Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 41

Sponsored Links

CHAPTER 41

Ɓacewa kuma Anty hajia?”eh Aisha tunda yayi wani yunƙuri akan safaran yara mata da akeyi hukuma tashiga cikin abun kaman fa da gaske daga baya shiru kikeji shikenan aka rufe babinn sa.

“Amma Anty hajjia su jami’a da muke dasu a ƙasar me amfanin su?

“Kina kallon movies?ta tabayita madadin ta amsa mata da tambaya da tayi”eh ina kallon ya amsa fuskarta dauke da mamakin ƙin amsa mata tambayarta da batayi ba.

Wata zuciyar tace yo ya zata baki amsa bayan mijinta da ɗanta duka suna cikin hukuman kuma ana damawa dasu.

Katse mata tunanin tayi da fadi”kaman de yanda kike gani a movies haka abun yake,hmmm ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa tsaye tana cewa”zanje na kwanta sai da safen ku.

“Da wuri haka karfa kisa abun a ranki ya hanaki sukuni abubuwa dasuke faruwa a wannan ƙasa tamu sai du’ai”in sha Allah shine kaɗai amsa data iya bata tayi wuce warta ɗaki.

Ahmad tunda ya baro sashin Ammin sa ya dawo part ɗinsa yasamo zarya cikin falon yama rasa meke masa daɗi,wani irin tunani zaiyi shifa ba yaro bane da zamasa auren haɗi wai ace amasa aure har biyu ciki ba zaɓin sa ko ɗaya aciki.

Harma gwara Basma tunda yasanta kuma tana sonsa shine de kawai sai a hankali,to ita wanda Ammin sa ta zaɓa masa fa?

Idan yarinyar ta kasance nakasasshiya ko bata daga tsarin macen da yake so fa,kai ina yayi saurin ture wannan tunanin.

ƴanya ze iya hakura ya amsheta a duk yanayi da ze ganta kuwa,kode zuwa ze yasamu ya lallaɓa Ammin sa a ware wannan auren tunda ba wanda yasan dashi.

Amma fa kai gaulane yama za’ayi kaman ka yaro ɗan kwalisa da kuɗinka da ajikan kana da kyau sannan ka haɗa duk komai wanda ko wace ƴa mace zata soka amma ace ka kare a auren haɗi gaskiya beyi ba.

Ire iren abubuwan zuciyar sa ke injiza shi dakyar ya iya shiga toile ya sakarwa kansa shawer ya jima tsaye a haka ruwan nabin jikin sa kafin ya kashe tap ɗin ya fito ɗaure da towel a ƙugun sa yana kuma tsane ruwan kansa da karami towel din ji yayi kaman yayi tuntuɓe da abu yasa shi janye towel yana binta da wani irin kallo wanda yasa jikinta yin sanyi cikin yauƙi da duniyanci ta miƙe tsaye tana cewa”haba my saura kwana nawane ashafa”sai kibari ashafa tukunna.

Rungumar sa take sonyi yayi saurin dakatar da ita ta hanyan daga mata hannu cike da ɓacin rai yake magana”sau nawa zance miki banason wannan ɗabi’ar yahudancin na rungume rungumen nan.

Please fita kikoma falo zan shirya kaina”haba my to mai aciki dan ka shirya a gabana ai yanzu munriga da mun zama ɗaya kazama ni nazama kai aiko nida nake ƴa mace ba wani abu bane dan nashirya kana kallo na.

Tunda tasoma magana yakafe ta da lulu idon sa kaman na maijin bacci saida takai karshe da magana da take kuma ba alaman zata fitan haka ya nufi clothes set ɗinsa ya dauki kayan sa yakoma toilet yasaka sannan ya zo.

Gaban tangamemen mirrown dayake jere da mayuka masu tsada da turaruka masu kala kala jere suke rurus kai kace kashiga kanti saida su,saida ya tsaya ya zaɓa sannan yafeshe jikinsa da turare kala uku duk ƙwakwafinka baka isa kace ga ainihin kamshin turare da yake ba.

A falo yasameta”me zaki sha akawo miki?

Shine tambayan da yamata sanda yake kaiwa zaune.

“Nothing ta amsa masa a taƙaice kafaɗan sa yaɗaga cikin ko in kula.

Ganin bazai tambayi dalilin zuwan nata ba yasata tasowa inda take zaune tazo da zauna kusa dashi ta ɗaura kanta saman kafaɗan sa tace”wai me yasa baka sona?

Me zanyi na burgeka a rayuwa harkaji kana sona?

Tabbas yasan basma na son sa kuma tana hakuri da duk wani halin ko in kula dayake nuna mata dan ko bakomai yasan sonda take masa tasa ta juran duk wasu rashin kulawa daga gareshi.

“I know yanzu de faɗamun meke tafe dake nasan de haka kawai bazaki zo a wannan lokacin ba?

Dan murmusawa tayi tace”ai tare muke dasu mommy na,sauri ɗaga kanta yayi saman kafadan sa yana cewa”shine kuma tuntuni baki faɗamun ba.

“Ba gashi yanzu kaji ba,dama zuwa mukai suga tsarin part ɗinda zamu zauna jibi idan Allah yakaimu masu dec_za suzo su duba suga ya yanayin tsarin zai kasance.

Kansa kawai ya gyaɗa mata yana mai cewa”kenan sun amince da tarewarki nan?meya canza ma daddynki ra’ayi lokaci guda haka?
Yakare maganan yana mai kamewa da ƙin sakin fuskan sa.

“Muje ka gaisa dasu mommy na,tafaɗa tare da miƙewa tsaye tana mai riƙo hannu sa.

