Furar Danko Book 2 Page 56
‘…..!!
5️⃣6️⃣
…….Kwana uku ya ɗan fara hucewa a dalilin murar zazzaɓi da Lulu ke fama da shi. Duk da dai tana nuna ita ƙalau take. Sai da murar tai mata tsanani ne ta haƙura takai zaune. Mata da miji sai ALLAH sai gashi yana tattalinta da matsa mata tasha magani. Harda haɗa mata shayin kayan ƙamshi da kansa. Idan yaga AA zai takura mata ya ɗaukesa ya kaima Iya Tabawa. Ya bata kulawa sosai harta samu sauƙi. Da ga haka aka shirya kamar basu ba aka koma nunama juna soyayya da tattali. Sai aikinsu da suka saka a gaba. Ita aunty Bilkisu ma sai abin ya koma bata dariya. Shiyyasa dai akace duk wanda ya shiga tsakanin mata da miji ya matse. Dan zasu shirya ne su barsa a ciki. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa mura na damun Lulu akai-akai. Ita abin har mamaki yake bata dan bata cika yawan mura ba a da. Sai dai ta danganta yanayin da sanyi da ake yi sosai harda dusar ƙanƙara.
Wasan su Smart na tafiya cike da nasarori da kalubale. Yayinda sunansa keta ƙara cigaba da amsa kuwa saboda yanda yake zura ƙwallaye a raga babu ko ɗar. In dai za’a kirayi sunan wani yaro mai tashe a wannan ƙarnin a harkar ball idan sunansa baizo na ɗaya ba dolene yazo ana biyu. Ballema ALLAH ya bashi farin jinin da akan ambacesan a farko. Sam baya wasa da addininsa. Sannan tsaye yake akan Lulu itama dan har yanzu shine mai ɗora mata karatu datai matuƙar maida hankalinta a kai. Wani lokacin kuma aunty Bilkisu ke ɗora matan.. A gefe kuwa sun matuƙar saka rayuwar Alh. Sulaiman a gaba, dan a yanzu haka ana tsaka da dambarwa ne tsakaninsa da amaryarsa akan Flash. Anyi-anyi ta bada taƙi. Yayi haukan yayi hargagin yayi kurarin duk da tana a gidan nasu tayi kememe. Hajiya Turai dai ce ƴaƴanta suka dawo da ita. Acewarsu sai da Mahaifin nasu ya bar mata gidan badai ita ta bar masa ba. Dan babu kunya suka dinga yaɓa masa magana musamman ma Tajuddeen, Alh. Sulaiman ranar harda hawayen baƙin ciki. Bai taɓa tunanin soyayyar da yakema Tajuddeen zai iya kallon tsabar idonsa ya masa rashin kunya haka ba, al’amarin ya girgiza zuciyarsa kam..
(Abinda kayi dole ai maka ai dama).
*_NIGERIA_*
Watanni kusan huɗu kenan abubuwa na’a rincaɓe musamman a ɓangaren Alh. Sulaiman Garko. Dan anata musu tsinci ɗai-ɗai na masifa ta yanda gaba ɗaya kasuwar tasu ma ta tsaya cak. Ga manyan kayansu da ke gaf da zuwa Najeriya ɗin. Duk yay wani iri da shi duk da har yanzu ma shi bako a fara taɓashi ba. Dan ko’a cikin yaransa kaf babu wanda aka taɓa. Sai aminansa da Hon. Nakowa kawai ya rage sauran duk suna hannun hukuma anyi ram da su. Kullum cikin kiran Daddy yake yana masa barazana. Shiko Daddy na maida shi mahaukaci da naɗe komai a waya tare da kunnashi. A gefe ɗaya ga al’amarin amaryarsa da yaƙi ci yaƙi cinyewa. Burinsa kawai ya amshi Flash ɗin hannunta koda zai kasheta ne shi babu ruwansa. Tayi-tayi ya saketa kuma yaƙi. A randa yaje har gida ya cima mahaifinta mutunci ta tabbatar masa anzo gaɓar da take jira, dan haka a ranar ta aike ma su