Mai Maganin Mata 18
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
Bisimillahirrahmanirrahim.
**
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*
*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*18*
“Fadeela kidinga haƙuri,dan Allah bafa ta haka ne zaki ƙwaci mijinki ba,sabida inde yana sonta azuciya ko bata gidan ay anyi aykin banza.”cewar murja bayan sun koma part ɗin fadilar.
Gyara zama fadeela tayi sannan tace”murja koya na tuna ƴar chadi ta hainceni ji nake kamar na shaƙe matsiyaciya tabar duniya,wannan abinda nai mata be gogen tabon datai min ba murja”ta faɗi tana huci.
“good tunda kinsan baze gogeba to se ki natsu kisamo mafita bata faɗaba,cikin ruwan sanyi ki amshi mijinki”
“Ay shiyasa nakeso inje niger da kaina can agadaz dan insamo magunguna na gani na faɗa”cewar fadeela tana murmushi.
“mtsuuuu ay kinji tsiyar taki fadeela,wai ance miki maganin mata ne zaman aure ko zama da kishiya,to yakamata ki farka haka fadeela,ko lahira fadeela seda hali me kyau,bare duniya kuma agidan namijin daba ubanka ba,zuwa yanzu fadeela kibar batun maganin mata agefe,kitashi ki natsu,tsafta,iya girki,iya gado kirsa da kisisina uwa uba adabun kalam, ladabi da biyayya,daga baya maganin sanyi yabiyo baya,dan ba wata macen da Allah beyita da niima ba saidai ciwon sanyi ya lalata,dan haka ki tashi kisha maganin sanyi zakiga ikon Allah dan alokacinne in kika sha maganin mata ze miki ayki.”
“Watakan murja in kana da sanyi ko kasha maganin mata abanza kenan?”cewar fadeela tana riƙe baki.
“sosai fadeela amma zakiban mamaki inkika gwada da kanki.”
Sun jima suna hira kan matsalar rayuwar kamin murja tabar gidan.
Murja na fita,fadeela ta miƙe dan fara gudanar da darasin na murja.
Farawa tayi da ɗora girkin datasan yana matuƙar so,bayan ta ɗorane ta fara gyaran gidan.
Ko ina saida ta share ta goge,ta waike toilet,ba abinda bata gyara ba guri ko ya ɗauki ƙyalli ga ƙamshi daga HUMKAM GIDAN ƘAMSHI DAKE KANO,tasa a koina na part ɗin nata,sannan ta kawo wani harabar gudan shima ta kunna.
Ta kammala abinci ta jere komai a inda yadace,sannan ta faɗa wanka,bata jima sosaiba sabida an fara kiran sallah,alwala ta ɗauro ta fito.
Kwalliya ta tsara ta gani ta faɗa,sannan ta feshe jikinta da turaruka,ta ɗauko wata doguwar riga tasaka me bin jiki,koya ta motsa se jikinta yayi rawa aciki.
hula tasaka kalar rigar,sannan tasa hijab tai sallah,tana idarwa ta cire hijab ɗin ta fice zuwa part ɗin fareedar.
Da sallamarta ta shiga,falon azaune tasameshi kan carpet alamun ya idar da sallah kenan.
Tunda ta shigo yake binta da ido harta ƙaraso inda yake.
Durƙusawa tayi har ƙasa tace cikin salon ɗaukar hankali take motsa baki da ido”prince tun ɗazu nake jiran shigowarka baka shigoba,shine yasa na biyo sawu”ta faɗi tana kamo hannunshi.
Murmushin ƙarfin hali yayi yace”to kun chager min kai fadeela,na rasa yazanyi daku wlh,abun na damuna”ya faɗi a marairaice.
Miƙewa tayi tsaye riƙe da hannunsa,shima ya miƙe,yana kallonta,shigewa tayi jikinshi,ta ɗora hannayensa akan mazaunanta,sannan ta kwantar da kanta a ƙirjinshi tace tana shafashi.
“kayi haƙuri prince duk laifinane, kuma hakan bazata ƙara faruwaba,kazo muje kaci abinci kayi wanka seka samu ka kirata awaya kaji halin datake ciki,inyaso koni se inje kanon in dawo da ita”ta faɗi amarairaice tana shafashi.
Shiko labeeb salon nata gaba ɗayaya gama daburtashi yama rasa akanme yakamata yayi tunani.
ɗaukarta yayi cak suka nufi part ɗin nata ta ƙofar baya sabida kar me gadi ya gansu.
Suna shiga be direta koina ba se ɗakinshi,tsayawa yayi yana kallon ɗakin fuskarsa ɗauke da murmushi komai yayi masa kyau sosai,ƙarasowa tayi ta shige jikinshi tace daidai kunnensa cikin muryar raɗa”ya maka kyau ne?”
Rungumota yayi ya sumbaci goshinta yace”sosai ma kuwa baby,Allah miki albarka”
“Amin the priceless prince”
Daga haka taimaka masa tayi yayi wanka ya kimtsa sannan suka nufi dinning dancin abinci.
Canma santi kawai yake mata,tana masa dariya har suka kammala.
*******
A can kano ko Ƴar chadi tayi iya yinta dan ganin ta sakko da fareeda amma hakan yaci tura,shiyasa ta buɗe mata wuta.
Ayko da ike tana tsoronta da gudu tazo ta buɗe ƙofar ta fita tsakar gidan.
Ay kamar jiranta take tako fara faɗa”shashasha wacce batasan me takeyiba,nice fa na haifeki da kaina taya kike tsammanin zan cutar dake,koda ace duk abinda nayi ɗin laifine ay dan de kisamu kwanciyar hankali nayi,amma da ike baki da hankali agaban kishiyarki da mijinki kika yace min baya, dan haka dole yanzu muyi shiri na musamman tunda kinga ay ta kama gida,tunda tunda muka taho ay be nemekiba”
Itade shuru tayi batace komai ba dan zuwa yanzu ta fahimci dan ita tayi komai dan haka zata bi umarnin mahaifiyarta inde tanason tsira da mutuncinta.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044