Hausa NovelsMusabbabi Book 2

Musabbabi Book 2 Page 10

Sponsored Links

 

 

MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere )

Page 10

Ya yi wata irin miƙa ya cigaba da cewa “Me yasa ki ka canja da yawa, ada ban sanki da yi min ƙarya ba, kina ƙoƙarin gaya min gaskiya komai ɗacinta, me yasa ni ban iya canja ki ba?, me yasa Musaddiƙ ne zai canja ki?. Nan ma wata irin siririyar dariya ya saki lokaci ɗaya ya ƙurama wayar hannunsa ido, tamkar yana magana da wani yace “ Duk wani motsinki yana kan idona, ko ina gari tare da ke ko ba na gari tare da ke nasan duk abinda ki ke ciki”. Ya aje wayar ya ɗauki kofin lemonsa ya cigaba da sha hankali kwance cikin nishaɗi da kwanciyar hankali.

Haj Rakiya dai ta ga ta kanta, domin haka ta ƙara kwana cikin cell cikin cizon sauro da yunwa, domin dai duk kiran da take ma Mallam Tasi’u to fa ya ƙi zuwa, sai da ya ga dama sannan wajen yamma ƙarfe biyar da kwata Mallam Tasi’u ya iso police station ɗin, fes da shi cikin shadda koriya mai ɗaukar ido, bai waiwayi Haj Rakiya ba har sai da ya dangana da tebur ɗin insifektan ya ji duk irin laifin da Haj Rakiya ta aikata, hannu kawai yasa ya dafe kansa, yana jin wani irin tsana da ƙyamar Haj Rakiya, da ko aka yanko masa kuɗin da zai biya na beli, ji ya yi babu yadda za’ayi ya yi asarar kuɗinsa akan Haj Rakiya, don haka ya nemi alfarmar ganinta kofur Lawal ne ya kai shi har inda take.

Sai da Mallam Tasi’u ya yi da gaske sannan ya iya lalubo Haj Rakiya acikin ɗimbin mutanen da ke cikin cell ɗin, yadda ta yi baƙin ƙirin ta fita hayyacinta ta yi mugun ramewa, ta kasa haɗa ido da shi, shi kuma sai banka mata wata muguwar harara yake yi, cikin kausasshiyar murya yace “ Rakiya, ni ba ni da kuɗin da zanyi belinki, ko da ina da shi kuma na rantse bazan asarar da su ta hanyar belinki da su ba, don haka idan har ki na jin kin gaji da zaman wajen nan, to ki fito da kuɗin da kika aje wanda ki ke cin kaji kullum kwanan duniya, kinga yau sai su yi miki ranar da ya kamata, ki fito da su ayi belinki da su”, nan da nan idanunta suka kaɗa su kayi jajir tace “ Ba ni da wani kuɗi yanzu a ɗakina, duk kuɗaɗena suna wajen Babaye Dillali da na yi nufin sayen gida ta hanyarsa, kuma ni kaina yanzu bansan inda zan gan shi ba, don kuwa ya rufe wayarsa”.
Mallam Tasi’u ya sakar mata wani sakaran kallo yace “ ke yanzu saboda rainin arziƙi har gida zaki saya amma ni bansani ba, ba ki kuma sa ni a cikin maganar ba to ai ya yi kyau”, ta marairaice murya tace “Don Allah kayi haƙuri……..?,
