Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 6

Sponsored Links

 

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

Bisimillahirrahmanirrahim.

*Gajeren labari Domin masoyana da basu da kuɗin siyan paid book ɗina,ga wannan tundaga farko har ƙarshenshi free ne kuji daɗinku,Saidai posting ba kamar paid one ba,Allah barmu da masoyanmu na gaskiya ameen*

*In kina group ɗina bakya comments zan cireki*

*meson karanta paid book ɗina tsawon shekata guda batare daya sake siyaba to 1500 ne register dani,meso seta tuntuɓeni a 07044600044*

*6*

Yau hajiyar labeeb tazo gidan na su,dan taji shuru be koma ya sanar da ita yadda akayi a asibitiba.

A falo ta zauna kan kujera yayinda fadeela ta haye kan ɗaya daga cikin kujerun ta zauna,tana kallon hajiyar ido cikin ido.

“ba zama ya kawoni ba shin ya akayi a asibitin da kukaje?”cewar hajiya fuska ba walwala.

Cikin rashin fahimta fadeela tace”hajiya waye aka kai asibiti kuma ba lafiya?”

“Labeeb be sanar dake saƙona na na kuje asibiti a aunaku bane?”hajiya ta faɗi a ƙufule.

“hajiya meya haɗamu sa gwaji muda muke lafiya lau”cewar fadila tana ɗan juya ido.

“ta ina kuke da lafiya kuwa tunda har yanzu kun gaza ajiye ɗa agidannan,kullum saidai aci ayi kashi,”

Wani irin bugawa zuciyar fadila tayi,dan se yau ta tuno da akwai matsala babba da zata fuskanta akan rashin haihuwarta daga ɓangaran hajiyar labeeb.

Bakinta na kakkarwa tace”hajiya komai fa lokacine kiyi haƙuri karki shiga hurumin ubangiji,tunda shikeda ikon badawa”

“Dalla rufemin baki ni zaki faɗawa Allah ke shi ɗin kika sani kika maidamin ɗa kamar wani shawaragi,to wallahi ki sanar dashi nazo,in har baa kawo canji agidan nan ba zan ɗauki mummunan mataki”tana gama faɗin haka tasa kai tayi ficewarta afusace.

Tana fita harabar gidan labeeb na shigowa a motarsa,da sauri yayi parking,ya fito ya nufo hajiya,jikinshi na ɓari,dan yasan tayiwa fadila zancan zuwa asibiti.

Durƙusawa yayi yana gaidata ayko rufeshi tayi da faɗa”watakan na bada umarmin kuje asibiti shine ka maisheni tsohuwar banzane,to wallahi nanda watanni biyu banji gamsasshiyar maganaba zakaga matakin dazan ɗauka tunda kai kazama sallamamme se abinda mace tace”tana kaiwa nan tasa kai zata fice daga gidan.

Da gudu ya bita a baya yana roƙon tazo yakaita gida,da ƙyar hajiya ta yarda ta shiga motar tashi tana ta faɗa har ya kaita gida shide se haƙuri yake bata.

Koda ya dawo gida samun fadila yayi tana ta kuka, ranta kamar ze fita,dan yau ƙaunar ta haihune sabuwa aranta,dan ta huce gorin hajiya da ƴan uwansa ko badan komai ba sai dan ta magance duk wata matsala da zata shiga
tsakaninta da mijinta.

Kusa da ita yaje yazauna ya kamo hannunta yace atausashe”baby abinda na guda kenan wannan kukan yasa ban faɗa miki saƙon hajiyaba wallahi,Allah yasani bansan kukan ki,hankalina tashi yake fiye da tunaninki,ki daure ki kwantar da hankalinki musan ta ina zamu magance matsalar”ya ƙarasa yana rungumota jikinshi yana shafa bayanta.

Ta jima tana kukan kamin tayi shuru,ta ɗago ta dubeshi asanyaye tace”tunda gobe monday prince muje asibitin adubamu dan musan abunyi inma lalurarce.”ta faɗi murya a dusashe.

“to baby amma de kamin hakan inaso kisawa zuciyarki haƙuri ki yarda da ƙaddara me kyau da mara kyau,ni mijinki ne me sonki kisa wannan a ranki”ya faɗi yana mata murmushi.

Hakade sukai ta maida yadda zaayi goben ,wanda hankalin ita fadila yafi na labeeb tashi.

Koda dare yayi bayan sun gama raya sunna baccinshi yayi,itako ta kasa bacci tsoronta Allah tsoronta suje ace itace bata haihuwar,shine ya janyo ƙauracewar bacci a idonta.

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button