zan sani ” ya faɗa yana hada kayan office din Malik ɗin. “Makomar Keivroto nake tunawa.”
“Hamm! Sannu ko? Allah ya taimakawa Dan Madam teresa uwar marayu, Malik kana da kome na rayuwa, don Allah ka kyale jama’a nan haka.”
“Ban san hannun da zasu faɗa ba ne, gani nake kamar za a zalince su?”
“Tow yayan Malik da Zeeno ko?” Fita yayi yana faɗin. “Ba zaka gane ba ne.”
“Da haka gara ka cigaba da rike su, kawai.”
“A’a bana ra’ayi, kawai barsu su gwada wani.” Ya faɗa yana barin bakin kofar, har ga Allah bai san wani hannu garin zata fada ba, sai dai a wannan lokacin zai dauka bai san waye mahaifinsu Wahida ba, haka ya fi kome yi miishi ciwo. Domin baya tunanin zasu samu wanda ba harin albarkatun garin yake ba.
**
Tun baya fitarshi, ta wuce bangaren Ammy. “Assalamu alaikum!” Sallamarta ne ya makale sakamakon hango Hafsy. “Wa’alaikumun Salam! Mamman Maidah kece?” Inji Hafsy tana mikewa da Yarta, Nimrah. Dauke kai tayi tana faɗin. “hmmm!” Ta faɗa can ƙasar makoshinta.
Zama tayi daidai fitowa Hassan yana kiran sunanta. “Moooo!” Haka suke kiranta, basu iya cewa Mommy ba. “Na’am Baby love!” Tabdauke shi tana lila shi. “Ummi!” Ta kwalawa yarinyar kira. “Na’am, Mommy!” Itama tabi bakin sauran. “Duba min Ammyn ta gama dan waken ne?”
“Tow!” Tana shiga ta samu ta gama kuwa, amso mata tayi, ta fito tana ajiye mata, ta saka tare da barbad’ad’a yaji.

“Zeeno kiyi hakuri mana, sai kace ba musulma ba. Ina ta binki ina baƙi hakuri amma sai wani share ni kike!”
Bata ce mata cikanki ba, haka ta zauna tare da saka hannu a cikin abincin, har lokacin bata d’ago kai ba, shigowarsu Malik yasa, Zeeno ta d’ago tana sakar mishi murmushi, tana mika mishi hannu. A hankali Hafsy ta cire hannunta, Malik ya zauna a gefen Zeeno. “Sannun da dawowa, ba zan iya tashi ba ne, karshe abincin ya fitar min a kai!”
Zama yayi ta kalli Elbashir ta ce mishi..”Uncle Elbashir!” “Madam Zainab, a waje Malik zaki ne a wurinki kuwa, abin wasan yara yafi shi, sauƙin ɗauka.”
“Daadi ka ji shi ko?”
“Hmmm! Ina da ja a cikin maganar nan”
“Allah kuwa, gashi nan ko.mace ce tayi mishi magana cewa yake ai sai ya kira Madam”
“Elbashir dauke matarka, ku bar gidan nan, kafin ka tado min rigimar da ba zan iya kwatar kaina ba!”
“Hmm! Dama yan mata kake kulawa, a waje.”
“Karya yake miki, Elbashir ka ji tsoron Allah. Yaushe kaga wata mace na kula wallahi Allah sai. Kama ka, mara mutunci. Abar kauna, kin san ba zanci amanarki ba, da gaske bana kula kowacce mace.”
Murmushi tayi ganin Elbashir, ya fita yana dariya. Sai da ta cinye dan waken sannan suka yiwa Ammyn sallama, yana rike da hannunta. Har cikin gidansu.

Bayan ta taimaka mishi, yayi wanka. Abinci ta zuba mishi. Tuwo ne tare da Ummi suka yi, ya ci sosai. Ya ce mata.
“Idan kika haihu a kawo za a yi sunan, sannan zamu zauna.na tsawon shekara daya domin hannunki ya faɗa da girki.”
“Duk yadda ka ce Mayor;” ta fada tana kwantar da kai a kafadarshi. “Kashe wutar ki zo nan!” Tashi tayi, ta kashe wutar falon ta zo.ta zauna a gefenshi. Janyota yayi ta zauna a cinyarsa. Hannunshi ya kai ya rungume ta, yana faɗin. “Nayi kewarki!”
“Na gode!”
Ya fada yana goga hancinsa a bayanta, gashin da suke fuskarshi yana tsikarar bayanta. Sauka zata yi ya rikota. Tunda cikin nan ya bayyana shi kenan ya zama marayan dole. Sai yadda aka yi da shi, yana fara tab’ata ta ga zai wuce iyaka, sai kawai ta fara gudu. “Zainaba ina kewarki!”
Kwantar da kai tayi a kirjinshi, tana rike hannunshi. “Mayor na gaji ne, jikina kamar ana duka na.”
“Ina jin ƙishirwa ki taimaka na kashe kishina!”
Juyawa tayi tana kallon shi, sumbatar bakinta yayi.
Ta kai hannunta wuyarshi, tana sauke wani irin ajiyar zuciya. A hankali ya shiga grabbing boons dinshi, sama yayi da rigarta. Idanunshi ya sauka a na fulaninta. Yana me sumbatarsu, kafin ya shiga binsu cikin wani fitar hayyaci da kewarta. Itama kamar zata susuce mishi domin ta kwana biyu ba ayi ban ruwa ba, yau kuwa kasa boye halin da take ciki tai, ta mika mishi baki daya abinda yake bukata. Kamar zai hadiyeta, karshe da labarin yayi labari. Cak yayi daki da ita, anan ya surfeta kamar zai kaita makera.