Bata kai aya ba ya dakatar da ita “ka da ki dameni da wani ban haƙuri ni meye nawa, dama a yanzu ai kinfi buƙatar mallakar gida fiye da komai”, ta dube shi sosai tace “ Ban fahimci maganar ka ba”, yace “ zaki fahimta, yanzu sai ki faɗi inda za’a sami kuɗin da za’ayi belinki”, ta yi jugum cike da tashin hankali sannan ta ɗago tace “ sai dai ka je ɗakina ka fitar da duk wani abu wanda idan aka sayar zai isa ayi belin nawa, sai a sayar kazo ka fitar da ni a wajen nan”, shuru ya yi yana yi mata wani watsattsan kallo, wanda yasa ta ƙara rikicewa domin babu komai a cikin idanunsa sai tsana, a hankali cikin magiya tace “ Don Allah ka taimake ni zaman wajen nan masifa ne, ka duba kaga yadda sauro ke kwashe dukkan albarkatun jikina, ga rashin bacci ga yunwa ga zazzaɓi mai zafi da nake ji a jikina”, ya watsa mata harara yace “ waye ya ja ma kansa idan ba ke ba, kaɗan ma kenan domin wannan masifar duniya ce kawai saura na lahira”. Yana gama faɗin haka ya juya ya fice a binsa.
Yana da kuɗin da zai iya yin belinta don haka ya wuce gidan da amaryarsa take ya sanar da amaryarsa Hafsatu ta fara shiri, domin zai saki gidan hayan da suke ciki, zata koma ainihin gidansa gobe da safe. Cike da mamaki Hafsatu tace “ matar ta ka fa, da kake shakkar tasan kayi aure”, ya girgiza kai yace “ Na dai gaya miki ki fara shiri kawai, dama kuɗin wata uku na iya badawa”. Daganan ya fice ba tare da ya yi mata wani ƙwaƙƙwaran bayani ba.
Kai tsaye gidansa ya nufa, duk wani abu na mora dake ɗakin Haj Rakiya ya nemi masu motar ɗaukar kaya ya kwashe zuwa gidan amaryarsa ya zube su anan, ya koma ragowar kayan kuma duk ya fito da su daga ɗaki ya zube mata su a tsakar gida, da shi da wasu almajirai suka share ɗakin fes sannan ya sallame su. Atakaice dai zuwa safe sun tare da shi da amaryarsa a ɗakin Haj Rakiya.
Ita kuwa tana can tana tsammanin dawowarsa amma har gari ya waye bai dawo ba, acikin mutanen cikin cell ɗinne ta samu wata mai ɗan sauran imani ta sammata kokon da aka kawo mata da safen, domin fahimtar da ta yi na Haj Rakiya tana cikin matuƙar yunwa.
Mallam Tasi’u bai iso police station ɗin ba sai ƙarfe goma shabiyu na rana, kai tsaye ya je ya biya kuɗin belin.
Ba’a daɗe ba aka fito da Haj Rakiya, sai tashin wari take, da sam mallam Tasi’u ya kasa tsayuwa kusa da ita, don ko da suka fito, dubu biyar ya miƙa mata yace “ Ragowar kuɗin kayanki da aka sayar sai ki hau mashin ki ƙarasa gida”, kafin ta buɗe baki ta yi magana ya wuce da sauri tana kallo ya tare a daidaita sahu ya shige ya yi tafiyarsa ya barta tsaye kamar wacce aka dasa.
Wannan ɗabi’un da mallam Tasi’u yake nuna mata, ya fara bata mamaki domin idan da ne akace mata zai iya yi mata haka zata ƙaryata, amma tasan yanzu dole saita daure ta kuma kau da kai daga duk irin wulakancin da zai yi mata, tunda asirinta ya gama bankaɗewa bata da wani bakin da zata kare kanta, sai dai ta lallaɓa, son zuciya da son abin duniya gami da kauce hanyar Allah duk shi ne silar faɗawarta cikin wannan masifar.

