Sanarwa

KO KASAN YADDA ZAKA NEMI LOAN NA AGSMEIS MARA INTEREST- NIRSAL BANK.

Sponsored Links

Kamar yadda babban bankin kasa CBN ya umarci bankin NIRSAL ya bawa “yan kasa bashi wanda babu kudin ruwa musamman ga musulmai domin cin moriyar arzikin kasa.
Bankin NIRSAL ya bude wannan bangare ga wadanda keda burin bunkasa sana’arsu ko kasuwancinsu a karkashi wannan tsari mai suna AGSMEIS (Agric Business Small and Medium Enterprises Investment Sceheme). A karkashin wannan tsari, gwamnatin tarayya ta yunkura wajan bunkasa ayyukan Noma da makamantan kasuwancin da suka shafi noma da kiwo domin kara bunkasa samar da abinci da kuma ayyukanyi ga al’umma.
YADDA ZA’A CIKE WANNAN PROGRAM:
Akwai matakai guda hudu da za’a bi cike kafin kammala shiga wannan program sune kamar haka:
Za’a shiga wannan website na hukumar: https://nibloans.nmfb.com.ng/agsmeisnoninterestlending sannan a danna New idan sabone ko kuma Returning idan kataba karba. Bayan haka shafin zai kawoka inda zaka kara karanta cikakken bayani gameda wannan program a inda zai nuna maka REFERENCE NUMBER dinka wadda zaka ajiyeta domin zatayi maka amfani nan gaba.
Sai ka shigar da BVN dinka domin a tabbatar da kaine ko kece ke neman wannan program (BVN Validation). Sai katafi Next
Zakaga bayananka sunfito domin tabbatarwa. Sai katafi Next
sai ka cike dukkan bayananka kamar su lambar wayarka, email dinka dadai sauransu.
Bankin Nirasal zai tura maka da sako cikin email dinka a inda zaka cigaba da wannan registration.
Bayan ka/kin shiga email dinki zaka sako daga Nirsal bank a inda za’a ga link wanda za’a danna wannan link domin cigaba da wannan cikewa.
Wannan link zai kaika inda zaka kara cike bayananka kamar su state dinka, local government dinka, karatunka dadai sauransu. Sai katafi next
Zai kaika inda zaka cike  cigaban bayananka kamarsu sunan kamfaninka, CaC Number, shekarar da kayi registar CAC dadai sauransu. Sai a danna Next
Zai kaiku inda zaku zuba dukkan abinda kuke bukata na kudi kamar su abubuwan da zaku saya, yadda zaku bunkasa kasuwancinku dadai sauaransu. Sai a danna Next
 
Daga nan fegin zai kaiku inda zaku saka email da lamabar waya ta Guarantor. Daganan sai ayi submitting na wannan application sannan a jira.

Domin Karin 

bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 

Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

Leave a Reply

Back to top button