Musabbabi Book 2 Page 7
MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere )
Page 7
A cikin cell ɗin tsakanin Haj kilishi da Haj Rakiya kamar zasu dambace, kowa a wuya yake, Haj Rakiya ta koma can gefe ta buga tagumi tunaninta ya kasu da yawa, kuɗinta masu yawa da bata san a wane hali suke ba, da kuma dalilin kawota wajen yansanda, haka zalika tsoro ya ƙara kamata abisa dalilin bata son mijinta ko dangin mijinta da dama sam basa ƙaunarta su san tana wajen yansanda, tunda take a duniya ƙafarta bata taɓa takowa ofishin yansanda ba da sunan laifi, ta watsama Haj kilishi harara tace “ In dai kece sanadiyyar zuwana wajen nan to Allah ya isa ban yafe ba”, ita kam Haj kilishi magana ma ji take idan zata yi kamar za’a cire mata rai saboda tsabar raɗaɗi da zuciyarta take yi, bata jin tana da lokacin sa’insa da Haj Rakiya domin masifar da take ciki ta fi gaban misali.
Ita kanta Haj Rakiya ba ta ƙara gane tana cikin masifa ba sai da kofur Lawal da abokan aikinsa mata biyu suka shigo cikin cell ɗin, kofur Lawal ya fito da vedio ya kunna ya ɗora a idanunsu, nan da nan jikinsu ya fara rawa, tambayar d suke ma kansu itace ta ya ya aka ɗauki wannan vedio? Waye kuma ya ɗauka?. Kafin su an kara waɗannan matan guda biyu sun fara dukansu kamar Allah ya aiko su, ihu da neman ɗauki kawai su ke yi musamman Haj kilishi da jikinta ya ƙara rikicewa, dole so ake su amsa laifinsu, wanda Haj Rakiya ce ta fara buɗe baki tace “ Ni rakiya ce kawai nawa, ga wacce ta yi komai nan itace ta yi asirin”, kofur Lawal yace “ kun shirya amsar laifinku” duka suka amsa “ Eh”, ya tashi ya fito ya ba sauran matan umarnin su fito da su.
A kujerun tuhuma suka zauna kowacce na sharar hawaye, da girmansu da komai yau sunyi mafi girman wulaƙanta, ko ido Haj kilishi bata iya ɗagawa saboda kunya musamman da aka shigo da su mallam Mahmud domin su ji abinda Zasu faɗa, irin baƙin kallon da Afrah ke yi ma Haj kilishi ya ƙara tilasta mata yin ƙasa da kanta. Insifektan da case ɗin ke hannunsa ya shigo ya ja kujera ya zauna yana yi musu wani irin sakaran kallo, Murtala na tsaye kusa da mallam Mahmud, Afrah ta ɗago da wayarta musaddiƙ ne ke kiranta, tasan idan ba ta ɗauka ba ya dinga kira kenan, don haka ta fice daga wajen ta fita can waje ta ɗauka.
Ta yi ƙoƙarin ɓoye duk tashin hankalinta domin bata son ya gane komai, hira kawai yake son yi da ita, haka dai ta dage su kayi ta hirarsu ba tare da ya gane komai ba, daga bisani dai ya gaya mata da yuwuwar ƙila shigowar dare za su yi, tunda har yanzu Haj Hudah bata fito da ga meating ɗin farko ba. Fatan dawowa lafiya kawai tayi masa su kayi sallama, da sauri ta koma cikin ofishin, inda ta tadda Haj kilishi da Haj Rakiya kuka shaɓe shaɓe gaba ɗaya Haj Rakiya ta gama zayyanama Insifekta duk abinda ya faru wanda ko musu ɗaya Haj kilishi ba ta yi ba. Duk wajen babu wanda baiyi tir da halinsu ba.
Insifekta ya dube su yace “ zamu je inda kuka binne asirin ku tono shi da kan ku”, nan ma Haj Rakiya ba ta yi musu ba tace “ zan kai ku wajen”, Haj kilishi kuwa babu bakin magana har aka ƙara fita da su, cikin motar yansanda zuwa bakin bishiyar kukar, murtala ya kwaso su mallam nahmud da Afrah a motarsa.
