Musabbabi Book 2 Page 12
MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
(mrs Aliyu Mayare)
Page 12
A gaggauce Afrah ta ɗago da idanunta da suka kaɗa su kayi jawur, ta ɗorasu akan Musaddiƙ tana cewa, “ A cire ciki yaya Musaddiƙ?”, ya gyaɗa kai shi ma damuwarsa ta ƙara yawa, a sanyaye yace “ Eh, ki yi haƙuri a cire domin samun lafiyarki, da kuma samun natsuwata”, duk yadda ta kai da tare hawayenta ka da ya sauka sai da ya gangaro saman kuncinta, cikin rawar jiki Musaddiƙ yasa harshensa ya shiga ɗauke hawayen na ta.
Ta runtse idanunta kam, tana jin nauyin faɗan abinda bakinta ke son faɗa, amma ba ta da wani zaɓi da ya wuce a yau ta bijirema umarnin mijinta abinda ba ta taɓa tunanin zata iya yi ba a rayuwarta. Ta buɗe idonta a hankali tace “ka yi haƙuri amma bazan iya zubar da cikin nan ba, bayan shi ne shaidar soyayyarka a gare ni, ko da zan rasa raina na yarda matuƙar ɗan da zan haifa zai rayu, domin ina da tabbacin zaka zamar masa uwa da uba, ba kuma zaka taɓa barinsa ya yi kukan rashin uwa ba”, nan da nan Musaddiƙ ya haɗe fuska, ya zare kansa daga kan gadon ya tashi tsaye, yayinda ta bi shi da kallo, ya dawo gefen da take kwance ya na kallonta yace , “ Kina tunanin zan iya yin wata kyakkyawar rayuwa ne ba tare da ke ba, me yasa ba zaki yarda da uzurina ba, tunda likita yace akwai matsala ai yakamata ki yi tunani babu yadda za’ayi na bari ki salwantar da rayuwarki saboda kawai ki kawo ɗana ko yata duniya, idan hakan ya kasance bazan taɓa yafewa kaina ba, don haka dole ki bari a cire cikin nan”. Ya ƙarasa maganar cikin fusata, Afrah ta goge hawayenta cikin dakewa tace “ Na shirya kawo ɗanka duniya ko da zan rasa raina, babu kuma abinda zai canja hakan, domin na riga na yankema kaina hukunci”, ya tsaida jajayen idanunsa akanta yace “ Ba zaki bi umarni na ba kenan”, ta girgiza kai tace “ wannan karon dai kayi haƙuri kayi min kuma uzuri, sannan ka fahimce ni”.
Ba tare da ya ce uffan ba ya juya ya fice daga ɗakin.
Lokaci ɗaya kuka mai ƙarfi ya ƙwacema Afrah yau itace rana ta farko da ta bijirema umarnin mijinta, haka zalika ba ta jin duk duniya akwai wanda zai sa ta ta zubar da cikin musaddiƙ.
Ba’a jima ba Musaddiƙ ya dawo tare da likitan, ya kawo shi ne musamnan domin ya yi mata bayani da bakinsa, amma wani abu mafi ɗaure kai shine yadda sam Afrah ta ƙi sauraron likitan, haka zalika abinda ya ƙara tsorata Musaddiƙ shi ne yadda duk bayanin da likitan ya yi mata bai tsorata ta ba, bai kuma sagar da guiwarta ba, domin dai ta dage tana nan akan bakanta na baza ta bari a cire mata ciki ba.
Likita ya dubi Musaddiƙ yace “ ka yi haƙuri babu wani abu da muka isa mu yi ba tare da amincewarta ba”, ya na gama faɗin haka ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice, cikin jin zafi da fushi Musaddiƙ ya dubi Afrah, ita kuma ta yi saurin kau da kanta domin ba zata juri ganin damuwar da ke cikin idanunsa ba, ya kasa magana sai kallonta da yake yi yana jin kamar ya yi mata kaca kaca amma ba zai iya ba, bai taɓa zaton Afrah ta na da kafiya haka ba, duk kallon mace mai sauƙi yake mata amma yau gaba ɗaya ta goge masa hadda. Shi ma ficewa ya yi ya na son ya sami wani keɓaɓɓen waje da zai je ya zauna ya yi kukansa sosai, ko ya samu sauƙin damuwar da ke damfare a cikin zuciyarsa. Itama can Afrah kukan take ta fi jin zafin yadda ta karyama Musaddiƙ zuciya fiye da abinda ke faruwa da ita domin dai tasan komai daga Allah ne ta kuma yarda da ƙaddara, mutuwa kuma tasan babu wanda zai tsallake sai dai idan lokacin mutum baiyi ba, don haka kare cikinta da kawo shi duniya shi ne abu na farko dake gabanta a yanzu.
