Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 49

Sponsored Links

CHAPTER 49

Hankalin Alh sunusi yayi ƙololuwar tashi dajin abunda dodon yanema a wajen dan haka kai tsaye yace”a gafarceni dodo wannan abunda kanema gareni yayi mun tsauri banajin wannan karon zan kawo ƴata nan duba da yanda aurenta ya gabato banaso tasamu matsala a gidan aurenta bason tayi kuka dani daga baya banason iyalaina suyi Allah wadai dani bazan iya ba bazan iya ba.

“Tashi kage ka’aiwatar da abunda muka saaka bama son gardama ko musu anan haka jiki ba ƙwari yafito daga wajen yana maida tufafin jikinsa daya cire sannan yanufi motar sa driver ya jashi suka fara tafiya sunyi tafiya madan nisa harsun fara shiga cikin gari yasa baƙo driver cike da tsoro da yanayin na uban gidan nasa yau yace”ranka ya daɗe Basma takira wayanka tunɗazu”uhmmm kawai yace kaman bazece komai ba sai kuma yace mai tace tana bukata?”ranka yadaɗe ban ɗaga wayan ba yasake amsa masa.
“Ok baƙo kiramun ita yanzu muji mai yake faruwa dan bata kirana a waya haka kawai,kiranta baƙo driver yayi saida yaji anɗaga sannan yamiƙa wayan wa Alh shikuma ya cigaba da tuƙi,bansan de abunda tace masa ba saide yanda Alh sunusi ya amsa cike da ƙaraji zai tambatar maka da antaɓa ƴar lelensa,yana kashe wayan yace”baƙo kaini company wajen Ahmad harni zama rashin mutunci auta taga abu tanaso ace bazata samu ba,me amfanin dukiyata idan har bazan iya siyamata duk abunda takeso ba haka yayi ta bambamin sa.

Kusan motarta data daddynta a tare suka shiga harabar company daidai kuma Ahmad da khalid da wasu ɗaiɗaiku sun fito daga masallaci sallar la’asar,khalid ne ya hangosu yana nunawa Ahmad cike da son zolayarsa yace”gafa Amaryarka da surukinka kode takasa hakura sai an ɗaurane yak….dukan wasa Ahmad din yakai masa yana dariya tare da kaucewa wannan ya hanashi karasa maganan nasa,nufosu sukai Alh sunusi na rungume da basma jikin sa itako sai shagwaɓa take zuba masa harda hawayenta abunda yake sake dagula ma daddyn lissafi ganin hawayenta,har kasa suka zube suka gaidashi.

Amsa musu yayi adaƙile”daddy da kanka da waya kai basai kazo ba khalid yayi maganan da ƴawun Ahmad harara ya bankawa khalid ɗin yana cewa”kuna ganin girman mutun ne daza kiraku ta waya ace kuyi kuyi”sai hakuri daddy yanzun ma khalid dinne yayi magana Ahmad kan tsaye yayi ya goyi hannunsa a ƙirjinsa yana kallon wani bangaren daban hakan dayayi saiya sake tunzura Alh sunusi”ina kayan suke?

“Wasu kaya kuma ranka yadaɗe?khalid ya tambaya cike da rashin sanin kan maganan.

“wai kai menaka sai ana magana kai tasaka baki kaman an kasa dakai basma ke cewa khalid hakan”yi hakuri Amarya yafaɗa yana ɗan bubbuga kafaɗa Ahmad tare da lumshe idonsa yasa budewa alaman rarrashi,lips ɗinsa ya ciza da karfi yana warr da idonsa wucesu khalid yayi dan barmusu wajen.

Hango Aisha tayi da laila dake shigowa ciki da alama suma ɗin daga masallacin suke suna ƴar hirarsu suna takawa sannu a hankali suna ƴar dariyar da alama sunajin dadin zancen dasuke”yauwa daddy ga yarinyar can itace wacce tayi ɗinki kuma daddy har agabansa takira sunan ka tsirara amma be tsawatar mata ba ta faɗa tana kumbura fuska tanuna ahmad ɗin da hannu dayayi kaman bashi a wajen.

“Yakuwa ze tsawatar da ubansa badamasi takira ai da yayi magana,da karfi ya rintse idon sa yana danƙule hannunsa.

“Keeee ƴar matsiyata mai wanki zo nan daidai sanda su Aisha sukaxo zasu gifta ta gefensu su wuce tafaɗi hakan,ja tayi ta tsaya batare da tace da ita komai ba.

Kallon ido cikin ido sukaiwa juna sai itace taji bazata iya juran kallon ƙwayar idon Aishan ba ta janye nata da sauri danjin yanda tsigar jikinta nawanj mimmiƙewa ga wani abu mai kama da tsoro na ɗarsu a zuciyanta.

“Kece?
Batayi magana ko tanuna tasan da ita yake ba,wai ko kurmace?yasake tambayarta a karo na biyu yanzun ma shiru tamasa bata tamƙaba.

