Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 30

Sponsored Links

 

*Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ne ba free book bane 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin Aminci kada ki karanta na sata na Allah ya isa. 0661110179 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in saki a Group ɗina*

 

 

Cappande. Acikin tafin hannunsa ya ɗebo sulallan Gwal ɗin da wasu yan guntu-guntun sanduna tare da birbiɗin yashin kana ya shiga jujjuyasu, ahankali ya maida kallonsa kan Innayi data gyaɗa masa kai alamar ya fito dasu hannunsa ya zura acikin tukunyar yashiga kalato salullan wanda na ainihin Gwalne aƙalla sun kai guda ashirin, karkaɗe yashin yayi tare da fitowa dasu kana ya ɗaura su akan rigarsa tare da gyara zaman sa abakin ramin ya tsura mata Ido Innayi ma ido ta zuba masa ganin yanda ya zauna yasa tashiga maida yashin ta rufe ramin kana ta sanya duwatsun ta rufe tare da tura fantekar kan ramin kallon Moddibo dake binta da kallo tayi kana tace.

“Ɗaura min randan nan akai”.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe still Idanunsa na Kanta cikin sanyin murya yace.

“Innayi wannan kamar Gwal?”.

Kai ta gyaɗa masa kana tace.

“Eh Gwal ne”

Still ba tare daya motsa ba ya sake kallon Gwal ɗin kana yace.

“Ina kika same su Innayi?”.

Girgiza masa kai tayi kana tace.

“Wannan ba lokacin tambayar ina nasamu gwala-gwalai bane. Moddibo lokacine daya kamata ace ka lissafa su muga adadin su kana musan nawa za’a samu mu haɗa mu karɓo Jameelu yanzu tashi mubar wajen nan mushiga ɗaki kaga dare ya tsala”.

 

Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

“Toh”,Kana yabi bayanta tare da tsira mata idanu cike da ɗumbin mamaki tare da tarin tuhuma ahankali ya sake kallon sulallan Gwal ɗin dake haɗe da waɗanan sanduna guntaye aciki asaman laɓɓansa yayi sallama tare da shiga ɗaki.

Wutan ɗakin Innayi ta kunna Atake haske ya zagaye ɗakin bayan Moddibo ta ratsa tare da rufe kofar ɗakin kana ta dawo kusa dashi ta tsaya  tare da sanya hannunta ta tsistsince ƴan guntulayen sandar ta shiga haɗawa kasancewar akwai wajen haɗawa ajiki Moddibo kuwa Idanu ya zuba mata cike da mamaki.

tana cigaba da haɗawa ga mamakinsa sai yaga ya zama sanda irin wanda manyan Limamai ke riƙe wa suna tafiya dashi sanda ce mai masifar kyau da tsari wacce da ka gani kasan mai tsadace.

 

Kallonsa Innayi tayi tare da cewa.

“Wannan sanda ce samansa inda ake riƙewa ne kaɗai keda Gwal sai kuma ƙasan sa inda ake dogara wa amma wannan bazan baka shiba saboda ba zaiyi daraja sosai ba. Saboda ahaɗe yake da sanda kana sandar kuma bazan siyar ba, sulallan dai zaka haɗa ka duba sai dai sunzo mana alokacin da bashine ba saboda sulallan baki ɗaya sun ƙare”.

Ido kawai Moddibo ya zuba mata still da shock atare dashi.

Innayi ta cigaba da cewa.

“Baki ɗaya nauyin karatunka.

Cin mu, shan mu, suturar mu, tun kana ƙarami da duk wani abinda ya kama  su nake ɗauka in siyarwa Alhaji Hashim mai sayan gwala-gwalai shiyasan farashin sulallan duk yanda suke zan faɗa masa adadin da suke yazo ya siya muyi lissafi muga nawa za’a samu”.

Kai Moddibo ya gyaɗa tare da cewa.

“Toh shikenan”.Yayi mgnar tare da lumshe idanunsa, baki ɗaya damuwarsa asamu kuɗin bawai tunaninsa ya tambayi ina tasamu gwala-gwalan nan ba sannan bashida kuzarin da zai iya tambayar ta, sandar na menene, kana bashi da ƙarfin zuciyar jin mai yasa baza asayar da sandar ba, ayanzu burinsa bai wuce asamu ahaɗa kuɗaɗen akarɓo J ba.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon Innayi kana yace.

“Toh zan tafi dasu ɗakina”.

Kai ta gyaɗa masa kana ya miƙe ya fita yana jin confidence da farin ciki yasan Gwal nada daraja duk da cewa ƴan ƙananun sulallane amma yasan da izinin Ubangiji zasuyi daraja.

 

Acan gidan Abba kuwa bayan tafiyar Moddibo Hajiya Karima ta kalli Abba daya zurfafa acikin tunani kana ta ɗan ya mutse Fuska tace.

“Alhji wai yanzu baza ka sake ƙara neman ragi ba? yanzu sai ka ɗauki Million ɗari da hamsin ka basu mai kake tunanin zai faru gaba idan sunji daɗi za’a sake ɗaukan ƴaƴanka ne fa!”.

Anutse Abba ya ɗago kansa tare da kallonta kana cikin sanyin Murya yace.

“Karima to me kike tunani?”.

Ba yabo ba fallasa tace.

“Ka nemi ragi”.

furzar da iska mai zafi yayi still Idanunsa na kanta kana yace.

“Karima kamar baki ji me yace ba, cewa fa yayi muddin aka nemi ragi akan rayuwar Jameel”.

 

Cikin sauri tace.

“Bafa za’a kashe Jameel ba, kawai Alhj idan zaka nemi ragi ka nemi ragi, sai kace baka sha zafin neman kuɗin ba zaka ɗauka agabtale ka basu kamar ba kasan darajar suba, amma babu yanda zaka ɗauki wannan maƙudan kuɗin ka bayar akan Jameelu!”.

 

Cike da mamaki Abba ya kalleta kana cikin ɗaga sautin murya yace.

“Karima to idan ban bada kuɗi akan Jameelu ba akan wa kike so in bayar? Shin Karima anya Karima?”.

Wani irin kallo ta masa kana cikin sauri tace.

“Anya me?”.

Dai-dai lokacin Hajiya Turai ta shigo baki ɗaya ta hargitse babu walwala afuskarta ta kalli Hajiya Karima kana tace.

“Ai dai kam abin nata da mamaki, idan bai ɗauki kuɗi ya bayar akan Jameelu ba akan wa kike so ya bayar?”.

Sai kuma ta maida kallonta kan Abba da idanunsa ke lumshe kana tace.