Har aka sallami Afrah daga asubiti babu wani jituwa tsakaninta da Musaddiƙ, domin duk hanyar da zai bi ta yarda a cire cikin ya bi amma ta ƙi yarda, don kuwa har Mallam Mahmud da Inna Halima ya kawo mata asibitin suka yi zama na musamman, amma fa Afrah ta ƙi yarda maimakon hakama cikin sani da hikimar iya zance irin na ta ta sami nasarar karkato da hankalinsu suka kuma yarda da cewa faɗen likita ba faɗen Allah ba ne, sannan Allah ba ya ɗorawa rai abinda ba zata iya ɗauka ba, don haka ya ga zata iya ne yasa ya bata cikin, idan kuma ta rasa ranta a wannan sanadin tabbas ta yi shahada ne, mutuwa kuma dama tana kan kowa.
Zuciyar musaddiƙ ta yi zafi ta yi ƙuna yadda yake ganin kowa ya kasa fahimtarsa, sun kuma kasa gane mugun halin da zai shiga idan ya rasa Afrah, wani ƙarin damuwar ma shi ne yadda yanzu ne ya ji yana sonta so na ban mamaki, yana ji aransa matuƙar ya rasa Afrah to sai dai ayi gawa biyu, don tabbas zai iya bin ta shi ma.
Nan da nan ya rame ya fita kamanninta, damuwarsa ba ta ɓoyuwa ako’ina, duk yadda Afrah ta so ta kwantar da hankalin musaddiƙ to yaƙi ba ta dama, don fushi yake yi da ita sosai.
Iya kulawa dai kam musaddiƙ ya na ba Afrah, ko da yake cikin fushi ko ya ya tace wani abu na yi mata ciwo zai kwasheta zuwa asibiti, ciki kam ya zo da lalura domin kullum Afrah cikin ciwo ta ke mai tsanani, ga watannin ciki sai gaba suke tun Musaddiƙ na sa ran Afrah zata haƙura ta bari a cire cikin har ya saduda, ya rungumi ƙaddara ya fauwalama Allah komai kamar yadda Afrah ta fauwala masa, kullum cikin addu’a yake da sallar dare baida wata buƙata data wuce Allah ya ja masa da kwanan Afrah, Allah ya sauketa lafiya, dole ya sakko daga fushin da yake yi, domin baya son ganin ta cikin damuwa ya kuma fahimci fushin da yake yi da ita yana jefata cikin damuwa, ya rungumi matarsa, tausayi da ƙaunarta sun rinjayi fushinsa. Ji yake hatta numfashi kamar ya yi mata, shi yake yin komai a gidan, ko ta ɗan sami ƙarfi tace zata yi wani abu baya bari, ta zama tamkar sarauniya.
Hatta Mama Hauwa a wani zuwa da tayi gaidata, tsayawa tayi ta sama sarautar Allah ido, ta zuba tagumi tana kallo gami da kakabin yadda musaddiƙ ya zama bawan Afrah.
Sai tsuma da rawar jiki yake yi, komai tana daga kwance shi yake yi mata, ta dai ƙare ta dube shi tace “ Ikon Allah, sannu Musaddiƙ da ɗawainiya”, ya ɗago cikin murmushinsa yace “sannu Mama”, ta jinjina kai tace “ yau ba ka da aiki ne?”, ya ɗan dubeta yace “ Ai yanzu ba kullum nake zuwa ba, saboda bana son ina barinta ita kaɗai, nafi so koma menene ace ina kusa da ita”.
Mama Hauwa ta yi jugum zuwa can tace “ lalle ka cika mijin marainiya”.
Har Mama Hauwa tabar gidan zuciyarta cike take da kakabi, lalle Afrah ta yi dace da miji na nunama sa’a, tana tafe tana jin wasu siraran hawaye na fita mata, na takaici da ƙarin nadamar yadda rashin rawakkali da kuma rashin hangen nesanta yasa ba Na’ima bace yanzu a wannan gurbin.
Har cikin zuciyarta tana jin dama Na’ima ce a wannan matsayin ba Afrah ba, lalle son zuciya ɓacinta, ta kai hannu tana sharar hawaye, tana tunanin yadda zata yi da Na’ima da har zuwa wannan lokacin babu ƙwaƙƙwaran saurayi balle ayi maganar aure.
Ko sallama da ita ba’ayi haƙiƙa wannan lamari yana tayar da hankalin mama Hauwa, musamman yanzu da gaba ɗaya itama Na’iman ta canja, ko kaɗan bata jin daɗin zama da ita.
A ɗan wannan lokacin bata isa tace tashi rana koma inuwa ba, ta dinga zumɓure zumɓuren baki kenan tana ƙunƙuni abinda duk duniya mama Hauwa ta ƙi jini kenan ga yaro.
Ga uwa uba Mallam Mahmud ta lura har yanzu yana da ƙullinsu a zuciyarsa, domin yadda gaba ɗaya baya bi ta kan duk wani lamari na Na’ima, tsakaninsa da ita ta gaishe shi ya amsa.
