Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 51

Sponsored Links

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/19, 7:08 AM] +234 903 661 7473: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Zaune suke sun tasa kayan dasu mama suka kawo masu sai guda
da shewa akeyi anawa uwar kirarin cewa tayi sa,an haihuwa wanan irin abin
arzikin haka ai kowa nason ya haifi haka a gidansa ya kumaga hakan.

    Ahmed din ne ya
shigo da abincin dabbobi niki niki a hannun shi zuwa wurin da aka kebe dabbobin
a bayan dakunan nasu na kwana.

    Sai ya samesu baje
baje da kaya a gaban su suna rabo yayi mamakin ganin hakan daga ina wanan kayan
ya fito hakane shiya fara gaidasu sukayi mai sannu da zuwa ya wuce.

    Uwargarke ya hango
kwance tun daga nisa tana tuka da bakinta tausayi dabbobin suka bashi yasan
hankalin shi ya dauke bai yawan basu abinci a cikin yan kwanakin nan daya fara
sha,anin bukinshi sosai.

  Gashi biyu harda
ciki akuya daya da tunkiya daya suna dauke da ciki a jikin su sai suka kara
bashi tausayi mikewa sukayi lokaci guda saidai banda uwargarke din don tana
kwamce har lokacin tana tuka.

   Abincin ya diba ya
zuba masu mai yawa ya dauki sauran yasa saman rumfar su ya debo masu ruwan sha
bayan ya gyara wurin ya aje masu a gaban su.

   Jada baya ya danyi
yana kallon dabbobin kafin ya tako zuwa wurin uwar garke din yazo ya tsuguna a
gabanta ya fara dan shafa bayanta a hankali kafin yace.

   Uwata wai fushi
kikeyi danine haka ko abincin baki kalla ba yau kuyi hakkuri bawai na manta
daku bane abubuwane sukai min yawa a kaina wallahi.

    Nasan kina jin me
nake fadi kiyi hakkuri ki tashi kici abinci kafin su raga maki jagwalgwalen su
subar maki sudi ya fada yana mikewa .

   Kallo ta bishi
dashi ya juya da niyar tafiya lokacin ta mike tana girgiza jikinta nan
kasusuwanta suka shiga sake sauti har yana ji daga inda yake zakace ko wani
abune ke wanan karan haka.

    Ita kuma sai yaga
ta dona kai ta dan sun suna abincin ta fitar da kanta ta nufi ruwan da ya aje
masu tana kwankwada a lokacin ya tako yabar wurin.

    Yazo daidai kofan
Dije ya sake samun su a yadda ya barsu da farko ana zaune ana ta kasafi abubuwa
daga can yaji muryan Dije na fadin kai Amadi yaka.

   Jin hakan yasa yaja
ya tsaya wuri daya tare da dan kallonta kai yaka nice ta fada a dan hasale tare
da yafutoshi da hannu alaman yazo.

    Gani  hakan ya tako zuwa inda suke harkokin su din
yaja ya tsaya tace wanga kaya dakagani daga gidan su amaryan ka yafito suna
sunka kawo muna shi a matsayin gara.

   Wanan uban kayan
haka Dije kamar abubuwan sunyi yawa aina gani ya fada yana sake bin kayan da
kallo tare da mamakin karara a fuskanshi.

    To uban zuga ko
gidan irin mu tallakawana haka akeyi al,adana da kowa yasan anayin shi tun
dacan mahaifiyarshi ta fada kekan baki da dabi,a ke dai san mutanen nan suna
cikin gidan nan kike batun sake layi.

   Jin hakn yasa ya
dan juya kamar a tsorace yace suna gidan nan dama Dije tace wallahi kaidai tun
dazun sunkazo suka kawo muna amarya nan muka gaisa .

   Yarinya haka
tubarkallah masha Allah Allah dai yabamu hakkurin zama da juna sauran mutane
suka amsa da amin shikuma ya juya da niyar barin wurin.

    Ina zaka so nake
ka tsaya a cire maka naka kason da zaka dauka da wanda zakaba abokan ka da
sunka tsaya ma harka  buki.

   Shi zai cire masu
Innan mu kibar yin haka ba sai abinda anka basu zai dauka ba amma ina na taba
jin ance wai yaro ya kwashi duk abinda yakaso.

    Rashida mika damun
rayuwan kina haka wanga abu don danga anka kawoshi so kike ku zauna ku rabawa
kanku a tsakanin daga baya kuma azo a tuna da wani aji kunya ?