“Aini Alhj naga ƙoƙarin ku ma da har kuka iya neman ragin da suka rage muku, kuma ai sunyi ƙoƙari ni dai anawa tunanin kada ku kuskura kada ku sake yin batun ragin wasu kuɗin, suje su kashe mana yaro abanza idan aka kashesa mai son sa keda asara wanda bai sonsa kuma bai damu ba”.

Ta ida maganar hawaye na ciko kwarmin Idanunta.

 

Hajiya Karima kuwa wani kallo ta watsa wa Hajiya Turai tare da cewa.

“To mekike nufi?”.

Taɓe baki Hajiya Turai tayi kana tace.

“To ai gaskiya ne duk mai son Jameelu ba zai so ace za’a sake neman ragi ba”.

Taɓe baki Hajiya Karima tayi tare da watsa mata kallon banza kana tace.

“Kenan kina nufin Ni bana son Jameelu?”.

Hannu Hajiya Turai ta buɗe kana tace.

“A’a wannan ke ki kafaɗa da bakin ki amma dai shawaran da kika kawo ba shawara me kyau bace”.

Hannu Abba ya ɗaga musu tare da kallon Hajiya Karima dake kumfar baki kana yace.

“Bana son hayaniya ya isheku.

Dan Allah kubarni inji da abinda ke damuna”.

Kai Hajiya Turai ta gyaɗa tare da tsuke bakinta alamun itama ba hayaniyar take soba.

Cikin sanyi ta kalli Abba tare da cewa.

“Alhj ga Million biyu a Account ɗina zan bayar ahaɗa”.

Wani shegen kallo Hajiya Karima tabi Hajiya Turai dashi kana cikin taɓe baki tace.

“Hmmm munafurci dai da neman gindin zama haddasu kaza acikin cin danƙo”.

Cikin sanyi Abba yace.

“Nagode Turai Allah ya saka da alkhairi ayanzu kyauta koda na Naira biyar aka bani ita ina buƙatar ta, xansa acikin tumunin kudin da za’a karɓo Jameel”.

Cikin sauri Hajiya Karima tace.

“Nima Allah ya bani in bayar”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Ameen”.

Juyawa tayi ta fice Hajiya Turai kuma ta zauna gefensa tana sake tausansa.

 

Acikin kwanaki biyu Moddibo ya saida gwala-gwalan da kuma motocinsa dana M Jameel Yayi total ɗin  kuɗin sun kama Million ashirin da biyar ya turawa Abba cikin account ɗin sa Alhamdulillah yanzu akwai Million casa’in da biyar acikin account ɗin Abba Aɓangaren Abban ma yana cigaba da fafutuka ganin ya samu kuɗi.

Acikin kwanakin baki ɗaya abubuwa sun kankama baki ɗaya sun sake maida hankalinsu kan neman kuɗin suga sun samu sun haɗa yau ya kama kwanan M Jameel goma kenan awajen Kidnappers din kana yau kwana biyu rabon Abba da Moddibo suyi waya da M Jameel Misalin huɗu na yamma Moddibo ya bar gidan Abba ya nufi gidansu bayan sun sake tattauna wa.

 

Acan ɓangaren Boka Kar’uzu kuwa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce gurfane agabansa cikin wata sandararriyar murya Boka Kar’uzu ya kece da wata mahaukaciyar dariya tare da jujjuya gashin dake wangamemen tafi  hannunsa kana ya ɗago kansa tare da Kallon Hajiya Bunayya da jajayen Idanunsa da suka tara kwantsa yace.

“Kin tabbatar gashin yaron ne dai ko?”.

Cike da ƙwarin gwiwa Hajiya Bunayya ta jinjina masa kai tare da faɗin.

“Tabbas na tabbatar Boka Kar’uzu Uban bokaye La’anannen Uban La’anannu Mugu Uban mugaye tsinanne Uban tsinannun wannan gashin kan Ramadan ne domin dana shafa  turare  na shafa kansa  bayan na fita naga gashi ya manne ahannu shine na tattare na kawo maka kamar yadda ka umarceni.

Wata mahaukaciyar dariya. Boka Kar’uzu ya sheƙe dashi wanda yasa bukkan da suke ciki ya hau girgiza cike da jin daɗin kirarin data masa yace.

“Hhhhh magana ta ƙare Ƙaramar la’ananniya me kafirar zuciya aiki ya riga yayi anwuce babinsa saura na Babban”.

 

Girgiza kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

“Agama da batun Ramadan ɗin kafin ayi na Haiydar to babu matsala wannan ba damuwa bace”.

Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe kana tace.

“Ni kuma Boka yanzu Abban Samira na nan amma nanda sati biyu masu zuwa zai tafi aikin Umrah, shiyasa nayi shiru da batun zuwan Samira nan  mu bari sai mahaifinta ya tafi  kaga ba kowa agida da banaso daga gidan Hajiya Bunayya arika zuwa ana daukan ta saboda sa idanawa. Amma Alhj na tafiya  idan ya kama ma ta dawo gidan ka idan kuma kaine ma zaka rinƙa kwana idan gari ya waye ka dawo to duk daya”.

Wata dariya mai masifar ƙara Boka Kar’uzu ya kece dashi kana buga ƙafarsa na hagu wanda baki daya ƙura ta buke wajen kana yace.

“Hhhhh saishi Boka Kar’uzu Uban bokaye La’anannen Uban La’anannu Mugu Uban mugaye tsinanne Uban tsinannun shaiɗani Uban shaiɗanu babu wata matsala da zaran ya tafi zan zo Ni da kaina dan zamu fi sakewa agidan naku acan ma zan tare in ragargaji sabon budurci”.

Kai Hajiya Lami ta gyaɗa tana murmushi kana tace.

“Yanda kake so haka za’ayi”.

Daga nan suka miƙe suka fita ta baya kamar yanda suka shigo suka nufi gida ransu fari soll musamman Hajiya Bunayya.

 

Acan ɓangaren Khausar kuwa sanye ta fito cikin hijabi maroon mai facemaks kafadarta rataye da jaka fari sol jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin turaren Oud Ma’aruf cikin yanayin sanyin ta da tun ɓatan M Jameel bata dawo dai-dai ba ta kalli Mommy dake zaune kan 2sitter kana tace.

“Mommy zan tafi”.

Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

“To kice ina gaida Ummi”.

Kai Khausar ta gyaɗa cike da nutsuwa ta fita tare da sanya Platshoe fari Anutse ta nufi coumpund ɗin dai-dai lokacin da Amina da Uncle Naseer suka shigo hannunsu sarƙafe da juna kallo ɗaya Khausar ta musu ta kawar da kanta gefe kana ta lumshe Idanunta.

