Sanarwa

Yadda Ake Gane Federal Civil Commission na Bogi.

Sponsored Links

A wannan lokacin da muke ciki mtane da dama sun baza idanun su a kafar sada zumunta na zamani kamar facebbok, Instagram da sauransu  domin hango dama ta aikin gwamnati ko kuma na kamfani mai zaman kansa, musamman yadda neman aikin a yanzu yazama abu mai bakar wahala saidai idan ansamu sa’a sosai ne ake iya samun aikin a ruwan sanyi.

To saidai wani hanzari ba gudu ba hakan yasa mutane da daman a fadawa hannun bata gari dake amfani da sunan wata hukuma domin karbewa mutane kudaden su,  musamman aikin damara da suka shafi police, Land Army, Air force, immigration dadai sauransu.

Yadda zaka gane wadannan bata gari:

Sukan bada wani link da zasu ce shiga nan domin yin rijista dazarar mutum ya shiga ya sanya bayanan sa bayan kwana daya ko biyu sai sufara kiranka a waya suce Congratulation! Kana daga cikin wadanda sukayi nasarar samun aikin inda zasu kara cewa yanzu za’a bude maka file sai ka turo kudi akalla N17,000 ko 20,000 daga nan sai su bukaci ka kara turo musu wani kudin bayan ka tura kason farko wanda suke kiransa da kudin Uniform, da sun kara karbe kudinka baza su sake sauraronka ba ko wayarka baza su kara dagawa ba.

KarantaDuk-wanda-ya-cika-neman-bashin-ranche na ……..

Hakane yasa arewa talent team sukeyin aiki dare da rana domin tantancewa Al’umma tsakanin aya da tsakuwa domin mugudu tare mu tsira tare, wannan tallan aiki na Federal Civil Service yana ta yawo a kafar sada zumunta dan haka sai a kiyaye idan kagani kafin ka rufta kafara zuwa hukumar ka nemi Karin bayani domin hakan shine zai bada saukin fadawa cikin ramin macuta na yanar gizo-gizo.

Leave a Reply

Back to top button