Musabbabi Book 2 Page 1
MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
Page 1
Jin muryar Haj kilishi cikin kuka yasa Haj Rakiya ta yi saurin gyara zamanta tace, “Haj lafiya me ke faruwa?, na jiki cikin wani irin yanayi, kamar fa kuka ki ke yi”.
Haj kilishi ta saki wata katuwar ajiyar zuciya tace tana kokarin tsaida hawayen da ke cigaba da sauka a kuncinta, “Kuka na ke yi Haj, domin ina son na sami sauki da sassaucin matsananciyar damuwar da nake ciki, shin yaushe zan samu nutsuwa da kwanciyar hankali?, yaushe zan samu cikar duka burikana akan musaddik?”. Jin hakan yasa Haj Rakiya ta fahimci inda Haj kilishi tasa gaba, don haka ta tabe baki, ta kara janyo kwanon abincinta ta jefa wayar a speaker out ta aje ta cigaba da cin cinyar kazarta hankali kwance, sannan tace,
“Subhanallahi yanzu kuma meya faru me ake ciki?”,
Ta goge hawayenta tace “Anya kina ganin shi ma Tsiduhu aikinsa yana yi kuwa?”, da sauri tace “kai ai bana tababa aikinsa yana yi sai dai ko jinkiri, me kika gani kika ce haka kuma?”.
A hankali cikin sanyin guiwa haj kilishi ta kwashe abinda idanunta suka gani ta gayama Haj Rakiya.
Ta kara da cewa “jin zuciyata nake kamar zata fashe, wani irin zafi jikina yake min, na rasa abinda ke min dadi, kinga annurin dake kwance akan fuskar musaddik kuwa, kinga yadda yake wasa da dariya da maigadi, baida wata damuwa, ni ke da kudi amma shine yake da farinciki, shi yasa nake tunanin anya aikin Tsiduhu ya ci kuwa”.
Haj Rakiya ta tsotse kashin kazar ta watsar gefe, sannan tace “Bana jin a jikina aikin nan baiyi ba amma me zai hana mu kara komawa mu yi masa bayani kila ko akwai inda aka sami matsala idan kuma hakane muna zuwa zai warware mana komai”, Haj Kilishi tace “Eh gara mu koma din zanfi samun nutsuwa, sannan kuma mu je wajen mai Rakwacam shima ina bukatar yasan komai fa ya canja, yakamata ya kara bamu tabbaci akan ajiyar mu ta karkashin bishoyar kuka, domin ina fargabar ko an samu matsala”.
Haj Rakiya tace “Bana jin haka kawai dai kina wannan fargabar da gangane , domin ko dazu naje na duba wajen amma dai mu je din don hannu da yawa maganin kazamar miya”. Haj kilishi tace “Hakane haj”, Haj Rakiya ta dan muskuta tace “To wai Haj ya maganar maganin da Tsiduhu yace ki sama Afrah a abinci, kin sa mata kuwa?”,Haj kilishi ta kara cika da damuwa tace “Har yanzu ban sami dama ba domin yarinyar tamkar ta gane ni ,nafa gaya miki ko shigowa ta daina yi yanzu, to ta yaya zan sa mata a abinci ta ci”, Haj Rakiya tace “Haba sai kace ba ke ba, tsakani da Allah, ai kwantar da kanki zaki yi ki bi duk hanyar da zaki bi domin ganin ta ci abincin”, tace “To ta yaya?”. Tace “ki gayyatota da kanki cikin gidan ai ba zata ki zuwa ba daganan sai kisan yadda zaki yi ta ci abincin”, Haj kilishi cikin gamsuwa da maganarta tace “zan gwada yin hakan, domin yarinyar nan itace bala’i a gare ni yanzu, the n dai da ita a tsakani to bana jin zan sami sukunin rayuwa”.Daganan suka cigaba da tattaunawa sun tsaida maganar cewa zasu fara zuwa wajen mai Rakwacam gobe, jibi kuma su wuce wajen Tsiduhu, kai wannan wahala da yawa take,
Haj Rakiya ta mika hannu ta kashe wayar tana buga tsaki, ta mike ta je ta wanke hannunta, ta dawo ta zauna tana murmushi, gaskiya babu wahalalle sai mai bin malamai da bokaye, yanzu wannan rashin nutsuwar ta haj Kilishi ai katuwar masifa ce, ita dai kam ta dawo daga rakiyarta, yanzu neman kudi ke gabanta, idan so samu ne duk ragowar kudin haj kilishi su dawo hannunta, gashi nan kullum kaji take ci, har wani ja ta fara yi sabida cin nama.
