Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 5

Sponsored Links

 

 

 

 Ban yarda wata ko
wani ya sake audio din wanan novel ba na sayarwa S Zaria tv dashi don haka idan
kikayi gangancin sakeshi sake da hukumace .

    Zan iya cewa wanan
zuwan bazatan da Abba yai masu a ranan
Kuma ya sauka dakin ummah fake da girki shine ya jawo fitina da zan iya
fada na farko dana taso gidan mu da wayona naga sunyi a tsakanin su .

   Don aka,idance Dole
mamace take karban Abba a duk lokacin da zai sauka garin zasuyi ta rawan kai da
rawan jiki da gyare gyare wai Abba zai dawo gida rana  .

     Ashe ba karamin
bakin ciki ummah take kumsa ba a hakan da ake mata din don abu mafi zafi da
munine ga mace don lokacin nunawa ne kawai batayi a fili kawai don har takan
zage ayi wasu aiyukan a tare damu da ita.

   Don ina Kan akwai
iya girki ba kadan ba abinci koda missali kai mata bayani zata zauna tayishi
kaci a cikin kwanciyan hankali da dadin rai.

   Shiyasa mama takan
gayatota ckkin dabara tazo saka hannu sai gashi yau ma da Abban yai masu zuwan
bazata dayace sunzo kaduna wani tarone daga nan ya yanke shawaran yazo gida
tare da abokan shi tunda yana kusa da gida duk hakan bai gamsar da mama ba sai take
ganin kullawa sukayi shida ummah cewa zai dawo a ranan girkinta din ranan.

   Bude abincin dake
gaban shi kamshin sakwarane ya bure falon ya lumshe ido yana kao hannu saman
marfin kulan miya wani kamshin dadi na miyat taushe ya kara bin bayan na sakwaran.

      Kai salma lalai
ke yar aljannace kamar kinsan nafi kwana goma ina marmarin wanan abincin a
raina wallahi sai gashi nazo na sama kinyi shi .

     Munafurcin banza
da wofi wa za a mayar yaro a nan an hada baki anyi abu zaku so ku dinkeni ta
baibai don anga sokuwa a zaune kome ?

   Lokaci daya duk
suka juyo suna kallonta a cikin mamaki Abba din yai karfin halin fadin wanan
wani irin maganane haka kikewa mutane  ?

     Aiko kamar dama
mama jira takeyi tayi cikin Abba tana fadin rufa min baki munafukin namiji
kawai kun kula da salma cewa yau zaka dawo kazo nan yanzun kana nuna cewa
tafiyan tazoma a bazatane.

    Au bani da halin
dawowa ko yaushe nayi niya a gidana dole saina kira na fada maki kome kike nufi
ban fahinci wanan maganan ba ?

  Wani kallon banza ta
watsa mai kafin tace au yanzu kasan wanan ashe ta juya wurin ummah tana fadin
mu zuba nidake a gidan nan salma dama ai a zuben muke ko na canza makine a
yanzu kuma ?

   Fita tayi daga falo
rai bace ya bita da kallo kafin ya juyo inda yake yana jan uban tsuki dagawa
ummah tayi daga inda take zaune tana fadin dama haka duniya take.

   Duk abinda mutum
yake shukawa na rashin gaskiya watarana shi zai fada da bakin sa duniyace kuje
na barku ga Allah daya haliccemu.

   Kada ki kara bata
min rai a wurin ya fada a hasale ummah tace Allah baka hakkuri saidai kayi
kuskuren fada masu asalina duk da bani kaidai yanzu barnan sunan ya shafaba har
da yayan ka dana haifa.

    Fita tayi don kada
ta sake hawayen da take tarawa a fuskanta ya sauko har ya gane hakan gareta
tayi saurin fita zuwa part din ta zuciyarta na cunkushe da bakin cikin abinda
ya faru din.

     Dakin kwananta ta
shiga tana sake kukan lokaci guda inda takai tsawin wani lokaci a hanka  muryan Abba
taji yana sallama a fadin tare da fadin koba kowane nan ya turo kofan .

   Daga inda take
kwance ta kalloshi tana dagowa shima kallonta yake yana mamakin kukanta duk da
yasan abinda takewa kukan a lokacin ina mamana takene ya sake tambaya .

  Da kyat ta iya budan
bakinta tabashi amsa da tana dakinta kwace kika barta ita kadai a can kina nan
kina wani shirme naki can na banza .

   Har yakai kofa yaji
tana fadin zaka iya komai a shirney gareni don kome akaimun kajamin shi da
yadda ka daukoni ka kawoni cikin yan uwanka tun farko ka darajani da dole kowa
naka ya darajani a yanzu dani da yarana duk ba a bakin komai muke a gidan nan
ba haka gun yam uwanka dake muna kallon uku saura a yanzu.

