Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 7

Sponsored Links

Chapter 7

Nakai kusan minti talatin ina cikin wannan yanayi natsoro dan ni kaina nakasa tantance shin ganin mutumin nan shi yasani tsoro ko ya?wata zuciyar tace shiɗinne bakiga yanda ya gargadeki da ido ba wannan ko kinyi abun azo a gani balalle ya ɗaukeki aikin ba,kawai ki tattara tsumman rayuwarki ki arce ba tare da kowa yasani ba.

Wannan shawara da zuciyata tabani yashigeni dan haka buɗe idanuna nayi dana lumshesu tuntuni nafara wulga ido naga kowa tsabgar gabansa yake wasuma sungama yanka har sun zo sun fara ɗinki kaman daga sama tsinkawo wata murya cikin kamala anmun sallama daga gefe na.

Amsa masa nayi fuska ba walwala yace”ƙanwata idan bazaki damu ba zan iya cewa wani abun?lumshe idona nayi sannan nasake bude su murmushi yayi mai sauti sai kuma ya ɗan kaɗa kansa yace naga tunɗazu kina zaune baki tashi kin ɗauki abunda kike bukata ba?shiru namasa ok na fahinta saurin kallon sa nayi jin yace ya fahinta a raina nace kode shima ya fahinci tsoron da nake ciki kaman kuwa yasan abunda dake cewa yace tsoro ko?wannan karon ɗaga masa kaina nayi alamar eh ƴar dariya yayi yace matsoraci baya zama goni kicire tsoro aranki ki hangowa kanki nasara karki hango daɗiwa kowace nasara tana tare da ƙalubale dan haka ki yaƙi tsoranki ki hango nasara dake gabanki maza ɗauki hoton da aka kabaki kije kizaɓi kayan da zakiyi amfani da shi,karon farko a rayuwata da wani yakarkamun gwiwa batare da sanin niɗin wacece ba”nagode nace dashi cikin sanyin murya wanda yake nuni da rauni na a baiyane.

Wani irin gwarin gwiwa naji da maganan da wannan dan uwa da nasamu ko sunan sa bansani ba take naji wani karfi ya shigeni kallo ɗaya nawa hoton na ajiye saman keken na nufi wajen tulin kayan na almakashi da tape na ɗauka sannan nanufi wajen kayan nayanka daidai abunda nake da bukata na yanka duk da kalan yadin irin mai tsilɓen nan ce mafi akasarin kiristoci sunfi amfani dashi sukan ɗinka dogin riguna amarya da kawayenta ranan aure mun dinka irinsu da yawa da wacce nakoyi ɗinki a wajenta wata ibo ce wacce muke kiranta da maman joy.

 

Cike da ƙorewa nayanka doguwar riga wato fitet gawn mai zizza namikawa yamun cikin ƙanƙanin lokaci nashiga sarrafa keken cike da ƙorewa ta da kuma son na burge kowa.

Dajin kare kukanka

Cikin wata ƴar bukka wani mutum ne zaune cikin kamilallaliyar fuska saide da kagansa kasan yana cikin matsanancin wahala duba da yanayin sa,wasu kattine majiya karfi suka shigo ƴar bukkar da yake tare da wasu manyan alhazawa biyu kugera aka kawo musu suka zauna suna fuskantar sa ɗaya yaɗago yana kallon masu tsaron sa yace”wai mai yasa kuke dauresane? kuringa sassauta masa”oga ai idan ba dauresan mukai ba zai iya guduwa ne.

Murmushin taƙaici yayi ya kalle su yace”wallahi dan banason saka ahalina cikin matsalane badan haka ba wannan igiyan be isa hanani fita daga nan ba wallahi.

Dariya duka suka kwashe dashi sai da sukai mai isarsu sannan Alhaji sunusi ya gimtse fuska kira sunan sa da ishaq” da kunyan duniya kwara ta lahira awajena da nabarka kafita ka tonamun asiri kwara na kasheka amma haryanzu de wata daman zan sake baka a karo na ba adadi ina waƴan nan ƙundaddakin suke?