 

Ido Uncle Naseer ya zuba mata tare da shafa kansa kana cikin sakin fuska yace.

“A’a Khausi ina zuwa da yamma nan?”.

Batare data sake kallon inda suke ba kana cikin sanyin murya tace.

“Zanje gidan su Asma’u ne”.

Langwaɓar da kai yayi kana yace.

“Ai haka dai maganar bata haɗa muba Khausar, ashe wai Malam Jameel aka sace Agaskiya garin nan ya fara bada tsoro bari muje na kaiki in jajantawa Ummi”.

 

Girgiza kai Khausar tayi kana tace.

“A’a kabari kawai”.

Cikin sauri Amina ta watsawa Khausar harara kana ta maida kallonta kan Uncle Naseer Shima ta hararesa.

Uncle Naseer kuwa ganin kallon da Amina ke jifansu dashi yasa ya ware idonsa tare da sakar mata da lallausan murmushi kana yace.

“Ohh Baby Colm down mu nayin Auren mu zan ɗauke ki mu gudu mubar ƙasar nan, kafin muma Akinnafemu tunda kinga anfara tsincr ƴaƴan masu kuɗi an ɗauke Malam Jameel next target ɗin su ni za’a ce za’a saɓe ko ke, kafin ma su ankara zamu gudu abinmu.

Dariya Amina ta ƙyalƙyale dashi tare da manna kanta ajikin damtsen hannunsa.

Khausar kuwa cikin sauri ta kawar da kanta gefe tare da lumshe Idanunta.

Ahankali Uncle Naseer ya ɗago kansa tare da tsura wa Khausar Ido tabbas soyayyanta acikin jininsa yake har yau har gobe zuciyarsa na muradin Khausar, itace burinsa Kawai zai Auri Amina ne domin cikar Burinsa amma Khausar itace muradinsa.

 

fesar da iska mai sanyi yayi yana jin wani irin yanayi agame da ita kana yace.

“Khausi jirani in ɗauko sakon Uwaniyona inzo in kaiki?”.

Da sauri Amina ta janye kanta dake manne adantsensa kana tace.

“Ka kaita kuma?”.

Kai ya gyaɗa tare da yimata raɗa akunne yace.

“Yes My dear wife ai jaje ne”.

Ashagwaɓe ta girgiza kai tare da cewa.

“Gaskiya Ni dai Uncle Naseer bana so ka tafi ka barni”.

Shafa fuskarta yayi kana yace.

“Bafa daɗewa zanyi ba”.

Khausar kuwa cike da takaicin abinda sukeyi tace.

“A’a Uncle Naseer ka bari ganan Haiydar ma zai kaini da mashin ɗinsa”.

Kai ya gyaɗa still Idanunsa na kanta yace.

“Ok”.

Dai-dai lokacin Haiydar ya fito daga sashen Abbansu hannunsa riƙe da key mashin dinsa.

Kallon Uncle Naseer da Haiydar yayi da murmushi afuskarsa yace.

“Uncle Naseer yau dai Addah Khausy ta yarda in jata amashin ɗina”.

Cikin alamun so Naseer yace.

“To ayi a hankali dai banda fifita”.

Dariya Haiydar yayi tare da cewa.

“Uhmm aikam zata sha fifita”.

Murmushi Uncle Naseer yayi tare da cewa.

“Dan Allah ka jata ahankali kada kayi mana asara”.

lumshe Idanunta tayi baki ɗaya bata da wani kuzari ɓatan M Jameel yayi masifar ratsata hakan yasa ko magana bata fiye yiba daga Um-sai Um-um.

Haiydar kuwa mashin ya ɗauko tare da ɗaukar ta suka fice kana Amina da Uncle Naseer suka shiga ciki.

 

Haiydar na isa kofar gidan Ummi yayi Parking ahankali Khausar ta sauƙa tana gyara zaman hijabinta kana atare suka shiga cikin Falon Ummi bakinsu ɗauke da Sallama.

Ummi dake zaune riƙe da carbi ahannunta Asma’u da Bashir na zaune gefenta suka Amsa Sallamar.

Cike da ladabi Haiydar ya gaisheta tare da sake yi mata jaje kana suka gaisa da Bashir tukunna suka fice atare.

Khausar kuwa cike da sanyin tace.

“Ummi ki kwantar da hankalin ki insha Allah yaya Jameel zai bayyana babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji addu’a mu bazai tafi abanza ba”.

Jinjina kai Ummi tayi cikin yanayinta kamar mara lafiya tace.

“Ameen ya Allah”.

Cikin sanyin murya Asma’u da Muryanta ya dishe da kuka tace.

“Babbar matsalar mu yau kwana biyu kenan Basu sake kira ba gashi baki ɗaya kuɗin Million Casa’in da biyar aka samu aka haɗa”.

Kallonta Khausar tayi tana cire hijabinta tace.

“Haka dai kika cemin jiya har yanzu kuɗin basu haɗuba”.

Kai Asma’u ta gyaɗa mata kana tace.

“Basu haɗu ba Khausar damuwar dake damunmu kenan wlh, baki ɗaya hankalinmu ya kasa kwanciya sai dai Yah Modibbo yace Abba ya nemi bashin banki amman sunce yau ko gobe zai samu kuɗin”.

Cikin sanyin murya Khausar tace.

“Insha Allah kuɗin zasu haɗu da izinin Ubangiji Allah ya karesa ya tsare lafiyarsa”.

Atare suka amsa da Ameen.

Shiru Khausar tayi tare da tallafe kuncinta kana ta kalli Ummi da Asma’u sai kuma ta fesar da numfashi kana buɗe jakarta tare da kwaso ƴan kunnaye da sarƙa da kuma zobe kala biyu da alamun nata dana Mommy ne,  hannun Ummi ta kama tasasu a ciki kana ta rufe hannun Ummin tare da cewa.

“Gashi inji Mommy na, tace Dan girman Allah da Manzonsa kada ki ƙi karba Ummi dan Allah kada kice komai a saidashi a haɗa kuɗin.

Cikin tsananin jin dadi Ummi ta kalli girman Gwal ɗin musamman na Mommy wanda a ƙalla shi kadai zai iya kai one Million da yan ɗori.

Hawaye na tsiyayo mata tace.

“Bazan ƙiba Khausar kicewa Mommynki ngd matuƙa ubanji yayi mata sakayya da gidan al’janna mai girma”.

Cikin sanyi duk suka amsa da Amin.