Baba Garko da video. Da kanta ta shirya taje har gidan ta danƙama Baba Flash. Har wulaƙanci Dada taimata saboda taje ta gaida amarya da duba yaranta. Ita dai bata tanka mata ba har Dadan tayi ta gama san ranta. Bayan wucewarta ne Dada ta nufi wajen Baba Garko. Ta sameshi da ƴan biyunsa da sukai kuɓul-kuɓul gwanin sha’awa. Takaici kamar zai tsayar mata da numfashi amma ta danne da ƙyar. Dama bata taɓa ɗaukar yaran ba tunda aka haifesa, dan haka yanzun ma kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta. Ko’a ƙwallar rigar Baba Garko, dan ya jima da fahimtar bakin ciki take da yaran. Sama-sama ya amsa mata gaisuwa ya cigaba dama yaransa wasa kamar ma ya manta da ita. Hakan ya sake Zafafa mata zuciya taji ta tsani yaran fiye da ko yaushe. A cikin tunzura ta ce, “Amma dai Alhaji bai kamata ka fifita rayuwar ƴar wasu akan naka ba. Yanzu yarinyar nan ta gama fetse mana yaro da iskance-iskanceta ta dawo tana mana barikanci. Ni na rasa mi Sulaiman yayi maka haka da zafi ne. Kabi ka tsangwamesa babu laifin tsaye babu na zaune. Idan ma maganar Mawaddat da Tajuddeen ce ya kamata ace ta wuce tunda dai tana gidan mijin da kuke son ganin nata da shi yanzu ai ko”.
Idan ɗakin ya tanka Baba Garko ya motsa, hakan ya sake harzuƙa Dada. Miƙewa tayi a fusace zuwa gabansa ta ɗauke Flash ɗin dake ajiye kusa da shi. Nan ɗin ma bai tanka mata ba harta fice, bai kuma nuna damuwa da ya bita akan flash ɗin ba ya cigaba da yima yaransa wasa. Hajiya Dada kam da masifa ta nufi sashenta. Harta ɗauki waya da nufin kiran Alh. Sulaiman akan yazo ya amsa sai kuma ta ajiye tana faɗin, “Bara dai naga wai ubanmi akema wannan tashin hankalin ne a ciki.” Ta ƙwalama mai aikinta kira. Jiki na rawa ta iso, a gabanta ta zube cike da girmamawa. Umarnin ɗauka mata tab.. a ɗaki ta bata. Babu jimawa ta dawo ɗauke da tab.. ɗin. Ita ta saka mata flash ɗin. Cike da gadara da ƙasaitar mulkin masu akwai Dada ta amsa ana wani gyara zama da busa iska tace mai aikin ta kawo mata lemo. Ita dai mai aiki umarni take bi.
Fuskar data fara bayyana ta saka ƙirjin Dada bugawa, jikinta ya fara tsumar kewa. Mawaddat ɗinta ce, yarinya mai hankali, mai sonta da ƙaunarta, sai dai ita kullum tana a cikin hantararta ne saboda tana ce mata kaza ba daidai bane kaza ne daidai. Kalaman Mawaddat suka cigaba da jan hankalinta kafin kace mi ta jiƙe sharkaf da zufa. Maimakon hasken ɗakin ta koma ganin duhu. Tun tana iya jin sauti da motsi har komai ya tsaya mata cak sai razanannen ihunta daya karaɗe kunnuwan duk wanda ke a kusa da sashen nata. Rige-rigen shiga masu aikin nata suka shiga yi inda take, sun sameta wanwar a ƙasa kofin lemon da aka ajiye mata ya kife da alama ma a kansa ta faɗa. Duk da hankalinsu ya tashi da ganin a yanda take sai da suka ɗauki tab.. ɗin suka kalla abinda ya razanatan. Yayinda mai tausayin cikinsu ta fita a guje kiran Baba Garko. Ai suma sai suka ƙare da ƙwalla ƙara a dai-dai shigowar Baba Garko da amaryarsa, dan tana tare dashi sanda mai aiki taje kiransa….
