Auren Wucin Gadi 54
CHAPTER 54
“Ai dama tunda naga wancan fitsararriyar ƙanwa taki taxo nasan dawata a kasa ashe keke sashin yimun rashin kunya,to wallahi bazan lamunta ba”wai Alhaji fisabilillahi ace mutum da ɗansa baze iya zama kona minti ɗayane ya fuskanci matsalansa ba kai kullum da kun haɗu kaman musa da fir’auna ai ba haka akeyi ba.
“Saiki faɗamun yanda akeyi yafaɗa a fusace kaman zekai mata bugu”Allah yabaka hakuri ya huci zuciyarka bana nufin ɓata maka nafaɗi hakan ba kuma Ahmad dakake magana kansa tun safe daya fita anan bansake sakashi a idanuna ba,sai yanzu daya kira yake cewa tafiyar ujulace ta kamashi jin faɗanka yasa shi kashe wayan sa.
“Karya yake yana nan ɓuyewa kawai yayi daga gareni ungo anshi wayan ki kiramun shi dan nasan inkece kikayi kiransa yanzun nan ze ɗaga niko danake maƙiyinsa bagashi yayi blocking wayana ba.
Ba yanda ta iya haka tasaka hannu ta karɓi wayan tashiga kiran sa saide kaman abun tsafi duka layinsa a kashe,ajiyar zuciya ta sauke tana maida waya ta ajiye bakin gado sannan tawuce tafita falo ta barshi a tsaye a ɗakin ƙerere kaman dogari,saida yayi tsayuwar kusan minti uku bayan barinta ɗakin sannan ya fito cike da fushi dan shi kadai yasan abunda yashirya ma Ahmad ɗin yana zuwa falo ya isketa zaune tana kallin tv labarun cikin gida kwafa yayi harya gifta ze wuce sai kuma yaja ya tsaya jin wani kanun labarin da yadauki hankulansu daga shi har Ammi.
Miƙewa tsaye Ammi tayi tana nuna tvn da yatsa”Alhaji mai nake gani haka?
Shima tsura mata ido yayi tana girgiza mata kansa kaman bashine yanzu ya gama tijare ta ba,kana nufin cemun bakasan abunda yake faruwa a company ba kenan?
Nan ma ɗaga mata kansa yayi dan shi kansa yashiga cikin matsanancin ruɗani”ana zargin cibiyar magunguna ta AL HAKK da fitar da gurɓatattun magunguna ba bisa ka’ida ba,dan haka hukumar nafdac ta ƙasa ta bada umurnin rufe wajen harsa tagama bincikenta.
Gumine yashiga karyo masa shide yasan basa sarrafa ko wani irin magani ba bisa ƙa’ida ba to meke shirin faruwa dashi?tambaya dayama kansa kenan kira yafara samu daga ƴan uwa da abokan arziki wasu jajanta masa sukeyi wasuko gulmace kawai yasasu kiransa haka ita kanta Ammi duk wanda yagani a labarai sai yakirata ita damuwarta ɗaya Ahmad ina yashiga gashi wayansa a kashe baya shiga,Anty hajiace takira itama jajen tawa yayar tata tayi sannan tadaura da cewa zatama faisal magana insha Allah daya shigo zata turashi can gidan naku yagana da Alhajin dan sanmu matsaya guda kafin sunan company sa yaɓaci godiya Ammi tayi ta zauna ta rabka tagumi,shi kansa Alhaji badamasi yama rasa mai zeyi dan kwata kwata jiyake ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak.
Alhaji sunusi yakira yana ɗauka yace”wai mai nake gani yanzu a labarai ne?
“Kaman yanda kake gani nima yanzu haka abunda nagani kenan narasa wake shirin ɓatamun suna company wallahi,na raini company na tun yana jariri harzuwa girmansa ban taɓa samun tangarɗa ba,nasha wahala kafin nakai wannan matsayi amma rana tsaka wasu da bansa kosu waye ba suke neman ɓatamun suna bani da maƙiyi kowani dana taɓa sa’insa dashi,ya kare maganan sa cike da rauni ƙwantar masa da hankali Alh sunusi yafara dan yasan koma waye yayi musu wannan abun to tabbas yasan sirrin abunda akeyi a wajen to amma waye shine de besani ba amma zeci gaba da baza yaransa dan su binciko masa gasu goga yanzu basama a ƙasa ko wace uwa duniya suka tafi oho tunda sanda yamusu rashin mutunci akan ɓacewar Ishak suka samu saɓani suka watse sukabar masa daban sa.
Haka yayi ta magana aransa amma a zahiri cewa yayi”ko zamu haɗu anjima da dare kaman yanda muka saba haɗuwane dan zuwa wajen shugaba ya taimaka mana koda wani abun.