Cikin sanyi Khausar ta fesar da numfashin kana a hankali tace.

“Amma Ummi Meyesa ba asa Police acikin maganar ba?”.

Cikin raunin murya Ummi tace.

“Sunce muddin Akasa police acikin maganar to abakin ransa”.

Cikin sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

“Innalillahi  akan ransa kuma?”.

Kai Asma’u ta gyaɗa Tare da cewa.

“Kuma batun kuɗi ma da suka ce da farko Million ɗari biyu sukace yanzu ya zama Million ɗari da hamsin saboda ragin da aka nema to yanzu sunce muddin aka sake neman ragi akan ransa”.

Aruɗe Khausar ta rintse Idanunta tare da cewa.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

Sai kuma ta juya tare da kallon Ummi cikin sanyin murya tace.

“Ummi kinsan wani abu?”.

Kai Ummi ta girgiza kana tace.

“A’a”.

Lumshe idanu Khausar tayi tare da cewa.

“Ummi ranan da Yah Jameel ya mai dani gida da muna tafiya munga wata mota tana ta binmu abaya”.

Sai kuma tayi shiru alamar tunani ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Ummi shine fa dama nace da za’a faɗawa hukuma zan iya bada number Motar saboda na zargi motar duk inda mukayi motar na biye damu wataƙil da hukuma zasu shiga za’a iya kama wa anda suka sace Yah Jameel, domin tun fitar mu motar ke bibiyanmu har saida muka kusa gidanmu suka daina binmu”.

Cike da mamaki Asma’u tace.

“Kai Khausar?”.

Kallonta Khausar tayi tare da gyaɗa mata kai kana tace.

“Wallahi kuwa Asma’u amma lokacin bamu kawo komai aranmu ba shima kuma Malam Jameel Bai kawo komai ransa ba”.

Girgiza kai Ummi tayi kana tace.

“Toh ya zamuyi idan an faɗa zai zama matsala zasu kashesa tunda sunce basu yarda afaɗa wa hukuma ba shiyasa dole muyi hakuri”.

Jinjina kai Khausar tayi kana cikin sanyin murya tace.

“Toh shikenan Ummi Insha Allah zamu cigaba da yiwa Yah Jameel Addu’o’i Allah ya bayyana shi”.

Jingina kai Ummu tayi tare da cewa.

“Yawwa shine abinda ya dace Allah yabamu Sa’a”.

 

Wunin wannan ranan haka Khausar tayi ta rarrashin Asma’u da Ummi kana tana sake basu ƙwarin gwiwa kan cewa da izinin Ubangiji M Jameel zai dawo bayan Sallar sala’sar ta koma gida tana isa gida daga bakin.

Barandarsu ta jiyo sautin kukan Ramadan cikin sauri ta cire takalminta tare da shiga falon bakinta ɗauke da Sallama.

Cike da damuwa ta sauƙe Idanunta akan Ramadan daya kifa kansa kan cinyar Mommy cikin rauni da raɗaɗin ciwo yake jujjuya kansa akan cinyar Mommy kana yana cewa.

“Mommy Kaina ciwo!,Mommy Kaina zai fashe!”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe Cike da damuwa tace.

“Subhanallah Ramadan yau tun safe kake ta cemin kanka na ciwo to meke faruwa ne na baka magani kasha abanza ko dai in kira Abbanka ne akai ka asibiti?”.

Cikin tsanananin ciwo ya Girgiza mata kai yayi kana cikin Muryan kuka yace.

“Mommy ni dai Banason allura aƙara min magani kar kaina ya fashe”.

Khausar kuwa cikin sauri ta cire hijabinta kana ta ƙara sa kusa dashi tare da ɗaura tafin hannunta akan goshinsa lokaci ɗaya zafi ya ratsa tafin hannunta har ƙananan jijiyoyin kansa sun tashi suna harbawa cikin sauri ta kalli idanunsa gani tayi sun kaɗa suyi jawur dasu kana yanayin su ya koma kamar ajuye.

 

Saurin kallon Mommy dake jera masa sannu tayi kana tace.

“Subhanallah gaskiya Mommy akaishi Asibiti”.

Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Ramadan dake ta juyi kana ta kalli Khausar dake cikin damuwa ta fesar da numfashi tare da cewa.

“Nima nace aikai shi asibiti amma yace baya Son allura da zaran nace akaisa saiya sa kuka”.

Girgiza kai Khausar tayi kana ta sake shafa goshinsa da yayi masifar zafi cike da damuwa tace.

“Mommy yaushe za’a biye masa jifa yanda kansa yayi zafi kamar wuta”.

Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

“Bari akwai maganin da Abbanku yace zai sayo masa yanzu bari idan ya kawo za’a bashi idan Allah yasa ya samu sauƙi shikenan idan kuma abin be lafa ba dole sai mutafi asibitin”.

Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.

“Toh shikenan Allah ya bashi lafiya Allah kuma ya dawo da Abba lafiya”.

Mommy na shafa kan Ramadan tace.

“Ameen”.

 

Acan ɓangaren Abban Jameel kuwa ahankali ya miƙe tare da kallon wayarsa kana ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da nufar toilet domin ya watsa ruwa baki daya baya jin daɗin jikinsa bakinsa ɗauke da addu’a ya shiga toilet din kana ya fara wanka.

Hajiya Karima dake zaune afalon kasancewar itace da girki tayi saurin kallon wayar Abba dake ruri miƙewa tayi tare da isa kan 3sitter ganin number babu suna yasa tayi saurin picking tare da kaiwa kunnenta tace.

“Assalamu Alaikum”.

Ba tare da mutumin ya amsa Sallamar taba yace.

“Ina Mahaifin Jameelu?”.

Da sauri ta gyara zaman wayar akunnenta tare da cewa.

“Me kuke so ku faɗa min nice mahaifiyarsa”.

Cike da gadara Mutumin  yayi gyaran murya kana yace.

“Dashi muke son magana, muna son muji shin kuɗin mu sun haɗu ne?.

Zamu faɗa masa inda za’a ajiye kuɗin sannan kuma da inda za’a zo akarɓi Jameel”.

Hajiya Karima kuwa cikin ƙasa da murya tace.

“Haba bayin Allah kuji tsoron Allah mana.

Yanzu fisabilillah ina zamu samu Million ɗari da hamsin wannan aiba rayuwa bane duk da cewa Mahaifinsa mai kuɗi ne ina zai samu wannan uban kuɗin acikin ƙaramin lokaci kawai dai ku temaka ku rage idan ku akayi wa haka ya zakuji? Gwara dai ana rage mugunta”.

