Matan Ko Mazan 33
💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 3️⃣3️⃣
Magana ake ta kayan kwalam da makulashe😋 Kun gane kalan Kayan makulashe din kuwa? Toh bari kuji yau na kawo maki shaharariyar nan da aka sani da Crave and Indulge mai gullisuwan en gayu🌚 Indai magana ake ta gullisuwa, tuwon madara, tsami gaye, kwakumeti, Ridi, da halaka kobo,garin danwake da yaji! toh ba Irin ta a Nigeria. Zaku iya order ma kan ku, yaran ku, loved ones dinku har ma kuyi ma ‘yan uwa da abokan arziki souvenir😁 Ga tsafta ga dadi kuma✅ zaku iya tuntuban su a shafin su na instagrams @crave_n_indulge ko kuma ku musu magana ta WhatsApp https://wa.me/message/SAFXLSMA7TI6L1
33
Duk tafiya akayi yarage daga ita sai Mama afalon dake kallon yanda take kuka, kaman taje ta lallasheta but itama at this point she support Babanta 100 percent, yayi maganin Hadiza, ya gyarata, kuma she trust Baba Hadiza zata ladabtu, kuma zata bada nata gudunmawan ma agayarata, tashi tayi tawuce corridor dakin dake kusada nata tabude daganan tace “taho ki shiga dakinki kiyi wanka ki chanza kayan jikinki kiyi salla” ahankali Hadiza ta tashi ta taho sai kallon fuskan Mama take data hade giran sama da kasa so kawai take Mama ta lallasheta but Mama nosend hatta shige dakin dake da yar katifa yar daidai akasa dawata yar fanka asama babu AC babu POP normal silin ne asama, sai akwatinan kayan ta kakap wanda Nura ya aiko dasu duk suna dakin nan aka ijiye, shiga ciki tayi Mama tasaki labulen ta wuce taje ya debo mata abinci da ruwa da kanta tazo ta kawo dakin, ganinta azaune yasa ta daka mata tsawa. “My friend stand up kije kiyi wanka nace!” Kallon Mama Hadiza tayi saitaga kaman ba Mama dake nan nan da itaba, jiki asake ta tashi taje bayi tai wanka Mama na tsaye akanta ta shirya tai salla tasa taci abincin dole taci kusan rabin tuwon sanan tawuce tafita da plate din tadawo daki ta kwanta tayi shiru tana kallon fankan dake kadawa asama yana kara dake damun brain dinta sai kawai taji hawaye yafito daga idanunta saita tashi ta zauna ta zubama akwatinan ta ido tana kallonsu sai kawai taji hawaye yakara fito mata a fuzar da iska komi da Zeenah tamata na dawo mata fresh yanzu da gaske Nuri is done with her tunda har yana dawo da komi nata gida wani kuka yazo mata tayishi ta gode Allah tai bacci.
