Musabbabi Book 2 Page 8
MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere )
Page 8
Alh yusuf sanda ya ƙurama hoton ido, ko kaɗan babu alamar kishi a tare da shi, illama murmushin sa na ƙaddara da yake ta faman yi, gami da zagaye ɗakin ba tare da ya cire ido akan hoton ba.
Ya ɗauke hoton ya shiga wajen kira, bugu ɗaya wanda ya kira ya ɗauka, babu wata doguwar magana yace “ Na ga komai, ka turo min accout number ɗinka”, ya jinjina kai lokaci ɗaya ya kashe wayar yana cigaba da girgiza ƙafafunsa.
Gaba ɗaya gidan mallam Mahmud murtala ya wuce, suna isa gida, da kansa mallam mahmud ya shiga gidan liman maƙocinsa, ya kira shi domin ya zo ya ga abinda aka tono, da kuma neman shawarar yadda za’ayi da shi. Liman ya daɗe ya daɗe yana addu’o’i, kafin ya ɗauki sihirin a hannunsa, sannan ya yi ta addu’a yana tofawa akai na tsawon wani lokaci, kafin daga bisani ya buƙaci a bashi ashana. Nan da nan Inna Halima ta tashi ta wuce Mama Hauwa da take tsaye sototo tana kallon duk abinda ke faruwa ba tare da tasan dalilin faruwar komai ba, ko kallonta Inna Halima ba tayi ba ta wuce ɗakin girki ta ɗakko ashanar ta kawo, liman ya ƙarɓa ya ƙara yin wata addu’ar sannan ya kona duka tukunyar sihirin da abinda ke cikinta, duk ido su ka sama tukunyar har sai da ta ƙone ƙurmus sannan mallam Mahmud ya matso kusa da liman yana kallonsa yace “ yanzu shikenan babu wata matsala, babu fargabar faruwar komai”, liman ya girgiza kai cike da alhini yace “ in sha Allahu babu komai, irin addu’o’in da nayi kuma ko da akwai matsala Allah zai kare komai, sai dai tabbas mallam duk wanda ya yi tsafin nan ya gawurta zaman irin su kuma a cikin al’umma masifa ne, domin wannan ba asiri bane tsafi ne, kuma akwai bambanci sosai tsakanin asiri da tsafi , sai dai kuma in sha Allah wannan dai tsafin ya riga ya karye, Allah kuma ya shiryi masu yi da waɗanda ke kai kansu don ayi musu, Allah ya tsare mana imanin mu”.gaba ɗaya suka amsa da “ Amin”, sannan ya dubi mallam mahmud yace “ shi kuma musaddiƙ ɗin idan ya dawo ka kawo shi wajena, saboda akwai wasu addu’o’i da zan ba shi na tsari, domin wannan rayuwar da muke ciki dole sai da addu’a, don muna cikin wani zamani da hassada da baƙinciki suke addabar raunannun zuciyoyi, hakanan ma baka takama mutum ba baka zubar masa ba ya zauna yana jin haushinka kamar zai kasheka, bayan babu abinda kayi masa, Allah dai yasa mu fi ƙarfin zuciyar mu”.
Gaba ɗaya suka amsa da amin sannan mallam mahmud ya yi masa godiya ya kuma raka shi har waje sannan ya dawo, bayan ya dawo daga rakiyar liman ne, shi ma Murtala ya yi musu sallama domin tafiya gida, gaba ɗayan su tun daga mallam Murtala, Inna Halima, da Afrah, sai da su ka yi masa godiya mai yawa,domin irin taimakon da ya yi musu, tare da sauƙaƙa musu komai, murtala ya nuna musu don ya yi ma musaddiƙ wannan ba komai ba ne, domin yadda ya ɗauki musaddiƙ a matsayin amini, haka zalika ya na ɗaya daga cikin masu yin bakinciki da halin da musaddiƙ yake ciki, zai kuma iya yin komai domin ganin ya dawo dai dai. Duk da haka dai sun ƙara masa godiya, sannan ya bar gidan.
Bayan fitarsa ne,haƙurin mama Hauwa dai ya ƙare musamman da ta ji irin bayanin da Liman ya yi, sai dai daga fuskar Inna Halima har ta Afrah babu wace take da sauƙin da zata tambayesu abinda ke faruwa, don haka ta taka a hankali ta koma gefen da mallam Mahmud ya ke, tana kallonsa ƙasa-ƙasa tace “ Wai mallam me ke faruwa ne?, na ji liman na maganar tsafi, ga kuma wannan mummunan abu da aka ƙona, wa aka yi ma tsafin ne, kuma wa ya yi?, don na ga babu wanda ya damu da ya yi min bayani”, Inna Halima ta tabe baki ta kau da kai, Afrah kuwa matsawa ta yi can kusa da tsohon ɗakinta ta cigaba da laluben wayar musaddiƙ, wanda har zuwa lokacin a kashe wayar ta ke.