Dai-dai lokacin da Abba ya fito daga wankan batare daya gama ba jin alamar muryan Hajiya Karima na magana ƙasa².

Yana fitowa ya Fisge wayar ahannunta tare da mannawa akunnensa dai-dai lokacin da mutumin ke magana cikin tsanananin fushi da gadara yace.

“Ok haka ma kuka ce. Wato wasa da mu ku keyi kun maida mu bamusan abinda muke ba, toh Insha Allah daga yau har gaban Abadan baza mu sake kiran kuba. Alhj Bashir ya maka kyau duk irin halarcin da gargaɗin da muka maka baka jiba har kuna sake neman ragi”.

 

Cikin tsanananin kaɗuwa, ruɗu, da tashin hankali. Abba ya girgiza kai kana cikin raunin murya yace.

“Dan Allah da m…”.

Kafin ya ƙarasa yaji ɗit-ɗit-ɗit alamar sun kashe kiran.

Cikin wani irin yanayi ya zauna tare da sake kiran layin yaji akashe Aruɗe ya shiga fito da sauran numbers din su yana kira amma baki ɗaya Switch off.

Kansa ya dafe da hannunsa na dama yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da wayar.

Cikin wani irin fushi ya miƙe tare da kallon Hajiya Karima dake tsaye azabure ya ɗaga hannunsa tare da kife ta da mari kana ya sake watsa mata wani gigitaccen marin da saida taga gilmawar taurari cikin wani irin fushi ya cigaba da yarfa mata maruka gefen hagunta da damanta.

Muryarsa na rawa yace.

“Karima na saki acikin wannan maganar tunda aka fara. Meyesa zaki ɗauka min waya. Karima kin cuceni. Wallahi Karima duk wani abinda ya faru da Jameelu kece sanadi kece kika ja ke kika cutar min da rayuwar ɗana”.

Da sauri ya dafe ƙirjinsa dake wani irin zafi kana ya ɗago ya kalleta da idanunsa da suka sauya launi zuwa tsantsar tashin hankali kana yace.

“Karima haka nayi dake kina gani ɗazu akan idonki na dawo daga Taraba naje na karamo kuɗi na sake karɓan bashin banki 50 millons yanzu ruwan kuɗi ahannuna Million Ɗari da arba’in da biyar ne Million biyar  ne kaɗai ya rage kuma nasan da izinin Ubangiji ba zasu gagara ba zan nemosu amman shine zaki nema min ragi”.

Hajiya Karima kuwa kuncinta ta dafe tare da sun kuyar da kanta ƙasa tana mai cike da taraddadi.

 

Cikin rauni da fusata Abba ya cigaba da cewa.

“Saboda bake kika haifi min Jameelu ba shine zaki salwantar da rayuwarsa, yanzu da ɗan da kika haifa a cikin kine zaki masa irin wannan abin? Karima kin cutar da rayuwata cuta mafi muni, muddin wani mummunan abu ya faru da Jameelu na bazan taɓa yafe miki ba”.

Cikin zubda hawaye Hajiya Karima tace.

“Haba Alhj wallahi ni ba haka nake nufi ba, kafahimceni tunda naga wancan karon ma da aka nemi ragin ai sun rage shiyasa nace barin ne mamaka sauƙi”.

Dai-dai lokacin Moddibo ya shigo falon idanunsa suka sauƙa akan Abba da jikinsa ke rawa idanunsa sunyi Jawur tamkar zai tsats-tsafo da hawayen jini yayin da numfashinsa ke seizing.

 

Cikin sauri Moddibo ya ƙara sa tare da riƙe Abba kana ya zaunar dashi akan kujera cikin sanyin murya yace.

“Abba mai ya faru?”.

Kasa cewa komai Abba yayi baki ɗaya baya cikin hayyacinsa numfashinsa sai kai koma yake cikin rauni da ficewar hayyaci yace.

“Karima kin cuceni Meyesa zaki min haka. Meyesa zaki ƙuntata min ta wannan hanyar!?”.

Cikin sauri Hajiya Turai ta shigo ganin halin da Abba ke ciki yasa kai tsaye ta wuce Bedroom ɗinsa tare da ɗauko masa magani kana ta kira Dr Muktar ya ɗagawa tace.

“Dan Allah Dr maza kazo jikin Alhj ya tashi gaba ɗaya ma numfashinsa sama yake yi”.

Da Ok Dr ya Amsa kana ta katse kiran tare da fitowa da magani ta ɓare tare da miƙa masa.

Cikin azabebben rawan da jikinsa keyi ya ture hannunta tare da cewa.

“Ba zan shaba Karima kin cuceni kin cutar da rayuwata, kin datse min farin cikina. Meyesa haka Karima duk abinda ya samu Jameelu Karima kece sanadi idan wani abu ya samu Jameelu Karima kece sanadi!”.

 

Ganin alamar baya cikin nutsuwarsa yasa Moddibo cewa.

“Dan Allah Abba ka kwantar da hankalin ka”.

Girgiza kai Abba keyi yana cewa.

“Karima kin cuceni kin cutar da rayuwata kin katse min farin cikina”.

Zama Moddibo yayi kana cikin sanyin murya ya shiga Furta.

_“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakil Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha La’ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin la haula Wala ƙuwwata Illah billahil aliyul Azhim”_.

Ahankali Abbah yafara bin bakinsa yana karato adduo’in tun yani yi Aransa har yafara afili.

 

Hajiya Turai kuwa number Dr Muktar ta sake Kira yana ɗagawa tace.

“Dr kayi sauri dan Allah ina katsaya har yanzu baka zoba kuma na faɗa maka jikin Alhj ya tashi gashi mun basa magani yaƙi sha”.

Cikin sauri Dr Muktar yace.

“Gani nan na fito dama yanzu zan wuce asibiti amma yanzu na kusa gidanku ma ina ƙara so wa”.

Cike da damuwa tace.

“Toh shikenan sai kazo dan Allah kayi sauri”.

Ta ida maganar tare da katse kiran kana ta juya ta fice.

Moddibo kuwa ciki sanyi ya riƙe hannun Abba tare da cewa.

“Abba dan Allah kayi haƙuri ka cigaba da Addu’a”.

Kai Abba ya gyaɗa kana ya cigaba da maimaita adduo’in but still ɓarin da jikinsa keyi bai dai naba saima ƙaruwa da yake.

Dai-dai lokacin da Dr Muktar yayi hong mai gadi ya buɗe masa kana cikin sauri ya fito daga motar hannunsa riƙe da fest aid box Hajiya Turai dake Safa da marwa a coumpund ɗin ta masa jagora zuwa ɗakin suna shiga Dr Muktar ya zauna kan 1sitter kana ya buɗe Aidbox ɗin sa tare da gwada Bp Abba.