3 dot taji ana kiran sunanta. “Khadija Khadijah” Adan firgice tabude idanunta jin muryan Baba yana tsaye gaban dakin batare daya shigo cikiba yace “Khadija” dasauri tace “na’am Baba” strictly yace “dauro alwala kifito falo ina jiranki” ahankali tace “tom” tashi tayi tana tangadin bacci tashiga bandaki ta dauro alwala ta dauko hijabi tafito falo Baba kadai tagani ya tsareta da idanu dasauri tasauke kanta kasa dadduma biyu ya shimfida afalon daya agaba daya abaya yace “hau dadduma muyi qiyamun laili” Gyadama Baba kai tayi yatada salla yafara karanto Al qur’ani kira’an Baba dadi sai kawai Hadiza taji abun ya tsuma mata zuciya, yaune rana na farko dataji aranta lallai fa tabar Allah for a long time cus bazata iya tuna the last time ta karanta Al Qur’ani ba wlh, sai kawai taji hawaye ya gangaro mata feeling fragile, Baba bai wani ja sallan da tsayi ba sabida ita, 5 raka’a sukayi yajuyo ya kalleta anatse ya daga hannu yace “idan bawa na cikin kunci, damuwa da fitinun jarabawa, bawa dan uwansa bazai iya magance masa matsalolinsa ba Khadija, ni ko mahaifiyar ki bazamu iya magance miki duk abinda ke damunki ba Allah kadaine zai magance miki kome kikeji, shine Ubangiji mai tsarki da daukaka, mai kuma mulki, Al Awwalu, Al Akhiru Al Zahiru Al Badin kuma, duk daren duniya Allah kan sauko dakansa ya amsa bukatun bayinsa, dan haka daga hannunki sama ki gayama Allah bukatun ki kakap, sannan ki rokeshi gafara bisa laifuffukan dakikamai, ki rokeshi haske da dacewa akan rayuwa babu abinda yafi karfin Allah, so kaima Allah kukan ki Khadija” Gyadamai Baba kai Hadiza tayi kuka na zuwanmata ta hannunta sama ahankali abin namata kaman ba itaba she can’t remember the last time datai salla haka ta roki Allah for anything, she’s feeling guilty kan tayi neglecting bautama Allah, sai kawai tafashe da kuka tace “Allah na tuba! Allah na tuba!” Sai kuka hakan yasa ahankali Baba ya juya yayi facing gabanshi, Hadiza tai kuka zuciyanta ya sosu she’s feeling kaman ma she don’t deserve rahaman Allah cus tamai laifi da dama, da kyar ta iya controlling kukan tafara addu’a azuciyanta, the first abu daya fito daga zuciyanta is Nura tanson aurenta da Nura tanason ya maidata, tanason mijinta, kawai saita shiga share hawaye, sosai tai addu’a saitaji wani imani da natsuwa na shiganta da tadade bataji ba, anan bacci yayi gaba da ita ta kwanta kan dadduman Baba tajuyo yakalleta yayi shiru idan yace bai damu da damuwa ta ba yayi karya, saisa ya kudirci anniyan zai gyarata yana kuma rokon Allah ya taimakamai yabashi iko dan idan Allah bai nufeta da shirya ba kome zaiyi abanza bazata shiryu ba, addu’oi yacigaba dayı har aka kira asuba sannan yatadata yace “taje tayo alwala tai sallan asuba” shikuma yawuce mosque.
Hadiza tadauka Baba wasa yake yana dawowa daga sallan asuba wanda bai dadeba dan normally sai gari yawaye yake dawowa gida but yau ana idar da salla yayi azkar yafito yadawo gida yakirata fitowa tayi ga mamaki ta ganin Baba tayi da bagadadi da gaske saikace yarinya shima Baba yasan duk tsiya ai ta iya alifun, ba’un, Al Qur’ani suka farayi from fathiha yana karantawa tana repeating after him, suna gamawa sukai alifun har karshe zuwa alifun bil fatha yana koya mata baki dalla dalla, daganan sukai tauhidi Man Rabbuka, Hadiza jitayi zatai kuka abu ya tsayamata awuya ganin yanda Baba ke koyarda ita abubuwan da yasan ta iya, ko su Aman dinta a islamiyyan su sun wuce abubuwan nan amman ya maidata yarinya, lekowa Mama tayi tagansu tadauke kai abinta takoma daki tana samin natsuwa ganin Baba yarike wuta.