Mallam Mahmud ya yi mata kallon tsaf yace “ Ba’a gaya miki bane saboda bai shafeki ba”, ta fiddo idanu waje cike da mamaki tace, “ Ban gane bai shafe ni ba, amma ai abinda ya shafeka ya shafe ni, tunda kuma naga ai har bare aka sako ciki, murtala da alama da shi a kayi komai, sai ni kace bai shafe ni ba” mallam Mahmud ya ƙara gyara tsaiwarsa yace “ Da ace maganar Na’ima ce ko ta sauran yayanki da sai nace ya shafe ki, amma wannan magana ce ta ya ta Afrah”, ran Mama Hauwa ya ƙara harzuƙa tace a zafafe, “ wai wace irin maganace wannan ka ke jifana da ita, yanzu don maganar Afrah ce sai a kasa gaya min wai me ku ka ɗauke ni ne?”
Kai tsaye mallam Mahmud ya bata amsa da cewa, “ Maƙiyiyar Afrah”, Inna Halima ta jinjina kai alamar ta ji daɗin amsar da ya ba ta.
Ita kuwa Mama Hauwa bata fita daga takaicin maganarsa ba, ya ɗora da cewa “ Ke Hauwa, na rantse ki ji tsoron Allah, ki yi ma kanki faɗa, ki sani ɗan kishiya ba abokin gaba bane, ki sauke baƙar aƙidar ki akan hakan, ya kamata ace ki kalli ko wane ɗa da irin idon da ki ke kallon ɗan da ki ka haifa, ko ɗan kishiya, ko ɗan maƙoci, ko ɗan unguwa da duk wani ɗa da zaki gani a duniya to ki sama kan ki son sa da son cigabansa kamar yadda zaki so cigaban ɗan da ki ka haifa, da za’a dinga samun irin haka to tabbas da an samu ƙarancin lalacewar tarbiyyar yara, “.
Za tayi magana kenan, ya ƙara katseta ya cigaba da cewa “ Ina matuƙar tsoro da fargabar ka da ke ma wata rana ki faɗa bin malaman tsubbu da bokaye domin ganin bayan Afrah, kamar yadda kilishi ta bi domin ta ga bayan musaddiƙ, don kuwa irin ƙiyayyar da take ma musaddiƙ irinta ki ke yi ma Afrah, shi fa ɗa ba a san mai morarsa ba, don Allah ki sassautama kanki ki dawo hanyar Allah da manzonsa”. Nan da nan fuskar mama Hauwa ta ƙara canjawa, ta waigo tana kallon Inna Halima da take faɗin “ Allah yasa ta ji nasiha”, ta ɗauke idonta akanta bata jin zata biyeta yau su aje abin faɗa, don haka ta dubi mallam Mahmud tace “ Haba mallam, wannan wace irin maganace, ni har wace ƙiyayya nake yi ma Afrah da zata zama abar kwatance tsakani da Allah da har zan shiga bokaye saboda na ga bayanta?”.
Mallam Mahmud yace “ To ai abin naku ne ya fara ba ni tsoro matuƙa, ( ya dubeta sosai) ko kinsan duk wannan halinda musaddiƙ ya ke ciki na lalacewa kilishi ce ta yi masa asiri shekara da shekaru, rayuwarsa ta lalace ya kuma zama abin ƙyama, wannan abin da liman ya ƙona asirin ne da aka tono”. Mama Hauwa ta yi salati ta sanar da ubangiji tace “ Amma lalle Haj kilishi ta yi asara, bata jidaɗin rayuwarta ba ta kuma taɓe Allah ya yi mana tsari da irin wannan baƙar rayuwar”, Inna Halima ta watsa mata harara tace “ Allah yasa abinda ki ke faɗa har cikin zuciyarki ne, don dai lokaci ya yi da yakamata kema kisan Annabi ya faƙu”, a fusace tace “ kinga Halima ka da ki ɓata min rai, me ki ke nufi ne?”, tace “ Ina nufin ƙiyayyar da ki ke yi ma Afrah ki ajeta hakanan, don babu wani amfani”, nan da nan mama Hauwa ta ƙara harzuƙa tace “ Dama irin kallon da kuke yi min kenan na maƙiyiyar Afrah?”, Inna Halima tace “ ƙwarai kuwa, tunda ba ki taɓa jin tausayin maraicin Afrah ba, kamar yadda ba ki taɓa yi mata kallon ya ba, yarinyar nan har fargabar zuwa gidan nan take saboda mugun idon ki a kanta, kuma ai ba sai kin buɗe baki kince ba ki sonta ba ayyukan ki ne ke tabbatar da hakan”, jikin mama Hauwa ya yi laƙwas ta juya ba tare da ta ƙara cewa uffan ba ta shige ɗakinta domin ta fi kowa sanin Inna Halima ba zata raga mata ba, da alama kuma yau a shirye take da ta yi mata tonon silili. Na’ima ta saki labulen ɗakin da tun dazu take riƙe da shi tana hangen abinda ke faruwa, duka tare da mama Hauwa suka shige cikin ɗakin.