Cikin sauri ya kalli Abba tare da cewa.

“Subhanallah jinin Alhj ya hau sosai na faɗa muku ku daina kawo duk wani abu da kuka san zai ɓata masa rai, ko kuma tayar masa da hankali”.

Ya faɗa tare da ciro sirinji kana yace.

“Alhj bari nayi maka allura baki ɗaya damuwa yayi masa yawa”.

Ajiye sirinji Dr Muktar yayi kana ya balli magunguna ya miƙa masa tare da cewa.

“Alhj gashi kasha”.

Girgiza kai Abba yayi cike da rauni yace.

“A’a bazan shaba”.

Asanyaye Dr Muktar yace.

“Ayyah Alhj dan Allah kasha mana”.

Girgiza kai Abba yayi tare da cewa.

“A’a bazan shaba menene amfanin rayuwata matuƙar dai bazan iya temakon Jameelu na ba.

Meye riban cigaba da rayuwata matukar Jameelu na baya tare dani?”.

 

Cikin sauri Moddibo ya Girgiza kai tare da cewa.

“Subhanallah Abba kada kace haka kada zafin damuwa yasa mu kaucewa lissafin hankali da na Musulunci Abba kayi addu’a dan Allah ka karɓi maganin kasha Abba. shin yakakeso nayi idan har kaima ka faɗi   ciwo ya kwantar da kai”.

Cikin tausayawa ya kalli Abba idanunsa cike da ruwan hawaye kana yace.

“Abba na tabbatar ko da J na nan bazai yi farin ciki da haka ba Abba dan Allah kayi haƙuri kasha maganinka, ganinka cikin dauriya shike bani ƙarfin gwiwa Abba bazan so ganin wani mugun abu yasa Meka ba. Idan har wani abu ya sameka  Abba ya zanyi da rayuwata!?”.

Ya ida Maganar tare da miƙawa Abba maganin karɓa Abba yayi tare da kaiwa bakinsa ya haɗiye miƙewa Dr Muktar yayi kana yace.

“Alhj bari a maka Allura”.

Kai Abba ya gyaɗa kana Dr Muktar ya masa bayan ya masa ya juya ya fice.

Sannu Ahankali Abba ya fara maida numfashi kana ya jingina bayansa da jikin kujera ahankali numfashinsa ya fara dai-dai-ta Atake zufa ya shiga tsats-tsafo masa agabaki ɗaya ilahirin jikinsa.

Moddibo kuwa ganin haka yasa ya miƙe ahankali tare da ɗaukan remote ɗin AC ya kunna kana ya dawo ya zauna agefensa.

 

Matsawa kusa da Abba Hajiya Turai tayi kana ta ɗauki hankief ta shiga goge masa zufa,

cikin sanyin murya tace.

“Sannu Alhj Ubangiji ya sawwaƙa maka, ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu Jameelu sai al’khairi”.

Kallonta yayi amma baice komai ba.

Moddibo ma ahankali ya dawo kusa dashi ya zauna kana cikin sanyin murya yace.

“Abba ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu J Abba yanzu fa abinda ya kawoni da mukayi waya kace ansamu kudin kwata kwata Abba yanzu fa Million biyar ne ya rage akan kuɗin da muke nema ai abu yazo ƙarshe insha Allah babu abinda zai samu J,

Kuma ma kafin inzo nayi waya da Ummi tace akwai wasu gwala-gwalai guda biyu gobe zata kaisu Taraba, da akan yau zata kaisuma to dare yayi, ta kuma cemin in sha Allah zasu iya kai two million.

Kajifa alamomin nasara Abba meye zai tayar maka da hankali!?”.

 

Ahankali Abba ya ɗago jajayen Idanunsa tare da kallon Moddibo kana ya kalli Hajiya Turai sai kuma ya maida kallonsa kan Hajiya Karima dake tsaye cikin rauni ya nuna ta da yatsa kana yace.

“Karima ce nashiga wanka suka kira.

Karima ta ɗauka wai tana musu maganan ragin kuɗin nace ta nema min ragi ne?

Tabarni mana Jameelu ba ɗana bane ai zan fashi ɗana amma Meyesa Karima zata min haka!?”.

Moddibo kuwa cikin wani azabebben tsinkewar zuciya ya riƙe kansa tare da cewa.

“Innalilahi wa’inna ilahi rajiu’n.

kika nemi ragin kuɗi kuma Aunty Karima amma gaskiya baki kyauta mana ba”.

Cikin tsananin tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar yaci gaba da cewa.

“Amma gaskiya baki kyauta manaba, ai wannan mugunta ne an saki ne ko kuma annemi wani temako awajenki  fisabilillahi? wallahi kin cutar damu wannan shine cuta mafi muni da kika mana bayan kinji gargaɗin da sukayi”.

Ya ƙarashe mgnar cikin raunin murya yana jin zuciyarsa na wani irin zafi da karaya.

 

Cikin sauri Hajiya Turai ta kalli Hajiya Karima tare da Girgiza kai cike da takaicin halayyar ta tace.

“Idan har ba tayi haka ba ai bata cika Yadukko ba, ai dama baka sanin mai sonka da gaskiya sai kashiga wani hali, wasu kuma burinsu su samu hanyar da zasu musguna wa rayuwarka suke nema”.

Kallon Hajiya Turai Hajiya Karima tayi kana ta kalli Abba da Moddibo cikin Muryan kuka tace.

“Agaskiya ni anyi min bahaguwar fahimta nima Ina son Jameelu tamkar ɗa yake awajena fa, ke Hajiya Turai da kike wannan maganar nida ke waya fara zama da Jameelu ne?”.

Banza Hajiya Turai tayi da ita tana jin wani irin takaicin abinda ta aikata aranta.

Sannu Ahankali bacci ya fara fisgar Abba saboda magani da Alluran da aka masa nan take Bacci ya ɗauke sa kwanciya Moddibo ya gyara masa akan kujeran kana ya miƙe tare da ɗaukar key ɗin motarsa zuciyarsa cike da rauni damuwa da tashin hankali duk sun bayyana afuskarsa.

Yana fita yashiga motarsa tare da yimasa key yayin da hawaye suka cika kwarmin Idanunsa Driving yake yana sake try numbers din da suke kira kasancewar duk lokacin da suka kira saiya yi copy amma baki ɗaya Swich off.