7:30 suka gama Baba yace “tashi kije ki daura abincin kari kiyi gyaran gida, tambayo Mamanki me za’a dafa” gyadama Baba kai tayi tawuce ciki ahankali tace “Mama ina kwana” batare da Mama ta kalleta ba tace “lafiya lau” murya chan kasa tace “me za’a dafa Mama?” Dan kallonta Mama tayi tace “ki surfa wake rabin tiya, saiki debi kadan ayi kosai, ki dama kamu asha dashi, ragowan kiyi alalen rana na gwangwani, injin nikanmu na backyard banason alalen nikan blender, buhun gawayi na kitchen ki hura wuta” ahankali Hadiza na kallon Mama kirjinta na bugawa tace “ba gas Mama”? Wani kallo Mama tamata tace “akwai amman jiya Baban ki yasayo gawayi buhu daya yace dashi za’a dinga girki yanzu” hawaye Hadiza taji sunciko idanunta tarikesu dasauri tace “Mama ban iya hura gawayi ba, shima wake ban iya surfaw……” dakuwan da Mama tamata yasa takasa karasa maganan, Mama da haushinta ke cikinta fall sabida yanda takaso auren gidan arziki yaro mai kudi tadawo mata gida tawani zabura tace “wlh kikkipa miki mari zanyi Hadiza kinci kaniyanki, are you stupid dazaki cemin baki iya surfen wake ko iya hura gwayi ba kin dauka nan Abuja ne? Dan mai garinku kafin kiyi aure ba da itace kuke girki agidan nan ba lokacin akwai gas ne? Sau nawa kika dafa alale agidan nan ki surfa waken kiyi komi? Hadiza kalleni nan wake up! Ki gaggauta tashi daga baccin dakike ubanki ba kowa bane haka ma ni uwarki, Babanki Malamin makaranta ne nikuma housewife ahaka muka raineku kuka taso, auren Nura shine ya jiyardake dadin rayuwa kikadan menene rayuwa adukiya, yanzu kuma kin kaso auren gidan ubanki kike look at everywhere” Mama ta nuna dakin da yatsu tace “bude idanunki da kyau ki kalla nan ba gidan Nura bane gidan mahaifinki ne Hadiza, ki gane banbancin so my dear bace min daga nan kije ki daura abincin safe” tashi Hadiza tayi ahankali tawuce tafito idanunta har zafi zafi suke mata tsabagen rashin jin dadin rayuwanta, tsakar gidan tafito zuwa kitchen dinsu ta tasaya tana kallon komi ga buhun gawayi ga murhun gawayin, ga tukwane, yanzu itane zatai aiki a kitchen din nan? Tasan tayi aiki aciki da but ta manta? She’s not use to old life nata again, ijiyan zuciya tasauke tasa hannunta tadauki kaskon wutan ta ijiye waje daya, tabude buhun gawayin, tadaga fararen soft hannunta dakeshan manicure ta kalla, kuka tafashe da shi ahankali tace “na shiga uku na lalace” goge fuskanta tayi da sauri kafin ahankali tasa hannun cikin buhun ta debo gawayin ta zuba a murhun, ledojin datagani da kyallen dinki na hada kasko tadeba ta zuba tana mamakin yanda take tuna yanda ake hura wutan yanzu, bataga kalanzir ba saitadau ashana ta kunna akai makamashin suka kama hakan yasa tafito tawuce flat nasu ta auno wake 8 cup tafito tadeba ruwa ta jika tadauki turmi ta bude tadauki tabarya ta kwashe wajen ta zuba tafara daka ahankali kirjinta namata badadi ko kadan.
Kafin kaceme hannunta sun sassage from surfen sakin tabaryan tayi ta zauna akasan simentin wajen jitake kaman zata sume ta jinginar da kanta a bango tana maida ijiyan zuciya tana yarfe hannunta, hayaki taga yana fitowa sosai daga kitchen din hakan yasa ta dafa bango da kyar ta mike tsaye ta wuce kitchen din, makamashin sun cinye gawayin bai kama ba sai hayaki suke, tari tafara sosai tafito daga kitchen din tawuce takoma daki tasami Mama afalo tana waya tace “Mama charcoal din yaki kamawa” batare da Mama tai magana ba dan waya take ta rarumi throw pillow kan kujera zata jefa mata da sauri Hadiza tafice takoma kitchen din ranta ba dadi.
