Hausa NovelsInda Rai Hausa Novel

Inda rai 5

Sponsored Links

*INDA RAI*

*By*

*MARYAM ABDULKAHI*

(💔💋Oum Shaheed💔💋)

*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION*

Page 05

Bismillahirrah’manirra’him

Sosai Maryama take kuka, saboda jin kalaman mahaifinnata, kenan haka za’a kaita ɗakin miji babu ko tabarma ko mai? Allah sarki Innata, Allah ya miki rahma, ban bari sunmmin aure da Ballo ba, amma an ɗauramin da wani, wanda ko saninsa banyi ba, ya rabbi ka a gajeni, “ki tashi kiyi wanka ki sanja kaya kafun suzo ɗaukar taki, cewar Innar Rabi, cike da tausayin Maryama fal ranta, amma babu yanda zata yi sai haƴuri da addu’ar alheri a rayuwar Maryama ɗin, “kallon ta tayi bata ce mata komi ba, daƙyar da ban baki ta samu ta shiga wankan, bayan ta fito Inna Rabi ta bawa wata sabowar atamfa, wanda ta ɗinkawa Rabi, bayan ta fi to mai kawai ta shafa ta ƙarɓi kayn bayan ta yiwa Innar godiya, ta saka, ba laifi ta yi kyau sosai, duk da bata yanayi mai daɗi, asalin kyanta na asalin fulani ya fi to, ma shaa Allah cewar Inna Rabi, nasiha sosai ta mata akan zaman takewar rayuwa, sannan ta tashi ta fita zuwa gida domin ta sanar da mijinta zata raka Maryama ɗin dan ganin gurin zamanta.

Zuciyar Sudais fal murna ya shigo cikin gidan kakan nasa cikin takon kasaita da lafiyar jiki, “yirrriiiiiii, Umma kishiyar Inna ta biga guɗa, Allah abun godiya, daga zuwa ziyara sai komawa da mata, kai maa sha Allah Alhamdulillah, shiko Sudais gaba ɗaya jin sa ya keyi kamar wani tsuntsu mai tashi sama, ɗan uwansa ne ya faɗa masa a ransa, wayarsa ya ciro a ajihu ya shiga kiran bro ɗinnasa amma swich up, haka yata kira amma still a kashe, take yaji ransa ya ɓaci, farin cikin da yake ciki ya rago, why my bro? amma bari ina kuma wa gida zan san yadda zanyi muyi magana da kai, zaman Hindun ya isa haka. Haka ya ci gaba da kiran abokansa ɗaya bayan ɗaya yana musu wannan albishir ɗin, lalle shiɗin mai sa’a ne, ana cewa mutum baya auran first love ɗinsa, to gashi shikan ya ƙaryata wannan batu.. Haka yata saƙe saƙe har sanda ya sake jin Umma ta sake ra gaɗa guda a karo na babu adadi, hakan ya sanar masa da ƙarisowar amaryar tashi, Alhamdulillah ala kulli halim, haka ya ta mai mai tawa a fili da ɓuye, Allah sarki hikima, idan Allah ya ce eh, to fa babu wanda zai ce ba haka ba.

INDIA

Duk wannan bidiri da akeyi a Niberia shi kuma Imran ya na can rai a hannun Allah, tun bayan gama wankan da ya yi kp zai samu salama zazzafan zazzaɓi ya rufar masa, sai da Sakku ta kira masa Aliyu shi kuma ya kira Anwar, sosai suka girgiza jin zuciyarsa ta taɓo,
ya Allah, wai mai yake damunsa ne haka? cewar doctor Anwar kuma yaya agurin Sakku, “a jiyar zuciya Aliyu yayi yace” har dai yanzu zan iya cewa babu abun da yake damunsa kamar rashin ganin wannan yarinya ta mafarkin nasa, anya kuwa ba gamo ya yi ba? ace kusan shekaru biyar ana abu ɗaya, amma shiru kamar cin kwan makwauniya, haka suka tattauna sosai inda daga ƙarshe suka yanke shawarar kiran ɗan uwansa Barisster Sudais su faɗa masa halin da ake ciki, domin ɓoyewa wani nasa kamar wasa da rayuwarsune.