Ahankali ya fito da Number M Jameel kana Yayi dearling cikin ikon Allah yaji wayar tashiga tana ringing lokaci ɗaya ya shiga cikin matsanancin farin ciki afili ya furta.

“Yau kuma wayar J tana shiga”.

Cikin sauri ya juya akalar motarsa zuwa gidan Ummi kana ya Parking awaje tare da buɗe gate ya shiga coumpund ɗin yana cewa.

“Ummi! Ummi!! Ummi!!!”.

Ummi dake tsaye Atsakiyar falo tayi saurin fitowa tare da cewa.

“Na’am Babana me yafaru?”.

Cike da walwala yace.

“Ummi wayar J ɗina yana shiga yau”.

Cike da farin ciki Ummi ta ware ido kana tace.

“Wayar Jameelu yana shiga?”.

Kai Moddibo ya gyaɗa still da murmushi afuskarsa ya gyaɗa mata kai kana yace.

“Wallahi yana shiga Ummi bari ma kiji”.

Ya faɗa tare da dearling number M Jameel aikuwa ya shiga ya fara ɗut-ɗut-dut cikin Sauri ya samata akunne da sauri Asma’u da Bashir dake Bedroom suka fito jiyo sautin su Ummi cikin farin ciki.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

“Bari in Kira nima”.

Ta ida maganar tare da dearling number kasancewar wayar na hannunta still ya shiga yana ringing.

 

Cikin sanyi ta juya ta kalli Moddibo tare da cewa.

“Babana to ya baya ɗauka kuma?”.

Cikin wani masifaffen tsinkewar zuciya da tsoro Moddibo ya kalleta cikin ƙoƙarin ɓoye tsoronsa yayi Murmushi tare da cewa.

“A’a Ummi Insha Allah tunda har wayarsa tana shiga zai ɗaga mu cigaba da kira da izinin Ubangiji zai ɗaga Agaskiya Ummi yau naji sanyi”.

Murmushi Ummi haram Asma’u, da  Bashir.

 

“Har naji hankali na ya dan kwanta wayar J ɗina ya shiga, kinga farko kafin mu rasa shi kiran wayarsa muka fara rasawa Ummi, yanzu kuma Insha Allah mun samu kiran wayarsa shi zamu ƙara samu next da izinin Ubangiji”.

Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.

“Ameen”.

Cikin jin sanyi Asma’u tayi murmushi kana tace.

“Alhamdulillah wayar Yah Jameel ya shiga gaskiya munyi farin ciki”.

Malam Ahmad daya fito daga wanka ya fito coumpund ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.

“Alhamdulillah Asma’u maza kawo musu abinci suci tunda mun samu wayar Jameelu ya shiga maza kawo musu abinci”.

Moddibo kuwa kallon Malam Ahmad yayi kana yace.

“Nikam ma Malam baki ɗaya cikina ya cushe baki ɗaya farin ciki ya cika min cikana”.

Murmushi Ummi tayi kana tace.

“Nima cikina ya cika baki ɗaya farin ciki nake ji”.

Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.

“Dan Allah ku zauna kuci abinci wayarsa muka fara rasawa yanzu kuma wayarsa muka faru samu insha Allah shi ma zamu sameshi nan kusa ”.

Dai-dai lokacin Asma’u tazo ta ajiye musu abincin.

Tun ɓatan M Jameel sai yau Ummi da Moddibo sukaci abinci mai nauyi acikinsu duk da ba dayawa suka ciba.

Miƙewa Moddibo yayi kana yace.

“Ummi bari naje in faɗawa Innayi ta tayamu farin ciki”.

Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.

“Aikam dai gwara kaje”.

Ficewa yayi tare da tafiya Driving yake Cike da farin ciki har ya isa gida yana zuwa ya shiga sashen Innayi.

Innayi dake ki shimfiɗe ta miƙe kana tace.

“Alhamdulillah Moddibo naga kana cikin farin ciki da alama akwai labari mai daɗi?”.

Kai ya gyaɗa still Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

“Innayi wayar J ɗina ya shiga yau”.

Kai Innayi ta gyaɗa tare da cewa.

“Alhamdulillah gaskiya munyi farin ciki. Allah ya bayyanar mana dashi”.

Ameen ya amsa tare da wucewa sashen sa cike da farin ciki yana shiga ɗaki ya kira layin Malam Arɗo.

Malam Arɗo na dagawa yace.

“Malam Alhamdulillah yau wayar J ɗina yashiga a cigaba da taya mu da addu’a a masallacai da makarantu”.

Cike da farin ciki malam Arɗo yace.

“Masha Allah da izinin Ubangiji zai fito Insha Allah zamu cigaba da addu’a”.

 

Awannan daren haka Moddibo Ummi, Asma’u Bashir malam Ahmad da Innayi suka kwana cike da farin cikin shigar wayar M Jameel.

 

Yayin da Aɓangaren Abba ya kwana cikin taraddadi da tashin hankali koda ya farka tsakiyar dare kuka yayi ta yi yayin da Hajiya Karima ke kuka tana basa haƙuri kana tana cewa bada niyya tayi ba.

 

Aɓangaren gidan Lamiɗo ma haka Khausar da Mommy suka kwana azaune da Ramadan da kansa ke masifar ciwo da zaran an bashi maganin da Lamiɗo ya kawo yasha ciwon zai ɗan lafa jimawa kaɗan kuma zai sake tashi tsakiyar dare ya farka ya riƙa kuka dole Ummi ta kira Abba ya kawo masa magani cikin ikon Allah yana sha ciwon kan ya lafa.

 

Washe gari; Moddibo, Malam Arɗo, Ummi Innayi duk wani makusancin M Jameel na cikin farin ciki kana duk wanda ya kira wayarsa zai shiga sai dai ba aɗagawa Wunin wannan ranan haka Moddibo yayi yana kiran layin M Jameel still ba amsa.

Zuwa yamma jikin Moddibo ya fara sanyi da lamarin ganin yana kiran wayar M Jameel baya shiga lokaci ɗaya tsoro ya fara kamashi hankalinsa ya tashi Misalin ƙarfe goma na dare yana gidan Abba zaune sun kira Jameel kuma sama da sau ashirin kuma duk  kiran yana shiga, sau dai ba’a ɗagawa, su kuma masatan basu kiraba.

Yayin da idanun Abba ke kumbure alamar har yanzu jinjinsa bai sauƙa sosai ba.

Cikin mutuwar jiki Moddibo ya koma gida kai tsaye sashen Innayi ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga.

Innayi dake zaune riƙe da carbi ta amsa masa cikin raunin Murya yace.

“Innayi”.