Mafici tadauka tashiga hurawa but still yaki kamawa fitowa tayi tawuce daki wajen Mama again data bita da kallo ganin tai buzu buzu duk toka toka akanta, ahankali Hadiza ganin Mama tagama wayan tace “Mama yaki kamawa wlh nayi nayi, gawayin baida kyau zoki duba dan Allah” wani matsiyacin kallo Mama tamata tace “Baban ki ya shigo gidan nan baki gama ba wlh zaki gamu dashi” juyawa Hadiza tayi takoma kitchen ta duka tasake deban makamashi tasa yagamaci still yaki kamawa kawai saita fashe da kuka she’s so fuatrated kaman taita zuba ihu takeji da kyar akaro na uku yakama tadaura tukunyan ruwa tafito tazo ta kwashe waken data surfa daga turmi taje gaban pampo tazo ta wanke da su attarugu da albasa taje chan backyard ta tsaya tana kallon injin din da ake mishi tadawan generator.
She used the injin before dan su basakai nika waje but yanzu batasan tayaya zatayi ba, ijiye bowl na surfen waken tayi tazo gaban injin din ta tattaba, sannan takama handle na igiyan ijiyan zuciya tasauke sau uku na gathering strength kafin ta fuza da karfinta wani tangal tangal tayi zata fadi ta dafe bango injin din yayi kuka. “Tututututututuuuuuuu” ya mutu bai kunnu ba, sake zuwa Hadiza tayi tasake fizgan igiyan wanan karan saida ta fadi duwawunta ya bugi kasa tace “wayyooo Allah na” lekowa wajen Mama tayi ganinta akasa tsaki taja kafin taje tajima kanta ciwo bari ta tayata tada injin din just for today, ja daya Mama tayi injin din yatashi takalli Hadiza tace “tashi ki wanke injin din kiyi nikan” da kyar Hadiza ta tashi Mama tawuce kitchen din dan ganin haukan datake, ganin ta hura wutan harma ruwan na shirin tafasa yasa tai murmushi tawuce takoma daki.
Da kyar tayi nikan ta kashe injin din takoma cikin gida, tana zuwa ruwan ya tafasa ta dama kamu tadaura mai awuta ta debi kullin kosai tana bugawa sai zufa take tasa gishiri da magi guda da albasa data yayyanka albasan shima saida yasata kuka sabida yaji, wlh zaku iya mata kuka kuka ganta a kitchen din nan, hannunta duk bakin gawayi harda fuska nan, tasoya kosen ta kwashe akula tafito daidai Baba da Baffa Amadu na shigowa har ranshi Baba yaji dadin yanda she manage tai girkin dan bai zacima zata iyaba that means yanada hope zata gyaru duk fitowa sukayi zasuyi kari zata tashi takoma kitchen Baba yace “ina zaki”? Ahankali tace “zanje nasa alalen a wuta ne” wuri ya nuna mata yace “zauna kiyi karin kumalo kema” zama tayi duk sukai kari ba laifi kosan yayi dadi wlh sosai, tafa iya girki dama kawai iskanci ne ke hanata yi, tass aka cinye ta kwashe komi tafito dashi takai pampo taje kitchen ta dauki buhun gwangwani tabude takai makawarara ta wanko tazo tahada tasa alalen ta zuzzuba a gwangwani ta jera a pot tasa a wuta sannan takoma tai wanke wanke tashiga share tsakar gidan tana gamawa tashigo falon su ta gyara har zuwa dakinta sai nishi take kaman mai asma, komawa kitchen tayi alalen ya nuna tadaura ruwan zafi dazatai wanka dan babu water heather agidan nan, ruwan na tafasa tajuye a bucket ta sirka ta tafi bayinta tadade aciki dan gashi tama jikinta lafiyayye tagaji, tafito tayi shafe shafenta tayi face routine nata ganin har tasoma samin wrinkles from this work datayi tasa kaya ta kwanta agado tana nishi barci kawai takeso tayi, harta runtse idanunta zatai bacci Mama ta kwala mata kira dasauri tabude idanunta daidai Mama na daga labulen dakin ta