Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 74

Sponsored Links

CHAPTER 74

“Izawaka’a yasake kira cikin ɗaga murya kaman ze tsage bakin sa hakan sai ya jawo hankalin ƴan tsirarun da hankalin su baiyo kansa da farko kowa kallon sa yake da mamakin me kuma yakawo shi nan?

Waƴan da basu san koshi waya ba kuma suka shiga tambayan junan su wannan ɗi waye?idan ance daddyn basma ne sai kaga sunyi shiru suna kallon sa yanda duk yake a firgice to idan wannan shine Alhaji sunusin da sukejin sunan sa da labarin sa to meya firgitashi haka tambaya dasuke ma junan su kenan.

Yayarsa mai suna balara ce ta matso inda yake ta riƙo hannun sa tana masa alama da ido yanda duka mutanen wajen suka maida hankulan su kansa saurin barin wajen yayi duka a birkice yake,amarya basma kuwa ji take kaman ta daura hannu aka takurma ihu takeji ganin yanda daddyna ta yazo ya yarfata cikin jama’a sai kiran izawaƙa’a yake sai kace mai bitan karatu.

Ammi ce takira kanwarta Anty hajia a waya take sanar mata da rashin lafiyan Alh badamasi nan anty hajia tamata Allah yakara masa lafiya takuma cewa”in sha Allah gobe zan shigo dubashi zamu kuma tsara yanda bikin zamu gudanar da komai cikin tsarin wayayyu tunda yace bayason ayi bidi’a a biki kingani ko
ta ɓangaren mu kuma gashi saura kwana uku auren yaya kuma banji kince komai ba.

“To ikilima mai kuwa zanyi bayan kinfi kowa sanin bafa son abun nan nake ba”yaya kenan ko baso kikeyi ba kinsande baza fasa auren nan ba,dan haka zefi kyautuwa kawai kisaki ranki ayi abun nan kede kawai kisawa abun albarka,cike da ƙosawa da maganan ƙanwartata tace”kede sai kinshigo goben,daga haka ta katse wayan tana sauke ajiyar zuciya Ahmad dake zaune a falon yana aiki a systerm ɗinsa maida kallon ta kansa Ammi tayi tana gyara zamanta tace”saura kwana uku a ɗaura auranka da basma ko?”ummm kawai yace yana maida hankalin sa kan aikin da yake ta systerm din sa.

Washe gari kaman yanda suka saba bayan yin sallan asuba Aisha da anty malika tare suka shiga kitchen don hada abincin karin safe nan Anty malika ta kalle Aisha dake jujjuya miya tace”yau saura kwana uku auren mutuminki haka kawai taji baganta ya faɗi tayi saurin waskewa tana basarwa tace”eh nima haka nakeji .

“Kikeji kuma?da mamakin anty malika tayi magana”eh to mai hadina da auren da zan dami kaina?”ke ko kike da haɗi da auren tunda kece matar sa ta farko kuma zaɓin Ammin sa mafisoyowa a ransa.

“Hmmm lalle kan Anty malika karfa ki manta idan kin manta natunatar dake nan gaban Anty hajia da kowa yace auren wucin gadi yayi dani tunda baze iya cewa Amminsa a’a ba”amma Aisha kinsan…katseta tayi tana faɗin”ba abunda nasani Anty malika nide kawai abunda nasani oga Ahmad yayiwa Ammin sa biyayya ne tunda baxe iya ce mata a’a ba na wucin gadi yake zaune dani da zaran yasamu sarari sakina zeyi nama gode Allah da basa muntare dashi gida ɗaya ba balle ya maisheni karamar baxawara sanadin wannan banzan auren nasa na wucin gadi tana kare faɗin haka jitayi kuka nashirin ƙwace mata hakan yasa.

Da gudu tafita a kitchen din tayi ɗakin zuciyarta na tafarfasa duk sanda da tuna wai da auren wani a kanta auren ma na wucin gadi jinta take kaman tayi hauka sabida baƙin ciki kuma ko shekara ɗari zatayi a hakan bazata iya nunawa cewa bata son auren ba kodan saboda yanda anty hajia tariƙe ta da ƴan ƙannenta zata iya yimata komai ciki kuwa harda hakura da wannan auren da mai shi ke kira da na wucin gadi.

Ta jima a ɗakin tamarasa me yakamata tayi kan wannan kaddararren auren gashi ko sanda Allah yayi haɗuwarta da Abban ta taɓoye masa zancen auren dake kanta batasan me yasha mata kaita ba.

Tana nan zaune tana karantar wasikar jaki khadija data fito daga wanka tayi shirinta na zuwa skul ta kalle ta tagade kaman hankalin ƴar uwatata baya tare da ita.

Matsowa tayi ta dafata tace”anty komai fa yayi zafi maganin sa Allah, akan ki zauna kina wannan tunane tunanen zefi kyautuwa ki fauwala ma Allah lamuran ki idan kuma Annanmu kike tunani addu’a zamuci gaba dayi mata kaman yanda kika koyar damu Allah ya bayyanata aduk inda take yasa tana cikin ƙoshin lafiya,ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi ta ƙaƙalo murmushi da iya karta fuska bekai ciki ba ta dafa kafaɗan ƙanwartata cikin so da kaunarta dan ita kaɗai take gani taji sanyi a ranta sai mubaraq tace”jeki karki ɓatawa yah malik lokaci kinsan shi bayason ashiga lokacin sa ko.