Juyawa yayi yakai dubansa ga Ammi da take zaune shiru be ɗauke idonsa daga kanta ba yace”gaskiya sunusi bazan iya zuwa ba dan iyalina tafara zargina gami da fitan dare da nake.
Tsuka mai tsawo Alh sunusi yayi daga can ɓangaren yace” aikin banza kenan ai tun tuni saida nace dakai a mata aiki ta yanda koda mutum tagani kana yankawa bata isa tayima magana amma kaƙi,ni kaganni nan wallahi iyalina bata isa ta buɗe bakinta ta tankareni da koda makamancin irin wannan magana ba.
Sauke numfashi Alh badamasi da duk abun duniya suka nemi tsaya masa yayi yace”kabar wannan maganan yanzu mayi zuwa wani lokaci dan yanzu bana cikin yanayin da zan iya fahintan inda zancen ka yadosa daga haka ya kashe wayan ya barshi sororo riƙe da waya a hannu wai yau shine badanasi ke kashewa waya zanyi maganin ka yace.
Ahmad dake can gidan sa kwance besan me ake ciki ba tunda yabi kashe dukkan wayoyin sa kuma be kunna tv ba balle yasan abunda ke faruwa a gari.
********
Aisha kuwa bayan gama wayanta da suhail jin bemata magana ba gani take kaman taci amanan soyayya dan haka kuka tayi kaman ba gobe karshe wani irin zazzaɓine yayi nasaran rufeta har haƙoranta suna kaduwa katkatkat.
Anty hajiya da tadawo gida har kusan sama da awa biyu jin shuru bataji ɗuriyar ta ba yasata miƙe tanufi hanyan bedroon ɗin nata dan ganin ko lafiya kuma ta faɗa mata abunda yake faruwa da surukin nata dan ta jajanta samunta tayi lulluɓe sai rawan sanyi take dan haka da sauri tanufi bakin gadon tana yayi duvet data rufa takai hannu ta taɓa jikinta zafi taji rau”Aisha baki da lafiya shine bazaki kirani awaya ki fada mun ba.
A matukar ruɗe ta ɗagota ta rungumeta dukkanta ajikinta saide jin yanda zafin jikin nata ke ratsata tayi saurin tallaɓota tana kiran”malika fito da mota muje asibiti jin yanda Anty hajia ke kwala mata kira cikin rashin nutsuwa yasa malikan fito aɗaki aruɗe tambaya take”Anty lafiya?
Yanda ta ganta da Aisha yasata ƙarasowa wajen nasu da sauri tana taɓa jikin nata jin yanayin zafin jikin nata yasata furta”ya Allah wai meke damunta ne ba ɗazun nan muka rabu lafiya lafiya ba?
“Yi sauri mukaita asibiti yanzun ba lokacin tsayawa surutu bane musamu wannan zazzaɓi yasake tukunna musan abunda ke damunta shigana ɗakin kenan na taddata lulluɓe sai rawan sanyi take takare magana kaman zatayi kuka.
Wani karamin asibitin kuɗi suka kaita taimakon gaggawa aka shiga bata anmata allurai da karin ruwa takuma samu tayi normal bacci,saida likitan yafita yake cewa”hajia ku kwantar da hankalinku komai normal tasamu tayi bacci yanzu”zazzaɓin fa?ta katseshi da tambaya.
“Shima ya sauka hajia”wai meke damunta harya haddasa mata mata wannan zazzaɓi lokaci guda malika ta jeho masa da tambaya,gyara zaman glass dinsa yayi yana kare mata kallo gaskiya ba karya bebin ta haɗu takuma takuma burgeshi da yanayin nutsuwarta kana kallonta kasan classic baby ce duka wannan a ransa yake magana”ina ganin kaman tana cikin damuwa shine abunda ya jawo mata wannan zazzaɓi kaman kuma tayi jima tana kuka saboda yawan sauke ajiyar zuci da take amma fa karku damu in shaa Allah normal zata tashi daga bacci daya dauketa amma dole yau zamu riketa da takwana sai munga yanayin jikin nata tukunna”ai wannan ba matsala bane dakta cewa Anty hajiya takara da cewa ko zamu iya shiga inda take?”show bakomai idan kuna da bukatan wani abu pls lemme no yafaɗa yana kafe Anty malika da ido kauda kanta tayi tana cewa natsani yawan kallo a rayuwa wallahi mutum har mutum gaka idan anganka wayayye amma sai shegen kauyancin kallo haka sarai yaji mai take cewa cikin harshe turanci tayi maganan Anty hajia kan tuni tayi shegewarta ɗakin da aka kwanta da Aisha bata masan abunda sukeyi ba awajen.
