KO KASAN YANDA AKE ISTIKHARA A MUSULMIN CI]
[ KO KASAN YANDA AKE ISTIKHARA A MUSULMIN CI ]
ISTIKHARA
GABATARWA
DAGA
WANI BAWAN ALLAH
Mecece Istikhara?
Istikhara a takaice shine :- baiwa Allah zaɓi akan al amuran ka.
Neman Alkhairin Ubangiji.. . Yana daya daga cikin abinda ke Sanya albarka a rayuwa istihara (Istikhara), Neman zabin Allah akan lamura .
Jabir Bin Abdullahi Allah Ta’ala ya yarda da su yace; Manzon Allah S.a.w ya kasance yana koya mana yin istihara (Neman Zabin Allah) a cikin al’amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin Alqur’ani…
ADDU’AR ISTIKHARA
اللّٰهُمَّ إِنِّيْ أَسْتَخِيْرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ العَظِيْمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلاَ أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلاَ أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الغُيُوْبِ اللّٰهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأمْرَ (وَيُسَمِّيْ حَاجَتَهُ) خَيْرٌ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِيْ وَيَسِّرْهُ لِيْ ثُمَّ بَارِكْ لِيْ فِيْهِ وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِيْ فَاصْرِفْهُ عَنِّيْ وَاصْرِفْنِيْ عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ، ثُمَّ أَرْضِنِيْ بِهِ
Allahumma inni astakiruka bi’ilmika, wa astaqdiruka biqudratika, wa as’aluka min fadlikal azhim, fa’innaka taqdiru wa aqdir, wa ta’alamu wala a’alamu, wa anta allamul guyub, Allahumma inkunta ta’alamu anna hazal amra (sai ya ambaci bukatar tasa), Khairunliy fiy diniy wama’ãshiy wa ãqibati amri faqdurhu liy wa yassirhu liy, thumma bãrik liy fihi, wa inkunta ta’alamu anna hazal amra sharrun liy fi diniy wama’ashiy wa ãqibati amri fãsrifhu anniy wasrifniy anhu waqduriyal khaira haithu kana thumma raddiniy bihi
FASSARA:
Ya Allah ina neman zabinka domin ilminka, kuma ina neman ka bani iko domin ikon ka, kuma ina rokonka daga falalarka mai girma, domin kai ne mai iko, ni kuwa bani da iko, kuma Kaine masani, ni kuwa ban Sani ba, kuma Kaine masanin abubuwan fake, Ya Allah! Idan kasan cewa wannan al’amari (sai ya ambaci bukatar tasa) alheri ne gareni a cikin addinina, da rayuwa ta, da kuma karshen al’amarina, – a wata ruwayar da magaggaucin al’amarina da majinkircinsa – ka qaddara mini shi, kuma ka saukake mini shi, sannan ka albarkaceni a cikin sa, kuma idan kasan wannan al’amari sharrine a gare ni a cikin addinina, da rayuwata da qarshen al’amarina – a wata ruwaya; da magaugaucin al’amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar dani daga gare shi, kuma ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma ka sanya ni in yar da shi.
TSOKACI: RAKA’O’INTA:
Maganar da tafi inganci ana yinta raka’a 2, wasu malaman kuma suna ganin Zaka iya yin sama da raka’a biyu.
DA WANE LOKACI YA KAMATA KA YI TA?
Magana mafi inganci zaka iya yin ta a kowani lokaci. Mafi falala cikin dare. Amma banda lokacin da aka hana yin nafila a cikin sa..
A INA AKE ADDU’AR?
Wasu malaman suka ce ana yin ta lokacin Sujuda, wasu suka ce ana yinta a zaman tahiya Bayan an gama yima Annabi Salati kafin ayi sallama, wasu suka ce ana yinta Bayan sallama. Wasu malaman suka ce ana fara yin istikhara sannan a nemi sharawa (amma neman shawaran ana yinta ga mutumin da ya dace mutumin kirki).
Wasu suka ce sakamakon istkhara dinka yana ga wannan mutumin kirkin da kuka yi shawaran tare.
Wasu kuma suna ganin shawaran ake fara yi Allah zai kimtsa maka nutsuwar abin.
Wasu kuma suna ganin (Bayan ka yi istikhara din idan alkhairi ne Allah zai kaddara sababin faruwar abin ka sami nutsuwa, idan ba alkhairi bane Allah zai warware abin..
WANI ZAI IYA YIMA WANI?
Wasu malaman suka ce Wanda bazai iya yiba to za’a iya yi masa.
Ana yin isikhara ga abinda yake halak ne, misala neman aure, aiki, yin tafiya, neman karatu kasuwanci da sauran abubuwa na rayuwa Babu shakka dae duk wanda yayi.
For download click Here:to
ALLAH YABA MU DA CEWA DUNIYA DA LAHIRA..