  Dije ke fadin wanan
maganan a hasale ga yayan nata dake faman rabon kayan cikin shagala da rudewa
abin yana ba tsohuwar haushi yadda sukeyi yasa ta tsare jikan nata tana fada
mai abinda ke faruwa.

   Don tasan tare suka
sha wahalan rayuwan su dashi yanzu samu yazo sun yi baja baja suna daukan
abinda suke so a tsakanin su ba tare da tunawa dashi ba.

   Shiko yana ganin
hakan ya juya ya tafi ba tare daya sake juyowa ya waigosu ba don kawai yaji
cewa iyayyen zahra amaryanshi suna gidan lokacin.

   Don hakane ita inna
harta samu daman yin yadda takeso da kayan ta raba yadda take ganin ya dace
kowa na wurin har da Dije suka saka masu ido ita kanwarta.

   Shine daya fita
daga gidan don ganin iyayyena a gidan sai bai dawo gidan ba a lolacin shine
dalilin daya fita tun safe baishigo ba sai wayan daya kira ya sheda min ya dawo
ya samu ina da baki ya tafi.

   Sai bai sameni ba
sai Hannatu data dauki wayan tana fada mai ina ciki tare dasu mama yace ta
sheda min hakan.

 Bakin ummah gaba daya
a ranan suka kama hanya suka koma garuruwan su da suka fito akabarsu da wasu
yan gari da take hurda dasu a nan suka tayata gyaran gida.

    Da yamma kowa ya
watse ya koma gidajen su hakan yasa tana kammala sallah bayan tafiyan Tani mai
aikin mu ta rufe part din ta don haka bata san wainar da ake toyawa a gidan ba
a lokacin

   Ta daisan cewa
Aisha tana gida har lokacin don ba a kaita gidanta ba ana rikici tsakanin su da
mijinta da danginshi.

    Wanan yasa fita ya
auku a tsakanin Abban mu da mama a daren wanda ba karamin fitana sukayi ba a
tsakanin su don Abba yace sun jawo mashi zubewan mutuncin shi a idon mutane.

   Ai garama auren
zahra din da kuke ganin bata dace ba yafi min wanan zuban mutumcin naku maimuna
yadda baki ba yarki tarbiya ba haka ta dauko min miji mara tarbiya mashayi yana
muna iskancin dayaga dama.

  Hakan daya fada ya
batawa mama rai sosai tace koshi ai baka san ko wani irin miji bane da har ka
fara yabon shi da wanan auren na zahar ai gara yarka ta zaunama a gida.

   Case dai yakai har
yan uwa suka shigo gidan da daren don da sauran yaran sukaga case din yana kara
zafi shine suka bugawa Hjyn su Abba sai gasu sunzo da yan uwan Abba din.

   Yake fadin
gaskiyane bata son a fada mata wallahi sai in rabu dake maimuna hakan ba wani
Abu bane gareni ita kuma ta bude baki tace dashi.

  Yo kasaka mana idan
ka sakeni shine me a yanzu Alh kana ganin zan mutune ko wani abu haka kawai zan
zauna kana zuba mim bakar magana kan laifin daban aikata ba.

   Niba irin matarka
bace da zaka zauna ka takata yadda kakeso tana nan lake dakai don jaraban tsiya
na kada ka saketa ta barka ko wani abu.

    Tana nufin wai
ummah a maganan ta shi kuma yace tafimin ke ai duk irin cin kashin da kuka zuga
nayiwa salma da yarta kada kice ban sani bane ko wani abu ina sane da abinda
kike nufi da hakan sarai wallahi.

   Da kyat dai aka
samu aka raba fadan nan kowa ya warse a kan da safe za a san abinyi akan auren
Aisha din aji inda aka tsaya ga zancen wurin mijin nata.

    Kowa ya watse cike
da bacin rai a zuciyar shi amma na mama yafi don ji tayi kamar ta mutu a ranan
don bacin rai.

    Ledojin pure water
ya sayo masu yawa zasu kai kwara ashirin ya loda a firdge din da suke a
corridor dina kafin ya kunna suka dauki aiki lokaci guda.

     Saida ya tabbatar
dasun dauka ya juya ya sake fita ya koma baya ya duba dabbobi kafin ya dawo ya
shige dakin namu bani falon ina ciki ina sallah lokCin ban daki ya nufa ya
watsa ruwa a jikinahi ya fito ya dauki dogon rigar jallabiyan shi ya saka a
jikinshi.