Ganin motar yansanda ta ƙara dawowa unguwar su Haj Rakiya, wannan karon harda jiniya irinta masu laifi, yasa nan da nan yara da manya suka fara dafifi wajen kallon abinda ke faruwa, fargabar haj Rakiya na gudun kada kowa yasan abinda ke faruwa ya ƙara yawa, domin dai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci magana duk ta cika unguwa.
Bakin ƙatuwar kukan Haj kilishi da Haj Rakiya suka tsuguna suka yi ta haƙewa, Haj kilishi ta riga ta sadakar da duk abinda zai faru da ita tana roƙon sassauci daga Allah, tonon asirin duniya ma kenan kafin aje lahira, yau itace rana ta farko da ta ji ta yi nadama har cikin zuciyarta akan abubuwan da ta aikata, ta ɗaga kai ta kalli ɗimbin mutanen da ke zagaye da su suna musu tofin Allah tsine, ta ji kunya iya kunya.
Haka suka fito da tukunyar asirin babu ƙyan gani.
Cikin bismillah kofur Lawal ya sa hankici a hannunsa ya karɓa, daga nan babu ɓata lokaci su ka ƙara dawowa police station ɗin.
A dai dai lokacin da aka fito da asirin kuwa a lokacin cikin mai Rakwacam da yake a kumbure ya yi bindiga ya fashe, sai kace almara, gaba ɗaya sauran jikin nasa ya zagwanye ya yi baki tamkar ƙonannen gawayi, wannan shine ƙarshen duk wanda yake jin zai ɗauki siffar ubangiji, masifar duniya dai ya gama ganinta saura kuma ta lahira, a haka matarsa da yan tsirarun mutane suka tarkata ɗan diddigar namansa aka binne a rami, don ba ma ce kabari ba. Wannan ishara ce babba.
Haka Haj kilishi tunda aka tono asirin take jinta wani iri, cike take da tsoro domin ba ta san abinda zai biyo bayan tonewar ba.
Insifekta yaso a maida su Haj kilishi cell a haɗa kuma komai a tura su kotu, amma dole yasa ya tsaya domin tattaunawa da su mallam Mahmud don yasan abinda su ke so.
Ko kai Haj kilishi bata iya ɗagawa saboda kunya da tashin hankali, haka Haj Rakiya tana rakuɓe jikin bango, ta tsani Haj kilishi fiye da tunanin mai tunani zaginta take sosai a hankali yadda Haj kilishin ce kaɗai zata iya jinta, duk yadda ta so ta tankama Haj Rakiya haka ta haƙura ta yi shuru, domin yadda kanta ke juyawa tana ganin kowa bibbiyu.
Insifekta ya cigaba da kallon mallam mahmud yace “ yanzu za muyi ƙoƙarin haɗa komai mu turaku kotu, idan kuna so har dukiyar musaddiƙ duk saita dawo muku da ita, haka zalika hatta Hannatu muna iya sawa a kamata daga can Abujan, haka itama Rakiya idan kuna so duk kuna iya neman kuɗin tarar haɗa hannun da aka yi da ita wajen aikata sharri”. Mallam mahmud ya dubi inna Halima da Afrah sannan ya maida kallonsa ga insifekta sannan yace “ Babu ko ɗaya da za’ayi insifekta, saboda duk waɗannan abubuwan ba su kai samun natsuwar musaddiƙ ba a wajen mu, dama mu buƙatar mu bata wuce ta tono asirin ba domin idan ta tono shikenan ya karye saboda haka tunda ta tone to bama buƙatar komai kuma”, Inna Halima ta ɓata fuska tace “ yaya amma ai yakamata a karɓoma musaddiƙ hakkinsa, kuma a hukunta su duka”, ya girgiza kai yace “ ki kwantar da hankalinki Halima, ita dukiyar na yi imanin babu abinda zata tsinanama kilishi balle Hannatu da mahaifiyarta, haka zalika na fi son musaddiƙ ya nemi nashi da kansa na fi son ya yi arziƙin da baida alaƙa da gado, don haka ki barta da dukiyar”, ya ƙara kallon insifekta yace “ irin girman zaluncin da ta yi ma musaddiƙ bana jin akwai wani hukunci da kotu zata yi mata, da zai gamsar da mu, don haka ba ɗan adam ba ne mu ke son ya yi mata hukunci, Allah da ya hana zalunci shi ne muke son ya yi mata hukunci ya yi ma musaddiƙ sakayya, saboda haka mun bar ta da Allah , mun barta da fitowar rana da faɗuwarta, tun daga kan dukiyarsa da tayi ruf da cikinsu zuwa wannan ɗanyen aikin da ta yi duk mun barta da Allah”,
Shurun da ya yi yasa Afrah ta amshe maganar tace “ Tabbas sakayyar Allah muke nema, domin Allah ba ya yafe laifin tsakanin bawa da bawa har sai sun yafema kansu saboda haka muna roƙon sakayya cikin gaggawa”.
