Hausa NovelsInda Rai Hausa Novel

Inda rai 24-25

Sponsored Links

*INDA RAI…*

*MARYAM ABDULALLAHI*

( Oum Shaheed )

*Daga ƙungiyar, ko da kuɗinki*……..

*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION*✊✊
*Page 24 – 25*

Nasha wahala sosai wajan neman kuɗin da zan kula da ƙanwata da ƴar jaririyarta, ta ɓangare guda kuma ga Bukar da mahaifiyarsa, idan aka samu akasi ko ya yake tofa haka zasu bar ta da yunwa babu tausaya wa, ga tsangwama da gori kullum, haka na samu na ƙoƙarta na kama musu gidan haya, ina yawan zuwa duba su duk sanda na samu dama, haka lokaci yayi ta tafiya, kwatsam na samu labarin dawowar abokin Babana, cikin farinciki na je garesa da murnata, anan yake shaidamin ya ji komi daya faru agun mijin Iyatu, muka jajantawa juna sosai, yace min na koma na taho da Haulatu da mijinta zai bashi kuɗi ya yi jari ya samu na kansa, cikin farinciki na shirya koma wa, ashe Alhajin yara ya samu labarin zuwana, a wannan daran yasa a kasheni, sai dai ban mutu ba amma na samu matsala a kaina sakamakon bugun da sukamin a tsakiyar kaina, to bayan gari ya waye jama’a suka kaini asibiti ganin jijiyoyin wuyana na har bawa, a sanadinyar wannan dukan jini ya shiga ciki kwakwalwata, abokin Baba ya kashe kuɗi sosai a jinyata amma ban dawo normal ba, ina iya aikata komi amma na manta duk wani abu da ya shafi rayuwata ta baya, cikj har da ƙanwata ɗaya tilo a duniya, gashi babu wanda yasan inda take saini, a wannan halin abokin Baba ya ɗorani a harkar wake, sosai Allah yasa min albarka a ciki har nayi aure, inda na auri ƴar gidan abokin Baba Balkisu, wannan shine taƙaitaccen labarina, a halin yanzu Allah ya yi wa Haulatu da ƴarta da ta haifa Maryama rasuwa..

Maryama ce kwance a gadon asibiti hannunta na dama saƙale da dirip ana mata ƙarin ruwa, lokaci ɗaya ta fige ta fice hayyacinta ta zama ƴar tsurut kamar wanda ta shekara tana jinya, Samha ce zaune a gefenta ta rafka uban tagumi abu goma da ashirin ya haɗe mata.

Doctor a zubar da cikinnan domin bana buƙata, cewar Daddy dake zaune a ɗaya daga cikin kujerun office ɗin doctor, da sauri doctor ya haɗiyar fara’ar da ke kan fuskarsa, “ban gane ba Alhaji,? akamme zan zubar mata da ciki,? bayan ba shege bane da ubansa na sunnah,, “nawa zan biyaka”?Daddy ya sake faɗa kai tsaye fuska babu walwala, da kallo mai cike da mamaki doctor yake bin Daddy, “kana ɓata mini lokaci fa, “bazan iya aikata hakan ba gaskiya Alhaji, “okay, zan nemi wani, ai shegun da yawa, za’amin abun da nake so akan naira miliyan biyar kacal, “zanyi nima Alhaji, zan zubar, amma ka fara bani kafin alƙalami, wani murmushin gefen baki Daddy ya yi yace shegiya naira, “bani accont number, jiki na ɓari ya bashi a take yaji ƙarar shigoqar naira miliyon biyu da rabi, “kabani zuwa gobe cikin zai bi rariya sai ka cikamin ragowar kuɗina…

Malam Bukar ne zaune a ƙofar gidansa gaba ɗaga abun duniya ya masa yawa, gashi tun yana sa ran ganin ta’inda Aminu zai bullo shiru, sake buga wata mahaukaciyar hamma mai nuna tsantasar yanda yake jin yunwa, ya zama dole ya nemi mafita, tashi yayi ya nufi gidan maigari, acan ya ji labarin ai sun wuce aikin hajji gaba ɗaya gidan, kuma ba lalle su dawo nan kusa ba, haka ya koma gida yana ta tsinewa Aminu zuciyarsa sam babu daɗi, yasan saboda ƙanwarsa tarasu ne da yanzu ya dawo, inama yace mishi ƴarta na raye, da ya yi amfani da wannan damar wajen samun kuɗi a sauƙaƙe, mtsss ya sake buga dogon tsaki ya shige ɗan akurkin ɗakinsa..