Inna Halima ta matsa inda Afrah take ta dafa bayanta, ta juyo da sauri tana ƙoƙarin goge hawayen da ke sauka a kuncinta.
Ganin hawayenta yasa nan da nan Inna Halima ta ji matuƙar damuwa, da sauri tace “Afrah menene kuma?”, shi ma mallam Mahmud da sauri ya matso yana ɗora ta shi tambayar akan na ta “ me yasa ki ke kuka?”.
Afrah tace “ Ina jin wani irin yanayi a tare da ni , Inna ina jin tamkar yaya Musaddiƙ yana cikin wata matsala, saboda bai taɓa fita aiki bai dinga kirana akai akai ba, musamman idan garin su ka bari, amma tun ɗazu da mu kayi waya har yanzu bai ƙara kirana ba, kuma abin damuwar shine yadda wayarsa take a kashe”.
Mallam Mahmud cikin damuwa, ya fito da ta sa wayar ya shiga kiran wayar Musaddiƙ, amma shi ma a kashe ya sameta.Inna Halima ta dubi Afrah tace “ Ba ki da nambar Haj Hudah, a kirata aji ko lafiya”, ta girgiza kai tace “ Ba ni da nambarta Inna”, ta ƙarasa maganar cikin nuna nadamar rashin aje nambarta ta a wayarta, gaba ɗaya sun shiga damuwa domin rashin sanin halin da Musaddiƙ ya ke ciki, daga bisani Inna Halima ta yanke shawarar ta tafi da Afrah gidanta, zuwa lokacin da za’a san halin da musaddiƙ ya ke ciki.Domin tana da yakinin in dai lafiya da kansa idan ya dawo zai taho gidanta ko gidan Mallam Mahmud din neman matarsa.
Tun shigar Mama Hauwa ɗaki ta zuba tagumi, danasani ne fal a ranta, “ wai Mama yanzu ana nufin shikenan Musaddiƙ zai dawo yadda ya ke kamar da, dan gayu, mai hankali da natsuwa?” Mama Hauwa ta waiwayo tana kallonta tace “ Ni ma tunanin da na ke yi kenan, ki kaga nadama ta fara cika zuciyata, domin dai idan har zai dawo musaddiƙ ɗinsa na da, babu da wacce ya dace sai ke, nadama na ke yi sosai, da na bari kin aure shi a yadda yake kinga da yanzu mun ci riba”, Na’ima ta saki ajiyar zuciya tace “ Eh mana Mama da mun sani mun karɓi umarnin baba, don dai musaddiƙ babu abinda ya rage shi sai wannan shaye shayen idan kuma ya daina to ni dai nan ta kusa banga namiji kamarsa ba”, Mama Hauwa ta gyara zama cike da takaici tace “ Mun yi gajen haƙuri, gashi kamar anyi miki ƙauri da jaɓa, babu wanda ke zuwa neman aurenki ko saurayi tun bayan auren Afrah ba na jin an zo kiranki zance sau uku, ba ki da wani mashinshini, idan nace abin nan baya damuna na rantse miki na yi ƙarya kin isa aure kin kai munzali, Afrah ƙanwar ki ce amma ta manta tana gidan mijinta sai ke gotai gotai da ke kullum muna jera kafaɗa da ke a gida”.