Da yamma koda Malik ya dauko yaran daga makaranta yana zuwa mai gadi yake faɗa masa ai Aishace ba lafiya hajia babba da hajia karama malika yake nufi sun tafi kaita asibiti basu dawo ba laluɓosu awaya kaji inda suke.
Haka ko akayi dan wayan yakira yamayi sa’a anty Malika ta tafi da waya nan take fadamasa asibitin da suke,shima yah Faisal malik yakira shi yake sanar dashi duk da tarin aiyuka dayake dasu a gaban sa haka ya tsallake yaje asibitin dan duba halin da suke ciki.
Alhamdullahi jikikan da sauki dan ba yanda sukai tsammanin samunta ba suka sameta anan malik yakoma gida da Anty hajia da yaran gida akabar Anty malika ta zauna da ita zuwa gobe in yaso yanzu malik ze kawo mata da duk abun bukata.
Tsaye yake ya kafe allon talbijin ɗinda yakusa rabin bangon falon da ido saboda girman sa,kanun labaran da aka gaba badawa ya kalla sai kuma yayi dariya yace”sunusi ruwa takusa karewa ɗan kada.
Yaron sa dake tsaye a bayan sane yayi magana”kwarai oga wannan karon sai mun rusa karfin ikon sa na zalumci da yarda Allah.
Shima ɗayan dake zaune ya miƙe tsaye cikin ƙunan rai yace”sai mun tabbatar anma iyayenmu adalci wannan karon koda zamu rasa rayuwarmu amma in shaa Allah sai an wanke mana iyaye a idon duniya.
Sai kuma wani da yashigo yanzu falon da sallama amsa masa sukai yashga bawa ogan nasu bayani akan aiki da aka sakashi.
“Oga yarinyar da kafaɗa haƙiƙa ɗiyar kace da wani irin sauri ya juyo dan tun dazun be juyaba yabasu bayane eh oga yace kana ya daura da cewa yaran su ukune Aisha itace babba sai khadija mai bimata sai kuma karamin su mubaraq suna zamane gida Alhaji suleiman mai fata amma bincikenmu yanuna kaman basa tare da mahaifiyarsu yanzu sun dawo zama wannan gidan ne watanni uku dasuka wace,ita Aishan tana aikine karkashin company A&b travel agent fanin ɗinki take awannan wajen sannan naji kaman jiya Alhaji sunusi yamata barazana kan wani riga data ɗinka ɗiyarsa tagani tanason wannan kaya amma bata samuba saboda Aisha ta nuna mata bakomai kuɗi ke iya saye ba,daga baya kuma ita Aisha ta daura wani rubutu a shafinta na IG inda take sanye da wannan rigar gashi nan.
Yamiƙa masa wayan dake hannun sa cike da ladabi saide duk ƙwafƙwafin sa be iya yaga fuskar ta ba sabida imoji data daura yarufe mata fuska”like father like dauther ya furta ciki ciki,maida masa wayan yayi yana cewa”ka binciko mana mahaifiyarsun ina take rasuwa tayi kokuwa?
Bayan yafurta hakan kuma sai yaji wani abu mai nauyi yazo ya tokare masa maƙoshi tuni launin fuskarsa ta canza zuwa ɓacin rai komawa yayi ya zauna saman kugera yana lumshe idonsa ganin hakan yasasu suka barshi shi kaɗai dan sunsan yana bukatar hutu.
Alhaji shamsu da Alhaji sunusi sai Alhaji bala inda sukai zama na ujula a wani gidan gonan shi Alhaji shamsun nan Alh shamsu yamiƙe tsaye yana cewa”sunusi wani mai ke faruwane?
“Kaman ya ya tambaya daga zaunen da yake.
“Oh bakama sani ba kenan to bara na tunatar dakai maƙudan kuɗaɗe muka saka wannan harka kuma kai da bakinka ka tabbatar mana da bawata matsala yanzu gashi matsalan ta fara kunno kai”kwarai faɗa masade ko yafi jin naka ankame mana kaya na miliyoyin dalalo a malesiya yanzu gashi gida nan ma matsalan tarafa kunno kai ina mafita.
Sauke ajiya zuciya yayi sannan ya dubi abokan nasa yace ku kwantar da hankulanku nan fa 9jace kuɗi zamu tura yanzun nan sai kaji an canza zance kuma wannan company tana gab da zama mallakinmu”kaman yaa suka furta a tare file dinda ke gabansa yatura masu budewa suka suna zaro idanu waje dan ganin abunda yaƙusan…