Tayi dariya sosai ta janyo waya ta kira Tsiduhu ta sanar da shi komai, ta kuma gaya masa ya shirya suna tafe jibi, ya kuma tabbatar mata babu wata matsala a shirye yake.
Shigo da kayan da akayi yasa Afrah ta shi cike da farinciki, sannu ta dinga yi ma Baba maigadi har ya gama shigo da komai, sannan musaddik ya shigo rike da ledar atamfofi, ta mika hannu zata karba da sauri tana yi masa sannu da zuwa, maikan ya sakar mata ledar sai kawai ya janyo hannunta ya matseta sosai a kirjinsa, yana jin kamshin jikinta, itama lafewa tayi a kirjin nasa tana jin wani irin dadi yana ratsa zuciyarta, gaskiya ne mahakurci mawadaci, a haka suka karasa cikin falon sai da suka zauna sannan tabar jikinsa cike da fara’a tace tana kallonsa “ yaya wadannan kayan fa”, ya yi murmushi yau jinsa yake cikakken magidanci, har wani girma yaji yana ba kansa .
“Albashina ne, naje nayo mana siyayyar kayan abinci, ki duba ki gani ina jin ai ban manta komai ba ko?” Tace cikin nuna godiya, “ Bana jin ka manta wani abu, Allah ya saka da alheri Allah ya kara budi ya kara wadata, nagode”yace “kin fi haka Afrah, duk abinda zan nema saboda ke ne, don ta ni na rantse miki ko nera bazan fita na nema ba, amma ina son ganin farincikin ki shi yasa zanyi komai domin na dauwamar da wannan murmushin a fuskarki,” ta gyada kai tace “Nagode da wannan kulawar”.
Ya mika mata ledar hannunsa yace “Ga wannan ki dauki guda biyu , idan zaki tafi islamiyya ki tafima da inna Halima daya”, bata gama wannan mamakin ba taga yasa hannu a cikin aljihunsa ya fito da kudi ya mika mata dubu biyar yace “wannan kuma ki kaima kawu Mahmud ya yi cafane”.
Kawai saita rungume shi sosai, harda kwallar farinciki, ya dagota yana share mata hawayen, “ meyasa kike kuka?”, ta lumshe ido hawaye ya kara fito mata tace “Kukan farinciki kawai nake yaya, Allah ya yi min dukkan gata na hadani da kai a matsayin abokin rayuwata”, ya girgiza kai yace “Ni zanyi ma Allah godiya da ya bani mata irinki, amma ni sai dai kawai ki yi maleji da ni”, ta bugama mai duka a cinyarsa tace cikin dariya “ kafi karfin maneji haba yaya , mijin nawa zaka kira maneji”, yayi dariya yace “Gaskiya ne fa”, ta fito da da atamfofin tana kallo, ta dago ta dube shi sosai tace “kai tsaya yaya, wadannan kayan da irin wannan siyayyar da kayi sun fi karfin albashinka, ya akayi haka?”.
Ya yi ajiyar zuciya yace “madalla da mata irinki me kokarin ganin ta san halinda mijinta yake ciki”. Ya kara matsantarta sosai yace “Haj tayi min karin wasu kudin bayan albashina”. Ta zuba masa ido tace “ Allah ya saka mata da alheri, lalle tasan martaba tare da darajar ma’aikatanta”.sun dade suna cigaba da maganganunsu, daga bisani musaddik shine ya tayata gyara cikin store suka jera kayan abincinsu a ciki lemo kuma suka shirya a cikin frij ragowar suka maida store komai ya yi kyau.
