TUNATARWA

KOKASAN FALALAR KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN ZUL-HIJJAH?

Sponsored Links

Allah ya daukaka wadan nan kwanaki da falala mai tarin  yawa wadanda bai sanya su ba a wani watan da ba shi ba.

   [FALALAR KWANAKI GOMA NA ZUL-HIJJAH]

1- Sune kwanaki sanannu a wajan Allah wadanda ake aiyukan ibada mafi girma acikin kwanakin shekara baki daya* Allah yana cewa:
{ ﻭَﻳَﺬْﻛُﺮُﻭﺍ ﺍﺳْﻢَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓِﻲ ﺃَﻳَّﺎﻡٍ ﻣَﻌْﻠُﻮﻣَﺎﺕٍ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﺭَﺯَﻗَﻬُﻢْ ﻣِﻦْ ﺑَﻬِﻴﻤَﺔِ ﺍﻟْﺄَﻧْﻌَﺎﻡِ} سورة ﺍﻟﺤﺞ.

2- Allah yayi Rantsuwa da wadannan kwanaki acikin suratul Fajr.
ﻭَﺍﻟْﻔَﺠْﺮِ ‏( 1 ‏) ﻭَﻟَﻴَﺎﻝٍ ﻋَﺸْﺮٍ ‏2 ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻔﺠﺮ 2-1
Ibnkasir yana cewa “Layalin Ashir” sune kwanaki goma na watan zul-hijjah yace kuma wannan itace magana mafi inganci cikin maganganun malamai.

3- Cikin goman farko ake kabarbari sabanin sauran watanni  ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺐر ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ ﻭ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ
Abu Huraira da Abdullahi Ibn Umar suna fita kasuwa cikin goman farko suna kabarbari mutane suna kabbara da kabarbarinsu fathul bari juzu’i na 1 shafi na 458 cikin hadisin Abdullahi bn Umar yace Manzon Allah s.a.w yace:
ﻣﺎ ﻣﻦ ﺍﻳﺎﻡ ﺍﻋﻈﻢ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭ ﻻ ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﻓﻴﻬﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺸﺮ ﻓﺄﻛﺜﻴﺮﻭ ﻓﻴﻬﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻬﻠﻴﻞ ﻭﺍﺗﻜﺒﻴﺮ ﻭﺍﺗﺤﻤﻴﺪ
Ma’ana Manzon Allah s.a.w yace Babu wata rana da aiki na gari yafi daukaka da soyuwa ga Allah fiye da kwanaki goma na farkon Zul hijjah saboda haka ku yawaita wadannan kalmomin
La’ilaha illalah Allahu akbar walillahil hamd.

4- Acikin kwanakin ne ake yin Azumin ranar Arfa ga wanda baije aikin Hajji ba,wanda Azumi yana kankare zunuban shekara guda biyu”* Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)*  ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805. Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)*.ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335. Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta.)

ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3853.

5- Watan Zul Hijjah shine cikamakin watanni sanannu wanda Allah yace ﺍﻟﺤﺞ ﺍﺷﻬﺮ ﻣﻌﻠﻮﻣﺎﺕ.
  Cikin wannan wata ne aka cika mana addini wato ranar Arfa kamar yanda Buhari ya ruwaito.

6- Mafi sune mafi Alkhairi da falalar kwanakin duniya baki daya”* Manzon Allah s.a.w yana cewa;  (mafi alkhairin kwanakin duniya,sune kwanaki goma na farkon watan zul-hijjah)*. ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 1133.
  Annabi s.a.w yace;  (Mafi falala da daukakar kwanakin duniya,sune kwanaki goma na farkon watan zul-hijjah,babu kamarsu a wajan Allah….) ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﺑﺮﻗﻢ 1150.

7- Ibn hajar RH.A ya ce: Acikin Fathul Barry dalilin da yasa wadannan kwanakin sukafi albarka fiyeda sauran kwanaki shine;
 Saboda Allah ya shar’anta ibadau mafiya tsada acikinsu kamar su;
Sallah da azumin da Sadaka da aikin hajji da sauran ibadun na musamman wadanda ba’ayinsu sai awadannan kwanakin kadai.
{Fathul Barry}.

8 . Hadisi ya tabbata cikin Bukhari daga dan Abbas R.A Yace: Annabi S.A.W yace:

 ﻣﺎ ﻣﻦ ﺍﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﻓﻴﻬﺎ ﺃﻓﻀﻞ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﺸﺮ، ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻭﻻ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ؟ ﻗﺎﻝ ﻭﻻ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻ ﺭﺟﻞ ﻳﺨﺎﻃﺮ ﺑﻨﻔﺴﻪ ﻭ ﻣﺎﻟﻪ ﻭﻟﻢ ﻳﺮﺟﻊ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﺑﺸﻲﺀ .

 Ma’ana: Ba wasu kwanaki da aiki na kwarai ya fi falala a cikin su kamar wadannan kwanaki na 10 (farkon) zulhajji Sukace koda jihadi? Yace: eh koda jihadi sai dai mutumin da ya jefa kansa da dukiyar sa cikin hatsari saboda Allah kuma bai dawo da komai ba.
            رواه مسلم

9- A cikin wadannan kwanakinne ake yin ayyukan Hajji da Umara da sauran ibadu mafiya tsada.

10- Acikin wadannan kwanakine akiyi layya da idin babbar sallah kuma suna cikin mafiya tsarar ayyuka da akeyi acikin wadannan kwanaki wadanda ba’ayi acikin wadansunsu.

DANA NAN DOMIN SAMUN WA ABUBUWAN

KOKASAN falarlar-rakaatiyil-fajar.

sallar-nafila-don-nemawa-yara-shiriya.

yawaita-istighfari-yana-janyo-samun.

Allah-ya-sanya-duwatsu-su-zama-turaku.

Allah ka sadam da alkhairi wadannan ranaku kuma ka abamu ikon yin ayyukan alkhairi acikinsu amin.

          { ﻭَﻳَﺬْﻛُﺮُﻭﺍ ﺍﺳْﻢَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓِﻲ ﺃَﻳَّﺎﻡٍ ﻣَﻌْﻠُﻮﻣَﺎﺕٍ}

        ، ‏( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺁﺗﻨﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻗﻨﺎ ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻨﺎﺭ ‏).

   ALLAH KA DATAR DAMU A DUNIYA DA LAHIRA.

                         (وبالله التوفيق).

DAGA DALIBINKU
  MUSA S ZAGE

Leave a Reply

Back to top button