“Ban gane mai kake nufi ba Alhaji? wani iri kamasa aure kuma? kamar wani ta tsuniya, kana nufin wannan ba ƙauyiyar yarinya zan nunawa dangina matsayin sirika?? tu kunna ma ya kakeso nayi da batun Salha? mai zan cewa ƴan uwana? karma ka fara abun da kasan bamai ɓullewa bane sam. “Kin gama? Daddy ya tambayeta, idan kin gma nima ki saurare ni kiji nawa baton.

Nan ya kwashe duk abun da ya faru a wajan ɗaurin auran Maryama ya faɗa mata, sannan ya ɗaura da faɗin, “sannan bayan fasa auran da ɗauɗn uwanta ya yi shine Abba ya nemi a ɗaura da mai sunansa, kinga nima kenan umarni a ka ban kamar yadda zan bawa nawa yaran, ina fatan gkin gane? kum.. “Dakata Alhaji, ta katsai mai magana, kana nufin ɗan uwanta ya fasa auran shine a ka ɗaura da nawa ɗan ko mai? to wlh da sake, dole a kwance, taya ma za’ace dangina suji wannan abun kunyar? wato shine kuka kwaso ta kula kawo min? wama yasani ko mayya ce, kawai sai ta fashe masa da kuka mai cin rai, “ya gama gane bawai auran ta kewa kukan ba, rigimar ahlinta take gudu, tashi ya yi ya matsa kusa da ita, ya kamo duka hanna yenta yana wasa dasu, sannan ya ɗaura kanta akan ƙirjinsa yana bugawa da ɗaya hannun, sai da ua tabbatar ta samu nutsuwa sannan ya fara mata magana, “ki fahimta mana Heart beart, bawai da son rammu komi ya faru ba, ƙaddarar muce tazo da hakan, yarinyar abun tausayice ki taimaka kitayamu riƙe amanarta kinji ƴar albarka? ya tambaya yana leƙa mata fuska tare da jan karan hancinta cike da so da ƙaunarta. Ajiyar zuciya ta sauƙe jin ziciyarta ta fara samun sauƙi, tabbas ƙaddararsu tazo, amma babu abunda zasu ce sai godiya ga Allah, “shikenan Alhaji, in shaa Allahu zanyi iya ƙoƙarina akan wannan sabon al’amarin, “yauwa ƴar albarka, tashi maza kije kimata duk wani abun da ya dace da ita, sannan kar de a mata abun da ɗana zai zama kamar ni mijin kan tace, ya ƙarishe maganar da salon tsokana, “dariya tayi ta nifi ɗakin Samha, in da aka sauƙe Maryama.

Sudais yana gurin ai saboda kiran gaggawa da ya samu akan wani kes na fyɗe, sauri yake ya ƙarisa aikin dake gabansa domin ya kuma gida yaga annurin zuciyarsa, ko ya ta ƙare da Mommy? kirrrrr ƙarar shigowar kiran ya tsaida shi daga aikin da yaje famanyi jawo wayar domin kasheta, dama sam idan zai yi aiki baya barin waya a kunne, yau ɗimma ɗokine ya mantar dashi, amma mai,, ganin kiran da number ɗin waje yasa ya ɗaga tare da sallama, daga can India Aliyu yace, “kana magana da Aliyu daga ƙasar India, wato de ni abokin……… Da wani sauri ya miƙe tsaye yana furta whattt, kana nufin ɗan uwana ba lafiya tun jiya? shine sai yanzu zaka faɗamin? innalillahi, ya rabbi, baya yayi jin juya na neman kadashi, kit ya kashe wayar ya hau tattare nasa inasa, yau komi dare sai yaje yaga halin da rabin jikinsa ya ke ciki.