To yanzu ne Mama Hauwa ta fara jin damuwa akan hakan.
Abubuwa duk sun juye ta inda bata taɓa tsammani ba, danasani kawai take yi, bata taɓa yi ma Afrah fatan samun miji irin Musaddiƙ ba domin bata son ta huta amma ya ta iya, haka Allah ya tsara babu kuma mai iya warwarewa.
Haj Hudah ta ƙara gyara kwanciyarta akan makeken gadonta mai barazanar cinye duk faɗin ɗakin, ba wani zafi ake yi ba, saboda tun shekaranjiya alamun shigowar sanyi ya nuna, amma zafin da take ji a cikin jikinta na danuwa yasa gaba ɗaya ta ƙure A.C ɗin ɗakin, fuskar wayarta ta ƙurawa ido, inda hoton Musaddiƙ ya bayyana cikin fara’a ya yi kyau har ya gaji , kwana uku kenqn bai samu ya zo aiki ba, amma ji take kamar shekara uku ya yi. Kuka take sosai tana jinta a cikin jerin matan dake cikin ƙuncin rayuwa, duk da rufin asiri data ke da shi, bata nemi komai ta rasa ba amma soyayya ta maidata fakira mara komai tana jin tamkar duk duniya babu wanda ya kaita talauci.
Ta kifa kanta akan wayarta kuka take sosai, ta so da musaddiƙ ta fara haɗuwa kafin Alh yusuf sanda.
Zuciyarta ta yi rauni da yawa bata da wani tunanin da ya wuce na musaddiƙ, don haka ya zama dole ta sanar da shi abinda ke cikin zuciyarta ko da hakan na nufin faruwar wani mummunan abu, domin nauyin soyayyarsa ya yi ma zuciyarta yawa, dole ta na buƙatar taimakonsa.
Don haka ta shirya sanar da shi komai, ta dafe kanta da yake sarawa, ɗayan hannun kuma ta dafe gefen zuciyarta da yake bugawa da saurin gaske, bakinta ya yi mata ɗaci, sai alokacin ta tuna yau tun abincin safe babu komai a cikinta sai ruwa.
Lalle so guba ne, ta zuro ƙafafunta ƙasa ta, dai dai ƙarfe goma da minti shida na dare, tana sha’awar ta sha ko da madara ne ko ta samu bacci ya ɗauketa.
Zaune a kqn kujera ta tadda Alh yusuf sanda ya ɗora kafafunsa a saman tebur ɗin gabansa, yana riƙe da rimot ya danna wannan tasha ya cire ya maida wannan tasha, sai dai kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci cewa gaba ɗaya hankalinsa ba kan talabijin ɗin yake ba, yana can duniyar tunani.
Motsin fitowar Haj Hudah yasa ya dawo hayyacinsa, ya juya yana kallon yadda take tafiya tamkar kazar da ƙwai ya fashema a ciki.
Ya jinjina kai yana cigaba da kallonta harta buɗe frij ta ɗakko hollandia ta juya zata koma ɗaki kenan, muryar Alh yusuf sanda ta dakatar da ita, “ Haj zo mu yi yar wata magana”.
Juyowa ta yi ta dawo ba tare da tace uffan ba, ta zauna tana kallonsa, a hankali tace “ Lafiya dai ko”.
Yace “Lafiya lau, magana dai zamu yi”
Ta aje hollandia a saman tebur tana ƙoƙarin gyara zamanta.
Tace “ To ina jinka”,
A hankali ya aje rimot ɗin hannunsa ya miƙe ya nufi wani ɗan lungu dake cikin falon ya ɗakko wani ɗan madaidaicin akwatin magunguna, tun kafin ya dawo ya zauna Haj Hudah ta canja fuska, domin ganin akwatin a hannunsa.
Ya dawo ya zauna gami da buɗe akwatin ya kwaso wasu kwalayen magunguna ya buɗe ya fito da su babu guda ɗaya da aka buɗe aka sha.
Ya ɗago idanunsa ya ɗora akan nata a yayinda ta kauda kanta.
“ me yasa ki ka daina shan maganinki”
Ya tambayeta fuska tamke,
Haj Hudah ta yi shuru gami da sadda kanta ƙasa, harga Allah bata son yin wata doguwar magana yanzu, domin halinda take ciki ya fi na tuhumar da Alh yusuf sanda yake mata.
Ta ɗago ta dube shi, fuska ba yabo ba fallasa tace”Don Allah mu bar wannan maganar sai zuwa gobe”.
A fusace cikin ɗaga murya yace “ me yasa zamu bari sai gobe, yanzu nake son sanin dalili, na haƙura na jure irin canjawar da kika yi tun bayan cin zaɓenki, to amma bazan juri wannan ba, ya zama dole ki gaya min dalilinki na daina shan waɗannan magungunan……….
Yar gidan Imam✍️