Hausa NovelsInda Rai Hausa Novel

Inda rai 28-29

Sponsored Links

*INDA RAI…🥰🥰*

*BY*

*MARYAM ABDULLAHI*

🥰Oum Shaheed🥰

 

*Daga ƙungiyar, koda kuɗinka….*👇🏽

*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION🥳*

https://chat.whatsapp.com/FI2ovuaHMbz0GBDNr2JeZX

*Sadaukarwa ga mosoyan, INDA RAI, 💋💋*

 

Page. 28&29

 

Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya taji kunya, yau ne ake hidimar ɗaura auran Amrish da Imran, ɗaurin aure mai cike da al’ajabi, domin tunbayan da ango yaga Amrish matsayin mrs dream ɗinsa ya kasa sukuni, kuma alamu sun nuna masa cewar bata sanshi ba, duk wannan lokaci da ya ɗauka yana maƙale da ita a ransa wato shikaɗai yake haukar sonta,? Alhamdulillah, kalmar godiya ga Allah yake ta mimatawa.

A ɓangaran Daddy faɗa yake shikaɗai a zuciyarsa, “wato saboda baya son zaɓin nasa shiyasa yaƙi zuwa wajan ɗaurin auran,? ciro wayarsa ya yi ya sake gwada kira still a rufe take, ji ya yi ransa ya sake ɓaci, amma dole ya haɗiye ganin taron jama’ar dake gabansa.

Haka aka gama ɗaurin aure babu ango, ɗaurin auran da ya tara manyan mutane, cikinsu hadda babban baƙo mutanen ƴar siya.

Mimi ce tsaye a bakin ƙofar toilet ɗin tayi bugun duniya amma Amrish taƙi buɗewa, daga shigarta wanka kusan awa ɗaya da rabi amma shiru, “shikenan, bari na kira miki mahaifinki aishi zaki sauraresa, tunda ni dai ban kai ba, ta kare maganar muryarta narawa, wanda jin hakan da Amri tayi ya raunana mata zuciya, tashi tayi ta buɗe ƙofar tayi sharkaf, “subhanallahi,” yanzu haka kika yi wankan da kaya a jiki,? murya a sake kamar babu komi a ranta tace. “Mimi hakanan yau nakejin nayi wankan, bankwana nakeyi da toilet ɗina, ta ƙarisa maganar da tura ɗan ƙaramin bakinta gaba, murna da farinciki a take suka bayyana a fuskar Mimi, tace maza kiyi sauri kiyi wankan kinji, kinga aunty Khadija na jiranki, “wow, yaushe my bloody tazo,? ita zata shiryani zuwa ga ɗakin miji, lalleni mai sa’ace. Kiyi maza ki fito dai kafun ta tafi, kinsan batason wasa ta wannan fannin, “to Mimi, kice ta fara miki mana kafun na gama, ko yanzu an daina yiwa Abee na gaye, tana ƙarisa faɗa ta rufe ƙofar toilet ɗin tabar Mimi tsaye sake da baki.

 

Faɗa Daddy yake yiwa Imran kamar zai ari baki, shide haƙuri yake bayarwa kansa a duƙe, sai da ya yi ya gaji sannan ya wullo masa keys na gidan da sai jiya ya zaɓa, “ka tashi ka shirya kaida abokanka ƙarfe biyar zaku je ɗaukar amarya. “Allah ya kaimu Daddy, na gode.

Maa shaa Allah!! ita ce kalmar da mutene ke faɗa ya yin da suka yi arba da wannan zankaɗeɗiyar amaryar, sosai Aunty Khadija bloody ta sanja mata kamanni, tayi kyau har ta gaji, jan lalle akamata sai ratsin baƙi kaɗan, wani cotton lece fari mai ratsin ruwan gold ne ajikints, ɗinkin riga da skert ne zun zauna ajikinta gwanin sha’awa, ko motsi tayi sai ƙamshin turaren Alif lail ya cika gun, ƙarfe biyar daidai motocin ɗaukar amarya suka iso.

Abun mamaki Amrish ce ke lallashin iyayenta, a maimakon su, gaba ɗaya sun kasa ce mata uffan, ganin abun nasu bana ƙare bane yasa Aunty Khadija shigowa ta fice da amarya, suna fita Mimi ta faɗa jikin Abee ta fashe masa da kuku, mutuwar, Raheem ta dawo musu sabowa fil, sai fatan Allah ya masa rahma, ita kuma su zauna da mijinta lafiya.

