TUNATARWA

WASU DAGA CIKIN ILOLIN WAYOYIN ZAMANI WATAU SMART PHONE….

Sponsored Links

 


       WASU DAGA CIKIN ILOLIN 

     WAYOYIN ZAMANI


Barka da zuwa wanan shafin namu mai albaraka .


Yau ma haka mun zo muku da wata nasiha akan amfani da wayar hanu.


                        Gabatarwa 


Daga naku 

musa s zage


           FITINAR WAYOYIN ZAMANI 


Sanin kowa ne cewar an samu ci gaba acikin rayuwar al’ummah ta dalilin fitowar wayoyin Salula. Musamman ta fannin Saukin sadar da Zumunci da sanarwa, da Watsa labarai, da isar da Sakonni, etc.


To amma wannan lamarin na wayoyin Salula bai tsaya iya bangaren amfani kawai ba. A’a akwai wasu illoli masu yawa wadanda wayar salula ta zama dalilin bullowarsu ko faruwarsu ko kuma bunkasarsu atsakanin al’ummah. Musamman Matasa.


In sha Allahu zamu dauki wasu daga cikin bangarorin da ta kawo illar, sannan muyi bayaninsu dalla-dalla.


1- TARBIYYA


Wayar salula ta zama babbar hanyar watsewar tarbiyyar Qananan yara masi yawa. Misali akwai Yaran da ta sanadiyyar Wayar salula sukan hadu da gurbatattun mutane a Internet ko a makarantu da sauransu.


Ta bangaren ‘Yan mata da samari ma haka lamarin yake. Zaka ga yarinya an hanata tsayuwa da wani saurayi, amma in dai yana da lambar wayarta shikenan zai iya kiranta su hadu aduk wajen da suka ga dama.


Wasu kuma da tsakar dare zasu kusan kwana suna buga waya atsakaninsu, suna zantuka irin na batsa da sauransu.


Kuma sanadiyyar haka babu wanda zai samu yin sallar Asubah acikin Jam’i. Hasali ma yawancin samarin da suke yin haka, dama sallar bata damesu ba.


Wasu kuma sun zama Qasurguman ‘Barayi ta sanadiyyar fafutukar neman kudin da zasu sayi KATI su sanya awayarsu.


Akwai kuma wadanda suka zama cikakkun ‘Yan Dampara ta dalilin shiga yanar gizo da wayar Salula. 

ZAMANTAKEWAR AURE


Akwai aurarraki da dama wadanda suka watse ta dalilin wayar Salula.


Misali akwai Matar da bayan an riga anyi aurenta kuma zata ci gaba da buga ma tsohon Saurayinta Waya, tana hira dashi. Amma daga ranar da Mijinta ya gano haka, shikenan sai kaga aurenta ya Mutu.


Akwai kuma wacce take yin “ABOKAI” Maza a University ko College din da take karatu. Wadannan abokan nata Maza, zasu rika buga mata waya suna sanin Sirrin irin zaman da takeyi da Mijinta. Wai sune masu bata shawara!! 


Hakika aurarraki masu yawa sun mutu ta dalilin haka.


Ta dalilin Chatting na Facebook ko Whatsapp akwai matan da hankalinsu yakan dauke daga kan Mazajensu da ‘ya’yayensu. Saboda basu da lokacin kulawa da Mijinsu ko ‘ya’yansu. Lokacinsu gaba dayaa na chatting ne!!


Daga Bangaren Mazaje kuma akwai wadanda suke mantawa da hakkokin iyalansu akansu. Sun Kulla abota da ‘Yan mata a Social Networks. Wasu ma har da Matan aure. Babu kunya, babu tsoron Allah ko yaushe suna chatting dasu. Kuma mafi yawan chatting din na batsa ne da ashararanci.


Akwai wadanda Manya-Manyan Passwords suke sanya ma wayoyinsu don tsoron kar matansu su leka cikin Whatsapp ko Facebook dinsu su ga abinda suke aiwatarwa.


Idan Matarka bata ganka ba, to ai Allah yana ganinka. Kuma akwai ranar da zaka tsaya gareshi, dukkan halittu suna kallonka, Kuma idanunka da hannayenka zasu bada shaidar Tabargazar da kake aikatawa.


