TUNATARWA
YAWAITA ISTIGHFARI YANA JANYO SAMUN ARZIQI MAI ALBARKA.
Sponsored Links
Daga cikin hanyar da Allah yake kawowa bayinsa arziki mai yawa anan duniya da lahira bayan Imani da jin tsoron Allah babbar hanyar itace:
YAWAITA ISTIGHFARI DA TUBA.
Yana nufin neman gafara da afuwar Allah da yafiyarsa ga abinda ya gabata na sabon Allah bayan tuba,da kuma neman yafiyarsa ga abinda kayi na laifi cikin abinda kasani da wanda baka sani ba,tare da neman afuwar Allah cikin abun da ka kasa na bin umarnin Allah da ibada.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
*(Dukkan wanda ya yawaita Istighfari ,Allah zai sanya masa mafita daga cikin dukkan kunci da yake ciki,kuma ya fitar da shi daga cikin dukkan wata Damuwa,kuma ya azurta shi daga inda baya tsammani)*.
@ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ ﻓﻰ ﺳﻨﻨﻪ
ﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:-
Dukkan wanda ya siffantu da siffar yawaita Istighfari,Allah sai azurta shi da:-
❶Allah ya saukaka masa samun arzkiqi kuma ya yawaiwata Arziqinsa.
❷Kuma Allah ya sanya masu sauki acikin dukkan al’amarunsa.
❸Kuma Allah zai bashi kariya aciki n lamarinsa,kuma ya karfafe shi acikinsa.
(
@ ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ( 450 /2 )
ﺇﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:-
Wani lokaci na kan sami kunci cikin wadansu al’amurana sai na dauwama yin ISTIGHFARI,na kanyi Istighfari a kalla sau dubu sai na sami budin Allah a cikin al’amaruna.
ﻗﺘﺎﺩﺓ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:-
Lallai wannan Alqur’ani yana shiryar da yi maku nuni zuwa ga cutukanku da maganin cutukanku,amma cutukanku shine SABON ALLAH DA ZUNUBI,maganin cutukar kuwa shine:ISTIGHFARI_*.
@ ﺷﻌﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ ( 6883 )
ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:-
Yawan sabo da zunubi yana janyo damuwa da tsoro da kuncin rayuwa,da cutukan zuciya,kuma babu wani magani ga wannan cutukan sai ta hanyar TUBA da ISTIGHFARI.
[@ ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ ( 191/4 )]
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺍﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
Allah ya datar damu Ameen.
وبالله التوفيق
daga dalibinku
musa s zage
.
Click To Comment