Auren Wucin Gadi 1
Chapter 1
Bismillahir rahmanir rahim.
__ƴan matan biyu tafe suke suna hira daka gansu kasan sun fitone daga gidan masu matsakaicin karfi duba da yanda kayan jikin su duka yasha jiki.
Fadila ta kalli Aisha tace”kawata nifa gaskiya nagaji da wannan rayuwa tamu kiduba dan Allah kigani an haifimu cikin talauci mun girma cikinta sannan aca wani takalan ya auremu kinga ko ba canji a rayuwar tamu kenan a haka zamu kare rayuwar mu daga mu har yaƴan da zamu haifa nan gaba.
Ɗan murmushi wacce aka kira da Aisha tayi tana dafa kawartata tace”fadila a rayuwa duk wanda kika gani cikin kowani irin hali to haka Allah yaso ya gansa ciki,da talaka da mai kuɗi duka matsayin su ɗaya awajen Allah.
Bawai dan Allah baya sonmu bane yayimu a matalauta sannan su mawadatan bawai Allah yafi sonsu akanmu bane yawadace su,yabasu ne don ya jarraba imanin su shin zasuyi taimako da wannan dukiya nasu da sadaka ko ko.
Misali yanzu aca yau wani hamshakin mai kuɗin dare ɗaya wani iftila’i ya faɗawa dukiyarsa aka wayi gari bashi da komai wallahi idan basa’a yaci ba sai ya kusa haukacewa,idan kobe haukace ba to wallahi halin da ze tsinci kansa ciki sai yafi wanda mu matalautan muke ciki muni.
Haka shima talakan wani idan yau cikin dare yasami kuɗi misali millon biyar tsaban farin cikin wani har mutuwa zeyi saboda yasami abunda betaɓa gani ko amafarki ba.
Ɗan dukan wasa fadila takai mata tana cewa”wallahi kefa muguwace kawata.
“To yanzu in banda abunki fadila tunda duniya ta xauna kin taɓa gani ko jin inda akace talakawa sun fito zanga zanga saboda su basu dashi kuma masu kuɗi sun riƙe abunsu basa basu?”a’a cewa fadila tana girjiza kanta”yo to mai nawani abun damuwa dan mu talakawa ne.
Naga ko annabawan Allah akwai talakawa,kede fadila ki godewa Allah dan duk halin da ake ciki na babu ba taɓa fashin ɗaura tukunya a gidan ku ba,amma mufa wallahi wataran sai ayi kwana biyu ba ɗaura tukunya a gidan namu ba.
Cike da tausawa fadila take kallon Aisha dan duk halin da suke ciki na babu da take rainawa su Aisha sun fisu rashi amma koda wasa baxaka taɓa jin Aisha na ƙorafi ba.
“Nikan kawata ya kukai da wannan masu ɗin kinnan?dan Aisha ta ƙore a dinki amma matsalar bata da keken dinki kuma bata da hanyan samu.
Nisawa Aisha tayi tace”wallahi kawata sau ɗaya naje na yini ina ɗinki tun karfe takwas ɗin safe naje bani nabaro shagon ba sai karfe shidan yamma amma wannan mutumin saboda rashin imani ya ɗauki ɗari biyar kawai yabani ko kuɗin abinci babu,wallahi sai da na haɗa masa riguna set baƙwai a hakan ma banda dogayen riga dana ɗinkawa wasu ɗinki express ina gani aka bashi dubu goma a riga uku.
“Kan bala fadila tace a masifance yanzu dama haka hafiz yayi miki rashin mutunci shine yake wani tambayata ya bakije ba,tab amma meyasa ke baki faɗamun haka yayi miki ba.
Dan ko ɗari ze baki akan kowace riga dakika haɗa yafi karfin yabaki ɗari biyar tunda ba koyo kike ba,sai kumfar baki fadila take kaman taga hafiz ɗin riƙo hannun Aisha tayi tace zo muje muji dalilin da yasa yaƙi baki hakkin ki.
“Haba fadila mai kuma zamuje muyi ai wannan zubar da ƙimane sannan ze zamana mun buɗe ƙofa dan a wulakanta mu yanzu da bansake zuwan ba bashi kenan ba,shima kansa yasan abunda yayi be kyauta ba kinga bashi da zarran aikowa yace naje.
Hakade sukai ta hiran suna tafiya har sukazo inda zasu rabu kowacce takama hanyan gidan su.
Alhaji badamasi dake zaune saman ɗaya daga cikin kugerun da sukaima falon ƙawanya ya kalli ɗansa Ahmad dake duƙe gaban sa cike da ɓacin rai yake magana”yanzu Ahmad saboda ban isa dakai ba,shine har ni zan yanke hukunci akanka amma kake neman zubamun ƙasa a ido?
“Ba haka bane ba,ai naje rannan,katseshi Alhaji yayi da cewa”to yanzu ma nace kaje haka gobe har sai kun fahunci juna da ita yarinya ƴar babba gida ga ilimi ga wayewa.
“Nide daddy gaskiya daso samune da anbar wannan magana dan ni kwata kwata wannan yarinyar batayi zubin irin mace da nake ra’ayin ba,wallahi.
“Shut up my friend yadaka masa ina magana kana magana sau nawa nabaka daman kafito da wacce kake so kakasa saboda haka wannan itace wacce tadace da rayuwar ka itace kuma zaɓin da nama dan haka kaje ku daidai ko kaje ko karkaje wannan ruwan kane yarage naka nagama magana itace matarka baka da wata mata bayan ita,umurni nake baka bawai shawaranka nake nema ba..
Ɗagowa yayi ya kalli hajiya mardiyya mahaifiyar Ahmad din da tunda suke magana bata samusu baki ba.
Yace”wallahi matukar yaron nan yaƙi zuwa su daidai ta da yarinyar nan to yanemi wani uban ba niba…..