    Bai iya furta
komai ba yabar mata dakin zuwa inda nake kwamce na kifa ciki kaina da bana son
kitso yana bajabaja a saman filo dagani kasan barcin wahala nakeyi a lokacin.

    Ya dan dade tsaye
kaina yana nazarina kafin ya fara kiran sunana a hankali da kyar ya samu na
amsa mai ina dago kai na kalleshi saida ya gyara tsayuwan shi a lokacin.

    Mamana meke faruwa
dake haka meke damun ki haka tun yaushe kike fama da wanan ciwon haka kika koma
kamar bake ba ?

     Kai kawai na iya
nuna mai na mayar da kan nawa saman filo na sada shiru Abban yayi yakafa min
idanu nadan lokaci kafin ya kwalawa ummah kira ta taso zuwa dakin .

  Tunkan ta iso yake
fadin wai tun yaushene yarinyar nan bata da lafiyane haka saida ummah ta hade
wani malolon bakin ciki a cikinta kafin tace dashi tun jiyane data dawo school
din take haka.

    Kin tambayeta meya
sameta na tambaya kai kawai take nuna min kuma taki cin komai tun jiya din sai
dan ruwan tea data kurba a cikinta da safe da zamu tafi asibiti.

    Subbahanallahi ya
fada kafin ya dubi lokaci ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi yana
fadin yanzu darene goma har ya wuce wa zamu sama da daren nan haka ?

    Dawai nace ko za,
, , , , kome ya fada jin tayi shiru ko za a kira malam bawa nan makwabcin ka
don yana kamun kai kasan irin haka ko wancan lokacin shi aka kira min a cikin
su hassan.

    Fita yayi ba tare
da magana ba yana kawai tsakar filin daya rabamu da part din mama ya dan kalli
kofan part din yana rufe don haka yasa kai ya fice kawai zuwa falon shi don har
lokacin akwai yan fadan shi a wurin suna fira su.

     Wani ya kira
cikin yaranshi ya turashi ya kira mashi malam bawa din suka koma ciki suna
maganan daya shafi harkam siyasan zafara din a lokacin ne mutumin ya iso tare
da makwabcin gidan mu din malam bawa duk da muna da dan nisa dashi.

     Falon yayi shiru
bayan ya shigobsun gaisa ta hanyar yiwa juna mubayi,a Abban yace wallahi dazun
na dawo na samu yarinyar wajena tana fama da matsakaincin ciwon kai shine na
tura a nemoka koda taimakon da za a iya bata.

    Na,am malam ya
fada tare da tambayan Abba din da kan yana mata nauyi ne ko kuma ciwone kawai
irin na ciwon kai dai haka  ?

    To gaskiya kodana
lekata ko magana bata iyayi a lokacin zan mace bata san nazo kantaba Na,am
malam ya kara fada to yanzun dole sai na ganta don musan ainihin matsalan nata
don zao yuyu in bada maganjn da bashine ba.

   Yan fadan Abban
suka amsa da fadan hakane ba matsala Abban ya fada yana kokarin mikewa yake
fadin zamu shiga sai ku jirani nan in fito zama suka gyara sukan  don sunga Abba gari kamar sunga central bank
ne su.

    Don sunsan cefanen
su lafiyace a ranan don mayayi shigar dare da cikar yafi haka yawa a wurin part
din mu yaiwa malam din iso malam ya tsaya daga waje Abba din ya fara shiga.

  Bayan yaiwa ummah
magana ummah ta mike zuwa dakina ta kara gyara min yanayina kafin ta fito tana
fadin su shigo ina nan kwance kamar yadda Abba din da ummah suka fita suka
barni.

   Ido ya dan kuramin
na dan lokaci kafin ya juyo zuwa inda Abba yake tsaye shima kallona yakeyi yana
ganin kamar ban numfashi a lokacin kun kaita asibiti ne ya tabayi Abba eh dazun
sun kaita akace ya fada.

    Alh wanan ba
laluran asibiti bane zuwa asibitine ma ya kara tayar da jikin ya koma haka don
gaskiya su hakan ma sukafi bukata don su samu daman shiga jikin dan adam sosai
a lokaci.

   Wa,iyazu billahi
ita maman  nawa ina ta hadu da iska kuma
naga ba fita sukeyi ba in ba zuwa makaranta ko wani abu ba da  zai fitar dasu a gidan nan ba.

  Su ko ina suna nan
musaman bandaki ko wani wuri inda shara yake taruwa ko a wurin da ba a cika
shiga kai da kaiba haka ko ina dai zance sunan a tare damu ako ina dan Adam ke
rayuwa inka debe wurin ibadan mu.

