Auren Wucin Gadi 23
Chapter 23
Kasa kunnen Anna tayi dan son tabbar da abunda kunne ta ke jiyo mata illa kuwa haka ɗinne dan Aisha kira take”Abba karka tafi kabarmu muna bukatar ka kazo garemu.
Fadila ranta in yayi dubu to ya ɓaci dan haka cikin ɓacin rai da ƙunan zuciya tanufi wajen shugaba tana zuwa ta zube gaban sa tayi sujjada,ta bude baki dakyar cike da taƙaicin abunda Alh shehu yamata tace”ya shugaba gani gabanka ina mai roƙon ka da a saukar da jinin Aisha ga dodo koda yau yau din nan ne ashirye nake dayin duk wani abu da kasani yanzu bani da haufi.
Dariya shugaba ya kece dashi sai da yaɗan tsagaita da dariyan ya gimtse fuska ya jawo wani kwarya dake gaban sa ya miƙa mata,karɓa tayi wani ruwane a ciki kaman jini karɓa tayi ta kafa kanta tashanye shi tass ta ajiye kwaryan masa wani madubi dake gefen sa ya jawo yayi wasu ƴan surutan sa ya watsa wani abu kaman hoda saman madubin madadin taga Aisha acikin sai ganin mahaifiyarta tayi,a razane takurma ihu ja da baya tayi tashiga girgiza kanta tana cewa”haba shugaba kaima kasan hakan ba zatayu ba,wannan fa dakake gani innata ce ko ita kanta Aishan da kyar na danni zuciyata na amince zan bada fansar jinin ta gaskiya a sake duba wannan lamarin kai ina.
Wani irin tsawa ya dakamata dayayi sanadin girgizan gidan baki ɗaya,cikin kakkausan murya yashiga cewa”jinin innar taki dodo ke bukata,bakece zaki zaɓawa kinki abunda yayi miki ba anan mu muke bada umurni kuma dole mutum yayi idan yanason zama lafiya acikin duniyar sa,maza tashi ki ɓacemun da gani kinɗauka kina kwance zakiyi kuɗi ba tare da kinbi ƙa’idojin mu ba.
Daddy ishaq
Tafitan dare yayi lokacin da yafita daga cikin gidan lokacin da yafita mai gadi yana baccin saida yayi ɗan tafiya sannan ya isko motar da datake jiran sa ɗan nesa da gidan.
Shiga cikin yayi suka dauki hanya suna gaisawa da wanda ke zaune a bayan motan,mutum mai suna balami bayarabe ne cikin gurɓatacciyar hausar sa yace”oga ishaq ina tayaka murna fito fatan zamu ɗaura aikin mu daga inda muka tsaya?
“In sha Allah ya amsa mishi sannan ya ɗaura da cewa balami abu na farko da nakeson fara sani shin Alh sunusi wani irin harkallah yakeyi har yanzu?
Sannan inason nasamo iyalina dan ina kyautata zato suna cikin garin nan ta kano tunda goga ya shaidamun ko last week sunje garin namu da alh sunusi harma yamun vedio iyayena da ƴan uwana na gansu suna cikin ƙoshin lafiya nakuma ji babana tsawon wannan lokaci yana koken rashina data iyalina baki ɗaya hakan yana tabbatar mun da cewa basa tare kuma har yau Alh sunusi besan inda suke ɗin ba bare ya cutar da rayuwar su.
“Karka damu oga damamu kaine damuwar mu tunda gaka kafito mun sameka sauran aikin neman iyalinka ya ratayane a kanmu dan haka karka damu zamusa abun yi.
Sauke ajiyar zuciya yayi kana yace”Allah yamana jagora yakuma bayyanar mana dasu cikin sauki”ameen balami ya amsa.
Safiyar litinin ranace da ko bature ance soronta yake,a gaggauce nake shiryawa duk da Anna jikin nata ba kwari,bayan su khadeeja sun wuce makaranta sannan na ɗan zauna kusa da Anna nace”Anna ni zan tafi gashi yau jikin naki sai a hankali dan kin matsa inje ne amma da ba abunda zesani yau in fita in barki gashi ba wayane a hannuna ba balle indan na fita nakira naji ya kike.
Murmushin karfin hali tayi sai dakyar ta iya cewa”Aisha idan kin zauna a gidan ma me zakiyi?
Kawai kijeki Allah ya tsareki yakuma bada sa’a.