Na’ima ta cika da fushi ta zumɓuro baki tace “ Ni mama na ji kamar ki na son ki yi min gorin aure ne”, ta kwaɗa mata harara tace “ Mara kunya, idan ma gorin ne ba za’a yi miki ba, ni bansan inda ki ka samo baƙin jini ba don ni zamani na farin jinin da na yi ba’a magana, amma ki dube ki ki gani ko biki ki ka je ba kya samo saurayi sannan ki ce wai zan miki gori to anyi miki gorin”.
Haushi da takaici ya ƙara kama Na’ima tace “ To idan kin san hakane me yasa ki ka hana baba aura min musaddiƙ ai da kin bari ya aura min shi tunda na dame ki ban sani ba”. Mama Hauwa ta cigaba da kallonta cike da mamakin yadda yar cikinta da ta ba dukkan gata ta ke gaya mata magana tamkar ba ita ta haifeta ba, ta manta duk sanda ka koyama ɗanka cin mutuncin wani, ƙarshe wata rana na ka mutuncin zai ci, tace ba tare da ta ɗauke idonta a kanta ba, “ Ni ki ke gayama haka, bayan alokacin da na hana ki auren nasa gata na yi miki”, Ta miƙe tana tunkuɗo baki tace “ Gata? wannan ba gata ba ne, gashi nan Afrah zata shiga rayuwar daɗi da kwanciyar hankali, ga martaba da ƙarin soyayya da ta samu da ga baba, to ni me na tsira da shi?, Kawai za ki sa ni a gaba kina min gorin aure, ni ma ai nafi ki son na yi auren, ko na samu wajen sakewa”. bata tsaya sauraren amsar da zata bata ba ta ɗage labule ta yi ficewarta, tana kunkuni tabar Mama Hauwa baki a wangame cike da tsoro da mamakin Na’ima da zata iya cewa ta canja.
Ƙarfe tara da rabi na dare, kofur Lawal ya ƙara leƙowa cikin cell ɗin fuska tamke ya dubi Haj Rakiya da Haj kilishi da suke zaune a takure cikin ƙaskanci, ya miƙa musu wayoyinsu yace “ Gashi nan ku ƙara gwada kiran nambobin mutanen da zasu yi belin ku”, gaban Haj Rakiya ya ƙara faɗuwa a karo da dama, numfashinta ya fara yin sama, bata taɓa sanin ta na tsoron mijinta haka ba irin wannan ranar, ko da wasa bata son yasan halin da take ciki, shi yasa ko ɗazu da aka kawo mata wayar ta kira me belinta ba ta kira shi ba, ƙawayenta biyu ta kira kuma babu wacce tace zata zo data gaya musu police station zasu zo su yi belinta sai su kama kame kame, har number Babaye dillali ta kira amma wayar shi na kashe, ta kira kawunta da shi kaɗai ya rage mata matarsa ta tabbatar mata da cewa suna asibiti tun rana hawan jininsa ya tashi , baisan wamda ke kansa ba, jin hakan yasa bata gayama matar kawunta komai ba. A yanzu bata da wani zaɓi da ya wuce ta kira mallam Tasi’u ta sanar da shi halin da take ciki. Cikin rawar hannu ta karɓi wayar, itama Haj kilishi cikin galabaita da rashin ƙarfin jiki ta amshi wayar, sannan kofur Lawal ya juya ya yi tafiyarsa. Haj kilishi ta kai hannu ta buge tarin sauron da suka yanyaɓe ƙafafunta, jikinta ya ƙara zugewa da zafi wani abu take ji a tsakiyar kanta ana fisgarsa, wanda idan aka fisga takan ji tamkar ana zare ranta ne saboda tsabar azaba.
Itama tunda ake kawo musu wayoyin su kira masu belinsu duka wayar Hassana da Hussaina akashe su ke tamkar waɗanda su ka haɗa baki, hakan yasa ta buga tagumi ta ƙurama wayar ido tana addu’ar Allah yasa ta same su yanzu, ko sa zo su cireta a cikin wannan masifar da take ciki, wannan cell da tashin hankali yake tun rana sauro ke kwasar rabonsa, tunda ko dare ya fara yi wasu irin manya manyan sauro bakake su ke yi tamkar zasu ja su, curi curi sauron ke sauka akan jikinsu, ga duhu babu haske, sai yanzu suka kunna hasken wayoyin su.