Ƙarfe 9:00pm kowa ya watse anbar amarya ita kaɗai a gidanta, sai a wannan lokacin ta samu damar yin kuka, yi takeyi kamar wanda ranta zai fita, yanzu ita aka yiwa auran haɗi,? tana yadda taga ya yi randa ta fara ganinsa sai ta sake fashewa da kuka.

A wannan halin ango Imran ya shigo ya tadda amaryar tasa tun daga ƙofar perlou yake jin sheshsheƙarta, tuni jikinsa ya hau rawa, ganin yana son shiga yanayi a take ya kama kansa, ya koma Imran sak, shiga bedroom ɗin ya yi bakinsa ɗauke da sallama, tananinsa ta masa banza, yana tsaye a kanta yanajin kukunnata har cikin ransa, yace” malama kin cika mini kunne fa, nannan ma shiru bata tanka masa ba, duk yadda yaso ta daina kukan ko ta masa magana fir taƙi haka, Ya Allah, samun waje ya yi daf da’ita ya zauna, ya ajiye ledar hannunsa a kan table, ganin ya mata barazana taƙi kulasa sai ya sanja shawara, saka hannu ya yi ya ɗago fuskarta, maimakon yace wani abun kawai ya ƙura mata idanu, wai yau shine tare da ita matsayin miji da mata, lalle Allah buwayi ne gagara misali, yana zan can zuci yaji ta gartsamai cizo a hannu, uchhhh, ya janye hannun da sauri, ita kuma Amrish ganin yadda ya yi alama yaji zafi sai abun ya bata dariya, sosai takeyi ya sake baki da hanci yana kallonta, sai da gaji dan kanta sannan kuma ta ci gaba da kukunta, shi dariya ma ta bashi, yaɗan murmusa kaɗan, “to beby, a tashi a rage kaya ayi wanka kizo maza kici abinci, tunda dukammu bama son wannan haɗin saimu lallaɓa da juna a haka, ras taji a ƙirjinta jin wai za’a lallaɓa da’ita, tura baki tayi kafun ta miƙe ta nufi ledar daya ajje, buɗewa ta hauyi ɗaya bayan ɗaya, ledar wani gashashen kifi ta ɗauko sai gorar ruwa, zama tayi kusa dashi tace, “pls ya’ya ɗauko mini plate mana, yunwa nakeji, shiyasama nake ta kuka tun ɗazu, da farko mamaki ya yi da yaga amarya mara kunya, sai kuma hakan ya bashi nishaɗi, tashi ya yi ya ɗakko mata da kansa ya juye mata ya miƙa mata, maimakon ta karɓa sai ta tura masa baki ta juyar da kanta gefe, “bazaki cibane? “bana saka hannu ƙarni, kai zaka bani a baki, haka yayana Raheem yake min, ta ƙarishe maganar cikin sanyi, gaba ɗaya ta gama rikitasa da wannan shagwabar ta’ta haka ya ciyar da ita sai da ta ƙoshi sannan ta ɗau ruwa tasha ta nufi toilet don watsa ruwa da wanke baki, tunda ya fara ciyar da ita shauƙi ke ɗawainiya dashi, da ta miƙe ya bita da narkakkun idanunsa da suka ƙanƙance.

Bayan ta gama wanka kawai ta fito a haka kamar yadda ta saba a gida, shaf ta manta da wani ango a ɗaki.

 

 

Assalamu alaikum

Dear family and friends

We come with our story a very nice one Ih-Shah Allah

It’s a Love story
Emotional heart touching love
True love

No matter what has happened. No matter what you’ve done, No matter what you will do True love doesn’t die

yeah yeah
Don’t let it go away forever

Don’t let it go to waste
Forever

With MARYAM ABDULLAHI🥰💞

Oum shaheed

Kar ku manta da sunan book ɗin shine ƘALB
Daga jin sunan kun san babu ƙarya.

https://chat.whatsapp.com/FI2ovuaHMbz0GBDNr2JeZX

Not editing

Leave a Reply

Back to top button