Cikin jin daɗi na amsa da amin ina mai rungumarta har nakai bakin ƙofa najuyo nace”Anna jiya nayi mafarkin Abbanmu ya dawo faɗada fara’arta tayi tace”to Allah ubangiji yakaddara saduwarmu Aisha amma ni harna cire rai da sake ganin Abbanku duba da yanda muka dauki shekaru mai tsawo kuma ko labarin wanda yace yaga komai kama da shine bamuji ba,duk da yanda mukai ta bibiyar labarin gidan.
Cike da rauni ta kare maganarta nace”Anna karki cire tsammani dan inaji a raina Abba ze dawo kuma zamuyi rayuwarmu kar ta da.
“Jeki aisha karki makara tace dani nasan maganarce bata so duk sanda mukai maganan Abba sai ta shiga damuwa amma nikuma a duk sanda natuna wani abu dq mukai da Abban mu ko a can garinmu sai nace Abba kaza da kaza kokuma garin mu kaza.
Ban samu abun hawa da wuri ba,dan haka dole tasaka ni takawa da kafa kafin na nasami abun hawa kaman daga sama wata mota ash colour tazo taja ta tsaya a gabana bude kofar akai a hankali sai ga wani hamshaƙin mutum dattijo ze kai kimanin irin ɗan shekara hamsin ko da dauriya amma kasan cewar sa cikin hutu jikin sa be nuna shekarun sa ba.
Da fara’ar yatare ni yana”a’a malama Aisha kece da sassafenan kice yau ni mai sa’ane tunda nayi tozali dake da safen nan,kallon sa nake cikin rashin sani amma duk da haka saboda girmansa da rusuna har kasa nace”barka da safiya.
Washe baki yayi kaman wanda akama bushara da gidan aljanna yace”yauwa Aisha tashi ki miƙe karki sakeyi mun haka ai irin wannan gaisuwar anbar yayinsa kaman baki gane ni bako?”Eh ina saurine nafaɗa ina miƙewa tsaye dan nafara ƙosawa da surutun sa.
“Ayyarh sunana Alh shehu nine wanda kwanaki muka gaisa dake da naje wajen ƙawarki”wayyo dan Allah alh kayi hakuri wallahi bangane ka bane kasan ranan dayake darene ban sheda fuskarka ba.
Ɓangaren Alh shehu kuwa ya shagala da kallon bakin ta yanda take mutsasu dakuma yanda take ɗan karkaɗa jikinta tana yarfa hannu yatafi can wani tunanin sa na daban harta aisha tagama bashi hakuri bisa rashin ganeshi da bata yi ba ta fara tafiya sannan ya ankare yace”am jima aisha cak natsaya daga tafiyar da nafara zo kishiga mota na rage miki hanya dan naga yau kaman ana wahalan abun hawa saboda tsadar man fetur da akeyi.
“Nagode amma kabar shi kawai zan samune yanzu kar kaima na ɓata maka lokaci nace dashi ina mai barinsa wajen tsaye dan harga Allah banason wani abu da ze shiga tsakanina da fadila har mamarta tasamu daman zuwa tama Anna rashin mutunci da tun farko nagane shi ba abunda zesani tsaiwa harna gaidashi ni ɗaya sai faɗa nake aciki zuciyata sai magana nake abuna ina ta buga sauri har Allah yasa nasamu abun haya sauke ajiyar zuciya na sauke lokacin da nashiga na zauna cikin napep din.
Ina sauka bakin ma’aikatarmu shima motarsa na tsayuwa a bayan napep ɗin kudinsa na miƙa masa na soma shiga ciki daidai motar Ahmad shima nashiga, saurin shiga ciki nasoma danma kar yace zemun magana amma ina duk girman shi da shekarunsa haka ya ajiye a gefe shima cikin sauri ya tunkareni yasha gabana.
Ja nayi da baya na tsaya ganin kaman ze fadamun jiki”aisha kitsaya ki saurareni da alheri nazo gunki ba dawani mugun nufi ba tun ranan da naje wajen kawarki muka gaisa naji kinshiga raina a takaice de inasonki kuma aurenki zanyi.
Awani irin zabure ahmad ya juyo yana kallon alh shehu daya tsare aisha da ido jin maganar nasa yayi tamkar anbuga masa guduma akai saida yayi tagaga kaman ze faɗi Allah ya bashi ikon tsayuwa da kafafunsa da sauri yabar wajen dan bayama so ya tsaya yaji wani amsa aisha zata bashi zuciyarsa ta buga.
Aisha ma dagudu batar wajen tana mai girgiza kanka hawaye nabin ƙuncin ta.