Su kansu basa jin daɗin kallon fuskokinsu saboda yadda suka fita hayyacinsu, itama Haj Rakiya har yanzu tagumi na kan kuncinta tana fargabar yadda zata kira mijinta.Bata sami ƙarfin guiwar kiransa ɗin ba har sai da ta ji Haj kilishi ta sami Hassana a waya cikin jigata daƙer maganarta ta ke fita saboda tsananin galabaitar yunwa da wahala da rashin sabo da zama a irin wannan wajen ta yi ma Hassana bayanin ta zo police station ɗin gangare ta yi belinta, hankalin Hassana ya yi matuƙar tashi ta so ta yi mata bayanin abinda ya kaita police station amma ta fahimci ba zata sami damar jin komai daga bakinta ba saboda ta fahimci tana cikin matuƙar tagayyara, don haka ta aje wayar tana kallon agogo dare ya yi amma bata da zaɓi da ya wuce ta tafi police station ɗin yanzu, gashi bata son mijinta yasan inda zata tafi wanda kuma tasan dole sai ya sani, ko da ba ta san laifin da tayi ba aka kaita wajen yansanda ba to fa tasan tabbas abin kunya ne da gori ace mahaifiyarka na ofishin yansanda a wannan daren. Tagumi kawai ta zuba tana tunanin ta yadda zata ɓulloma mijinta.
Cikin samun ƙarfin guiwa Haj Rakiya ta danna nambar Mallam Tasi’u, har ta ƙaraci kukanta ta katse bai ɗauka ba, a ƙalla sai da ta kira shi sau shida sannan ya ɗauka yana daga kwance gyefensa amaryarsa salaha tana danna masa ƙafafu yana lumshe ido ya na buɗewa yana jinsa kamar wani saurayi, sai da Haj Rakiya ta gama masa bayani, ta yi zaton zata ji shi cikin damuwa, ya na kuma tambayarta dalilin tsareta a wajen yansanda amma ga mamakinta sai ta ji yace “ Gaskiya bazan iya fitowa yanzu da daddaren nan ba sai dai ki yi haƙuri ki kwana sai gobe zan zo”, kawai ji ta yi ta fashe da wani kuka mai ƙarfin gaske tace “ Don Allah ka taimake ni ka taho yanzu, na rantse maka sauron wajen nan kaɗai ya isa ya yi ajalina”, tsawa ta ji ya daka mata abinda ba ta taɓa ji daga gare shi ba, nan da nan ta sami natsuwa, yace “ ke ba gidan uban da zan fito yanzu salon a sace ni, yadda babu tsaron nan, idan ba zaki bari sai gobe ba to ki san yadda za ki yi”, bata fita daga cikin mamakin da take yi ba kawai sai ta ji muryar mace tana cewa “wai wacece ne haka?”. Ta so jin abinda Mallam Tasi’u zai faɗa amma kawai sai ta ji ya katse wayar, kanta ya dinga juyawa jiri na fisgarta kamar zata faɗi, shin wacece a kusa da mijinta a wannan daren?, cikinta ya dinga ƙugi, shin me yake shirin faruwa ne?.
Cikin muguwar tsana da ƙiyayya ta juya tana yi ma Haj kilishi wani irin mugun kallon ta na ji tamkar bata taɓa tsanar wani abu ba sama da tsanar da ta yi ma Haj kilishi.ita kam Haj kilishi bata san ma me take yi ba domin kanta na ƙasa tun bayan gama wayarta da Hassana ta dafe kai tana jinta a wata duniya da bata saba da ita ba, inda kowa ke rayuwa irinta mahaukata wasu tsirara wasu suna dokin kara, wasu suna goye da tsummokara wasu ba ɗankwali, shin wannan wace irin duniya ce, nan da nan Haj Kilishi ta ɓalle gyelan kanta ta cire takalmanta ta goya su a bayanta. Cikin gigita Haj Rakiya ta yi baya tana faɗin “subhanallahi , lafiya kuwa Haj kilishi”, dariya ta fashe da shi tana nuna Haj Rakiya tana faɗin “ irin shigar mutanen duniyata kenan, nayi kyau ko”.
A gigice Haj Rakiya ta yi baya, tana kallonta tana so ta tabbatar da abinda take zargi, Haj Kilishi ta cire ɗankwaki ta wurgar ta yo kan Haj Rakiya ta shaƙe nan da nan idanun Haj Rakiya suka firfito ta shiga kakarin mutuwa, gami da ƙoƙarin yin ihu domin neman ɗauki, ihunta ya janyo hankalin jama’ar police station ɗin, da sauri kofur Lawal ya ɗauki makullin cell ɗin ya nufi cell ɗin a gaggauce domin sanin abinda ke faruwa da yasa Haj Rakiya irin wannan ihun me kama da na nemen ceton rai………………..
Yar gidan Imam✍️