Saida suka gama komai yamma likis, sannan musaddik ya tashi zai fita .
Afrah ta zuba masa ido ta ji wani iri a cikin jikinta, domin ranta ya bata cewa wajen shaye shayensu zai tafi, a sanyaye tace “ yaya musaddik, don Allah ka daure kada ka yi almubazzaranci da abinda ya rage maka ma’ana kada ka fita kaje ka sha wani abu da zai sa ka wulakanta , kada ka je ka sha abinda zai maida min farincikina bakinciki”.
Jikinsa ya yi sanyi a hankali ya koma ya zauna ya kama kansa ya rike tam, kawai sai yaji hawaye yana fita masa, ta dawo kusa da shi ta zauna tana kallonsa cike da damuwa da kulawa tace “ka daina kuka don Allah “.
Ya kara yin kasa da kansa domin baya son taga hawayensa, nan da nan itama taji na ta hawayen yena sauka a saman kuncinta, yace kai a kasa “ki yi hakuri Afrah ki barni na fita, na rantse miki ji nake kamar zan mutu idan ban sha ba, ki barni na je nayi miki alkawarin bazan sha da yawa ba”, ta ji wani abu a ranta, a hankali ta goge hawayenta tace “Tashi ka tafi Allah ya shiryeka”.
Sai da ya dauki wasu mintoci sannan ya iya tashi amma ya kasa hada ido da ita har ya fice.
Ta koma ta zauna sosai akasan dakin tana tunanin akwai wani abu a boye a cikin lalacewar rayuwar musaddik, amma yau ta tabbatar musaddik ba dai dai yake ba, akwai sa hannu a cikin lamarinsa, shin waye yake son ganin bayan musaddik? Waye yake adawa sa ganin kyawun rayuwarsa? Waye zaiyi masa irin wannan mugun abin?.
Kamar amsar tambayarta kawai ta ji wayarta ta dauki kara tana dubawa ta ga Haj kilishi ce.
Cikin dimbin mamakin ganin kiranta a wayarta abinda bata taba gani ba, da sauri ta dauka ta sa ta a kunnanta, bayan gaisuwa sai taji Haj kilishi cikin sanyin murya tace “ idan babu damuwa ina son ganinki yanzu”. Cikin nauyin murya tace “Babu komai gani nan zuwa”. Ta yi kasa da wayar tana mamakin wane irin kira take yi mata.
Daga bisani dai tashi tayi ta sanya hijabinta ta fice zuwa cikin gidan.
Tana shiga falon cikin sallama, tayi mamakin yadda taga Haj Kilishi ta amsa mata cikin fara’a da annashuwa, abin mamaki har tana ce mata “ shigo ki zauna”.
Cikin karin mamaki ta lalubi kujera ta zauna, sun gaisa cikin kwanciyar hankali, ta kwalama mai aikinta kira tana shigowa ta dubeta tace “ ki kawo ma Afrah abinci”, da sauri Afrah ta dubeta tace “Allah Haj na koshi Allah amfana”, Haj Kilishi ta canja fuska ta dubeta tace “Dama ina son na tabbatar da abinda nake zato ne yasa nace a kawo miki abinci, da gaske dai fushi ki ke da ni ko Afrah”,Afrah tayi saurin cewa “A’a fushin me zanyi da ke, ni babu abinda ki kayi min”, ta dubi mai aikin tace “je ki kawo mata abinci”, ta wuce da sauri ta fita, maganar da Haj kilishi ta yi yasa Afrah ba ta kara yin musu akan cin abincin ba, harta kawo abincin ta aje ta fita babu wanda ya yi magana sannan Afrah ta dan gyara zamanta tace “Haj kince kina son ganina”, ta gyada kai tace “Eh haka ne, Afrah naga abubuwa na ta faruwa wanda raina baya min dadi, tun ranar da ki ka zo neman taimakona agame da musaddik na ki miki, naga gaba daya daga ke har musaddik din duk kun canja min, wanda na shiga damuwar hakan, na kuma yi nadama kwarai da gaske”.