Sosai, ya murzata son ran shi, sannan ya koma gefe yana ajiyar zuciya bayan ya janyota jikinshi, yana shafa bayanta. “Na gode sosai, ban san me zance miki ba, amma ina da yakinin kin fahimci yarena.”
Baki daya ta saka hannu ta rungume shi, tana me barcinta.
***
Fitowa tayi daga wanka, tana kallon Elbashir da yake rungume da yarsu. Yana waya kasa-kasa. Ganin ta fito ya kashe wayar yana murmushi. “Kin fito!”
“Hmmm!” Ta ce kafin ta koma ta fara gyara jikinta, sannan ta koma tana kallon wayarshi da take haske. Ya share kamar bai san me ke faruwa ba.”
“Dadyn Nimrah ana kiranka”
“Hmm! Na gani amma kawai”
Bata ce kome ba, ta kashe wutar dakin ta kwanta, kwantar da yarinyar yayi.yana me kashe wayar. Sai lokacin ta dauke ajiyar zuciya, amma kuma zuciyarta bata yarda ba.

****
Wurin karfe biyu, ta farka ta ga bayana nan. Tashi yayi zata shiga ban daki, ta ji muryan shi a Falo, ban dakin ta shiga tayi abin da zata yi ta fito ta leka falon. Yana tsaye yana waya, da alamu yana jin dadin wayar.
“Na gaya miki, zan sauke ki a school kada ki damu.” Juyawa tayi ta koma dakinta ta kwanta tana jin zafi a ranta. Haka yazo ya kwanta sannan ta sauke ajiyar zuciya, rungumeta yayi, suka cigaba da barci.

An ce yau da gobe bai bar kome ba, domin tun Elbashir yana waya a sace, har ya fara yin wayar a fili. Haka yasa Hafsy fuskarta wani yanayi da ta rasa wanda zata gayawa, sai ta fara ramewa wanda hakan ya sa lallai shiga damuwa. Idan suka dawo da Malik zai fita idan ya fita ba zai kuma dawowa ba, sai dare ya raba.

Wanna abin ysa ta nufi wurin Malik, da sassafe, sakamakon fadar da suka yi. Har Elbashir ya mare ta. Domin rashin kunya tayi mishi. Ya mare ta, lokacin da tazo da assussubar fari, ko masallaci bai je ba. Yadda take kuka zata baka tausayi. Zeeno da itama taji abin wani irin yasa sai da ta damu.
“Shi kuwa sai ya dake ta, yar shi ce? Nace yar shi ce Malik? Gaskiya wallahi ba zai yiwu ba. Kuma itama shegiyar ya mari Kawata akanta, sai naci ubanta dole ma na nimo ta” yadda take masifar karamin haushi taji ba. Daga masallaci, gidan Malik suka nufa.
Sai da suka shiga falon Malik ya ce masa. “Zauna na kira ta” ya faɗa yana nufar cikin dakin Zeeno ganinsu kamar zasu shige jikin juna ya ce mata. “Hafsy zo nan!”
Mikewa Zeeno tai, ya mata wani irin kallon gargadi, fuskarshi babu fara’a.

Yasata komawa ta zauna, tana bata rai. Ita bata so haka ba. Taso lallai sai ta yiwa Elbashir rashin mutuncin. Lokacin da suka fita, suka shiga tattaunawa. Ita kan Hafsy ta kasa magana sai kuka take, ganin yadda take kuka Malik ya kalle shi yana faɗin. “Bashir meye tayi maka da zafi kake mata hakan? Idan laifi tayi sai ka gaya min na mata fada kawai dai ka dakar musu Y’a xaka ji dadi idan mijin Wahida ya dake ta ”
” Malik, maganar gaskiya yarinyar bata da kirki. Jin ina waya da wata mace, sai ta buge min wayata. Abokiyar aiki na ce fa?”
Wani kuri Malik ya mishi yana son lallai yasan, wacece abokiyar aikinshi.
“Hmmm! Wacece ita?”
“Tana nan dai tare muke aiki da ita.”
“Hafsah wai ashe abokiyar aikinshi ce.”
Cikin kuka ta ce mishi. “Baban Hussaini! Musanya kalaman batsa suke, ban hana shi aure ba, amma kuma kalaman da basu da ce ba, maganar gaskiya zuwa yanzu na fahimci bani yake bukata ba, wani abu be can don Allah ka saka shi ya sake ni.”
“Kiyi hakuri dun abin bai kai haka ba.”
Dakyar ya lallabata ta koma cikin gidan, “wace ce ita? A ina kuka hadu?”
“Malik Ummi ce!” “Ummi kuma wace ce ita!”

Sai da ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fada mishi. “Kanwar Zainab ”
“Karya kake Bashir na zaka lalata zumuncin da muke da matarka ba, gobe gobe sai na maida ita wurin danginta kuma.na hana a baka auren…
Mai_Dambu
*Arewabooks iya book 2*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/30, 10:31 AM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button