Cikin sanyin jiki da rashin ƙwarin guiwa Haj Rakiya ta tare a daidaita sahu ta wuce gida, sai dai ta rasa dalilin da yasa gabanta ke faɗuwa, haka zalika har ta kai gida nambar wayar Babaye Dillali take kira, amma a kashe, haka ta shiga gida cikin tashin hankali, sai dai kuma shigarta gidan ya ƙara tattago mata wani tashin hankalin, domin ganin tarkacen kayanta a zube a waje, cikin rawar jiki ta ƙarasa bakin ƙofar ɗakinta inda take jiyo muryar Mallam Tasi’u, yana ba da labarin irin mugun abinda Haj Rakiya ta aikata, ta ji ya ƙara da cewa “ Ni a yanzu duk duniya babu wacce na tsana sama da ita, ashe yar dakon shaiɗan nake zaune da ita, ni kaina Allah kaɗai yasan mugun abin da ta ƙunsa min”, bata fita daga fargabar maganarsa ba kawai ta ji muryar mace ta yi dariya tace “ shi yasa ma ka ke tsoronta ashe an gama wankema kasha ne, amma dai bata jidaɗin rayuwarta ba, wannan ma ai abin tsoro ce”, yace “ Abin tsoro ce kuwa sosai, kuma kada ki ƙara cewa ina tsoronta, kawai dai ina rakata ne kuma a yanzu dai komai ya zo ƙarshe”. Cikin tsananin rawar jiki ta yaye labulen don taga wacece a cikin ɗakinta, kuma meye dalilin ganin kayanta a waje.
Tana faɗawa ɗakin daga Hafsatu har Mallam Tasi’u tsayawa su kayi suna kallonta, kafin ta yi kan Hafsatu ta shaƙeta tana tambayarta dalilin kasancewarta da mijinta, a fusace Mallam Tasi’u ya tashi ya ɗauke Haj Rakiya da mari, wanda hakan ya yi sanadiyyar dawowarta hayyacinta, ta tsaya ta dafe kuncinta tana yi masa kallon mamaki, tace “ yanzu ni ka mara akan karuwa”, Hafsatu zata yi magana Mallam Tasi’u ya rigata cikin fusata yace “ kada ki ƙara kiran matata ta sunna da karuwa…” ta fiddo idanu gaba ɗaya waje tana makerkyata tana maumaita “ matarka?”.
Ya matso kusa da ita sosai yace “ ƙwarai da gaske matata ce na aureta” ta yi ƙasa da kanta tana sharar hawaye tace “ Matarka, ka yi aure baka gaya min ba kuma ka sata a ɗakina, sannan kuma ka watsar min da kayana waje”.
Ya kafeta da ido, yayin da Hafsatu ta koma ta zauna akan kujera ta harɗe ƙafa tana yi ma Haj Rakiya kallon biyu saura kwata, gami da wani murmushin rainin wayau.
Mallam Tasi’u yace “ Na fitar da kayanki waje ne saboda bazan iya zama da mushirika irinki ba, wacce ta maida bin bokaye da malaman tsubbu ibadar rayuwarta, ni gaba ɗaya tsoro ki ke ba ni, don haka na yanke duk wata alaƙa da ke tsakanin mu”, a gaggauce tace “me kake nufi da faɗin hakan?”. Ya tsaida idanunsa kem a kanta sannan yace “ ina nufin na sake ki saki uku tabbatar babu kome, don bana son wani abu ya ƙara shiga tsakanina da ke, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu”.gaba ɗaya ji tayi jiri na fisgarta, kuka take yi sosai wannan karon da ƙarfi take kukan tana kira ma kanta ta shiga uku ta lalace, lokaci ɗaya kuma ta durƙushe ƙasa tana yi masa magiya, ya dubeta sosai yace “ Me ki ke so na yi miki kuma, kada ki ɓatama kan ki lokaci, kada ki manta saki uku na yi miki”.
Ta kasa ɗagowa daga durƙuson da ta yi, gaba ɗaya duniyar juya mata take yi tana jin kamar ana fisgar naman jikinta, shin ina zata?, kawunta na gadon asibiti bayan ma hakan matar kawun nata ba sauƙi gareta ba, ko kawun nata ya barta ta zauna a gidansa to a gaskiya zaman bazai mata daɗi ba don tafi kowa sanin rashin kirkinta. Lokaci ɗaya Babaye ya faɗo mata arai, da sauri ta miƙe tamkar hauka sabon kamu ta fice da gudu ko abin hawa bata nema ba da ƙafarta ta cigaba da tafiya zuwa gidan Babaye.
Bata daɗe da fita ba me sayen kayan ɗakin Haj Rakiya ya kira mallam Tasi’u ya sanar da shi yana ƙofar gida, ya dubi Hafsatu yana dariya yace “ yanzu zaki fanshe shaƙar da Rakiya ta yi miki, da kuma ribar shurun da ki kayi ba ki tanka ta ba”, ta yi dariya tace “ Ina jira maigidana nagode”. Da sauri ya fita, tare suka rankaya zuwa tsohon gidan da ya ɓoye kayan. Mai sayen kaya ya gani ya kuma yi tayin mutunci don haka mallam Tasi’u ya sayar masa, take ya cake masa kuɗinsa ya kwashe kayan. Mallam Tasi’u ya fitar da kuɗin da ya yi belin Haj Rakiya, a cikin ragowar yaba Hafsatu dubu ashirin ta ja jali, wai bakinta har kunne don murna ta yi ta godiya. sauran kuɗin ya jefasu a aljihunsa dasu yake sa ran yin jali shi ma hankalinsa kwance ya yar da ƙwallon mangoro ya huta da ƙuda.

