Dabarun Rubutun Waka

DABARUN RUBUTUN WAKA  KASHI NA GOMA MABUDI DA MARUFI.

Sponsored Links

        

           DABARUN RUBUTUN          WAKA  

                   KASHI NA SHA DAYA 

                   MABUDI DA MARUFI


Barka da zuwa wanan shafin namu mai albaraka .

     Gabatarwa 

         Daga 


Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.


  by

 msz


       (3)  MABUDI DA MARUFI                 (Introduction and Conclusion).     

    Ana so, mawaki ya tabbatar da wakarsa, tana da mabudi da kuma marufi. A nan ana nufin wakar ta fara da yabon Ubangiji da kuma salatin Annabinsa (SAW), a lokaci guda kuma a rufe ta da su. Misali, a wakar Mu’azu Aliyu Hadejiya ta GASKIYA BA TA SAKE GASHI:            


MABUDI:

Ya Allah Sarki mai rahama,

             A gare Ka muke son albarka.

Domin tsarkin Dakin Ka’aba,


Albarkar Annabi manzonKa.


MARUFI:            

Ya Allah taimaki bayinka,        

 Duk wanda yake son manzonka.


 Mu’azu Hadejiya nan ya tsaya,

M.S.Z. mai neman albarka.


         (4)  MA’AUNI (Metre).


 Ana so, mawaki ya sama wa wakarsa ma’auni. A nan ana nufin ma’aunin da zai kasance ya auna wakarsa, wanda ta hanyar amfani da ma’auni ne, za a iya yayyanka waka, kana baitotinta su kasance kai-da-kai, ba kai da gindi ba.


  Idan muka koma ga tarihi za mu ga cewa, wakoki a kasar Hausa sun samu kafuwa ne daga wakokin larabci, kasancewar ba a san wakoki a kasar Hausa ba, sai bayan zuwan musulunci da ilmin larabci kasar Hausa. 


 Waka ta samu tagomashi sosai lokacin Shehu Usman Danfodiyo, shi ya sa tun daga lokacin har zuwa yanzu, za ka samu ma’aunan wakokin kasar Hausa suna da nasaba da ma’aunan wakokin larabawa. 


Ma’aunan wakokin larabawa goma sha uku (13) ne, wanda ga su kamar haka:

 

(1) Dawil 

(2) Madid 

(3) Basid 

(4) Wafir 

(5) Kamil 

(6) Hajaz 

(7) Razaz 

(8) Ramal 

(9) Munsarih 

(10) Hafif 

(11) Mukutalib

(12) Mutakarab

 (13) Mutadark


(5)  AMSA-AMO (Rhythm).


Ana so, mawaki ya yi wakarsa da amsa-amo, wanda a larabce ake yi wa lakabi da kafiya.


 Ma’ana ana so waka ta kasance tana da harafi iri daya, wanda da shi ne baitukan waka za suna karewa. Amsa-amo ko kafiya ta kasu kashi biyu ne: karama da kuma babba. 


Karamar kafiya, ita ce ake samu a tsakiyar baitin waka, yayin da babbar kafiya take zuwa a karshen baitin waka. Karamar kafiya tana iya sauyawa a kowane baiti, amma babbar kafiya ba ta sauyawa, da ita ake tafiya har karshen waka. Misali, a wakar IMFIRAJI, littafi na daya, Juzi’i na daya, na Aliyu Namangi:


                   Gaisuwa ko ta dace,

            Gun Ma’aikin nan da an ce,

            Ran Musulmi kar shi sance,



            Bisa sonsa mu ko amince  

           Mai sonsa ba zai bakin ciki (ba).


Idan aka lura za a ga na ja layi ga wasu haruffa; harrufan da na ja wa layin su ne karamar kafiya, idan za a lura harrufan sun kare da ce ne. Babbar kafiya kuma za a gan ta a cikin baka-biyu.

Reading more……Yadda-ake-rubutun-wakokin-hausa.

Reading more……In-ba-A -kano-ba-to-sai-ina.

Reading more……layya-da-abin-da-ta-kunsa-takaice.

Anan zamu diga aya sai kashi nagaba sai mu dora inda Aka tsaya.


                    Domin Karin

 Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 


Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode

Leave a Reply

Back to top button