kalleta hannunta rikeda kayan wanki ta zudda akasa tace “kin wanke bayinka gidan”? Girgiza matakai Hadiza tayi Mama tace “ga kayan nan ki hada da naki da kika cire jiya dan ba’a tara wanki agidan nan kije ki wanke kiyi amfani da ruwan kumfan ki wanke bayukan gidan” duk yanda Hadiza taso tadaure saita kasa danta gaji ainun, fashewa tayyi da kuka tace “Mama harda ke baki sona ko yanzu? Mama kasheni zakuyi da aiki? Wlh bayana ciwo, hannuna har bororo yayi sabida surfen danayi kalli” tanunama Mama hannunta dahar yayi ja yayi bororo tace “Mama nagaji, Mama wlh nagaji” dudda ta bala’in bawa Mama tausayi amman ta daure tace “Dan girkin dakikayi na bakinmu kadai bawai girkin tukunya lamba goma ba, da dan sharan tsakar gida da wanke wanke da gyaran falon nan dakikayi shine kika gaji? Bayanki na ciwo? Surfen wake gwangwani takwas bama tiya daya ba shine hannunki har yayi bororo? Lallai Hadiza kin sami duniya, kinsan akwai matan da kullum aduniya sai sun surfa kayan hantsi buhu buhu sabida su sami abin ciyar da bakinsu abinci? Kinsan matan dake zuwa aikatun suna share big big organizations din nan irinsu bank da hospital sannan su wanke bayukan suyi komi sabida su sami kudin ciyarda kansu da iyalansu? Hadiza kinsan menene rayuwa kuwa? Sabida kin dandana dadi? Hadiza kinsan the amount of work people are doing in this life just to survive? Kinsan akwai wayanda yasan kashin damukeyi ne aikinsu? Kinsan akwai wayanda gyaran kwatane aikinsu? Kinsan akwai yan aikin kwadago? Kika har sunyi doro tsabagen aiki? You are complaining sabida kin share falo, kin dafa abinci? To ba ciwo baya ba, ke bayan ya karye ma kinji, tashi ki karasa aikin ki, jeki wanka bayikan gidan nan ki hada kayan nan ki wanke su tass you lazy girl, u might be 33 but mu muka haifeki you must work this work, da kinsan bakison aikin dabaki kaso auren ki kin dawo mana gida ba, da baku nan aini ke komi dakaina da tsufana banda yar aiki, yanzu ko kin kaso aure kin dawo gida ai Alhamdulillah nima nahuta, you don’t expect me to be entering kitchen gaki agida, kezaki komi Hadiza yanzu kika fara, bayan ya tsinke ma inyaga dama you will get use to it, tashi kona kira Babanki wlh ai yana wajennan” tashi Hadiza tayi kawai tafashe da kuka tace “na shiga uku” Mama tace “tukunna saikin yabawa aya zakinta Hadiza don’t think punishment ne wannan this is normal aikin gidan Babanki which You MUST DO” cikin kuka sosai Hadiza tace “Mama to nayi order washing machine da generator? Na yarda zan dinga wankin a washing machine, koba wuta saimu tada gen, Mama ni gas dinma zan iya sayo wani daban tunda bakuso ina girki da naku, please Mama dan Allah Mama basai Baba yasani ba kurufamin asiri Mama ki yarda wlh zanyi order yanzu nabiya kudi akawo” wani kallo Mama tamata ganin har yanzu da sauranta Mama tace “Hadiza dagani har Babanki are not interested in your money, kudinki is useless agidan nan, abinda Allah ya hore ma Babanki yasaya dashi zamuyi amfani, shikuma zamuci dan haka ko amarfi don’t even dream of zaki sayo wani abu ki kawo cikin gidan nan, karki bari nadawo nasameki zaune adakin nan”.
Kuna ganin idan Baba da Mama suka gyara mana Khadijatul Kubrah bazatama Ummi fincikau ba kuwa🤣
Tundaga Alifun Ba’un fa aka fara mata.
Akwai wani magana da manya keyi na cewa no matter inda kasami kanka arayuwa always remember where you are from 💔