    Ikon Allah Abba ya
fada malam yace da alama ai ba shiganta sukayi inma shigantane zasuyi bayanin
dalilinsu na raban ta din sukayi.

    Matsowa yayi har
inda nake yana fadin hjy sallamu alaikun sai ummah ta mike tsaye daga inda take
zaune wurin kaina taja dan baya kadan daga wurin su.

    Kan nawa ya dafa
ya fara karanto min addua cikin dan daga murya kafin na fara dan motsa hannuna
a hankali ya kara sautin karatun shi kafin can na sauke nauyayyen ajiyan zuciya
da dan gyara kwanciyana.

   Ya juya wurin Abba
yana tambayan shi menene ainihin sunanta fatima zarah ya fada ku saba da
kiranta da wanan sunan suna na musulunci na yanka abune mai muhinmanci da
akeson bawa yasaba da amsa kirashi dashi don ko a kabari da sunan shi na ainihi
za a tashe shi.

    Amma yanzu wanan
yawan sauya sunan yana kara taimakawa shedanu wurin saurin shiga izuwa jikin
bawa alamane na yawaita bidi,a ga al,umma wani sunan ma nasu ne muke aro muke
kiran yayan mu dashi.

    Zaku kirata da
fatima ko zarah don zarah sunane na musulunci duk sunane daya shafi addini
wanan din mai babban suna kamar wanan ba lalai bane a sauya mata sunanta na
kwarai da akai mata huduba ko walima dashi ma,ana saddakan makon haihuwan ta.

    A sabule ya iso
gari don ranan darasin kanshi dauka dai yayi amma bawai ya fahinci wani abune
sosai daga ciki yana zuwa dakin shi ya bude ya shiga.

   Jin motsin  bude kofan shine yasa Dije ta leko daga
dakinta don ganin wanda ya shigo sai hangoshi tayi yana shiga dakin nasa a
lokacin tayi.

   Shiru shiru bata
jishi ba yasa ta mikewa zuwa dakin daga kofa ta tsaya tana magana Amadi lafiya
yau ka dawo haka da wuri gida nayi jiran ka shigo banga shigowanka ba.

   Jin shirun da
tayine yasa ta daga tsohon labulen dake kofan dakin nasa kwance yake saman
tsohon katifan shi dake yashe kasan dakin ya kwanta yayi rubda ciki.

    Ikon Allah yau
Amadi kaine da wanan irin kwanciyan da ba, a son ga musulmi ya kwanta ya kifa
ciki bansan ka da irin wanan kwancin ba haka ?

    Jin shiru baiko
motsaba yasata kutsa kai cikin dakim gabaki daya Amadi fa wai lafiya kake yau
din ko wani abin ke samun kane ?

     Hannu ta mika ta
dafo kafadan shi wani zafi ya daki hannun nata da sauri ta jaye hannunta saman
jikinshi da sauri tana irin salatin su na mutanen da sai ta dauko wanan kafin
ta aje ta dauko wani ta dora a kai.

    Amadi jikin ne
yayi tsanani haka ka dawo baka fada min ba yanzu ina amfanin kwanci da ciwo
haka a cikin daki ni Dije ta ina zan soma a garin nan.

   Allah kazama muna
gata ya Allah ka dubemu mun tuba Allah ta fada tana kokarin kara taba jinkin
nasa taji saidai tana kai hannu taji kamar kara zafi jikin nasa yayi a lokacin
kuma.

    Hankali tashe tayo
waje zuwa dakinta tana jawo gyalenta na sallah ta dora saman kanta ta nufi waje
gidan makwabtansu ta nufa saidai ba taimako don maigidan bayanan don haka ta
fito daga gidan.

   Malam Tanimu ta
hango kofan gidansa wurin sana,anshi ya dan rarafo yasha iska don bai gama
farfadowa daga tausan da gina yayimas bako a lokacin.

   Ganin ta a hargitse
yake tambaya Dije mai kamu ince ko lafiya ina fa lafiya malam Tanimu jikana ya
dawo min a cikin wani yanayi na rashin lafiya yana kwance a dakinshi rai a
hannun Allah.

    Subbahanallahi ya
fada yaba yunkura saidai gefen kafadab shi da gina ya taushe yayi tsami a
lokacin yasa ya koma da sauri yana yamotse fuskanshi kafin yace meke damun
shine ?

    Dama tun kan ya
fita yake fadin sanyi yakeji da kuma nauyin jiki na jiya kuma yace kai ke dan
sara mai haka dai ya fita yau din zuwa daukan karatun shi na boko sa yakeyi.

