fasaha

Muhimmiyar Sanarwa Ga Masu Amfani Da Account Na Opay Saboda Gudun Matsala 2023.

Sponsored Links


MASU OPAY ACCOUNT KU LURA SOSAI SABAWAR DAMFARA DA HARKERS SUKRYI


Dazu da safiya ina cikin danna waya, kwatsam sai naga kira ya shigomin da wata bakuwar lamba, banyi kasa a guiwa ba na daga tare da Sauraron wane zaiyi magana. 

Namiji ne ke magana cikin harshen Turanci ya shaidamin cewa shi ma’aikaci ne daga Bankin Opay sunaso suyi Verifying account dina dan haka za’a turomin wasu lambobi in fada masa su, na tsaya ina sauraronsa, yacigaba da cewa, karna kashe wayar in duba gurin message dina, nan take naga an turomin OTP.

Menene OTP?

Wasu lambobi dake iya bude dukkan wani abu dakasa lambobin sirri (password) na lokaci guda (One Time Password) dazarar ka manta za’a turoma zakayi amfani dasu a matsayin password, kuma ana turosu ne a layinda kayi register na account dinka kokuma wani abu daban, domin tabbatar da cewa tabbas kaine mai layin.


Bayan an turomin da lambobin kai tsaye na fahimci cewa dan Damfara ne, ya umarceni da in karantomasa Lambobin saina karantamasa wasu daban sabanin wanda aka turomin, nanfa yace dani badaidai bane, zasu kara turamin wasu, cikin kankanin lokaci aka kara turomin, nakara karanta masa ba daidaiba. 

Daga nan ne ya fahimci cewa nagane cewa dan damfara ne, ya zageni tare da kashe wayarsa.

Karin haske:-

*Wannan Abin zai iya faruwa da kowanne account ba dole sai Opay ba.

*Dazarar ka basu wadannan lambobin to kaitsaye zasu shiga account dinka kuma zasu yashema dukkan abinda keciki

*Babu wani banki da suke kiran mutum suce ya turamusu wasu lambobi koda kuwa ma’aikatanne suka kira ka.

Muyi kokari mu wayarwa da makusantanmu kai musamman awannan lokacin da amfani da banki yaxama kusan dole ga kowa da kowa, zasuyi amfani da wannan daman domin damfarar mutane.

Idan kun samu dama kuyi sharing ga ‘yan uwanku, kokuma kuyimusu bayani da baki yadda zasu fahimceku.


Allah ya kiyaye

Copied!✍️

Leave a Reply

Back to top button