      Kana ya juya ya
fita zuwa masallaci din a lokacin su suka tayar da sallahsu a unguwar duk da
ina zaune ina addua bai hana ya fada min cewa ya fita zuwa sallah ba.

    Bai shigo ba sai
bayan sallah isha,i ya dawo a lokacin na hada mai abinci na aje mai a dining
din mu dan karami da aka kafa min gefe daya a falon don cin abinci.

    Ga kamshin turaren
sandal na wuta dake tashi a dakin ko ina saidai dan duhun da falon ya dauka don
ban kunna wutan ba a lokacin.

  Ya kunna wutan ya
shigo dakin na ina tsaye na idar ina nade sallayan danayi sallahn akai na dan
juyo ina amsa mashi sallaman shi.

   Ya amsa yana fadin
na barki ke daya ashe hannatu din ta tafi ban sani ba nace eh da yamman nan ta
tafi wai akwai abinda zatayi a gida tace.

   Tayi kokari sosai
wallahi samun amini haka a yanzu sai an tona na nade hijab dina ba tare dana
bashi amsa ba na nufi inda wayana yake aje na dauka kana nakai zaune saman
gadon.

    Abinci yana falo
na fada ina zama saman gadon idan kin idar sai ki tashi muje muci don nasan
yanzu hutu kike son kiyi tunda da gajiya a jikinnki yanzu.

   No ni ba zan sake
cin abinci ba don munci da hannatu kafin ta tafi dazun shine baki jirani nazo
munci tare na ciyar dake da hannayena ba koda yake kuma gara da kikaci da ita
din don zakifi sake jiki da ita kici sosai.

    Nidai ina zaune a
inda nake ina jinshi sai dan murmushi danayi kadan lokacin a fuskana sai naga
ya kai dan kwance yayi rigingine yana fadin.

    Na saka ruwa a
cikkn freezers din nan na waje don nasan idan mutane sun gane zasu dinga zuwa
suna tambaya a basu hakan yana da kyau ai na fada.

    Can kuma sai dakin
ya dauki shiru na dan lokaci don kowa da irin tunanen da yakeyi a zuciyarshi
lokacin don nidai tunane nakeyi akan zancen fridge din yayi yanzu din shi kuma
yana tunane akan yadda rayuwa zai kasance a garemu.

    Mun dan kai wani
lokaci na zata yayi barci ne a hakan sai na kawar da shirun da fadin kada kai
barci a hakan bakaci abinci ba fa.

    Idona biyu ina dai
tunanen duniya ina jiran ki tashi ki bani abincin ya fada cikin basarwa dan jin
nayi kafin can na mike ina fadin muje din na zubama sai naga ya miko min
hannayen shi.

   Alaman na kamashi
ya mike ai sai na kalle ina zan iya daga karfafa irin ka haka Master nine ma
mai karfin zahra zaki iya ai ki gwada ki gani mana na dan make kafadana alaman
naki.

    Ban kuma wuce ba
na tsaya a kanshi tsaye yace to ki zauna kada ki gaji yana nuna min wuri a
gefen shi kusa da inda yake kwance din.

   Kallon wurin nayi
sai na dan juya da niyar komawa inda na bar wayana in zauna naji ya koma
hannuna yajani zuwa jikin shi na fada mai lokaci guda ba shiri a jikin nasa ya
mayar da hannayen shi ya rufmu a tare.

    Idanuwana na
runtse lokaci guda don jin jikin mu daya hade a wuri daya lokaci guda Zahra
banda abinda zance dake sai in kara gode maki.

    Ban taba yin
tunane ko tsamanin saka rai da samun ki a matsayin mata a gareni ba sai gashi
Allah ya mallaka min ke yau a matsayin matar sunna ta aure a gareni.

     Kokarin nake na
kwanci kaina daga yadda muken don a sabon abu naga abin yana faruwa dani
lokacin wai nice a jikin wani namiji hakan nan ?

    Yana kokarin  wasa da sassan jikina kuma kwance wuri daya dashi
a lokacin duk da ina kokarin janye jikin nawa baisa inji alaman yana da niyar
sakeni ba shi a lokacin.

   Ganin hakan yasa
nayi karfin halin fadin don girman Allah Master ka bari ka barni in samu
natsuwa a jikina please na fada a cikin karfin hali.

   Lokaci daya da fadin hakan tsam naji ya
sakeni ya koma gefe daya yana numfashi a hankali kafin naga ya mirgina ya tashi
zuwa falo ba tare da yin magana ba.