    Yanzu shine nace
bari nazo ko za a taimaka min ko wani shawara na samu ga mutane indai da kai
barin bashi wani magani ya shaka in,sha Allahu zai samu lafiya indai ya shaka
wanan din.

   Kinsa sana,ar tamu
dole saida tambaye tambaye don haka na aje wanan danaji ba daidai sai nadan yi
amfani dashi naji wasai.

      Mikewa yayi da
kyat ya shiga gida ya dan dauki lokaci kafin ya fito sai gashi ya fito da
kullin dan bakin leda a hannunshi yana fadin ina ai Amadi yaron kirkine bada
kamar shi a unguwar nan baki daya .

    Ki kai mashi wanan
insha Allahu yana amfani dashi kome ke damunshi da yarda Allah zai sake indai
yayi amfani da wanan dai ya aje sauran a wurinshi.

     Godiya sosai Dije
ta fara yi mashi kafin ta dingisa kafantal taja zuwa gida yana kwance yadda ta
barshi ta zaunava kusa dashi tana bude ledan kafin ta debo ta turmuza bashi a
hanci ta koma gefe ta zauna ta kafa mai idanu tana tunane a zuciyar na jikan
nata.

   Kafin dan wani
lokaci taji ya saki wani irin atishawa da karfi lokaci guda tana zaune saida ta
zabura daga inda take zaunen tana ambatan sunnan shi take fadin Amadi sannu
sannu kaji Amadi.

   Wani atishawan ya
kara sakewa har yana dan dagowa daga kwancen da yake dije sai fadi take
Alhamdullilahi barka Amadi sannu kaji Allah ya yaye sai kuma tasa kuka lokaci
guda.

    A hankali ya fara
bude idonshi yana ganin dishi dishi a dakin kafin ya sauke kallonshi kan Dijen
yana fadin Dije lafiya  dakyat yake wanan
maganan lokacin.

     Sannu Amadi ta
fada a cikin muryan kuka tana share hawaye da gefen gyalen ta tace yaya jikin
hankalina ya daga sosai banda dabara shine na tafi wajen malam Tanimu yabani
wanan na shaka ma tana nuna mai kullin dake hannunta din.

   Kallon maganin yayi
a hannunta kafin ya yunkura da niyar tashi jiri ya mai dashi ya kwanta yana
lumshe idanunshi a hankali tare da jin wani iri a idonshi ya mayar ya rufe.

    Kaci wani abin
kuwa yau ta tambayeshi ya dan girgiza mata kai yana gyara kwanciya ta mike ta
fice daga dakin kwano ta dauka ta fice daga gidan .

   Wurin masu sayar da
abinci layin ta nufa ta sayo shinkafa da taliya da ganye a sama ta kawo mashi
dakyat ya tashi ya fita ya wanko bakin shi ya dawo ya ya zauna ta kara tura mai
abincin gaban shi .

   Saida ya dan samu
natsuwa ya bude kwanon shinkafan ya kalla yasan saye tayi don basu da halin
dafa wanan a gidansu tausayin kakan yaji ya kara shigan shi lokaci guda yana
tausayawa tsohowan kan irin rayuwan da suke fuskanta din.

   Mikewa tayi ta fice
daga dakin ruwan zafi ta hada mai ta kai mai bandaki ta dawo tana ka gama tashi
ka watsa ruwa a jikin ka ko zakaji karfin jikim naka ko ?

    Sai kuma takai
kallo ga kwanon dake rufe har kaci abincin ke nan ta tambaya tana kallon
fuskanshi ba zan iya cin wanan din ba dije ya fada ya kokarin mikewa ta sakw
fadin me zakaci to ?

   Banjin cin komai a
yanzu ya fada tare da mikewa da karfi ya barta dakin tsaye tana mamakin shi
dama ita din da yunwa tare da marmarin shinkafan take saidai babu halin hakan a
gareta.

  Yasa ta daukan
kwanan zuwa waje ta zauna ta faraci tana lumshe idanu wani gefe kuma tana jin
zafin kudin data fitar ta sayo wanan abincin gashi yanzu baici ba ta bata kudin
a banza.

   Shiko yaki cine don
yasan itama tana so ko kan ya fito har ta kusa gamawa da abincin ya fito daga
bandakin wankan maza yayi na watsawa aji iska a jiki kawai a lokacin.

   Alwala ya zauna
yayi don ya rama sallolin dake kanshi yana kallon dijen a fakaice tare da
girgiza kanshi ya mike zuwa daki ya gabatar da sallah bai sake fitowa ba sai
washegari.

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [12/25/2022, 5:50 PM] +234 803 800 7509:
🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,,

 🌱TUMFAFIYA
BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

  🌱TUMFAFIYA
SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,,

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣

Leave a Reply

Back to top button