“Aisha a kayi kiranta daga bakin ƙofa,ɗagiwa tayi tana amsawa da
Na’am anty hajia
“To yi maza kifito dan nasan halinki yanzu sai kice zaki zauna bakiyi breakfast ɗin ba harsai ya huce.

Fitowa tayi hannun ta riƙe da jakar makarantar mubaraq tana biye dashi duka kallon ta suke ganin yanda jikinta yake a sanyaye”lafiya?meke damunki?ko wani yamiki abunda bakya sone Aisha?

Duka wannan tambayan ajere tayi mata kuma a ruɗe take da ganin sauyawar nata dan tana matukar kaunar yarinya saboda kyawawan ɗabi’unta.

Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙaƙalo murmushi tare da sakin fuska tana tattara nutsuwarta tace”la Anty hajia wallahi bakomai kawai de natsaya ina shirya mubaraq ne yau da kaina.

Numfashi ta sauke tana cewa”to haɗa muku breakfast din”ke fa anty hajia bazaki ci komai bane?”ƴar dariya tayi tana jan hancin mubaraq dayayi maganan tace yau tare da ƴar uwata zamuyi kari a gidanta”Anty nima zan biki gidan Ammi yafaɗa cike da yaranta.

Malik ne yaɗan kalle sa yace”sannu ayawo wayace maka ana zuwa yawo ranan skul”D nimafa inason zuwan dande kar na magana ne kace nafiye son yawo cewan khadija dake zaune ummu salma namata dariya tace”to ai yanxu gashi kiyi maganan hararan ta khadijan tayi tana cewa”to ke wayasa bakin ki ai badake nake ba

“To ai….kallon da malik yayi matane ya hanata yin magana ta dauki shayinta tana kurɓa dariya Aisha da malika suka kwashe dashi ganin yanda tayi Aisha tace”kwantar da hankalin ki autar Anty tawaje na bagani ba,tafaɗa tana nuna kanta takare da cewa bama harka da masu muzurai ganin yanda Aisha tayi tana kwaikoyon yanda malik yayi yabata dariya sai gashi tana kyalkyalewa da dariya dayiwa khadija gwalo murmushi anty hajia tayi.

Bayan duka sun fita Aisha ta gyara inda suka ɓata ta tattare komai takai kitchen ta wanke duka a jiye komai a ma’adarsu ta wanke hannun ta tana gogewa da towel anty malika tashigo kitchen din cikin shirinta nafita shigowa kitchen ɗin tayi tana kallon Aisha da murmushi a saman fuskanta ita kuma Aisha kame fuska tayi taƙi kulata dafa kafaɗan ta tayi tabude bakin ta a hankali tace”Aisha dan Allah kiyi hakuri naga kaman fushi kikeyi dani banyi haka da wata manufa ba.

“Bakomai tace tana kauda kanta daga barin kallon ta”haba ƴa uwa dan Allah fa nace tafaɗa tana marairaice fuska tanayin kalan tausayi,vashiri tasakar mata murmushi mai sanyi tace karki damu ya wuce saide naji ba daɗine lokacin dakuma duk sanda na tuna da auren wani a kaina wanda besan darajata ba balle ya mutantani,balle ta auren da akayi mana hmmm koda yake na wucin gadine kaman yanda yace din yaɓata mun lokacina ya rabani da wanda yakemun soyayyar gaskiya kukane ya kubce mata dagudu tafice daga kitche din ta faɗa ɗaki tana kulle ƙofan tare da nufan toilet shima ta kulle ƙofan.

Komawa ciki Alh sunusi yayi a mugun hargitse zuwa cikin falon nasa a inda yabar abokan nasa nan yazo yasame su duk miƙewa sukai Alh bala da Alh shehu cikin matsanancin tsoron mai kuma yafaru Alhajin duk yabi yabirkice daga fitan yarinyar can haka”lafiya?

Zubewa yayi saman kujeran dake falon yace dafe da kansa kaman zeyi kuka yace”ku baku gane komai tattare da yarinyar da tafita yanzu bako?

Harsuna haɗa baki wajen cewa “a’a ba mugane komai ba”ina kyau tata zaton wannan itace yarinya da take bibiyar mu,kuma ina tsammanin taji duka abunda muke tattauna wa akai”shisa ashe naganta duka a firgice inji Alhaji shehu yafaɗa yana sharce zufa yana kakkaɓe babban rigarsa miƙewa duka sukayi suka shiga zage falon ko wannan su yana cizon ɗan yatsa ganin abun harinsu wacce suke nema ido rufe amma basu ganeta ba harsai da tabar wajen”inde hakane akwai gagarumin matsala Alhaji.

Allah de yasa bata leƙa cikin wancan ɗaki taga wani ba,cewar Alhaji bala aikuwa be gama rufe bakin sa ba suka miƙe suka nufi kitchen din a guje

Leave a Reply

Back to top button