Ta numfasa tana kallon Afrah wacce gaba daya ta yi shuru tana saurarenta abubuwa da yawa kuma na yawo a cikin kwakawalwarta, har ta cigaba da cewa “shi yasa naga dacewar na kiraki na baki hakuri, saboda duk wani abu da zaisa na nisanta da musaddik bana kaunarsa domin musaddik yana da matsayin da yayan da na haifa ma a cikina basu da shi, wani lokacin ne kawai za’a ga kamar ina baya da lamarinsa to ba komai yasa haka ba sai takaicin halinda ya jefa kansa na shaye shaye abun na yi min zafi”.
Ido kawai Afrah ta sa mata ta kuma rasa dallin da yasa bata yarda da ko kalma daya da Haj kilishi ta fada ba, domin dai batun ta na son musaddik wannan ma bai taso ba.
Afrah tace “Babu komai Haj ki kwantar da hankalinki ni gare ni tuni komai ya wuce, rashin shigowata kuma uzurori ne su ka yi min yawa, shi ma kuma yaya musaddik din yanzu akwai hidima me yawa a kansa, saboda haka sai anyi hakuri da mu”, ta gyada kai tace “To shikenan, Allah ya yi mana jagora, ki ci abincin”, Afrah tasan idan tace zata cigaba da musun cin abincin Haj kilishi zata cigaba da maganganunta da ta gaji da ji, don haka ta janyo faranti ta zuba abincin dan kadan.
Idon Haj kilishi na dore a kanta harta ci abincin cikin bismilla wanda ko da da gaske asirin ne wannan bismillah da tayi babu tasirin da asirin zai yi babu abinda zai sanetw, balle ba wani abu bane face dakakken garin sassaken baure da Tsiduhu ya bata.
Jin zuciyarta ta yi fes, domin tana ganin zubar da kimarta da ta yi ta ba Afrah hakuri, bai tashi a banza ba, tunda ta sami cikar burinta.
Afrah kuwa tana gama cin abinci, ta dan cigaba da zama kadan, kafin daga bisani tayi sallama da ita ta koma bangarenta.
Haj kilishi ta saki tsaki bayan fitarta ta furta a fili, “ Na tsaneki Afrah, na tsane ki, lokacin ganin bayanki kuma ya yi”. Da kanta ta tashi ta dauki sauran abincin ta zubar a kwandon shara. Tana jin aranta daga yanzu zuwa ko wane lokaci asirin Tsiduhu zai fara tasiri a jikinta. Rashin sani ya fi dare duhu.
Yau talata, tun goshin azahar Haj Hudah ke yawon gaida marasa lafiya a asibitoci tana taimakawa wanda rabonsa ya rantse. Musaddik kuwa da ya dan sami dama yakan sami wajen da zai lafe ya dan bushi sigarinsa. Sai dai ziciyarsa na cika da jindadin yadda Haj Hudah ke kokarin taimako duk da yasan abin duk riya ce, tunda komai ta yi sai media sun dauka sun watsa ma duniya. Ga wani abu daya da yake kara sa shi farinciki shine yadda a yanzu duk fitar da zasu yi da ita take sa hijabi maimakon dan tayani gantalin gyalen da take sawa a da.wanda duk sanadiyyar nasihar da ya yi mata ne.
Suna kan hanyar dawowa gida karfe biyar da kwata na yamma, dukkan idanun Haj hudah suna kafe akan musaddik ko yaya ya motsa jin tsigar jikinta ta ke tana tashi, tana jin musaddik tamkar wani jininta, tana damuwa da shi da lamarinsa kai kace wani ne shi acikin rayuwarta, me yasa iya kuncin da take ciki da ta ga musaddik sai ta manta da komai sai farinciki kawai?, tana kokarin nemo amsoshin tambayoyin da ke dankare a cikin zuciyata ne, daya daga cikin wayoyin ta ta dauki kara, ta dauka ganin Alh yusuf sanda ne yasa ta dauka cikin rashin nuna murna da ganin kiran nasa suka gaisa, yadda musaddik ya ji suna magana ne yasa ya gane Alh yusuf sanda ne, haka zalika rashin fitar sautin muryar Haj Hudah da murna yasa musaddik ya ji a jikinsa kila saboda yadda Alh yusuf sandan baida lokacinta yasa ta canja masa, baya son shiga abinda bai shafe shi ba, amma gaskiya da yace Haj hudah tana kokari sosai wajen rashin samun lokacin mijinta.