Duk wannan maganganun da su ke yi Haj kilishi tana jinsu daga cikin cell ɗin, tsoro fa ya kara kamata, bata son a barta da Allah tana tsoron sakayyarsa a gareta, hawaye ya cigaba da zuba daga idonta babu ƙaƙƙautawa.
Insifekta yace “ kunyi tunani irin na mutanen kirki, dama kuma duk abinda mutum ya yi kansa ya yi ma alheri da mugunta, hukuncin Allah kuma shi ne hukunci”, murtala yace “ Hakane mungode da haɗin kan da ka ba mu Allah ya saka da alheri”,
Insifekta yace “ Babu komai, sai dai mu ma zamu yi namu aikin, domin zamu cigaba da ajesu anan har sai masu yin belinsu sun zo”, Murtala yace “ wannan aikin ku ne kuna iya yin duk abinda ya kamata, mu zamu tafi idan babu wata matsala”.
Yace “ Babu damuwa, sai takarda kawai da za ku sa mana hannu”.
Murtala ya miƙama takardar ya sa hannu sannan cikin yi ma Allah godiya suka fito ba tare da sun bi ta kan su Haj kilishi ba. Tun acikin ofishin yansandan Afrah take jin wata irin damuwa hankalinta ya karkata ga wane hali musaddiƙ ya ke ciki, yakamata ya kirata yadda baya daɗewa bai kirata ba amma gashi har sun fito daga cikin police station ɗin bai kira ba, itama kuma ta yi ta kiransa wayar na ta ringing amma ba,a ɗauka, ta yi masa uzirin ko yana wani wajen ne da ba zai iya ɗaukar waya ba. Amma me ya sa gabanta ke faɗuwa?.
Haj Hudah ce cikin matsanancin tashin hankali gaba ɗaya a firgice take, sam babu nutsuwa a jikinta, tana durƙushe gaban musaddiƙ wanda gaba ɗaya ya gigice ya fita hayyacinsa, wani irin amai yake yi baƙi me mugun wari, gaba ɗaya idanunsa sun juye, wannan itace rana ta farko da Jikin Haj Hudah ya taɓa jikin musaddiƙ, duk kuma da rikitaccen halin da take ciki bai hanata jin wani irin sanyi da jin daɗi a tare da ita ba, ƙam ta riƙe hannunsa tana murzawa, kafin daga bisani da taimakon sauran jami’an tsaronta aka sanya musaddiƙ a mota zuwa Abuja clinic. Haj Hudah na rungume da kansa a cinyarta, duk aman da ya ɓata mata jiki bai dameta ba , damuwarta ɗaya shi ne sanin abinda ke faruwa da musaddiƙ cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya ya canja.
Kai tsaye gado aka ba musaddiƙ aka ɗaura masa ruwa gami da taimakon gaggawa da suka fara ba shi, amma yadda numfashi ke yi masa wahala yasa dole likitoci suka sanya masa oxcigine, wanda hakan ya ƙara dugunzuma zuciyar Haj Hudah, kuka sosai take yi sai kace wacce aka yi ma wata gagarumar mutuwa.
Dai dai lokacin wayar Alh yusuf sanda ta ɗauki ƙara, da sauri ya ɗauka lokaci ɗaya ya kara wayar a kunnansa, ya ɗatsu yana sauraron abinda wanda ya kira shi yake gaya masa, yana cigaba da gyaɗa kai kamar tsohon ƙadangare, yana gama wayar, ya yi murmushi yasa hannu ya shiga whatsapp ɗinsa ya shiga fito da hotunan, ya yi wata irin dariya gami da miƙewa ya na yin zooming ɗin hoton, Haj Hudah ce rungume da musaddiƙ a kan cinyarta idanunta na fitar da hawaye ………..
Yar gidan Imam✍️