A ƙalla sai da musaddiƙ ya yi kwanaki huɗu a ssibiti kafin a sallame shi, wanda zuwa wannan lokacin Haj Hudah ta kasa daurewa dole tun ranar da Afrah ta kwana washegari direbanta ya dawo da ita Minna, domin yadda musaddiƙ da Afrah ke cikin shauƙin soyayya abin yana dugunzuma zuciyarta, bata son zuciyarta ta tabbatar da ƙiyayyar Afrah a cikinta don haka ta tattara tabar garin, bayan ta gama biyan kuɗin na asibitin musaddiƙ ɗin, haka zalika ko da aka sallame shi direban ta ne ya zo ya tafi da su Minna. Sai waya kawai ta yi da Musaddiƙ ya yi mata godiyar irin ɗawainiyar da ta yi da shi, daga bisani ya miƙama Afrah wayar itama ta yi mata godiya sosai.
Isar su gida Baba maigadi ya ji daɗin ganin Musaddiƙ cikin lafiya, kallo ɗaya kuma ya yi ma fuskarsa ya tabbatar da wannan shine asalin Musaddiƙ ɗin da ya sani, Allah abin godiya, Bayan sun gama gaisawa da Musaddiƙ ne cikin irin girmamawar da yake yi masa tun farko, sannan kai tsaye Musaddiƙ ya nufi ɓangaren Haj Kilishi, Afrah tana tsaye tana kallonsa, a yayinda Baba maigadi ya yi gaggawar dubansa yace “ Musaddiƙ ina zaka je?”, ya ja ya tsaya ba tare da ya juyo ba yace “ zan shiga na je na duba Haj da jiki ne”, Baba maigadi ya wage baki cike da ɗimbin mamaki yace “ yanzu Haj ce zaka je don duba lafiyarta? Kasan abinda ta yi maka kuwa?”, ananne ya juyo yana dubansa gaba ɗaya, shi kuma Afrah yake kallo yace “ Afrah, kin ko yi masa bayanin komai”, kafin ta yi magana Musaddiƙ yace “ Na sani Baba, ta kuma yi min bayanin komai, amma hakan bazaisa na ƙullaceta ko na wofintar da ita ba, a yanzu tana buƙatar kulawa, bani da wani abu da zanyi mata domin huce haushin abinda ta yi min, kuma tunda Allah ya yi min sakayya meye amfanin jin haushi, ko ƙullatarta”.
Afrah ta harɗe hannayenta a ƙirjinta tana yi ma Musaddiƙ wani irin kallo me cike da nuna jarumtarsa da kuma tsananin ƙaunarsa, sosai take alfahari da shi matuƙar alfahari.
Ya cigaba da cewa cikin rashin nuna damuwa da irin kallon namakin da Baba maigadi yake yi masa. “ Duk kuma abinda tayi kanta ta yi ma, tsakaninta da Allah kuma ya rage domin ni tuni na yafe mata har cikin zuciyata”.
Baba maigadi cike da ƙaunar halayyar Musaddiƙ da kuma ƙara tabbatar da cewa Ya dawo musaddiƙ ɗinsa, ya jinjina kai yace “ Ta ya ya Allah zai bar duk wanda ya taɓa mai kyakkyawan hali irin na ka, Allah ya yi maka albarka, sai dai kuma Haj bata gidan?”.
“ Ina aka kaita?” Lokaci ɗaya suka haɗa baki da Afrah da Musaddiƙ suka tambaya, Baba maigadi ya jinjina kai cike da jimami yace “ Ai abin na Haj ya ci tura, zama tare da ita tamkar ganganci ne don haka jiya Hassana da Hussaina suka kaita gidan mahaukata na cikin gari, tunda shi ma maigidan Hassanan yace bai yarda ta zauna ta yi jinyarta ba, sai dai ta zaɓa ko jinyar ko aurenta, dama Hassanar ce mai tausayin don Hussaina tunda ta zo ta ganta sau ɗaya bata dawo ba sai da zasu kaita gidan mahaukatan”.
Musaddiƙ ya nisa cike da ɗimbin damuwa yasa hannunsa ya shafi fuskarsa yana faɗin “ Hasbunallahu wani’imal wakil”, Afrah tace itama wannan karon akwai damuwa akan fuskarta tace “ Haj ce ke gidan mahaukata, ke duniya ina zaki da mu”.
Baba maigadi yace “Ta na can Afrah, domin halin da take ciki ya ƙazanta tunda harta fara duka ga uwa uba tonon asirin da take ta yi ma kanta”.
Wasu siraran hawaye suka zubo da ga idanun Musaddiƙ cikin mutuwar jiki yace “ Allah ya bata lafiya”, ya juya ya shige ɓangarensa, Afrah ta bi bayansa.
Baba maigadi su ka bari baki sake, yana jinjina zuciya irinta Musaddiƙ, lallle musaddiƙ mutum ne ya kuma cika ɗan halak wanda ba ya rama sharri da sharri, Haj kilishi dai yau babu wani boka da zai iya cireta daga wannan masifar da take ciki, kuɗi kuma gasu nan basu hana masifa faɗa mata ba babu wani rana da suka yi mata, dama kuma ƙarshen duk wanda ya kaucewa hanyar Allah kenan, mu da aka bamu kur’ani har me muke nema a duniya babu warakar da babu acikin kur’ani, ya Allah kasa mu fi ƙarfin zuciyar mu………..

Yar gidan Imam✍️

Leave a Reply

Back to top button