Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 31

Sponsored Links

Chapter 31

Gudu kawai Anna take tana janye da hannu Aisha wacce batasan dalilin gudun nasu ba.

Saida suka shiga wani lungu sannan suka tsaya Anna tana haki ita ma Aishan haka kallon Anna tayi kafin tayi magana Anna ta rigata fadin.

“Aisha kiyi maza ki barnan kuka karki kuskura kice zaki juyo duk abunda kunnuwanki zasu jiyo miki,kuka Aisha ta fashe dashi tace”dan Allah Anna ni ki nutsu kimun bayani ta yanda zan fahinta,

Waye wannan din damuke gudun na sa?

Kuma meye alakarmu dashi dakika saka muke wannan gudun domin sa?

Dan Allah Anna kicire ni a duhun nan ta yanda zan iya fuskantar sa,idan yafi karfin ki ai befi karfin hukuma ba.

Maganganu mutane da suke jin yana kusonto su shiyasa Anna yin karfin hali cewa da Aisha”maza kitashi ki tsiratar da rayuwarki data ƴan uwanki amsan waƴan nan tambayoyin naki zaki samesu gida cikin tsohuwar akwati dake cikin ɗaki hanzarta kije ki dauki ƙannenki kije gidan haj ikilima.

Aisha sai kinzama jaruma kafin ki iya yakan sa wannan yaƙin na mahaifinkine ki kaddara a ranki tamkar muna tare dakene maza miƙe…..kafin Anna takai ga karshe maganan ta suka jiyo wani dargagegen ƙato yana cewa sauran”kuzo gata nan jin haka yasa Anna ture Aisha dake kuka ta ƙankameta tana”wallahi ni ba inda zani nabarki.

Da karfi Anna ta tureta daga jikinta tana”yazame miki dole Aisha kimun alkawarin zaki kula da kanki dama yan uwanki kizamo mai hakuri da mutune ita duniya makaranta ce mai zaman kanta maza gudu karki kuskura ki juyo sugane fuskarki.

Atare suka mike tsaye Anna tayi kudu da gudu dan son daukewa wayan nan kartin hankali yayinda Aisha tayi arewa tana kuka tana gudu kaman ranta ze fita kukan rabuwa da Annanta haka suka rabu kattin nan suka rufawa Anna baya.

Ahmad zaune yake yayi zurfi cikin tunanin sa har besan sanda Abokin sa faisal da khalid suka shigo office ɗin nasa ba,saida faisal yabuga table din gaban sa sannan yayi firgigit yadago yana kallon su.

Yatsine fuskan sa ya ɗanyi yana mikawa faisal ɗin hannu suna musabaha zama sukai saman kujera”guroom to be abokina yafaɗa yana dariyar shekiyanci.

Khalid ya amshe da cewa”karshede wani ze angonce sai mucire shakkun ko aljana ta aure shine saboda naga kaman matan ma tsoron su yake.

Dariya suka fashe dashi a tare taɓe baki yayi yace”kai kasani de da shegen gulma ba abunda ka iya sai kai kawo da ƙule ƙule katashi daga ɗan kasuwa kanason komawa dallalin haɗa aure.

Sosai maganar tasa tasaka khalid dariya dan yasan kan suhail yake magana shiko yanzu daya shigo nan ɗin dan suna tare da faisal ne yasa be nemata ya haɗasu a waya kaman yanda suhail ɗin ya bukata tun jiya yadame sa da kira ba.

Rike baki faisal yayi yana mai cewa”kace basai na wahala wajen neman mata ba kenan.

“Raba kanka da sharrin sa faisal da ina dillancin hada aure ai da banbari ya amince da wannan chewin gum ɗin tasa ba,kaide kawai ayi sha’anin ne.

“Sai naji abun alheri abokina cewa faisal yana ɓagarar da maganan Ahmad din nacewa na khalid dillalin haɗa aure.

Taɓe baki yayi yana wani basarwa kaman badashi yake maganan ba.

Damuwa fal ransa yamasa wanda ze tunkara da wannan abun,wai kaman sa ace za aura masa mata har biyu amma ba zaɓin ransa ko ɗaya ciki.

Gwara basma yasanta amma wancan ta WUCIN GADIN fa?

