TUNATARWA

MECECE DUNIYA A MUSULUNCI?

Sponsored Links

MECECE DUNIYA A MUSULUNCI?

 ‘Yan uwa wannan rayuwar ta duniya fa rudani ce da wasa, da yaudara mai dauke hankali.. Shaitan yana amfani da ababen cikinta wajen yaudarar da zukata da shagaltar da tunanin Bil Adama.

 Rayuwar nan ta duniya Mafarki ne wanda ke cike da alkawura marassa tushe, Marassa makama.. Wanda yayi sammakon farkawa daga wannan mafarkin shine wanda ya rabauta.

 Ita rayuwar duniya tamkar cin kasuwa ne. Lokutan da Ubangiji ya baka awannan rayuwar sune tamkar kudaden cin kasuwar.. Babu wanda ya rabauta sai wanda yayi amfani da kudinsa wajen sayen abubuwan da zasu amfaneshi idan ya koma gidansa na ainahi.

 Wato yayi amfani da lokutansa wajen neman ilimin addini da kuma aiki dashi, Ko taimakon addini da jikinsa da Aljihunsa da basirarsa da dukiyarsa
Yayi amfani da ranakunsa wajen neman halal da sada zumunci  da tai makun mai karamin karfi da dararensa wajen nafilfili da Zikirin Allah da Karatun Alqur’ani da kira zuwa ga tafarkin Allah.

  Amma wanda yayi amfani da lokutansa wajen Kallon abinda ya haramta,  kamar su caca da shan kyan maye da zaman gulmace-gulmace, da cin mutuncin Musulmai, da tafiya wajen sa’bon Allah, rushe tarbiyyar al’ummah, to wadannan sune sukai asarar lokacin su sune   asararru, sune wadanda basu ci ribar kasuwancinsu ba. kamar yadda Allah yake ce:

 Ya kai ‘Dan uwa!! Ko kasan cewa duk abinda kake aika tawa koke  gadara dashi awannan duniyar (Kudi, Mulki, daukaka, dukiya) sai da wasu suka sameshi kafinka?.
  Kuma yanzu dolensu sun tafi sun barshi?. Suna Qarkashin Qasa suna girbar abinda suka shuka na alkhairi ko sharri??.
Yadda yanzu basu nan sai dai labarinsu, mafiya yawansu ma ko labarin nasu babu.  To hakanan kaima gobe sai dai labarinka… Jibi kuma ko labarin naka ma babu!!!.
 Lahira ita ce gidanka na ainahi.. Gidanka matabbaci.. Yi Qokari ka tanadar ma kanka guzuri mai yawa ta hanyar Ibadah mafi saurin tseratarwa daga wuta. Wato Zikirin Allah safiya da maraice..
Yima guzurinka Stamp na Ikhlasi. da Kuma ka zubar da Miyagun kaya daga cikin guzurinka ta hanyar Istighfari. kamar yadda Allah yake cewa :
                     


 Ka Qamsasa guzirin naka, ka Qara masa tsada ta hanyat Salati da Tasleemi ga Annabinka mafi daraja. Annabi {Muhammadu S A W} Alfaharin Banu Hashim, Farin cikin Halittu, {Annabi Muhammadu}.  

 tsira da amincin Allah su  tabbata agareshi da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa yardaddu da mabiyansa har zuwa ranar sakamako. Ameeen.

    Daga dalibinku
      musa s zage
            kano.

Leave a Reply

Back to top button