   Abinci ya zauna
yaci kafin ya gama yajewa iyayyen shi saida safe a nan ne dije ke nuna mashi kayan
da aka deba muna cikin na garan da aka kawo muna din a gidan.

  Inda  take mashi bayanin komai bai tsaya saurarenta
ba ya mike yana fadin da safe zai shigo ya kwashe don dare yayi a lokacin.

   Y nufi kofan gidan
ya rufo masu gida ya juyo ya shige part din namu shima ya rufe saboda tsaro ya
tsaya ya duba ko ina kafin ya juya ya shige dakin ya rufo.

   Koda ya shigo dakin
ya hangoni na sunkule a wuri daya saidai kafafuwana suna kasa hakan yasashi
tsayawa ya dauki kafan ya dora min su saman gado tare da daukan wayana dake
hannuna ya aje a gefen gado kafin ya fada bandaki ya dan jima yayi broshe ya
fito.

    Ya dan dade a
tsaye yana kare min kallo yadda na kwanta da a laman a firgice na kwanta ko
kuma damuwa yasa na kwanta a hakan da nake kwance din.

    A hankali ya tako
zuwa bakin gadon ya hau gefen gadon shima a hankaki don kada motsin shi ya
tayar dani barcin dana samu din ina yi a lokacin.

    Haka ya kwanta
yana dan juyi a hankali yana faman yan sake saken maganganu a zuciyar shi kafin
ya mirgino zuwa inda nake yana jin nimshina na sauka a kunnuwan shi.

    A daidai lokacinne
ya sake ajiyan zuciya yakai hannunshi saman jikina ya rungume ni yana mai jin
wani iri a zuciyar shi lokaci guda.

   A haka barci ya dan
fara satan shi a hankali ya fara runtse idanuwan shi a hankali ya kara manna
jikin shi danawa ya fara barci.

   Can wajen asuba ya
falka a lokacin na kara dunkulewa sosai cikin jikin shi barcin ya gagareshi
komawa baisan sanda ya dauki hannayen shi ya fara dan wasa da sassan jikina ba
a hankali.

    Jin hakan kamar a mafalki yasa na bude
idanuwa a cikkn magagin barci ga idanuwana da nauyin barci lokaci guda nake
fadin wai hannatu meye hakane ?

    Murmushi yayi ya
ci gaba da abinda yakeyi a lokacin matsawan da yayi da yin hakan yasa na bude
idona da kyau ina dahintar abinda ke gudana a tsakanin mu a wanan daren.

  Saidai ban yarda
nayi motsin da zaigane cewa na falkaba sai faman runtse idanuwana da nakeyi ina
maijin yadda bakon yanayin ke ratsa min jikina har ina son kasa control din
kaina a lokacin.

    Sosai yayi duk
wani wasan da zai motsa sha,awan da namiji da mace dani don a karshe na kasa
hanashi ko boye nasan abinda ke faruwa a lokacin a hankali kunnuwa ke jiyo min
kukan akuyan na a cikin wanan daren.

   Wasa wasa ta fara
wanan kukan nata cikin wani irin sauti hakan yasa naga ya mike zaune da sauri
yana laluban fitilan hannun shi .

   Sai can ya lalubota
ya haska kan agogon bangon dakin da muke kwance din a cikinsa karfe hudu saura
kwata  lokacin sai kuma ya kashe ya san
jima a zaune bai kwanta ba.

  Ita kuma akuyan bata
sake kukan ba don tayi shiru haka yasa ya koma ya kwanta a rigingine ko zataci
gaba da irin kukua haka kukan da yasan bata faye yinshi ba sai idan wani abu ya
faru da ita take haka.

  Barci ya dan
daukeshi kuma aka fara kiraye kirayem sallah yasa ya mike ya shiga bandaki
wanka yayi ya fito ta samu na samu barci sosai
ina kanyi a lokacin.

  Ina jin bugo
kofanshi na bude idanuna da kyar na iya mikewa na fada ban daki wanka nayi na
dauro alwala na tayar da sallah ina idarwa nadan zauna nayi kirari ga ubangijin
mu Allah tare da fado madhi irin bukatuna dake raina.

   Na shafa na fito
falon mu har lokacin kofan yana rufe yadda yake naji ana buga kofan ta baya sai
mamakin hakan ya kamani a zatona wanine yake son shigowa part din

   Yasa na nufi kofan
da mamaki ina kai aka kara bugawa wanan karon da dan karfi yasa na fara kokarin
bude kofan inga waye a wanan lokacin haka ?

Leave a Reply

Back to top button