Cikin wata irin murya Alh yusuf sanda yace, “kina tare da musaddik ne?”, duk da tambayar ta yi mata bazata bai hanata bashi amsa ba tace “Eh munq tare, naje asibiti ziyara ne yanzu muke hanyar komawa gida”, wani bushasshen murmushi ya yi sannan yace “Yana da kyau hakan”, sam bata wani zumudin jinsa a wayar, don haka ta yi masa sallama, sai dai kafin ta kai ga aje wayar, ya kara watso mata wata tambayar, “ Har munyi sallama, ga mamakina yau ba ki tambaye ni yaushe zan dawo ba kamar yadda ki ka saba kullum mu kayi waya”, ta dan shaki numfashi kafin tace “meye amfanin tambayar idan har nasan amsar”, nan ma bai ja maganar ba ya yi sallama da ita ya kashe wayar.
Zubama wayar tasa ido ya yi, na rasa tunanin da ya yi kawai sai ya fashe da dariya sosai, ya tashi ya shiga shawagi a tsakiyar dakin, yana jin wata iska na shigarsa, maganganun Haj Hudah ko kadan basu dame shi ba, illa kokarin gano asalin gaskiyar da ke cikin maganganun nata.
Haj Hudah ta maida kanta kasa, yau damuwa ce fal a ranta, domin duk dadewar da Alh yusuf sanda yake yi baya tare da ita, abin bai taba damunta irin na wannan lokacin ba, ta dawo da kallonta ga musaddik wanda wayarsa ta dauki ruri da sauri ya dauka, “ Ranki ya dade mace daya tamkar ya dubu, kamar kin san ke nake tunani”. Tagumi kawai Haj Hudah tayi ta zuba masa ido tabbas shi da matarsa ne, domin yadda yake jifanta da kalamai masu matukar ratsa zuciya, ji take kamar da ita yake, itama fa tana bukatar irin wannan kulawar, musaddik daban yake acikin maza. Hakanan kuma take jin zafi da kuna a cikin zuciyarta, irin zafin da take ji a duk lokacin da ta ji musaddik da Afrah akan waya, wai me ke faruwa ne?.
Bata samu amsar tambayarta ba, direba ya tsaida mota a harabar gidan. A fusace ta fito daga cikin motar, tana yi ma musaddik wani irin kallo me cike da jin haushi, baisan ma abinda take yi ba domin har yanzu yana kan waya da Afrah.
Ta sauke wani tsaki a hankali, tana jin kirjinta ya kusa fashewa da takaicin rashin dalili, hakan yasa ta bude jakarta ta fito da nera dubu ashirin ta matso sosai kusa da shi ta dora masa a saman cinyarsa, sai alokacin ya juyo suka hada ido sosai, wani irin kallo ta sakar masa wanda baisan da me zai iya fassara kallon ba, lokaci daya kuma ta yi wani bushasshen murmushi, sannan ta wuce da sauri cikin gida.
Shi dai bai aje wayar ba illa kallo da ya bita da shi harta bacema ganinsa. Ya fito a motar ya tura kudinsa a aljihu yana yi mata godiya a cikin zuciyarsa, bayan sun gama wayar ne ya jefa wayar a aljihu ya yi sallama da sauran jama’ar wajen da wadanda suka dawo tare sannan ya fice, ya kama hanyar inda yake leka abokansa. Sai dai zuciyarsa babu abinda take bijiro masa da shi illa fuskar Haj Hudah dake cike da tashin hankali da kunci gami da takaici, wanda ya danganta hakan da kila ta sami matsala da mijinta ne dazu a waya, ko ma dai menene Allah ya kawo mata agaji domin dai a ganinsa Haj Hudah bata cancanci wannan irin rayuwar ba, tana da kirki a ganinsa.
Yar gidan imam ✍️