“No kibarshi next time zan haɗu da itane,ɓata fuska tayi.

Riƙo hannunta yayi ya maidata xauna kusa dashi abunda be taɓa yi ba kenan cikin sanyin murya yace”kinga be dace sai ta tako taxo har gida sannan naje nace zan gaisheta ba,kuma kinga irin kayan da ke jikina.

******
Aisha kusan kwana tayi tana tunanin abun bacci duk gwanin iya satan sa ranan be ɗauketa ba.

Kusan raba dare tayi tana tunane tunane karshe kawai taji kuka ya kubce mata da wani tunani ya faɗo mata na ko Abban ku shima irin wannan mutuwan yayi.

Shassaƙan kukanta shi yatashi khadija dake bacci cikin sauri tamiƙe zauna tana subhanallahi Anty Aisha lafiya kike kuka warhaka kode haryanzu mutuwar samiran ne?

Rungume khadija tayi sai kawai itama khadija tasaka kuka duk da batasan abunda yayar tata kema kukan ba.

Dakyar sukayi shiru Aisha ta riƙo hannun khadija murya na rawa tace”khadija yanzu muma irin mutuwar da iyayenmu sukai kenan?

Tureta khadija tayi tana mai girgiza mata kai tana cewa”a’a Anty aisha iyayenmu basu mutu ba.

“ki nutsu khadija bani da kowa sai keda mubaraq kune kaɗai dangin dake gareni khadija ina ji ajikina kaman wani babban al’amari ze faru dani wanda ze nisan tani daku.

“Dan Allah Anty aisha kibar faɗin haka ba abunda ze rabamu kuma Anty akwai abunda baki sani ba amma yazama dole ki sani Abban mu be mutu ba yana raye.

Tureta tayi daga jikinta tana girgiza kanta hawaye na fareti saman kyakkyauwar fuskanta”karki soma khadija kode kema sun juya miki tunanin ki ne?

Kinga idan zaman mu anan ze kawo mana matsala to yanzu basai gobe ba zamu bar musu gida tunda amfani suke da ƙarancin tunanin mu dakuma rashin gatan mu.

Tana kaiwa nan da maganar ta tanufi wordrobe dinsu ta soma zazzago da kayayyakin su ƙasa kaman wata zautacciya haka takoma sai kuka take tana surutai duk yanda khadija tayi kokari dan ganin yayar tata ta nutsu abun yaci tura tun sunayi su biyu har hayaniyar su yatada mubaraq dake bacci shima yashiga taya ƴan uwan nasa kuka duk da besan abun da suke wa kukan ba,ganin Aisha na haɗa musu kayansu cikin wata ƙatuwar jakka tana kuka yashiga cewa”Anty aisha ina zamu je?

Ko kema zaki tafi kibarmu kaman Anna.

Jin abunda yaron yace batasan sanda tasake kayan dake hannun ta yafaɗi ƙasa ba,jawo shi tayi ta rungume shi tasaki wani kuka mai sauti.

Ganin haka ita ma khadija tazo ta faɗa jikin su Aisha tahaɗa su duka ta rungume su kuka sukeyi sosai Anty karki tafi kibarmu shine kawai abun yaron yake iya cewa”ba inda zani na barku kaji yi shiru ka kwanta na fasa kankameta yayi sosai gani yake kaman idan yasake ta zata tafi ta barsune har barci yayi awun gaba dasu baki ɗayan su a haka.

WASHE GARI

Diran mikiya Ahmad yayi ma gidan Antyn nasa dan son gani wacce mai kasada ce ta yarda da auren sa.

Lokacin da yazo gidan yaran suna shiga motan malik ze kaisu makaranta mamaki shimfiɗe saman fuskan yake binsu da kallo ina Anty hajiya ta samu waƴan nan yara musabaha sukai da malik har ƙasa khadija ta zauna tana gaidashi hakama mubaraq fuska sake ya amsa dan tarbiyar yaran yabirgeshi haka kawai yaji kaunan yaran yana tambayan malik”ina Anty tasami kyawawan yara haka?

Dariya malik yayi yana cewa”kyauta daga Allah ku ba kunƙi kuyi aure kutara musu jikoki ba,dukan wasa yakai masa yana gocewa sallama sukai yashiga ciki su kuma suka shiga mota suka wuce.

Sallama ɗauke a bakinsa yashiga falon,bakowa sai tv dake aiki shi kaɗai wulga idon sa yasoma yi can sai ya hango kaman gilmawar mutum dining room haka kawai yaji zuciyarsa na ingiza shi zuwa wajen.

Cikin takunsa na jaruman maza isa zuwa wajen,be kaiga ganin fuskarta ba saide tsuran jikinta kawai daya gani yaji tsigar jikin sa na tashi daure take da towel iya gwiwa kanta ba ko hula sai gashinta dake ɗaure da rebon tsaye take taba ƙofan baya da alama yunwa takeji sosai ko kuma sauri take soyayyan dankalin turawa ta zuba kaɗan cikin plate tana tauna a hankula jutawa tayi da nufin ta tafi ɗaki kawai ta ga mutum tsaye ba zato tasaki wani irin gigitaccen ƙara tana sakin plate ɗin hannun ta yafaɗi kasa tare da saurin ƙanƙame towel ɗin datake daure da shi dan karya faɗin.

Shikansa Ahmad wani irin abu yaji kaman electric shock ya jashi nunata yake da yatsa yanason magana amma ya kasa sai zuba mata ido kawai da yayi ba lalle ka gane yanayin da shiga ba.

Leave a Reply

Back to top button