Kallonsa tayi cike da kulawa kana tace.

“Na’am”.

 

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana cikin sanyin murya yace.

“ Innayi hankalina ya soma tashi wayar J yana shiga ba’a ɗauka sannan mutanen nan basu sake kira ba”.

Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da cewa.

“Ba komai Moddibo Insha Allah ka kwantar da hankalin ka”.

Girgiza kai yayi kana yace.

“Anya kuwa Innayi?”.

Cikin bashi ƙwarin gwiwa tace.

“Ba komai Insha Allah ka cigaba dayi masa addu’a da izinin Ubangiji zai fito yanzu idan sun sake kira kuce musu an samu kuɗin Insha Allah Million biyar  bazai gagara ba koda a masallatai anemi temako za’a samu  su  haɗu”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Toh Innayi Allah yasa su kira ɗin dan yanzu kam ma cikon Million ukune”.

Cikin jin daɗi Innayi tace.

“Alhamdulillah Allah ya bamu sa’a”.

Amin yace

Sanna ya miƙe ya koma sashen sa cike da damuwa. Washe gari jin sauran kuɗin da ake buƙata, Lamido ya bawa Mommy da kanta ta kaiwa Ummi su sau dai sam basu kuma kiraba.

 

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya yau kusan kwana ki shida kenan duk lokacin da aka kira wayar M Jameel zai shiga sai dai ba’a ɗauka.

 

Yayinda Ramadan kuwa ke kwana da azabebben ciwon kai idan aka bashi magani yasha ciwo ya lafa anjina kaɗan kuma ya sake dawowa.

Ga ɗaya Mommy da kwausar sun shiga damuwa, sun kai asibiti har cikin Taraba anyi hoton kan da duk wani gwaje-gwaje amman babu wani ciwo dake kansa, dan da farima likitocin sunyi zaton brain cancer ne.

baki ɗaya yaron ya fita hayyacinsa saboda tsananin ciwon kai.

Yau kimanin kwana shida  kenan da aka fara samun wayar M Jameel na shiga.

Washe garin rana ta bakwai.

Da safe bayan an idar da Sallar Asbah Moddibo na fita a masallaci ya kira wayar M Jameel.

Cike da mmki tsoro ya janye wayar a kunnenshi sabida jin ance masa Switch off.

cikin mutuwar jiki ya nufi gidan Ummi yana shiga ya samu Ummi zaune akan Sallaya hannunta riƙe da Carbi.

Cike da ladabi ya gaisheta kana cikin sanyin murya yace.

“Ummi”.

Kallonsa tayi tare da cewa.

“Na’am Babana”.

Cikin raunin murya yace.

“Ummi na kira wayar J ɗina baya shiga”.

Ahankali Ummi ta jingina kanta da jikin kujeran falon kana tace.

“Nima na kira wayan Jameelu na baya shiga bansan Meyesa ba Allah yasa al’khairi ne”.

Cike da sanyi Middibo yace.

“Amin ya Allah in sha Allah ba komai Ummi”.

Cikin raunin murya Ummi ta lumshe Idanunta tare da cewa.

“Hmmm,Hmmm Ubangiji Allah yabamu ikon cinye jarrabawar da zai jarabce mu”.

Cikin sanyi Moddibo yace.

“Ameen”.

Miƙewa Moddibo yayi kana yace.

“Ummi bari naje gidan Abba naji koshi ya kira ya shiga”.

Kai Ummi ta gyaɗa Muryanta cike da rauni tace.

“Toh”.

Cikin sanyin jiki zuciya cike da karaya Moddibo ya nufi gidan Abba yana shiga coumpund ya ga Abba na ƙoƙarin shiga falo dawowansa daga masallaci kenan.

Ƙara sawa Moddibo yayi tare da miƙa masa hannu sukayi musabaha kana cikin sanyin murya Moddibo yace.

“Abba wayar J ɗina baya shiga”.

Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa hawaye masu zafi suka shiga bin kuncinsa Shar-shar-shar kamar ƙaramin yaro baki ɗaya ya rame cikin raunin murya yace.

“Aliyu dama wayar Jameelu da kira yake shiga. Wani sanyi ne dama hankalina ya tashi tun jiya nake kiran wayar baya shiga, dama ni banyi farin ciki da shigan wayar Jameelu ba. Aliyu inaji Ajikina kamar akwai wani abu da bamu san menene ba jikina na bani ko ina Jameelu na yaje baya cikin walwala na rasa tudun dafawa”.

Cikin sauri Moddibo ya runtse Idanunsa zuciyarsa na bugawa da masifaffen ƙarfi kana cikin raunin murya yace.

“Abba insha Allah J yana cikin ƙoshin lafiya mu cigaba da masa addu’a amma nima baki ɗaya hankalina yayi masifar tashi”.

Cikin rauni da tsanananin tashin hankali suka ci-gaba da tattaunawa.

 

Acan gidan Lamiɗo kuwa  Mommy, Khausar da Lamiɗo basu rintsaba a wannan daren.

A kan Ramadan suka kwana yanata kuka baiyi bacci ba.

Washe gari Bayan an idar da sallan Asbah Hajiya Bunayya ta shigo falon Mommy ahankali Ramadan dake kuka ya miƙa mata hannu kana cikin wata raunan’niyar murya mai cike da wahala yace.

“Ummah! Ummah! Kaina zai fashe kaina zai faɗi Wayyo Allah na Kaina! kaina”.

Baki daya jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu dasu yayinda idanunsa sukayi ja.

Cike da tausayawa Khausar ta ɗaura tafin hannunta na dama akan goshinsa Idanunta cike da ruwan hawaye kasa riƙe hawayen ta tayi jin yanda kan ke harbawa da masifar ƙarfi.

Kuka sosai Ramadan keyi kana cikin tsananin radaɗin ciwo ya riƙo hannun Mommy kana yace.

“Wayyo Mommy Kaina zai fashe. Mommy Kaina Wayyo zan mutu Mommy Zan mutufa”.

Wani irin miƙa Ramadan yayi tare da cewa.

“Momyyyyy zan mutuuuu”.

Cikin sauri Lamiɗo da yanzu ya shigo ya karɓesa ganin yanda idanun yaron suka juya da sauri ya fara ɗan bubbuga kumatunsa yana cewa.

“Ramadan! Ramadan!”.

Wani irin juyawa Idanun yaron yayi tare da wulƙitawa kana yaja dogon numfashi….!

 

 

 

*Zuwa yanzu dai mun gama ratsa tsakiyar labari babi-babi na zaren na dab da fara warware wa.*

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button