Har tsawon wannan lokaci da ake neman awa ashirin da huɗu Imran bai ko motsaba, abun ya basu mamaki sosai, saboda bai taɓa samun hakan ba, sunyi iya yinsu amma sai da suka dan gana dashi asibitin da yafi kowanne a ƙasar India, SANJE VANI, a can doctor Sin yaci gaba da kulawa dashi, sosai yake samun kulawa kasancewar an san abokinsa doctor Anwar.

Da wani irin gudu a ɗari uku da hamsin Sudais ya ƙarisa gida, ko sallama bai samu dan yiba ya wuce ɗakinsa, acan ya tarar da komi a gyare a killace sai tashin ƙamshin turaran wuta ɗan asakin cadi yake tashi, kasan cewar Allah ya sa masa son ƙamshi har fiye da tunani, bai gama wannan tunanin ba ya sake ganin uawar ɗakin nasa an janja komi an gyara har zanin gadon sabone, yama manta da wai wata Maryama balle auransa, jawo jaka yayi ya hau haɗa kayansa, cikin saudu sauri ya keyin komi, domin yamma ta tyi , kusan biyar na yamma.

Janye da jaka ya fito babban palon gidan, wanda yaji komi na more rayuwar duniya, kai tsaye ban garan mahaifinsa ya nufa bayan ya bar jakar a palo, sallama yayi aka amsa masa, bayan ɗan shiru da ya biyo baya Sudais ya katse shirun da sanar da mahaifin nasa aikin gaggwa ya taso musu daga gurin aiki, in da zai wuce SINGAHO yanzu, kallon sa Daddy yake tun fara maganarsa, “kenan sasoda mun maka aure baka so shine zaka bar ƙasar? ya masa tambayar idonsa akan ɗannasa, “ba haka bane Daddy, “to ya ne? nifa na haifeka, bayan dogon nasiha daya masa ya ce kuma doe ya bar tafiyar zuwa safiyar gobe idan Allah ya kaimu, ba haka Sudais ya so ba amma dole yabi umarnin mahaifin nasa, jiki a mace ya fice daga ɗakin yana jin sam murnar auran da ya keyi ya juye zuwa wanin kalar damuwa a ransa.

A can ban garan amarya sai shiryata Mommy take yi, har wannan lokacin bata sanar da kowa nata ba, ta bari kawai zuwa gobe taje da kanta ta sanar musu, sosai ta shirya maryama da kaya masu masifar kyau, ga turarurruka masu ƙamshin gaske, ba ƙaramin kyau sirikar tata ta mata ba, maa shaa Allah, to yanzu sai kitashi muje na rakaki ɗakin naki ko? “sake ƙasa da kai ta yi amma ta kasa cewa komi, haka ta kamata har zuwa part ɗin ɗan nata, in da anan zasu zauna kafin komi ya zama normal.

Nasiha sosai iyayen nasu suka musu kafun su musu sallama da fatan alheri su bar musu ɗakin.
Da kyar Sudais yake jan numfashi bayan fitar iyayen nasa, jin wani maye ƙarfe yana jan sa zuwa ga wannan daddaɗan ƙamshin, tunawa yayi da sallar na filar annabi ya koyar damu, a hankali ya tashi ya ƙarisa in da take ya riƙo hannunta, “kinada tsarki? ɗaga masa kai tayi a hankali, har wannan lokacin ta kasa gane wani yanayi take ciki, farin cikin ganinsa a matsayin miji ko mai,” ki tashi muyi alwala ko? ba tace masa komi ba ta zame hannunta daga nasa ta nufi toilet. bayan sun gabatar da sallar yayi mata tambayoyi ta amsa cike da kunya…

WRITING BY OUM SHAHEED

Leave a Reply

Back to top button