Kauda kansa yayi gefe yana tuna abotarsu tun suna ƴan samari suka taso amma dare daya saboda abun duniya sunusi abokin sa aminansa da yafi yarda dashi duk duniya sama da kowa idan kacire mahaifinsa yau shine yake neman ganin bayansa akan dukiya.

Shirun da yayi besake koda kallon inda yake ɗin ba hakan yasake ƙular da shi dan haka cike da mugunta yabuɗe tafin hannun sa ɗaya ya shaƙi iska yafara wasu surutai kai nan da nan wanda akakira da ishaq yayi sama yariƙe wuyansa da hannu yayinda idanunsa kaɗa suka fiffito kaman zasu faɗo sai kakarin yake Alhaji sunusi yada ya tabbata amininnasa ya galabata sannan yasauke hannun yana saukewa kuwa ishaq yafaɗo ƙasa sau tari yake a wahalce zuciyan shikuma sai kiran sunan Allah yake da kakkausan murya alhaji sunusi yace”zankuma tambayanka ina waƴannan ƙundaddaki suke?amma ina ishaq be masan yanayi ba sabodq suman da yayi cike da takaici suka fito daga bukkar yana mai cewa masu tsaron nasa”a daren yau kuɗauke shi kukoma can gidan gonata da zama dan zaifi nan zan kuma irinƙa samun ku ta waya”angama ranka yadaɗe suka amsa masa suna take masa baya.

Ahmad
Ƙurawa allon systerm dake gabansa ido yayi yana ƙare mata kallo yanda take ɗinkinta batare da tana kallon hoton ba,tsaɓanin sauran da sauke ɗan kallon hoton lokaci zuwa lokaci“ƴan yarinyar nan zatayi abun kirki kuwa?ya tambayi kansa”me kawani sa systerm a gaba kana kallon ta idan so kake ka kalleta kawai umurni zaka bada tataho da keken nan kaga sai kaji daɗin kare mata kallo.

Mtsss tsuka yayi cike da jin haushin kansa shi yamarasa mai yaɗauki hankalinsa wajen kallon nata.

Munada aiki mai tarin yawa a gabanmu amma katsaya kana ɓata lokaci wajen kallon duniya khalid yasake faɗa.

Shide Ahmad banza yamasa yana ɗaga wani wayan bayan sun gama magana yadubi khalid yace”saif ne yana magana akan kayan da aka tura masa yakuma ce yaturo samfarin wanda zasake ɗinka masa.

Wajen nasu babba company yana da fannoni daban daban akwai magina sunada kwararrun masu zane wato architect akwai masu walda ƙofofi da tagogi sai masu ɗinki suna kuma da motocin sufiri masu tafiya garuwa suna kuma yin kasuwancinsu ta online suna aika kayayyakin su garuruwa da dama harma da ƙetare irin su chadi cameroon ghana niger cotouno sudan dade sauransu.

“Ok kasaka hannun kawai ake jira yanzu zasuyi lodi dan komai ya kammala.

Ataikaice de saida kusan kowa yagama yarage dagani sai wata yarinya wacce zatakai sa’ata muka rage kallona tayi a raunane tace”kema baki gamaba”eh na amsa mata dan zuwa yanzu ga ƴunwa gakuma gajiya duka sun addabeni sai kusan karfe biyar da rabin yamma muka gama kusan atare gugan kayan nayi na linke nasaka a ledar da nagani kowa nasawa na ɗan juya nakalli yarinyar nace yar uwa fatan nasara murmushi ta sakarmun nima namai damata muka fito a tare kusan a tare muka fito da Ahmad dake ta zabga sauri khalid na biye dashi a baya danshi yarasa gane saurin me abokin nasa yakeyi haka garin dauka jakata data zame daga kafaɗata kawai sai naji na bugu da abu ɗago kanda zanyi mukai ido hudu dashi bansan sanda nafurta”fatan nasara oga Ahmad ba.

 

Ƴan uwa karku shagala ku manta wannan littafi na kuɗine ki biya 300 dan samun complet dinsa.

 

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button