Sosai sukayi kuka bayan gama jin wannan labari mai abun tausayi da sukayi, Amrish dake tanada matsalar ɓacin rai ta sanja kamanni, fuska ta yi jajir da’ita, kafun kace me tuni jikinta ya fara rawa idanunta sun rikiɗe sun koma kalar blue, da sauri Abee ya kamata ganin ta sandare a zaune, addu’a yahau tofa mata a fuska da duk jikinta, daga bisani Mimi da Mama suka ɗauketa zuwa ɗaki suka kwanta, acan parlou kowa su Abee suna tattauna yanda za’a samawa Amrish maganin wannan matsalar nata, babu dama ranta ya ɓaci ko taji wani abu na tashin hankali shikenan sai ciwo ya tashi, shiyasa ma bata yi karatu a nigeria ba.

Amma Aminu ya labarin Imran, ya ko kayi da shi Alhajin yara,? yaushe kuka yanke auran zai kama, ga kamata ayi a wuce gun domin mu fuskanci gaba.

Kai a ƙasa Aminu yace wa sirikinnasa, “lokaci ya yi da ya kamata mu sanar da Salman cewar akwai yaro mai kama dashi, ko hakan zai taimaka masa wajan tuna wani abu daga garesa, “kana nufin ka shirya tunkarar Alhajin yara yanzu,? ina jin hakan a jikina Baba, “okay, Allah ya taimaka, sai ka shirya zuwa ƳAR SIYA kenan. In sha Allah Baba, amma sai bayan an ɗaura auran, saboda tanan ne zan iya samun damar ɗaukar Imran ɗin muje tare.

 

“Alhaji ya kamata kasan miye girman alƙawari, sannan ka sani, rana irinta yau za’a ɗaura wannan babu fashi, “miye hujjarka na cewa aurennan babu fashi,? “kasani baka da hujja a hannu. Kana wasa dani kenen,? to kasani nasan komi a kanka da duk wasu miyagun ayyukanka, fasa wannan auren dai dai yake da na tona maka asiri matsayinka na makashin ƴan mata. Saura kaɗan Alhaji Auwal ya faɗo ƙasa daga kan kujera, “a’ina ka sanni? murmushi Amini ya yi mai ciwo kafun ya miƙe ya gyara zaman hularsa yace, “la sanar da yan uwanka ranar satuday kamar yanzu zaka ɗaurawa ɗanka Imran aure da ƴar wajena, fatan alheri, yasa kai ya bar shi zaune kamar an dasashi, lalle yaronnan yana wasa da wuta, amma zai nuna masa ai nayin kalarsa

 

A har gitse ya nufi part ɗin Imran kamar zararre, ko sallama babu barai neman izini yasa kai ciki ɗakin, ya shiga domin basa umarnin barin ƙasar baki ɗaya, sai dai tuni ya manta ƙudirinsa ganin Imran riƙe da pic ɗin matar ɗan uwansa Sudais, mai hakan ke nufi,? wato dama sadaukarwa Sudais ya yi bayan ya gane miye matsalar ɗan uwansa, tab lalle akwai yaƙi, dan bazai iya bar masa ba domin ta riga tashiga ransa sosai ya kwaɗaita da’ita, maimakon ya yi abun da ya kawo sa kawai sa kai ya yi ficewarsa, har ga shigo ya fi ta Imran bai sani ba, tuni ya yi nisa a duniyar tunani, gaba ɗaya ya zama shiru shiru, baya magana da kowa tun bayar tafiyar ɗan uwansa da jn cewar ya saki matarsa ya sake zama mai sanyi, ya tara ƙa sunba har ta masa muni, hakanan ya ji yana tausaya musu duka su ukun, daga shi har Sudais da matarsa, ya zama dole shima yabar ƙasar bari na dogon lokaci…

 

*Shin waye Salman?*
*Ina labarin bawan Allah Sudais?*
*Shin cikon Maryam zai zube ko kowa?*

*Waye mai rabon auran Maryama?*

*Imran*
*Alhajin yara*
*Sudais*

Leave a Reply

Back to top button