“Ke mara mutunci ƴar matsiyata ana miki magana kinyi shiru,murmushin gefen baki ta mata sannan ta bude idon fes kanta tace”kinsan anmun tarbiya da zan tsaya ina musayar ƴawu da manya bane shiyasa kece inaga zan kusa yi dake tunda tazarar dake tsakani na dake bawani abun azo a gani bane.

A ƙufule Basma ta maida kallon ta kan daddyn nata tace”kagani ko daddy?
“Eh nagani yace yana sake kallon Aisha sosai da taki kallon sa koda sau ɗayane yace”kee wakike da suna komade yane inason yanzun nan kije ki ɗauko kayan da tagani tace tanaso ko nawane inde harka ta kuɗine zanbiya dan farin cikin ƴata,mai amfanin neman kuɗin idan bazan sama mata dukkan abunda take so ba dashi.

Yakare maganan sa yana sake jawo basma zuwa jikin sa ita ko sai sake shegewa jikin sa take tana ta taɓara ita ala dole shagwaɓaɓɓiya.

“Yi hakuri malam tafaɗa da muryarta mai sanyi dakuma daɗin sauraro.

“Malam malam kuma yasake maimaita sunan.

“Oh Alhaji tasake faɗa ganin kaman ya raina malam dinɗa takirashi dashi,tana dan dafa goshinta alaman mantuwa.

Jinjina mata kai kawai yayi amma ransa fal mamaki yake shida ko maza ƴan uwasa basa iya musamasa idan yafaɗi magana idan ko yace tanason wani abun jiki na rawa ake masa,ita wannan ɗin wacece?

Suwaye iyayenta?
Dole yana son sanin wani abu daga gareta,kaf rayuwansa mutum ɗaya ke iya tsayuwa gabansa ya kallesa ido cikin ido yafaɗi abunda ya gadama kuma shiɗima yanajin yagama da rayuwan sa to ita wannan yarinya wacece,tunani dayake tuntuni kenan har saida Basma ta taɓashi sannan ya dawo daidai.

Inda Aisha ke cewa dashi”bafa komaine kuɗi ke iya saya makaba,akwai abunda koda kudin ka saida rabonka kafin ka mallaka yana dakyau yaran masu kuɗi nan yawancin su susan da haka,dan haka nima anawa ɓangaren hakane koda kuɗinku…sai kuma tayi shiru cike da jin haushi Alh sunusi ya hayayyaƙo kaman ze daketa dan haushi yace”zan baki 5m nasan ba kuɗin kayanki bane kawai zan bakine dan kije ki rage zafin talauci dake damunku keda iyayenki da yawanku dama talakawa idan talauci yamuku ƙatutu ganin kuna samun dama kaɗan kan masa hali zaku so nuna isarku.

Hmmm”Alh kenan banso kai da kanka da girmaka kafaɗi haka ba,amma amsan bazata gagara ba,riga de mallakinane kuma nike da ikon sai dawa ko bada kyautarsa ko kuma na kyakketa nazubar duk yana….”ke dakata ko ubanki be isa ja da niba balle ke wannan umurni nake baki kai tsaye ba wai dogon surutu ba kuɗin kikeso zabaki jeki kawo kayan yanzu yafaɗa cike da bada umurni yana sake murtuƙe fuska kama hadarin gabas yanda fuskar tasa takoma lokaci ɗaya duk wani dake waje tsaye saida ya tsorata amma abun mamaki Aisha ko ako aƙwalarta dan addu’an neman tsari kawai take cikin zuciyarta fal tsorone kaman tasaki gudawa dan tsoro amma bazaka taɓa gane haka akan fuskarta ba.

Hannu ta haɗa waje ɗaya alaman ban hakuri tace”anty basma wannan abu tsakaninmu ne yo mai nasa mahaifinki aciki gashi kinsa namasa rashin kunya,rigane kingani kinaso saide kalma guɗa daya takk shine ya hana na mallaka miki wannan riga kuma ba abunda ze sa kisame sa.

“Zaki kuwa rasa wani naki yafaɗa cikin fushi”na daɗe da rasasu saide idan karan kaina zan rasa,zuwa yanzu kuwa tafara tsorata da Alh sunusin.

Saurin ɗagowa shima Ahmad din yayi dan jin abunda Alh sunusin ya faɗa akan riga zarasa rai yafaɗa azuciyan sa amna azahiri sai cewa yayi”dan Allah daddy ayi hakuri abun bekai ga haka ba”ya kai mana MY kabani mamaki tunɗazu ka tsaya shiru kaman bakai a wajen ƴar mitsitsiyar yarinyar nan daddy na faɗi tana faɗi saikace sa’anta dolene a koya mata hankali,wani mugun kallo ta watsa mata daya sata yin shiru tana kunkuni……

Alkalami🖊️
Yafi takobi ⚔️

Leave a Reply

Back to top button