Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 11

Sponsored Links

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

Bisimillahirrahmanirrahim.

**
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*

*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

 

*11*

 

Sai bayan ya dawo masallacine ya shiga ɗakin na fadila,wacce ke kwance kan gadonta tana kuka,

Da sauri ya ƙarasa gunta ya kamota ayko ra fincike tace cikin fushi”haka mukai dakai,laveeb nace haka mukayi dakai,watakan tun kan aje koina shine har ka fara wulaƙantani, to wallahi bazan yarda da haka ba”taci gaba da kukanta.

Zama yayi gefen gadon yace a tausashe “nifa kinga fadila tun farko abinda na tsana kenan yasa nace bazanyi auran nanba,kika takura,to gashi anyi fisabilillahi taya zanyi disvirgin ɗin yarinyar mutane kuma in tsallake inbarta ba tare dana bata kulawaba,toko a bariki muka haɗu mace tai maka kyautar virginity ɗinta ay dolenka ka girmamata bare kuma aure, da kinsan ciwon kan da zaki sani kenan ay da baki sa na auretaba”ya faɗi cikin faɗa faɗa.

Sosai hankalinta ta tashi ranta ya ƙara ɓaci da jin kalaman dake fita a bakinsa, amma haka ta daure tace”shine kake min faɗa dan na nuna kishina akan abinda nakeso?”.

“To ay kece da abun haushi taya kece kika sani abunnan kuma ki wani zo ki kwanta kina sharɓar kuka,wanda inda arziƙima kece zakije ki kula da ita baniba,tunda de kece silar komai”

Shuru tayi batace komaiba hakan ke nuna alamun ta saduda hannu yasa ya janyota jikinshi ya rungume yace a atausashe”don Allah ki kwantar da hankalinki ni banyi aure dan in ɓata mikiba sedan neman haihuwa da mukeyi,in kina tada hankalinki zakisa nakasa yin abunda yadace pls kidena dom Allah”

Shuru tayi ta dena kukan,sannan ta ɗago tace”nide ka cikamin alƙawari ka saketa da zaran ta haihu don Allah ”

Shuru yayi na ƴan sakanni sannan yace “to iya rigima naji muje kiban abinci nakaiwa ƴar mutane”

Miƙewa yayi ɗauke da ita suka nufi dinning,yana ɗan tsokanarta.

Kulolin abincin ta tayashi ɗauka sannan suka nufi sashin amarya tare.

Har lokacin tana ɗaki kwance ta farka amma bata sakko ba.

A Falo fadila ta zauna sannan shi ya shiga cikin ɗakin,da sauri ya ƙarasa inda take yana faɗin “iam sorry sweetheart,naje masallacine kuma naje gurin uwargida muka gaisa gatacan afalo ma tazo duba jikin naki”ya faɗi yana rungumota jikinshi.

Murmushi tayi ta sunkuyar da kai ƙasa tace akunyace”faɗa mata kayi banda lafiya?”

“Eh mana baby,ay dolene duk mesona yasoki babyna kuma ya tayani ji dake shiyasa na faɗa mata taso muje tana falo”ya faɗi yana sunbatar bakinta.

A hankali ta zuro ƙafarta ƙasa shikuma ya taimaka mata ya ruƙo kwankwasonta ta fara takawa a hankali,zuwa falon.

Fadila lokacin datai arba dasu labeeb riƙe da ƙugunta sun nufota ji tayi kamar ta fita da gudu sabida tsabar ɓacin rai game da hakan,amma haka ta jure, ta zauna har suka ƙaraso ya zaunar da ita sannan shima ya zauna gefen amarya,yayinda fadila kecan gefe,haka tai ta maza ta jure.

“aunty ina yini ya ayki?”cewar farida atausashe.

“lafiya lau ƙanwata ya kwanan amarci?”

Shuru tayi ta kasa amsawa sede murmushi kawai datayi.ta sunkuyar da kai.

“ance bakiji daɗiba to Allah ƙara lafiya,ni na tafi”ta faɗi gamida miƙewa azatonta labeeb ze biyota se ji tayi yace”ok to baby sena shigo zuwa anjima mungode.”

Koda ta waiga taga me yakeyi,sai taga ko kallonta beyiba yana matsawa amarya cinyoyinta ne.

Da sauri ta ƙarasa ficewa daga ɗakin zuciyarta na shaida mata dolene ta ɗauki mataki na gasken gaske.

Shiko abinci ya zubo ya shiga bata tana masa shagwaɓa shima yana ci har ta ƙoshi sannan ya ɗauketa zuwa toilet wanka yay mata sannan ya ƙara gasata aruwan zafi tana ta masa kukan zafi wai gun ke mata.shiko sai aykin rarrashinta yake tayi.

 

 

 

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button