3- YADUWAR BATSA


Tabbas wayoyin salula sun taka babbar rawa wajen yaduwar Hotuna da Videos na batsa atsakanin Al’umma fiye da yadda mutum yake tunani.


Akwai wadanda suke shiga shafukan turawa na batsa domin dauko abubuwa sannan su rika watsawa aduniya, Ko kuma zuwa ga abokansu. 


Akwai kuma wadanda suke tura ma junansu ta Computer, Akwai kuma wadanda suka bude groups a Facebook da Whatsapp musamman don Gurbata tarbiyyar Al’umma.



Akwai Fitsararrun Mata wadanda suke bude irin wadannan groups din musamman wai don koyar da Jima’i!!


Idan kayi musu Wa’azi sai suce maka ai suna yi ne don habbaka gyaran zaman aure.. To tambayar anan ita ce : Waye ya koyar da Iyayenta da Kakanninta? Shin su ba Mata bane? Ko kuma basuyi zaman auren bane?


Akwai wadanda su sun wuce nan ma!! Wadannan sune ‘YAN MADIGO. Wadanda Allah ya riga ya kwashe musu albarka.


Babu kunya babu tsoron Allah, zaka ga suna Qirkirar labarai na batsa, Hirarraki na batsa, Har da lambonin wayoyinsu, Kai har ma akwai wadanda suke hada aure atsakaninsu irin AUREN ‘YAN MADIGO!!


Akwai kuma wasu Tambatsatsun Samari, Wadanda suke bude shafukan batsa, Basu da aiki sai rubuce-rubucen batsa, Da kuma hirar batsa tsakaninsu da irin wadannan Matan. 


Kwanakin baya mun fara rubuce-rubuce akansu anan Zauren Fiqhu Facebook amma sai na fuskanci cewar suna da Magoya-baya da yawa. Domin kuwa ban dade da fara rubutun akansu ba, sai sukayi mun Chaa! Har da masu gaya mana bakaken maganganu acikin comment!


Don haka ya zama wajibi Mazaje su rika leka wayoyin matayensu. Wallahi in ba haka ba, Wata matar zata aure maka Matarka ba tare da saninka ba, Ko kuma matarka ta zama Angon wata Matar! (SUBHANALLAH)!


4-Ciwon Baya:


Yawan dukawa domin duba sakonni ko kallon waya ya matukar wahalar da bayan masu amfani da wayoyin, 

5- Sanya Bakin Ciki Da Damuwa:


Dadewa ana kallon fuskar waya yana jawo damuwa har ma da bakin ciki, saboda mafi yawan lokaci ana tsammanin samun sako daga abokai da dangi, in sakon bai shigo ba sai a shiga damuwa ko ma bakin ciki, duk lokaci da mutum ya bata wajen amfani da wayar ya na nufin ya yi hasarar yin wani abu mai matukar muhimmanci Kenan.


Wallahi ‘Yan uwa bala’in nan ba Qarami bane!! Ya wuce dukkan tunaninmu!


Maluma suna da babban aiki agabansu na wayar da kan al’umma dangane da irin wadannan matsalolin. 


Yin irin wadannan Wa’azozin yafi alkhairi fiye da irin Lakchochin nan Masu cike da Hayaniya da Zage-Zagen raba kan al’ummah.


Hadin kai da samun Ingantacciyar tarbiyyah shine abu mafi Muhimmanci. Ba wai rarraba kan al’ummah don kwadayin Shugabanci ko neman abun duniya ba!


Allah yasa mu gyara. Allah ya taimaki Addinin Musulunci da dukkan masu son ci gabansa. Allah ya karya kafirci da fitsaranci da masu son yaduwarsa adoron Qasa. Ameeen.


Anan zamu diga aya cikin wannan topic namu  anan ya kamala, domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauran su. 


 Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.


  DAGA NAKU 

 MUSA S ZAGE 


   {{{{{za muka wo muku kadan daga cikin mfanin ta Anan Gabba… .}}}}}}

Leave a Reply

Back to top button