An ɗauki Dada babu alamar rai a tattare da ita ga jini na zuwa ta inda gilashin kofi ya jimata ciwo. Shi kansa Baba Garko a kiɗime yake dan bata taɓa kasancewa a irin hakan ba duk wannan rikicin da akeyi. Iyaka dai ta suma da’an zuba mata ruwa ta farfaɗo. Amma yau babu abinda basu gwada mata ba ko motsi. Da tab.. ɗin ya fita a hannunsa, dan yasan koma mi ya sakata a wannan halin bazai kasance ƙaramin ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya isa kunnen ƴaƴanta da jikoki. Kafin wani lokaci asibitin da aka kaita ya cika da Garko family, zuri’ar Uncle Khamil dake Abuja ne kawai babu suma suna tafe sai na auta dake a Saudiyya. Har zuwa washe gari ba’a samu kan Dada ba, dan haka hankalin kowa ke’a tashe. Hatta shi uban gayyar a wannan karon hankalin nasa a tashe yake. Dan koba komai fa yana son matarsa, sannan itace uwar ƴaƴansa. Tun shekarun ƙuruciya suke tare har zuwa tsufa da daɗi babu daɗi tana zaune da shi. Washe gari zuwa sha ɗaya na safe auta ya iso tare da nasa iyalinsa, tamkar shi Dada ke jira ya iso ta farfaɗo, sai dai fa numfashin farko da taja ta fesar da jini ta fesoshi. Wani sabon tashin hankalin kenan, dan likitocin ma sun kasa musu bayani, sai kai-kawo da shigi da fici sukeyi. Duk wanda suka tunkara sai dai ya zame da faɗin yana zuwa. Duk wannan abun da akeyi babu Alh. Sulaiman sai ƴaƴansa da uwar gidan sa. Karan farko da Tajuddeen yaji baƙin cikin halin mahaifin nasa. Shin wai minene na wannan gabar, a ganinsa mahaifiya ai tafi gaban wasa. Dada na a irin wannan yanayin har yace yanada wata hujjar cigaba dayin gaba. Duk wanda yaga Dada a jiya zuwa yau dolene ya tausaya mata. Shi kansa Baba Garko ya ajiye makaman yaƙinsa harda hawaye yake da sambatun ta tashi dan ALLAH kada ta tafi ta barsa. Cikin ɓacin rai Tajuddeen ya dannama ubansa kira. A lokacin yana ɓoyayyen Companyn sa suna tattaunawa da yaransa malami da wasu abokan cinikayyarsa mazauna Legos akan kayansu da suka iso Nigeria a daren jiya. Sai dai sun rasa yanda zasu fidda kayan daga bakin ruwa saboda kamar fa an saka musu ido… Yana ɗaga wayar Tajuddeen ya fashe masa da kuka cikin masifa yake faɗa masa “Yanzu nan Dad har kanada lokacin nishaɗi haka mahaifiyarka kwance ranta a hannun ALLAH tana aman jini likitoci tun daren jiya tsaye a kanta. Anya kuwa kana fatan gamawa da duniya lafiya Dad. Ace iyayenka ne abokan gabarka. In dai dan ni kakeyi toka ajiye dan nikam dai na haƙura da Mawaddat koda ace sonta zai zamar min ajalina. Duk ƴan uwanka gasu nan har wanda basa ƙasar kai kaɗai ne ka fita zakka a cikinsu saboda son zuciya. Idan ta mutu sai kazo zaman gaisuwa ai” ya faɗa yana yanke kiran wani irin kuka mai cin rai na kufce masa…
*_★UK★_*
…..A dalilin wayar Tajuddeen da mahaifinsa su Lulu suka san halin da ake ciki. Domin suna tsaka da ganin zaman meeting ɗin Alh. Sulaiman da abokansa ta direct camara ɗin su. Hankalin Lulu ya tashi matuƙa, dan koma minene ya faru Dada ba abar yardawarta bace ba. Kuka ta fara cikin tashin hankali ta shiga neman layin ƴan uwa. Da kyar ta samu Uncle Amin ya ɗaga. Cikin kuka take faɗin yanzu nan Dada na’a irin wannan halin amma babu wanda ya faɗa mata. Lallashinta Uncle Amin ɗin ya farayi akan ta kwantar da hankalinta tai mata addu’a daga inda take. Amma ina Lulu taƙi saurarensa. Shima Smart ɗin ta matuƙar tayar masa da hankali, dole ya saya mata ticket dan bazai juri ganinta a haka ba. Sai dai ita kaɗai zata taho banda AA. Ta barsa wajen Iya Tabawa da aunty Bilkisu da har yanzu bata kammala ganin likita ba duk da tana a gida lokaci-lokaci dai take zuwa ana dubata asibitin……..✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
Zafafa
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*