“Gaskiya an cuceni yafurta hakan afili ba tare da yasan ya furta hakan ba,dan yanda abun yake cinsa arai haka shi kaɗai yake ta surutu a ransa kaman wani zautacce.

“Lafiya abokina?
suka haɗa baki wajen tambayan sa cike da kulawa dan ganin yanda ya faɗa lokaci ɗaya kana ganin sa kasan yana cikin damuwa kawai faɗine baze yi ba.

Shiru yayi musu batare daya iya cewa komai dasu.

Dafashi khalid yayi yana cewa”na ɗauka munzama ɗaya bakada wasu waƴan da suka fimu meyasa bazaka iya share damuwarka damu ba.

Shin muda muke faɗama tamu damuwar bamusan muɓoye maka bane?

Kode baka ɗaukemu kaman yanda muka dauke kabane”ashe mu bamuda hankali ko bamusan ciwon kanmu bane muke fada maka tamu damuwar ko.

Faisal ne yafaɗi hakan cikin ɓacin rai ganin kaman ransu yaɓaci dashine yasa shi fesar da iska mai zafi ta bakin sa yace.

“Wallahi ba haka ne?

“To yayane suka hada baki wajen tambayansa.

Hmmm yasauke ajiyar zuciya yana cewa”wallahi bansan ta inda zanfara bane kuma bansa wanda zan tunkara da wannan abun danake ganin sa kaman a shirin film.

“Oh ashede haryanzu baka daukemu a matsayin ƴan uwanka ba kenan?
Cewar khalid.

“Haba khalid meyasa kake cewa haka kaima kasan bani da kamarku yayi maganan da tsigar lallashi.

Hmmm”karya kake damuna da wannan matsayin a gunka bazamu zauna muna tambayanka damuwarka kake wala wala damu ba.

Faisal kan yacika harya batsa saboda fushi ya dauki wayan sa daya ajiye saman table yamike tsaye yana mika musu hannu batare da yayi wata magana ba kana gani kasan fushi yayi.

Riƙe hannun sa Ahmad yayi ya zagayo gaban sa suna fuskantar juna yace”yanzu faisal fushi kake dani?
Ninefa abokin da kazaɓa tun muna yara a bainar jama’a.

Murmushin gefen baki faisal yayi yace”ko wancan lokacin ma ƙuruciyace tasani zaɓanka me za’ayi da aboki irinka mu idan mun ɗauki damuwarmu ko matsalarmu da muke tun kararka ai bamu da wayone kuma bamusan ciwon kanmu bane.

“I’m sorry F
Hmm kawai faisal yace yana mai zare hannun sa daga rikon da yamasa yanayin gaba.

“Ai nace kai hakuri ko?
Dan Allah khalid kasa baki yayi hakuri yazo mu zauna muyi magana nidinma ai bani da kamanku kawai de banson tada muku da hankaline ku ma.

Yayi kalan tausayi abunka da ɗan uwa kuma abokan juna dole suka zo suka zauna su kai shiru suka zuba masa ido danson jin abunda ze fito daga bakin sa.

*********
Aisha gudu take tana kuka baiwar Allah haka tanufi gidan nasu tana zuwa bata tsaya ɓata lokaci ba dan bata da nutsuwar tsayuwa tayi tunani ko dayakar wani abu.

Tana shiga ɗakin kai tsaye wajen akwatin karfe tanufa tana budewa wani kundi taci karo dashi bangon sa an rubuta mai DERTINY da manyan harufa harta dauko zata rufe akwatin idon ta yasauka kan wani album na hoto dauka tayi idanunta yana tsiyayar da hawaye harta kai bakin ƙofa tasake waigowa tayi wa gidan dakuma ɗakin su kallon karshe abubuwan da suke agida tare da Annanta da kannenta yana fadomata arai sauri fita tayi a gidan gudun kar maman salmanu tafito ta ganta ta tsareta da tambaya dakuma tuna maganan Anna.

“Allah yakaremun ke Anna ya kuɓutar dake daga hannun waƴan nan azzaluman sai inda karfina yakare wajen wannan yaƙin koda zan rasa rayuwata ne saina cikawa Abbana burin sa,daga haka tasakai fita.

Leave a Reply

Back to top button